Author : Nimcyluv Category : Complete Novels
iya'' murmushi yayi yace ''good, ki tabbatar kin yi aikin daidai da daidai if anything goes wrong akayi suspecting ɗin mu sai na ɓatar dake, kin gane?" Jinjina kanta Na'ema tayi sannan tace '' but i will need Time'' jawota yayi ya rungume yana faɗin '' take your time '' daga nan kuma labari ya canja salo, her moans filled every where in the toilet, Samha da fito War ta kenan daga ɗayan toilet ɗin tayi tsaki tace '' Allah wadai, wai mutum ya zo karatu amma...'' girgiza kanta tayi without completing her words
Cire hijabin ta Samha tayi tana wanke fuskar ta, her hair flared up behind her, bayan yan mintina sai ga Na'ema ta fito bayan ta fara gyara kanta, she was surprised da taga Samha a wurin at the same time wani tsoro ya shige ta idan fa Samha ta ji komai ko ta san komai? Ganin kamar Samha bata ganta ba yasa tayi saurin fita daga bayen,bayan ta kawai Samha ta gani
Andrew shima tun da ya fito ya ga Samha ya kasa tafiya, her hair , her shape and most importantly the way she carries her self yake ƙara tun zura sa akan wanting to sleep with her, she is different and so she will taste different he was sure.
Ƙarasowa yayi batare da ta sani ba ya saƙalo hannun sa holding her waist,'' hey beauty your shape really tur....'' bai ƙarasa maganar ba saka makon wani irin wawan naushi da ta kaima sa in his chin, yayi taga taga zai faɗi but he steadied him self yana riƙe haɓar sa mamaki a fuskar sa, Samha ta juyo a fusace tace '' Anduro ne sunan ka ko android,stay away from me '' ta ƙarashe maganar cike da gargaɗi sannan ta sa hijabin ta leaving him standing in the toilet as she exited
Tafiya take tana huci, Allah gayen nan ya raina ta amma zata koya masa hankali...
Emmanuel ne ya matse Ra'esah da jikin sa yana ƙoƙarin haɗa bakin su while his hands roam on her body,sai kuka Ra'esah take tana ture sa, amma yafi ta ƙarfi she felt helpless and humiliated
Cire hular dake kanta yayi,her shoulder length hair came into view.
Sai ihu Ra'esah take amma kasancewar wurin yayi nisa da inda mutane suke, no body heard her. Emmanuel yayi dariyar mugun ta yace '' scream all you want,Babu wanda zai jiki balle ya taimake ki,not even your so called heroe friend.'' idanun Ra'esah sunyi ja, ga wani ɗaci da baƙin ciki da take ji daga ƙahon zuciyar ta,No body had ever touched her the way he did,
Sai kokuwa suke, he felt dole ne ma ya cimma burin sa, har ya kusa zame mata skirt from no where yaji ance '' Troubling the lady?" Suka juyo it was.....
Chapter twenty three: they were in danger
Wani irin sanyi Ra'esah taji a ranta ganin Fateemah,and she felt weak,irin raunin da za kaji when you're being mistreated suddenly sai kaga wani wanda kake jin zai iya tsaya maka, that's how she felt
Emmanuel ya dakata daga abinda yake ƙoƙarin yi, ya juyo... Kafin ya idasa juyowa Fateemah ta rugo da wani matsanancin fushi da tsana ta fara shaula ma Emmanuel bulalar dake riƙe a hannunta,idanun ta sunyi wani irin burki cewa at the moment kamar wata mai aljanu
Wani irin ihu Emmanuel ya saki completely letting go of Ra'esah yana soshe soshe Dan gaskiya bulalar ta ratsa shi saboda sports ɗin dake jikin sa sun bi jikin nasa Saboda zufar da yayi while struggling with Ra'esah
Fateemah furiously tabisa ta cigaba da dukan sa, tana zagin sa '' who asked you to touch her huh? Dan ubanka waye ubanka? Do You think we are weak huh? Kuma zaku iya yin yanda kuka ga dama?..." On and on she went tana cigaba da dukan Emmanuel cikin fitar hayyaci, she hated that he touched Ra'esah ta tsane sa,why would he touch her innocent friend?
Ra'esah ta zube inda Emmanuel ya barta tana cigaba da risgar kuka kamar ranta zai fita, tana kallon yanda Fateemah ke cin uban Emmanuel, wani irin ƙaunar Fateemah na ƙara shiga ranta bata San inda Fateemah ta samo wannan courage ɗin har haka ba,inda itace? She would never be able to,she has always been the weak one. Da ba dan Allah yasa Fateemah ta zo ba, would he have managed to achieve his aim saboda ita ta kasance mai rauni?
Emmanuel sai ihu yake ya kasa komai yanayin Fateemah ya tsorata shi sosai,aside from that bulalar ƙara ratsa sa take from every angle non stop.
Kamar walƙiya, Chibuke yayo kan Fateemah ya wanka mata mari tare da wurgar da ita, bata kasance ko ina ba sai kusa da Ra'esah, tana faman huci
Sauran members ɗin dark flames sukayi kan Emmanuel asking if he was okay sai sabbatu yake shi bazai bar Fateemah ba,ganin yanda Fateemah ta ɓata masa jiki da tabon bulala yasa zuciyoyin su ƙuna
Mathew ya cire belt ɗin sa ya nufo kansu Fateemah,miƙewa sukayi Fateemah na zaro ido tana ƙara tura Ra'esah bayan ta protectively, yanda Ra'esah take ji game da fateemah at the moment? Wani irin so da ƙaunar Fateemah take, shima Andrew da Emmanuel da chibuke suka zaro nasu belt ɗin suka yo kansu,
Hankalin Ra'esah yayi ƙololuwar tashi,ita ko Fateemah tun lokacin da taga Emmanuel da Ra'esah taji ta tsane su,she never hated them before but now? Dan haka duk da tsoron sun data keji,duk da sun fisu yawa she will protect Eysah, bakin rai bakin fama, there's a 🔥 flame of hatred burning in her eyes
The guys begun closing in on them circling them kowa da mugun kallon da yake musu,kamar zasu jibgi wasu ƙarti, amma ganin yanda Fateemah ke kallon su wani irin shakkar su,ya shige su,at the moment Fateemah looked like she was possessed, idanun ta sunyi ja, gashin ta scattered
Ra'esah kuma tuni hawayen ta sun bushe, she decided Bata so taji tsoro kuma,bata so ta zama mai rauni
Andrew yace '' wato dan kunga wannan yarinyar tana tare da ku thats what gave you the courage to beat anyone of us right?"
Emmanuel yace'' yau idan ban yi ƙasa ƙasa da yarinya na keta mata rigar mutunci ba Allah ya tsine''
Ra'esah da wani irin courage tace '' toh AI dama tuni kai tsinanne ne sai dai tsinuwar ta daɗu'' ta ƙarashe maganar eyes burning with fire
Mathew'' yace yau dai daga mu sai ku, not even that girl can save you''
'' you have no saviour and we will show no mercy '' inji chibuke yana ƙara naɗar belt ɗin a hannun sa
Fateemah tace '' Mu'ai da Allah muka dogara,ku baku isa kuyi mana abinda Allah bai mana ba''
Emmanuel yayi smirk,idon sa yayi wani sunkuce ce saboda bulolin da ya sha,yace '' kai haba dai! Da gaske?''
Itama Fateemah smirk tayi tace '' Abu a zahiri ''
'' yau dai sai dai Uwar ku ta haifi wasu amma ba ku ba!!"
Fateemah tace '' I'd love to see you try'' with a big grin
Tana faɗar hakan dark flames begun attacking,cikin su,su Fateemah suka yi suna gantsara masu cizo,naushi da kuma ya kushi every where
Suku ma dark flames suna faman dukan su da belt, they endured it Dan da gaske Fateemah take da tace bakin rai bakin fama
Faɗa suke ba ƙaƙƙauta wa, dark flames duk da yawan su,sun jibgu suma dai su Fateemah sun daku iya kar dakuwa amma akwai taurin rai, they won't give in
Suddenly Andrew ya kai ma Ra'esah wani irin wawan punch on her lower abdomen, ƙara Ra'esah ta saki tare da zubewa ƙasa
''RA'ESAH!!!!!'' Fateemah ta faɗa tare da fisge kanta zuwa wurin da Ra'esah ta zube, Ra'esah could barely breath,
Emmanuel yazo yayi halbi da fateemah daga kan Ra'esah,mulmula tayi kanta na buguwa da wata bishiya a wurin, wani irin jiri take ji, idanun ta na rufe suna buɗe wa a ɗishi ɗishi ta hango dark flames zagaye da Ra'esah
Emmanuel na Faman yin ƙasa da wandon sa, while Chibuke ya duƙa bringing down skirt ɗin Ra'esah that was clutching tightly onto her skirt tana kuka....
Miƙewa Fateemah tayi regardless of how weightless she felt tayi kansu da gudu, ture Chibuke tayi dake ƙoƙarin cire ma Ra'esah skirt su ka mulmula towards another side Chibuke a sama
Wani ihun shaƙiyanci yayi yana faɗin '' who's at the top now hah?" Yayi maganar yana ƙoƙarin sa bakin sa cikin nata,turesa ta fara yi,shi kuma ya ƙara riƙe ta jikin sa, ita ma dai,she felt gross and disgusted by his touches.... idanun ta sunyi ja, amma baza tayi kuka ba
Sauran suna wani kallon su,suna shewa tare da faɗin saura Samha Emmanuel da ya kusa cire wandon sa yace '' where is ur heroe friend,I don't see her any where" Ya ƙarashe maganar yana leƙa side by side cike da iskanci sannan ya juyo yana kallon sauran dark flames ɗin yace ''Or Do you?"cike da murna suka ce 'No' suna kwashe wa da dariya, it will be fun to take this girls
Ra'esah da fateemah har sun sadakar sai yanda ta Allah ta kasance when suddenly
'' Are You sure you looked properly? or maybe your eyes deceived you" swiftly suka juyo inda Muryar, they were shocked to see Samha,idanun ta sunyi ja kamar gauta zuciyar ta na mata wani irin ciwo, ji take kamar ko mai zata yi ma waɗannan tsinannun bata biya ba
Ra'esah da fateemah wani irin relief ne ya wanke su...
Ɗaga Ra'esah da fateemah suka yi, with a smug expression
Chibuke yace '' well, well,well look who is here?''
Andrew yace '' it's MS feisty''
'' ki dai kin iya ɓata show ko?" Inji Emmanuel yana gyara wandon sa,
Andrew ya ƙara faɗin '' a'a ai taxo akan lokaci,yanzu ba sai a haɗa da ita ba? To make it complete!"
Dukan su sukayi wani ihu suna faɗin '' PERFECT" Samha kallon su take before her eyes slowly fell on Fateemah da ta rarrafo tayo kan Ra'esah da take nan kwance wani irin ciwo marar ta ke mata, Zuciyar Samha ta karye,with a breaking voice tace '' me ya faru?"
Kafin Fateemah ta bata amsa
Andrew yace '' I did! Na naushe tane a wurin and she was breathless for a moment na ɗauka mutu.....'' kafin ya ƙarasa Samha tayi wani tsalle ta cafko wuyan sa ta shaƙesa kamar idon sa zasu zubo,
The others were stunned,sakin wuyan sa tayi ta fara kai masa consecutive punches a fuska, a ciki before she focused on his lower abdomen inda ya kai ma Ra'esah naushi ta fara naushin wurin itama, fuskar Andrew tayi ja ba abinda yake faɗi sai 'shit' da zage zage,
Fateemah ta tallabo kan Ra'esah ta jingina a kafaɗar ta sannan ta matsa da su zuwa wani bishiya suka zauna watching as Samha delt with Andrew
Sakin sa tayi ta dawo kan Emmanuel,sauran kuma sukayi ƙoƙarin shigar masa haɗasu Samha tayi ta na ta jibga, all those taekwondo and karate moves da ta koya a shekarun baya bata taɓa gwadawa akan kowa ba,sai gata yau she was demonstrating them on dark flames with everything she got. At the moment kamar wata mahaukaciya, bugun su take tana faɗin '' why did you,why did '' abinda take faɗi ke nan, her hair was scattered idanun ta sunyi ja.... Su Andrew sai ihu suke their faces red, gashi duk tayi musu jina jina, ta miƙe tsaye ta fara kicking ɗin private parts ɗinsu, sai kururuwa suke, tun mutane basu fargar ba,har suka farga suka zo wurin anata kallo as usual Babu wanda yayi attempting ɗin rabawa, Amma mutane sun sha mamakin ganin yarinya ɗaya tal akan zaratan maza guda huɗu beating them mercilessly,tun kafin suga fuskar ta kowa sai faɗin Samha yake,they were sure she was the only person who could do that
Wurin ya cika da hayaniya,mr kanya da Wasu daga cikin malamai suka iso wurin, suka ƙarasa ciki suna ƙoƙarin rabawa amma ina, Samha bataji ba,ba ta gani ba!
Mr kanya ma da ƙyar ya samu ya fisgo Samha ya riƙe ta amma sai ƙoƙarin ƙwacewa take, hawaye na gangarawa daga idanun ta take faɗin '' ku barni inci ubansu, la'anannu,how dare they? Waya basu permission ɗin taɓa su? WHO told them they will get away with that?" Sai surutu Samha take kamar wata zautacciya, Fateemah ta riƙo Ra'esah da ke tafiya da ƙyar suka ƙaraso wurin su Samha, Samha sai bala'i take akan mai za'a taɓa mata yan uwa? Suko su Fateemah ganin yanda take ta faɗa akan abinda aka yi musu, their love and respect for her grew, Samha tayi buɗu buɗu duk ta fita hayyacin ta, gashin ta ya rufe fuskar ta jan idon ta kawai ake gani, mr kanya tsigar jikin sa sai tashi take, mutane bakin su ya kasa shiru
Can na hango Na'ema cikin mutane fuskar ta ɗauke da murmushin ganin yanayin su Samha and she felt bad for dark flames.
'' Samha'' Ra'esah ta kira ta weakly,da sauri Samha ta kai duban ta wurin su,fisge hannun ta tayi ta matsa inda suke engulfing them in a hug, hawaye na zuba daga idanuwan su su uku, '' I'm sorry '' she whispered
'' ba laifin ki bane'' Fateemah ta faɗa tana ƙara rungume su
Rabuwa sukayi, Ra'esah da fateemah suna share ma Samha gashin ta zuwa baya,she looked scary
'' Are You guys alright?" Ta tambaya tana binsu da kallo as if trying to figure out idan wani abu na damun su, girgiza kansu sukayi ta ƙara rungume su
Mutanen da ke wurin gulma na caccakar ransu, so suke su san abin da ya faru yet No chance, dark flames ko jikin su yayi musu tsami ana su hasashen dakyar idan zasu iya tafiya ma.
Principal ya juyo ya kalli students ɗin sannan ya kalli malaman,da sauri suka fara korar dalibai, wasu kuma suka fara cicciɓar dark flames to the clinic.
Su Samha suka juya su uku zuwa hostel ɗin su riƙe da Ra'esah,da tace bazata tafi clinic ba, duk inda suka wulga sai an kalle su har suka iso suka tura ƙofar suka shiga iska na rufo musu ƙofar.
Saman gado suka aje Ra'esah Samha ta shiga bayi ta haɗa mata ruwan wanka, ta fito suka raka ta zuwa bayin....
Bayan wani lokaci Ra'esah ta fito sanye da wata doguwar riga mara nauyi tana tafiya a hankali,magani Fateemah ta bata sannan ta kwantar da ita a duvet ɗin da suka shimfiɗa tsakiyar ɗakin
Samha ma tayi wanka ta fito sanye da riga da wando palazo Fateemah ta shiga, bayan duk sungama suka kwanta, tsakiyar ɗakin with Ra'esah in the middle Fateemah da Samha on each side
Sannan suka rufa da wani blanket ɗin,they drifted to sleep
Na'ema CE ta turo ƙofar ta shigo, tsaya wa tayi tana kallon su cike da tsana,she doesn't just hate Samha she hates the others too,she wish a calamity could befall them
Tsaki taja sannan ta haye saman gadon ta tana tunanin yanda zata aiwatar da aikin Andrew.
Wuraren ƙarfe biyar bayan sun yi Sallah sun ci abinci,suka ji an ƙwanƙwasa ƙofa, Na'ema ta miƙe taje ta buɗe ƙofar, wata yarinya yace tsaye bakin ƙofar saye da Over sized hoodie,tana da green eyes and a pale comolexion, gashin ta baƙi with bangs '' Hi'' yarinyar ta faɗa, tana sakin wani mummunan murmushi
Haɗe fuska Na'ema tayi tace '' Yes? Who are you looking for?" Yarinyar bata amsa Na'ema ba sai bangaje ta da tayi ta shige ɗakin
Na'ema was furious taxo ta dinga balbalin bala'i, su dai su Samha sun zubama yarinyar da ta shigo ido,she looked some how familiar,
Na'ema ganin ba wanda ya tanka mata yasa ta zo tace '' kun santa ne?" Girgiza kansu sukayi suna ci-gaba da kallon yarinyar still, itama su take kallo
Na'ema a fusace ta ja Gashin yarinyar sai ga gashi a ƙasa. Waro ido sukayi su dukan su, Na'ema ta ci-gaba da cire kayan dake jikin yarinyar ɗaya Bayan ɗaya,they were shocked,it was.....
WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
_*𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17
𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑓𝑜𝑢𝑟: 𝑆𝑎𝑣𝑒 ℎ𝑒𝑟
Waro ido Sukayi dukan su bayan Na'ema ta gama cire kayan dake jikin yarinyar,Damn! It wasn't a girl,it was *ADRIAN*
Murmushi yayi yace '' hi girls'' ganin yanda suka wani tsare sa da ido, baki buɗe,wani irin haushi ne ya ƙume Na'ema,taja tsaki tare da koma wa ta kwanta saman gadon ta
Adrian Kuma ya isa kusa dasu, kwashe wa suka yi da dariya Fateemah tace '' Hello Adrian or Adriana, '' suka ƙara ƙyalƙyace wa da dariya, Adrian joined them too
Bayan sun dena dariyar ne ya kalle su,su duka ya ce '' hope you are all okay? I took a very big risk to check up on you '' ya faɗa yana fara basu labarin abubuwan da suka faru kafin ya iso,his wig almost falling in front of the matron,yaci tuntuɓe skirt ɗin sa ya kware ana ta masa dariya,bra ɗin daya sa almost fell off, on and on he went
Su Ra'esah nata dariya,he was happy to see them laughing yaji daɗi da basu kasance cikin baƙin cikin abinda ya faru ba.
Na'ema sai tsaki take ja, 'haushi wan kill her' Adrian ya zauna dasu for a long time kafin ya miƙe ya ƙara shirya wa in his disguise ya fita
Fateemah tace '' Na'ema,ba zaki mana sannu ba?"
Tace '' me ya sameku da zan yi muku sannu? And idan nayi muku sannu,will it change anything?" Ta faɗa a zafafe
They were all stunned,akan me Na'ema za tayi reacting the way she did? Kamar dama can she has personal grudges against them
Samha ta taɓe baki bata ce komai ba, wayar ta, ta jawo ta kira Salmah su kayi video call, Samha tayi introducing ɗin Ra'esah da fateemah, they chat for a while yanda suke magana da juna kamar sun san juna they were free.
Bayan kiran ya ƙare sukayi Sallah suka tafi cafeteria,yau idanun mutane akan su yafi na koda yaushe, maganganun mutane na shiga kunnuwansu but they didn't care. They sat at their usual spot Amma basu yi ordering ɗin komai ba
Wasu yara su huɗu masu suna rising stars, suka fito saye da kaya irin na mawaƙa holding mics and guitar dama kuma daga lokaci zuwa lokaci