Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 69

69K to 72K   out of 206.1K words

aka banko ƙofa....






















WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17


Chapter twenty five: we are going home

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼? (𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17



𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑓𝑖𝑣𝑒:𝑊𝑒 𝑎𝑟𝑒 𝑔𝑜𝑖𝑛𝑔 ℎ𝑜𝑚𝑒



da sauri suka kai duban su wurin ƙofar banda Samha da har yanzu idanun ta suke rufe, zuciyar ta sai bugawa take da tsananin ƙarfi she felt so helpless,so desperate, har ta fara hasaso yanda rayuwar ta zai kasance idan wani abu ya faru da ita, suko dark flames sai kallon juna suke especially Andrew, da yake tsira ra,

Dr Ahmad ko kallon su yake ba ƙiftawa, idanun shi sunyi wani irin mugun ja ƙirjin shi sai sama yake yana ƙasa, ran shi yakai maƙura wurin ɓaci,ganin abinda ke faruwa ba ƙaramin sukar zuciyar shi hakan yayi ba, wani irin ciwo yake ji tunda ga ƙasan zuciyar shi musamman idan ya kalli Andrew da Samha dake kwance daga ita sai singlet wasu garadan maza dafe da ita

Sakin Samha sukayi tare da miƙewa, Andrew yana ƙoƙarin maida wandon shi Dr Ahmad kicked him on his private part da ƙarfin tsiya ihun Azaba Andrew ya saki tare da dafe wurin yana faɗin '' Shit man, what's....'' maganar ta yanke lokacin da Dr Ahmad yayo kansu su duka ya haɗa su yana ta jibga,babu ɗaya cikin su da ya iya yin wani abu ko yunƙurin ramawa,dama ba ƙarfi gare su ba kawai Dai sun Sha protein shake ne sun gaji, sai ihu suke suna ƙarawa, Dr Ahmad idanun shi sun rufe bai ji bai gani, duk ya musu kaca kaca, babu wanda bai karya ba cikin su,saboda azaba harda fitsari suka saki,ya fasa musu baki da hanci, ya karya hannayen su da ƙafafun su,his main focus was Andrew, A
Hankali Samha ta fara buɗe idanun ta tana sake lumshe wa har yanzu jin ta take babu ƙarfl
maganin bai gama aiki ba, bayan kashe ma mutum jiki,zai iyasa mutum yayi losing conscious hakan ne ya faru da Samha, Da ƙyar idanun ta suka buɗe juyo da kanta tayi inda su Andrew suke, kafin idon ta ya sauka akan Dr Ahmad da ya gama fita hayyacin shi '' Ya Ahmad'' ta kira In a whisper sai sannan Dr Ahmad ya dakata da jibgar su Andrew da yake, ya juyo da sauri ya ƙaraso inda Samha take ya cire farar rigar shi ya ɗago ta ya samata, hugging her tightly kamar wani zai ƙwace masa ita, itama Samha ƙanƙameshi tayi hawaye na kwararowa daga idon ta, tace'' naji tsoro sosai da Allah bai kawo kaba, da sun....'' Dr Ahmad da zuciyar sa ke ƙara ƙuna yace '' shhh, ya isa haka, I'm here now'' ya faɗa yana shafa bayan ta in a calming manner,wayar sa ya ciro daga aljihun sa ya daddanna ya maida cikin aljihu kafin ya miƙe tare da Samha bayan ya ƙara rufe ta da kyau ya fita daga clinic ɗin ba tare da ya kalli inda dark flames suke ba,
Suko Saboda azaba,suma sukayi nan wurin,duk wannan abin da ake mutane na a exam hall kuma babu kowa a clinic ɗin. Bayan kusan 30minutes da fitar Dr Ahmad wasu mutane saye da baƙaƙen kaya suka shigo clinic ɗin su biyar, huɗu suka cicciɓi su Andrew suka fita dasu ɗayan kuma ya tsaya ya goge blood stains ya gyara wurin har sukayi suka gama suka fita daga makarantar babu wanda ya gansu

Hostel Dr Ahmad ya nufa da Samha,bazai iya tafiya da ita ba a wannan yanayin da take if not da tuni sun bar makarantar, matron tayi masa jagora har zuwa hostel ɗin su samha bayan sun kawo ta karɓi Samha ta shigar da ita ɗakin duk da bata san abinda ya faru ba, baye ta shiga ta haɗa ruwan zafi sannan tazo ta taimaka ma Samha ta shiga kafin ta fito ta bata wuri, Bayan minti goma Samha ta fito ɗaure da towel, ɗaya kuma tana tsane gashin ta, taji sauƙi sosai amma fuskar ta har yanzu bata dawo normal ba, she felt nostalgic and for the first time in a long time tayi kewar iyayen su, tayi kewar gida tayi kewar rayuwar su ta baya gefen gadon ta Samha ta zauna ta fara kukan da bata yi ba na tsawon lokaci, kuka take kamar ranta zai fita tun tana zaune saman gado har ta zame ta kwanta ƙasa tana cigaba da rusar kuka

Matron Ce ta buɗe ƙofar ta shigo dama bata yi nisa ba taje cafeteria karɓo ma Samha abinci, jin kukan Samha yasa ta shigowa, ganin Samha kwance ƙasa ta ƙaraso da sauri tana tambayar ta mai ya faru? Rungume ta Samha tayi cikin Muryar kuka tace '' Nayi kewar gida,nayi kewar iyayena i missed everything '' lallashinta matron tayi bayan ta daina kukan matron ta ɗago ta, ta zaunar da ita saman gado ta buɗe cupboard ɗin ta ta ɗauko mata wata baƙar Abaya da baƙin pant da singlet ta bata tasa, karɓa Samha tayi ta koma toilet walking slowly, itako matron ta shiga jimami,bata taɓa ganin yarinyar na kuka ba,she was always cheerful what happened all of a sudden? Matron na Nan zaune har Samha ta fito miƙe wa tayi ta riƙo hannun Samha dake tafiya slowly ,ta zaunar da ita ta bata abincin da ta karɓo,kaɗan Samha taci sannan ta kwantar da ita saman gado ta rufa mata duvet , ta fita daga ɗakin closing the door.

Buɗe idanun ta Samha tayi tana ƙara damƙe duvet ɗin a hannun ta, abubuwan da su Andrew suka yi mata, na kai kawo a kanta,ƙara fashewa tayi da kuka mai sauti kafin taja duvet ɗin ta rufe har fuskar ta zuciyar ta na mata nauyi

Wurin karfe ɗaya Samha ta buɗe idon ta jin ana jan duvet ɗin,su Ra'esah ta gani tsaye akanta '' ya jikin Samha?" Ra'esah ta faɗa tana ƙara kai hannunta a goshin Samha, Fateema tace '' kin karɓi magani a clinic?" Su anasu tunanin Samha bata da lafiya, lokacin da suka gama exam suka tafi inda suke haɗuwa ko da yaushe idan sun gama exam basu ga Samha ba shine suka tafi class ɗin su, Adrian ya faɗa musu Samha ta tafi clinic can suka sake nufa ganin ba kowa suka yo hostel and they found her

Samha sai kallon su take da idanun ta da suka kumbura kafin ta tashi zaune weakly tace '' naji sauƙi'' Fateema ta zauna gefen daman ta Ra'esah on the left, Sukayi shiru na ɗan lokaci kafin Ra'esah tace '' gida zaki ko?" Tayi maganar idanun ta ƙasa, bata so Samha ta tafi '' ban sani ba '' Samha ta faɗa jinjina kanta Ra'esah tayi kafin tace '' Amma kina so ki tafi?" Kallon ta Samha tayi sannan tace '' idan zan tafi zaki bini ne?" Murmushi Ra'esah tayi sannan tace '' idan da dama ba'' Fateemah tace '' Wallahi ban so ki tafi, ji nake ina ma ace zangon bai ƙare ba'' Ra'esah ma ta jinjina kanta agreeing with what Fateema said, Samha sai binsu take da ido,kafin tayi murmushi sai kuma tayi dariya she felt relieved, tace '' ai hutun zai ƙare kafin kusani and we will be back again '' '' hakane fa,but kafin then,kewar ku ta gama da rayuwa ta'' inji Ra'esah tana yatsine fuska ba shiri suka kwashe da dariya, kafin suka cigaba da hirar su

Dr Ahmad motar sa ya nufa ya buɗe Boot ya dauki wata riga baƙa yasa saman baƙin wandon shi da baƙar singlet, sannan ya nufa office ɗin principal duk inda ya wulga sai anjuyo ,ladies were gushing

🗣️'' wow is he a model?"

🗣️'' I'm a fan''

🗣️'' I want Him ''

Wannan sune abubuwan da yan mata ke faɗa, Ameerah ce ta taɓo zeenah dake zaune kusa da ita a ƙarƙashin wata bishiya tace '' Zee wancan ba gayen ki bane?" Da sauri duka suka kai duban su inda take nunawa, '' shine wallahi '' inji Maryam

'' ko mai ya kawo shi?" Inji Hauwa
Zee bata saurare su ba,sai dai gani sukai zee ta antaya da gudu ta nufi principal office suma tashi sukayi suka bita.

Lokacin da Dr Ahmad ya isa office ɗin principal yana magana da mr Bolaji malamin English, da sauri principal ya sallami English teacher ushering Dr Ahmad to come inside

Shigowa Dr Ahmad yayi har yanzu fuskar shi ba walwala, Bayan sun gaisa da principal ba wani ɓoye ɓoye ya shiga zayyana mashi abinda ya faru

Principal ba abinda yake ina banda zufa, bayan Dr Ahmad ya gama bayani principal yace '' yanzu ina yaran?'' Dr Ahmad yayi shiru for a minute yana kallon wani wuri kafin yace '' I have taken them with me'' yayi maganar idanun sa na ƙara wani irin duhu, dawo da duban sa yayi ga principal daya jiƙe sharkaf da gumi, idan iyayen yaran sun zo neman su me zai ce? Their parents are top politicians,but then again he can't afford to offend the ZAKEE'S can he? Ganin yanda hankalin principal ya tashi yasa Dr Ahmad faɗin '' zan dawo da su after few days, kuma zan tafi da yarinyar '' yana gama faɗan hakan ya fice daga office ɗin

Yana tafiya ko kallon gaban shi bai yi,ga wani irin ciwon kai da yake ji, tun lokacin da sukayi waya da Samha yaji muryarta ayanda take ya kasa natsuwa hakan yasa ya fito daga office ɗin sa ya zo directly ELITE ACADEMY, Office ɗin principal ya fara zuwa asking for permission to see her, tunda exam suke principal ya ce ya bari su gama,amma Dr Ahmad ya kasa haƙura sai da principal ya kira one of the teachers ya raka su har class ɗin su Ra'esah and the invigilator ya faɗa masu Samha ta tafi clinic,
Godiya yayi masa kafin wannan malamin ya jagorance shi zuwa clinic ɗin along the way wayar sa tayi ringing daga ƙarshe dai kwatance yayi ma Dr Ahmad kafin ya rabu dashi ya amsa kiran

Ji yayi yaci karo da mutum,ya kalli ƙasa zeenah ce sai tangal tangal take zata faɗi ya ɗan taro ta itako da gangan ta faɗa jikin shi pretending kamar bata da lafiya, huci mai zafi Dr Ahmad yayi, tare da jan ƙaramin tsaki yace '' ke meye haka?" Ɗago kanta Zeenah tayi their eyes met tana wani ƙara lafewa jikin shi tana kukan ƙarya tace '' dan Allah ka kaini clinic, cikina ciwo yake I'm on my period bazan iya tafiya ba'' tayi ƙarashe maganar tana fashewa da kuka,
Sosai taba Dr Ahmad tausayi

Ɗaukar ta yayi ya nufi clinic ɗin da ita, ita ko sai ƙara lafewa take jikin sa daddaɗan ƙamshin sa na shiga hancin ta

Su Ameerah suka fito daga inda suka ɓoye Maryam tace '' shegiya Zeenah anyi makira'' Ameerah tace '' kinga laifin ta? Gayen ya haɗu fa,if I get a chance...'' Hauwa tace '' kada ma ki fara'' barin wurin sukayi zuwa clinic ɗin suma


Su Samha suna tsaka da hira aka ƙwanƙwasa ƙofar, '' Come in '' Ra'esah ta faɗa, turo ƙofar dr Ahmad yayi ya shigo ido biyu suka yi da Samha Da sauri tayi ƙasa da kanta, su Fateemah suka zaro ido suka haɗa baki wurin faɗin '' Brother in law '' ɗan murmushi Dr Ahmad yayi sannan yace '' ya kuke?" '' lafiya lau ya hanya?"
'' Alhamdulillah '' yayi maganar tare da kallon Samha da har yanzu kanta ke ƙasa yace '' we are going home '' ɗago kanta samha tayi,amma har ya juya ya fita ajiyar zuciya ta sauke she felt miserable
Su Ra'esah suka nufi wardrobe ɗin ta suka fara shirya mata kayan ta cikin akwati already har sun fara kewar ta especially Ra'esah

Ita dai Samha ta nan zaune tana kallon su, they were arranging the clothes in silence Babu mai magana

Wuraren ƙarfe biyu da rabi Ra'esah ta fito ɗauke da akwatin, Fateemah kuma riƙe da hannun Samha, dukan su fuskokinsu ba walwala, Dr Ahmad ya ƙaraso ya karɓi akwatin ya nufi mota dashi,to their surprise sai ga mutane suna fitowa daga hostel suna yi ma Samha bye,she didn't expect it suna kuma faɗa mata how much they will miss her, Samha sai murmushi take kafin su fara hugging ɗinta one by one, Ra'esah da fateemah suka koma gefe because idanun su har sun ciko da hawaye duk da suma gobe ki banda gobe zasu tafi.

Dr Ahmad yana ta jira yaga Samha tazo but she was taking so long hakan yasa ya dawo, kusan tare suka shigo wurin da Na'ema

Ta wutsiyar idon ta Samha ta hango Na'ema dake tafiya side by side da dr Ahmad sai kallon sa take kamar mayya'.

Wani irin zabura Samha tayi sai gata gaban Na'ema kafin Na'ema tayi wani yunƙuri Samha ta ɗauke ta da mari, everybody was stunned wurin yayi tsit, mutane na mamakin wato ita Samha even on the last day sai tayi faɗa!

Dr Ahmad shima ya tsaya chak yana kallon Samha.

















WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17

Chapter twenty six: the cold treatment

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑆𝑖𝑥: 𝑇ℎ𝑒 𝑐𝑜𝑙𝑑 𝑡𝑟𝑒𝑎𝑡𝑚𝑒𝑛𝑡



Kafin Na'ema ta gama warke wa, Samha ta cakumota tana huci tace '' Why did you do it?" Na'ema ta zaro ido cikin ina ina tace '' me nayi?" Tayi maganar ita ma tana cakumo wuyan Samha,ƙara ɗauke ta da wani mari Samha tayi cikin ihu tace '' Me yasa kika samin magani cikin abun sha?" Jin abinda Samha ta faɗa yasa kowa zaro ido wasu na rufe baki sai ƙusƙus ake, Dr Ahmad ya maida kallon shi ga Na'ema yanzu yake gane ita, she was the girl who was with them randa suka yi video call da Samha

Na'ema ta rama marin da Samha tayi mata, tace '' EHHH!!! I drugged you akwai abinda zaki iya yi ne? Na tsane ki Samha idan da za'a bani wata dama dana kawar dake'' wata shegiyar dariya Samha tayi sannan tace '' ai nasani, ba sai kin faɗamin ba,tun lokacin da kika wanko shegun ƙafafun ki,ki kazo wai kina so muzama ƙawaye i knew right then wani abu kike shirya wa, kuma haƙar ki bata cimma ruwa ba'' Samha ta ƙarashe maganar ita da Na'ema suna kai wa juna duka,kan kace me, har sun kai ƙasa suna tumurmusar juna, da sauri Fateemah da Ra'esah suka ƙaraso da wasu daga cikin yan hostel ɗin ana rabasu,sai an rabasu su sake ƙwace wa su cigaba,

Mutane sunyi mamakin jin abinda ya faru kenan duk ganin da suke kamar Samha ba tada lafiya ashe magani aka sa mata? Amma me yasa? Basu da amsa, Ƙara ƙwacewa Samha tayi suka haɗe da Na'ema suna cigaba da dukan juna kamar zasu kashe juna, mutane sai ƙoƙarin raba su ake amma abu yaci tura, ganin haka Dr Ahmad da yake tsaye wuri guda kamar an ɗasa shi ya matso ya finciko Samha holding her tightly sai ƙoƙarin ƙwacewa take amma ta kasa, su Ra'esah suka ja Na'ema gefe gabaki ɗaya wurin sai hayaniya ake

Ganin Samha tare da Dr Ahmad,kuma sannan abinda tayi nufin ya faru bai faru ba wani haushi ya ƙara turnuƙe Na'ema kawai sai ta dawo da faɗan kan Ra'esah,ta ɗauke ta da maruka har guda uku, Ra'esah ta dafe kuncin ta hawaye wasu na bin wasu,zaro ido mutane Sukayi, da sauri Fateemah ta saki Na'ema kafin ta ishi ishi ta kafta mata wani wawan mari

Faɗa ya dawo tsakanin Fateemah da Na'ema, Ra'esah ko ba abinda take in Banda hawaye ganin Na'ema ta kusa fin ƙarfin Fateemah Samha ta warce hannun ta da Dr Ahmad ya riƙe ta isa wurin, ta taya Fateemah wurin cin uban Na'ema sai da suka mata ligya mutane suka ƙara rabasu,this time around suka barta suka isa wurin Ra'esah dake kuka rungume ta suka yi su biyu ta ƙara fashewa da kuka she wish itama tana da ƙarfi kamar su ahankali Samha tace '' it's okay '' Fateemah tace '' ya isa haka '' suka cigaba da lallashinta

Mutane ko babu wanda yabi takan Na'ema da take nan kwance she couldn't move jikin ta sai ciwo yake sai ma Ra'esah da suka je suna lallashi...

Bayan komai ya lafa suka raka Samha har wurin motar su by then it was 3:39 dr Ahmad tuni ya shiga yana warming ɗin motar ya kuma kira Salmah ya faɗa Mata suna tafe,tayi mamaki but she didn't waste time ta shiga kitchen ta fara haɗa abincin tarbar ƙanwar ta.

Koda suka kawo bakin motar sai da Samha ta ƙara lallashin Ra'esah,

Ra'esah na kuka tace '' ba wai ina kuka ne dan ta mare Ni ba,kawai ina kewar kine Samha '' shiru samha tayi kafin ta jawo Ra'esah ta rungume sannan tayi ma Fateemah dake tsaye gefe tana kallon wani wuri saboda bata so aga hawayen ta alamar ita ma tazo,matsowa Fateemah tayi tana goge hawayen ta before she joined in the hug samha tace '' nima zanyi kewar ku sosai and take care of ur selves while I'm away '' jin jina kansu sukayi kafin su rabu, Samha tana share masu hawayen su.

Duk abinda suke Dr Ahmad na kallon su ta mirror, buɗe ma Samha seat ɗin gaba Ra'esah tayi Samha ta shiga, Ra'esah tace '' Brother in law Dan Allah wata rana ka kawo Samha gidan mu kaji?" murmushi Dr Ahmad yayi yace '' Yes Madam!" Murmushi Ra'esah tayi itama tace'' thank you '' Fateemah ta ƙara da faɗin '' and take care of your lady'' dariya suka yi ita da Ra'esah ita ko samha tayi ƙasa da idon ta, jinjina kansa Dr yayi, rufe musu ƙofa Ra'esah tayi sannan suka matsa baya bidding them a good bye kafin Dr Ahmad yayi reverse suka tafi, Fateemah tazo kusa da Ra'esah ta rungume ta '' it's okay Eysah '' tayi whispering

Share hawayen ta Ra'esah tayi sannan suka juya suka koma cikin makaranta.


Tunda suka ɗau hanya babu wanda yayi magana,from time to time Samha ke satar kallon shi amma shi ko sau ɗaya bai kalli inda take ba.

Jingina kanta samha tayi tare da lumshe idanun ta

After a while suka iso, yayi Parking ya fita ya buɗe Boot ya ɗauki akwatin Samha yayi ciki dashi, Samha tabi bayan shi da kallo

24 / 69