Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   63 / 69

186K to 189K   out of 206.1K words

ta turo baki looking so cute ta ƙara Matsowa tace '' Ni na dafa my efforts can't go to waste dole sai kaci!" Tayi maganar tana kai cokali full of noodles wurin bakin shi,buɗe baki yayi zaiyi rejecting ta tura masa '' yauwa '' ta faɗa tana ƙara mashi more and more Ahmad was Dumbstruck dole saida ya kusa cinye wa sannan ya ture yace ya ƙoshi,ajiye wa tayi ta miƙa masa ruwa karɓa yayi ya sha '' Thank you '' Murmushi tayi a genuine one

'' Next time don't get yourself hurt...I don't like it! Tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka!"

'' why? Is It my love Uhm my lady? Soyayya tace...faɗa min!" Miƙewa Samha tayi da sauri fuskar ta a shafe of red saboda blush ta nufi kofa Ahmad na dariya sosai...he loves when she does that

Tana buɗe ƙofa sai ga Amreesh shima zai shigo hararar shi tayi harda murguɗa baki saboda laifin shine

Wucewa tayi ya shigo, Ahmad ya dena dariya ganin Amreesh ya shigo ya zauna, '' Does it hurt?" Amreesh ya tambaya yana kallon fuskar Ahmad fuskar shi still blank

'' ka damu ne?" Yayi maganar yana matsar da fuskar shi dab da ta Amreesh '' Are You going to kiss me?" Amreesh ya tambaya yana ture fuskar Ahmad a frown settling on his face dariya yayi sosai which made Amreesh smile a little

'' kada kayi tunanin na damu fa? Next time kasake yin haka nima zan ƙara maka danawa!" Amreesh ya faɗa seriously,he didn't like the way Ahmad was slapped.....

Bayan kusan minti biyar na shiru Amreesh yace '' That silly brat...me take anan?" Wani irin sheepish smile Ahmad yayi kamar wani teenage boy da ya fara soyayya for the first time
'' Do you like her?" Amreesh ya sake tambaya bawai don bai sani ba he has noticed everything tun ba yau ba!

Miƙewa Ahmad yayi with a dreamy look and a blush a fuskar shi yace '' I love her kamar raina ZAKEE...'' taɓe baki Amreesh yayi '' The brat?" Da sauri Ahmad ya dawo daidai inda Amreesh yake '' No no, she's not a brat... Ina son ta sosai '' yayi maganar with a smile a fuskar shi ''l love her tun ranar da na fara ganin ta, it happened naturally Zakee.. love at first sight!" Ya ƙarashe maganar tare da wani ƙanƙame Amreesh kamar shine Samha suka faɗa saman gado

'' You're officially Mad Sebastian! Sake Ni!" Ƙin sakin Amreesh Ahmad yayi at the same time aka turo ƙofar, gaba ɗaya mutanen gidan suka shigo it will make you wonder me yake kawo su at a moment like this?

'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Muhammadu? Ahmadu?'' Uncle Ismael ya kira ido waje yana kallon su Uncle Naseer da sauran mutanen dake wurin baki sake...

Ahmad da Amreesh basuyi saurin sakin juna ba kamar yanda mutum zaiyi when caught in an awkward situation...yanda kowa ke kallon su sun riga da sun san abinda ake nufi da kallon that they both were gays

Miƙewa Amreesh yayi walking slowly ya fita daga ɗakin not sparing anyone a glance they weren't worth it

Suka bishi da wani matsiyacin kallo kafin su juyo da kansu towards Ahmad murmushi me kyau yayi ya faɗa saman gado tareda faɗin '' No need for interrogation..duk abinda kuke tunani hakane...y'all can leave '' yayi maganar dismissively yana kashe yar ƙaramar wutar dake kunne.... Juyawa sukayi suka fita cike da taraddadi....


WAYE SHI?(Behind the mask) Book 2 paid book ne ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin 9138091955
SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number+234 9138091955



















WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁
https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt

Chapter seventy seven: The nostalgic feeling......


Slowly take saukowa daga stairs ɗin hannunta ɗauke da small pebbles da wani rober band,saye take da riga da skirt na Atamfa tayi ɗaurin ɗankwalin Zara Buhari Gashin ta packed into a high ponytail ga wani vanilla scent dake fita daga jikin ta kafafunta saye da slippers baƙaƙe flat fuskar ta ɗauke da murmushin dayasa dimples ɗinta lotsawa she looked breath takingly hot, ɗazu Amreesh ya fita kuma yace yana dawowa zasu koma gidan su,she was happy beyond words

'' Young Master Emrys da Sebastian aka kama tare saman gado doing the deed!" Ɗaya daga cikin ma'aikatan dake jera breakfast a dining ya faɗa karaf! Sai a kunnen ta, tsayawa tayi chak tana sauraren su ɗayan ya zaro ido tare da rufe bakin shi cikin ƙasa da murya yace '' You mean they were gays?" Ɗayan daya fara magana ya jinjina kai yana ajiye plates da cokula kafin yace '' ai ba abin mamaki bane! Ni dama tuni nasani,kalli yanda kowa ya tsane young Master Emrys Amma master Sebastian was always with him idan ba abinda ke faruwa ba kenan You tell me!" Shima ɗayan ya jinjina kanshi yama Dena aikin sai tsayawa yayi da tagumi a fuskar sa yaji dayan na cigaba da faɗin '' dama me kake tsammani? Two freaking hot ass men suna zama wuri guda na tsawon lokaci batareda mace ba What do you expect?"
Ɗayan ya sauke ajiyar zuciya yana fuskantar wanda ke magana tuntuni yace '' Toh matar young Master Emrys fa?" Ɗayan yayi ƙwafa yace '' That's just for name sake! Tun yaushe suke a gidannan? Ka taɓa ganin wani act of affection displayed towards her daga gareshi? I bet ko i love you Bai taɓa ce mata ba!" Ɗayan ya kwashe da dariya yana dafa kafaɗar wanda ke magana tuntuni '' Wallahi mutumina da detective kazama! Kai! Ni inama ace zasu ɗan shigar dani cikin harkar,na tabbata ba ƙaramin benefit zan samu ba!" Suka kwashe da dariya suna cigaba da maganganun su na banza

Salmah was infuriated how ever akwai abinda suka faɗa da ya tsaya mata arai,the fact that koda yaushe itake faɗar soyayyar ta ako da yaushe ba Amreesh ba,her eyes stung tears welled inside,kafin su zubo ta share sannan ta yi amfani da ɗaya daga cikin duwatsun dake hannun ta da kuma robber band ɗin ta saita wanda ya fara magana tunda farko she fired it directly on his mouth '' Damn shiiit!" Ya furta yana dafe bakin shi na biyun dake dariya ya dakata yana tambayar '' what's wrong?" Kafin ya amsa aka sake firing na biyun shima between his legs shine yace a shigar da shi harka
Haka suka fara ihu Salmah bata sarara masu ba saida duwatsun dake hannun ta suka ƙare, Ahmad dake kallon komai tuni ya fara dariya...his anger dissipated,tun da suka fara maganganun su yake jin su.. .. kasancewar su farare don ba yan Nigeria bane yasa fuskokinsu musamman hancinsu yayi jawur... Mutum zaiyi tunanin ba zafi sai pebbles ɗin sun same ka zakayi bayani

Suna tsaka da tsalle tsalle mutanen gidan suka fara saukowa from the other side, kowa sai kallon ƙasa suke ganin duwatsu suna mamakin daga ina? At the same time suna kallon ma'aikatan da suka kasa tsayuwa wuri guda sai soshe soshe suke...

'' Kai! Meye haka?" Hajiya zakiyya ta daka musu tsawa '' Nothing ma'am!" They managed to say idon su ya sauka akan Salmah da fuskar ta take matuƙar tsuke, instantly suka gane daga ina duwatsun ke zuwa and she heard them!
Bayan kowa ya ɗau sit ɗinsa harda su maraƙisiyya they thought Amreesh na wurin but to their dismay Babu shi!Salmah ta sauko daga inda take her eyes filled with fury
Kowa ya juyo yana kallon ta dai dai ma'aikatan ta tsaya

'' Repeat what you say!" Ta basu order suka shiga kallon kallo ido ya raina fata ,faɗuwa ƙasa sukayi suna bata haƙuri '' we were wrong forgive us ma'am!'' suka faɗa tare da dungu Newa ƙasa kamar za suyi mata sujuda

Matsawa tayi tana kallon su idonta blank Babu ko ɗigon tausayi '' You were defaming the character of my Husband are you mad?''

'' Wallahi shine ya fara babu ruw...!" Kafin ya gama magana Salmah ta ɗauke shi da wani gigitaccen mari ɗayan ya firgita hakan yasa ya faɗi zaune his body shaking ta bala'in basu tsoro

Mutanen dining kowa ya dakata daga abinda yake aka zuba musu ido

Salmah ta zauna majestically saman couches ɗin ƙafa ɗaya saman ɗaya '' Oya ku fara tsallen kwaɗo forth and back... Idan kuka tsaya....'' tayi shiru da wani glint a idonta na mugunta Hajiya Maleeka dake kallon Salmah felt yarinyar tana da wani irin similarity da Amreesh kawai sai mutum ya kula sosai kafin ya gane hakan sannan it's not obvious saboda Maybe she hasn't reached a point of break down...she won't break, she will become stronger,dole tayi wani abu before then! Hannunta dake riƙe da fork ɗin taƙara damƙewa babu wanda ya gani

Tuni ma'aikatan guda biyu suka fara abinda Salmah tace it freaking hurts suna yi suna bada haƙuri har suka fita daga parlorn

'' ke dalla malama ke wace ce da zaki zo kina bawa mutane order?" Maraƙisiyya ta faɗa a fusace ta iso inda Salmah take,it became more interesting saboda kowa dake wurin ya sake bada attention su Sultana suka iso ready to beat her if necessary
Ihu maraƙisiyya ta cigaba da yi ma salmah akai

Miƙewa Salmah tayi unexpectedly ta shaƙe wuyan maraƙisiyya,idon maraƙisiyya suka fito waje sauran suka ja baya mutanen dining suka miƙe su Hajiya Turai ta matso ta fara ƙoƙarin ƙwace maraƙisiyya dake ƙakarin mutuwa su Hajiya zakiyya sai ihu suke Salmah zata kashe musu ya

Su Uncle T sunyi tsaye unable to do anything
'' yesterday you pushed me to the pool..'' Salmah ta faɗa tana ƙara matse wuyan maraƙisiyya,idon Salmah suka ƙara wani duhu like she intended to murder someone '' I could kill you...! Stay away daga duk abinda ya shafe ni!" Salmah ta iyarda sentence ɗin da wani irin devilish smile completely different from that innocent looking girl tana kallon su sultana...

Da sauri Hajiya Turai ta riƙe maraƙisiyya tana zagin salmah ta uwa ta uba,yan samarin gidan ma suka kasa cewa komai, perhaps at this point suma sun fara gajiya da dramar gidan nasu!
Swiftly Salmah ta juyo gefen Hajiya Turai ta kalleta in a way that made her quiver calmly tace '' Ma'am I respect you kema ki kama kanki.... I can do worst..Bazan so kiga wannan side ɗin ba na fiso murabu lafiya..''

''. amma kedai anyi tsigaggar albarka shegiya mai kama da aljannu...'' Mariya ta zagi Salmah,wani mari Salmah ta sauke mata dayasa taga walƙiya '' i don't entertain insults...kibi ahankali!" Samha ce ta sauko ta zauna saman railing ƙarfen stairs ɗin tana kallo kamar ta samu movie tace. '' A free show without me..not fair!" Suka juyo suna kallon ta,itama tayi shiga irin ta Salmah she looked dashing... Ahmad ya ɗauke idonshi daga abinda ke faruwa a Tsakiyar falon ya dawo da shi kan Samha his heart beating uncontrollably '' Ya Allah...'' dirowa Samha tayi ta ƙaraso wurin kallon su tayi one by one kafin idonta ya sauka akan Ja'afar a smirk made a way to her face, he was the same guy from the other night sauke idon shi yayi...

Salmah ta ƙara gyara tsayuwar ta kafin tace '' You all may leave..idan kuma da me magana zai iya yi!" At this point abinda Salmah tayi ma maraƙisiyya ya basu tsoro duka yarinya kamar wata possessed

'' wannan Amreesh ɗin daki ke taƙama dashi...you're bound to lose him in one of these days! I curse you" Hajiya Turai ta faɗa kafin tabar wurin da maraƙisiyya da Haryanzu bata dawo dai dai ba

Wannan furucin na Hajiya Turai yama Salma zafi kuma ya tsaya mata a zuciya mafalkin tane yashiga dawo mata tiryan tiryan '' it's just a dream!" Salmah ta faɗa inaudibly to her self Idonta lumshe, koda ta sake buɗe su every body has left ita kaɗaice ta rage itada Samha

'' You' okay?" Samha ta tambaye ta, jinjina kanta Salmah tayi feeling a sudden anxiety.... Upstairs ta wuce Samha kuma ta wuce kitchen ta haɗo musu break fast.... '' My lady!" Dr Ahmad ya kira from behind da sanyayyar murya, losing balance ɗinta Samha tayi ta kusa faɗuwa yayi saurin tarota her chest pinned on his da sauri ya sake ta his heart beating wildly,idon shi ya sauka akan ƙirjinta.... '' Slightly bigger'' maganar ta suɓuce daga bakin shi,kare ƙirjinta Samha tayi ta ɗauke abinda ta haɗa tabar kitchen ɗin '' Pervert!!" Ta furta kuma ya jita saurin rufe bakin shi Ahmad yayi damn!me ya kaishi faɗar haka?
Ji yayi kamar yata jibgar kanshi amma sai ya tausaya ma kanshi kawai
******
Da ƙarfe goma su Salmah suka gama loda kayan su cikin mota Ahmad shi zai maidasu according to abinda yace Amreesh was busy Salmah kamar tayi kuka ji tayi duk excitement ɗin da take ji ɗazu has dissipated

Samha kuma taƙi kallon gefen Ahmad har yanzu she still feels embarrassed by what he had said earlier wai ƙirjinta ya ƙara girma to Meya kai idon shi wurin?

Bayan yan mintina suka kawo parking yayi a parking lot ya buɗe musu ƙofar ya Ciro masu kayan su and he took it in,wani dogon numfashi Salmah da Samha suka ja Finally air of freedom yanzu babu wani drama

Kallon itacen gidan sukayi and the fruits Plus inda Salmah da Amreesh sukayi wasa in the past.... Iskan ƙarshen December making the trees to sway daga nan zuwa can

Shiga cikin gidan sukayi dai dai Ahmad zai fita sallama yayi musu yaɗan saci kallon Samha da ko inda yake bata kalla ba rather sai gaba tayi abinta

Salmah tayi mashi godiya and then he left.
Sunyi mamakin ganin ko ina tastas, Amreesh had it under control...

Wurin ƙarfe biyu na rana suka shiga kitchen suka dafa abinci it felt good again abinda basuyi ba da daɗewa they experienced a nostalgic feeling...

And they even played like they used to Salmah ta tuna lokacin da ta ci karo da Amreesh the very first time they met itada Samha suka kwashe da dariya tuna yanda Salmah ta ɗane Amreesh...
*****
Da ƙarfe tara suna zaune suna kallo saiga Amreesh ya shigo his dressing all black,his jet black hair into a ponytail ...lips ɗinsa glistening idon shi looking very dark. Fuskar shi as handsome as ever.. Directly stairs ya haye Salmah da Samha exchanged glances kafin Salmah ta tashi tabi bayan shi,he was in the toilet,zama tayi bakin gado tana jiran fitowar shi after a while ya fito ƙugun shi ɗaure da towel ruwa na ɗiga daga gashin sa disappearing into the towel,ido suka haɗa ta jaye nata, gaban madubi ya isa kunce towel ɗin ya fara with a smirk on his face Salmah ta jawo pillow ta ɓoye fuskar ta heart banging,ƙamshin sa taji close to her da sauri ta buɗe ido he was looking down at her his Ocean Blue eyes holding something in them... something unusual, slowly tayi ƙasa da idonta ashe yasa ƙaramin wando...

Miƙar da ita yayi suka isa gaban mirror ya miƙa mata cream ta taya shi shafawa,her movements were slow, ganin hankalin ta bai wurin yasa ya miƙe itama sai ta tsaya tana kallon shi

'' What's wrong Mahee?" Ya tambaya yana riƙe haɓar ta '' Nothing!" Ta faɗa tana ƙara tuna abinda ma'aikatan nan suka faɗa ɗazu does he really love her? Kodai...

Rungumeta yayi ta baya sniffing her, lumshe idonta tayi Suka tsaya haka naɗan lokaci kafin slowly Amreesh yace '' If I...idan wata rana na tafi wani wuri ban dawo ba...will you miss me? Will you wait for me?" Da sauri Idonta suka buɗe ta kalleshi ta cikin madubi What The heck😡! Wane irin tambaya ne wannan!?💢

Cire hannun shi tayi daga jikinta '' Are You eloping with someone? Ka samu wata zaka barni ko? Shine yasa kake irin wannan maganar! Toh ai zaifi idan ka fito fili kace kana so murabu!" Salmah tayi maganar cike da zafin rai ta ture Amreesh out of the way hawaye Masu zafi na ratata daga Idonta ta nufi hanyar fita

Har ta kama handle ɗin Amreesh ya mayar ya rufe pinning her on the door '' ba haka nake nu..''

'' Toh me kake nufi!? Are You hiding something from me? Oh....na tuna ashe auren contract ne,i bet lokaci yayi da zaka rabu dani isn't it?" Tayi Maganar tana kallon cikin idon shi more and more tears streaming down her face, kiciniyar kwace kanta take wani haushi na ƙara ƙumeta ganin Amreesh bai tanka ba sai kallo da yake Binta dashi,her almond eyes filled with tears damn! It's doing something to him

Duka ta fara kai mashi a ƙirji still wanting to escape riƙe hannun yayi before he crashed his lips on hers,taƙi buɗe bakin...ɗan cije leɓenta na ƙasa yayi she gasped...ya tura bakin shi cikin nata,his large frame looming over her small one... Tun tana son ƙwace kanta harta Dena and begun kissing him back....

'' I can never imagine living without you Mahee.... Every breath.... You're my life line,you're the best thing that has ever happened to me!" Amreesh yayi whispering when their lips parted yana kallon fuskar ta

Comment and share pls

WAYE SHI? (Behind the mask) Book 2 paid book ne ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin 9138091955
SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number+234 9138091955







.












WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁
https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt

Chapter seventy eight: A sinful desire....

Tsit Salmah tayi idon ta akan shi ya riƙa hannun ta ya ɗaura saman ƙirjinsa '' My heart beats for you, it may take time to properly express what I feel..but trust me, you mean the world to me!" Salmah taji wani irin rauni swirling over her she didn't know how to react kawai sai tayi tip toeing ta haɗe bakin su tana mashi wani irin kiss,it was different from the usual, kamar tana faɗin duk wani abun da takasa furtawa both her fears and wishes

Amreesh ma haka kissing her back with all he has got..he just knew deep down kamar komai yazo ƙarshe wani gagarumin abu zai faru da zai raba shi da ita he just feel it

Daga kiss Abu ya koma romance in full swing daga bakin ƙofa zuwa tsakiyar gado,zuwa

63 / 69