Author : Nimcyluv Category : Complete Novels
WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter one: the contract
Nigeria Abuja: Asokoro
05:00pm
BLOOM HEALTH CARE PRIVATE HOSPITAL
Dr Ahmad's office : Office ne daya amsa sunan sa Office. Everything in the office was sky blue and white kama daga curtains,sofas,rugs and walls. Daga tsakiyar Office ɗin kuma kujeru ne na alfarma an shinfiɗa rug sky blue and a center table daya kasance fari.
Tsaye yake kusa da windown office din,hannunsa biyu saye cikin aljihun wandon suit dinsa da ya kasance sky blue. Hannayen rigar nade suke zuwa guiwar hannun sa that was white. He was standing straight,hakane ya bani damar kare ma bayansa kallo. Dogo ne sosai Masha Allah tsayin sa besa ya kasance me doro ko wani naƙasu da za'a iya alaƙantashi da tsayi ba . His black hair was parked into a pony tail.
Ƙamshin turarensa ya mamaye kowane kusurwa na officer ɗin. Yaɗan sauke ajiyar zuciya Tare Da duba wrist watch ɗinsa daya kasance silver color to complement his white shirt. Turo ƙofar office ɗin akai . a young man of about 35 years ya shigo saye da farar riga irin na doctors. Shima dai dogo ne,don tsayin su xeyi ɗaya da wanda ke tsaye a bakin window
The only difference is that wannan shi Black beauty ne. He was also wearing round frame glasses. Takowa yafara yi a hankali yana ƙara gyara files ɗin da ke hannunsa.
Zama yayi a seat ɗin da ke bayan desk ɗin da aka rubuta DR AHMAD hakan na nufin shine Dr AHMAD ɗin.
Bayan ya gama arranging ɗin files ɗin dake saman desk ɗin sa, yaɗan ɗago ya kalli mutumin dake tsaye kusa da window wanda bema Nuna Alamar yasan da wanzuwar mutum awurin ba for some seconds. Murmushi me kyau yayi tare da faɗin"Sorry mutumina, na ɓata maka lokaci" ya ƙare maganar yana kallon shi. har shuɗewar yan mintuna mutumin bece komai ba. Ajiyar zuciya doctor Ahmad ya sauke dama yasan baze amsa ba.
"What does the report say" ya faɗa ina a deep and serious tone after kusan minti biyar batare da ya juyoba. "The same thing,ba canji" doctor Ahmad ya Amsa
"But i think I have a solution " doctor Ahmad ya faɗa ina a serious tone. Jin hakan yasa mutumin ya bar bakin windown yafara takowa zuwa cikin office ɗin .(Masha Allah fata Barak Allah ahsanul khaaliƙin) wani irin masifaffen kyau ne dashi, Abu mafi ɗaukar ido a fuskar sa,shine idanun sa da suka kasance Cat eyes with an ocean blue orbs,and In between his eye and brow akwai black dot a wurin da makes him look like a piece of art work. his pink heart shaped lips glow kamar ya shafa man baki. Yana da Arched eye brows da suke cike da baƙin gashi kamar na wata mace thou gashin girarsa ze iya fin na wata macen (kamar dai ni☹️) Hancinsa dogo amma ba dogo can can ba. Yana da doguwar fuska da take glowing kamar new moon. Yana da saje amma beda gamu . Duk da wannan fuskar sa adaure ba fara'a. Its his personality.His got a long and elegant neck with a big Adams apple idan yana magana Adams apple ɗinsa bobs up and down in a sexy way. Kayan dake jikin da basu ɓoye ainihin siffarsa ta ƙarfafan maza ba.Ga wani irin kwarjini da cikar haiba da Allah yayi masa. Takowa ya cigaba da yi, doctor Ahmad kuma ya bishi da idanu har ya zauna akan sofan dake cikin office ɗin. "Ina jin ka " yafaɗa a gajiye tare da gyara zaman sa a sofa ɗin ya lumshe idanun sa. Miƙewa Dr AHMAD yayi ya zo ya zauna kusa dashi tare da dafa kafaɗarsa "Get marry" ya faɗa yana karantar yanayin fuskar sa ko ze ga wani reaction but there was none. Ya cigaba da faɗin"Ina ga yanzu abu guda kaɗai zaka iya yi domin samun mafita,kuma wannan shine aure"! Dr Ahmad ya ƙarashe maganar cikin son shawo kanshi. Bayan shuɗewar wasu mintuna buɗe idanunsa yayi tare da kallon Dr Ahmad da har yanzu yake nan zaune ba tareda ya canja position ba ko ya ɗauke hannunsa daga kafaɗar da ba.in a husky voice yace" Me ya haɗa aure da matsala ta kuma?" "Ita has everything to do with your problem zakee!if you are lucky to get a nice woman,zata iya zama silar warakar ka! Zakee pls you have been avoiding this amma yanzu i think this is the only solution to the problem! Nasan Kai baka damu da yadda ka ke ba amma,there are ppl who care. Kayi tunanin Grand parents and your father ko dansu pls you have to do this "! Dr Ahmad ya ƙare maganar da Alamar roƙo. Ajiyar zuciya zakee ya sauke after a while yace "akwai matar da zata so ta kasance with a person like me? Ni bazan cutu ba amma ita pa?" Ya ƙarashe maganar yana maida idanunsa ya lumshe.
" Kabar duk wannan wurina,I will handle it pls" Dr Ahmad ya sake faɗa yana kallon zakee. "Okay" zakee ya faɗa bayan shuɗewar mintuna daɗi sosai Dr Ahmad ya ji har yana ƙoƙarin rungume zaki,Da sauri ya buɗe idanun sa yana jefa mai haramta. Komawa baya Dr Ahmad ya yi yana yar karamar dariya "You are a killer joy man" "hmm" kawai ya faɗa cike da ƙosawa. Dr Ahmad ya tashi ya fita daga office ɗin gabaki ɗaya. Bayan fitar Dr Ahmad miƙewa zakee yayi yabar HOSPITAL gabaki ɗaya.
Dr Ahmad bayan ya dawo bega zaki ba, shima kawai se ya fita daga office ɗin haɗuwa yayi da wata nurse a hallway "Dr har zaka tafi"? Ta faɗa yana wani yatsu ne yatsu ne ita ala dole se taja hankalin shi. "Hmm" ya faɗa batare da ya kalle ta ba. Yay gaba abinshi ta bishi da ido tana raya abubuwa a ranta.
___________'_______________
Sanye take da hijabi baƙi wanda yaga ruwa har ya gode Allah doguwa ce ita chocolate complexion, tana da manyan almond shaped eyes wanda kalar ciki ya kasance baƙi amma farin cikin yayi jaajur saboda tsabar kukan da yaci. Lips ɗin ta da suka kasance red color sun bushe sun yi ƙamau ƙamau hancin ta ƙarami kuma ba dogo na she has dark eye brows and long lashes da suka jiƙe da hawaye sun yi zaƙo zaƙo. She over all has an oval shaped face.
Takalmin ƙafarta sun tsupa sun ƙoƙe. Tafiya take batare da sanin inda take jefa ƙafa ba all she could hear was the doctor's warning "idan ƙanwar ki ta wuce yau batare da amma ta aiki ba she could lose her life" and since then take ta neman inda zata samu kuɗi amma har yanzu . What should she do? She didn't want to lose her sister. Ita kaɗai ce familyn da ta rage mata ina the world she has no one other than her sister" Ya Allah" ta faɗa hawaye na ƙara gangaro wa bisa kyakkyawar fuskar ta. Tafiya take batare da ta lura da ta kawo saman tutu ba, tuƙi yake a hankali yana tunanin maganar da sukayi da zakee, when suddenly,she appeared in front of him idan ba dan Allah yasa,ya taka burki da sauri ba,da ba abinda ze hana ya buge ta. Ita kam tun lokacin data lura da motar nan tay shahada dan ta sadaukar se motar nan ta buge ta hakan yasa ta rufe idanun ta gam tana jiran ta Allah ta kasance. Fitowa yayi a fusace yana faɗin "Are You crazy?baƙi da hankali kina ganin mota zaki tsaya ta buge ki Salam ki jama mutane?! Buɗe idanun ta tayi a hankali se kuma ta juya ta kalli mutumin dake ta mata bambancin bala'i before she could stop herself kawai se ya fashe da kuka. Dr AHMAD wasu stunned tunda shidai be mata komai ba ne was only scolding her for the good of her self! Ita kuma ana ta bangaren tana jin
Akan me ze dinga mata faɗa bayan nesa abinda ke damun ta ba? Juyawa tay ta fara tafiya. Saurin shan gabanta yai yana faɗin "yi haƙuri,ina zaki? Shigo mota in sauke ki" girgiza kanta tay tare da faɗi ina a trembling voice"motar ka baza ta iya kaini inda nake so ba, Im out to look for money Dan ayi wa ƙanwata aiki" ta ƙarashe maganar zuciyar ta na mata raɗaɗi wasu hawaye na bin wasu Dr Ahmad looked at her for a while wondering what could be wrong with her sister? Juyawa tay yafara tafiya
"What if I pay the money!?" Ta tsinkayi Muryar shi yana faɗa. Tsayawa tay tare da juyowa ta kalleshi . Slowly ya Jin jina mata kanshi affirmatively.
Ze biya kuɗin? Akan wane dalili? Me yake so ina return? Wannan sune abinda ke yawo akanta
Kina shigo mota se muyi magana. Ya faɗa yana buɗe mata gaban motar. Tsayawa tai tana ƙara bin shi da kallon as if searching for answers on his face
" Your sister is waiting" hakan da ya faɗa yasa ta taki a hankali ta zo ya shiga motar shi kuma ya shiga driver side yafara tuƙasu
"So meta ke damun ƙanwar taki?'ya faɗa bayan sun ɗauki hanya
Hawaye da suka silalomata ta goge tare da faɗin"lung Cancer final stage" innalillahi wa inna ilaihi raji'un Dr Ahmad ya faɗa. Ita kuma ta cigaba da goge hawaye ta trying so hard not to break down
"What if I offer you a contract in return for your sister's operation" ta tsinkayi Muryar sa
WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter two:the contract
Da ma Maki ta juyo tana kallon sa contract? In return for her sister's operation? To amma wane irin contract? Zata iya?
Those are the thoughts running in her mind to amma ba batun zata iya bane ko baza ta iya ba. She will just agree after the payment of her sister's surgery they would settle. Tayi nisa cikin tunani ta tsinkayi muryar sa yana faɗin "if you agree,zan biya kuɗin duka,You will only sign the contract and you won't back out harsai contract ɗin yay expire" ta ji ya sake faɗa still driving ba tare da ya kalle ta ba. After a while da dasashshiyar murya tace "wane irin contract?" "Aure" ya faɗa dai dai da yana shiga asibitin da ta mai kwatance "AURA PRIVATE HOSPITAL" parking yay a parking space sannan ya juyo yana kallon ta steadily kamar yadda ita ma take kallon shi ba ƙyaftawa. Ɗauke idanun ta tay saboda kwarjinin da yay mata"think about it, ƙanwar ki is in the hospital, Rai a hannun Allah and you have no way to save her. Na kawo miki mafita bazaki karɓa don ceton ran ƙanwar ki ba? And i promise you baza ki Cutu a wannan contract ɗin ba" Dr Ahmad ya faɗa convincingly
tare da buɗe kofar ya fita ya zagayo ta gefen ta ya buɗe mata ƙofa fitowa tay suka fara tafiya tana gaba yana biye da ita a baya. Kalaman shi sun matuƙar yin tasiri a zuciyar ta. Juyowa tayi ta ɗan kalleshi se kuma ta tsaya Tare Da juyowa ta fuskance shi" you are right,bani da wani abu da yake da muhimmanci a wurina sama da rayuwar ƙanwata i will do anything for her" ta ƙarashe maganar idanun ta na cikowa da kwalla. Murmushi yay tare da jin jina kanshi" bazakiyi nadama Ba insha Allah.whats the room number?" Ya tambaya. goge hawayen ta tay Sannan tace "room number 10" jinjina kanshi yayi Sannan ya wuce counter ita kuma ta wuce ɗakin. Da sallama a bakin ta tashiga. Tsayawa tay tana kallon ƙanwar ta that was lying on the bed with life supporting machines she looks lifeless. Da ƙyar take ɗaga ƙafarta har ta ƙaraso gefen gadon ta zauna tana kallon ƙanwar ta ta. Hannun ta na ƙyarma ta riƙo hannun ta cikin na ta "Samha" ta faɗa zuciyar ta na karyewa hawaye wasu na bin wasu "ki tashi Samha,i'm afraid,Dan Allah karki barni kamar yanda mama da baba suka barni! You are the only family I have left pls ki tashi." Magana take tana risgar kuka kamar ranta ce fita. Samha kaɗaice familyn da take da ita, Their father passed away few months a go wannan shine yay sanadin tashin ciwon Samha, and here she is. Turo ƙofar akai it was Dr Ahmad ya tsaya yana kallon yarinyar kawai. Daga gani shekarunta ba za su wuce 18 ba and she's going through so much, ko ina iyayensu? Bashi da amsar tambayar hakan yasa ya idasa shigowa ya tsaya daga gefen ta "be kamata ki dinga kuka ba . Kamata yay kimata addu'a uhmm?" Allah shi yake raya wa kuma ya kashe and your sister is still alive so you should be grateful Dan Allah ki dena kuka" jin jina kanta tay tana share hawayen duk da sun ƙi tsayawa Sannan ya ƙara da faɗin" i have paid for the surgery, it's scheduled to take place at 07:00pm kuma yanzu ƙarfe 6:40 so minti ashirin ya rage ki tashi ki je gida ki huta" ya gama maganar yana kallon ta cike da tausayi. Still holding on to Samha tace" I don't want to,Ina so in tsaya har se angama surgery ɗin an fito da ita. I want us to go home together" shiru Dr Ahmad yayi kafin yace "Sallah pa?" She was on her period hakan yasa ta girgiza kanta ba tare da tace komai ba. Ze sake magana aka buɗe kofar wasu nurses guda biyu suka shigo
Gaida Dr Ahmad suka fara yi kafin su yi masu bayanin sun zo shirya samha ne for her surgery.Miƙewa sukayi ita da Dr Ahmad suka fita daga ward ɗin while nurses ɗin suka fara shirya samha. "Na gode" ta faɗa lokacin da suka fito daga ward ɗin " You have done me a favor I can never repay a rayuwar nan" ta ƙarashe maganar dai dai suna zama on the waiting chairs ɗin da aka aje a ball way ɗin daga inda suke banda da theatre room ɗin dan haka a gaban su aka fito da samha on a wheelchair to the theatre room ɗin. "It is not a favor, you have agreed to the contract! Fatana bazaki saɓa maganar ki ba" jin jina kanta tay
Dan ita agareta wannan babban favor ne. Da Allah be kawo shi a wannan gaɓar ba da yanzu tana can tana cigaba da gara ranba with out a guarantee if she will get the money." Baki faɗamin sunan ki ba! Dr Ahmad ya faɗa yana kallon ta. Ɗan satar kallon shi tay kafin tace "suna na Salmah,amma ana kirana da Mah Mah" jin jina kanshi yayi kafin shima ya faɗa mata sunan shi, ya ƙara da tambayar iyayensu? "Iyayen mu sun rasu" ta faɗa da karyayyar murya. Allah ya jiƙan su" Ameen."lokacin sallah yayi,zan tafi amma zan dawo" ya gama maganar yana miƙewa. Jin jina kanta ta ƙarayi batare da tace komai ba.Bayan ya tafi ta maida kanta towards the surgery room zuciyar ta na bugawa da ƙarfi thinking of the possible outcome Imma ƙanwarta ta rayu ko akaasin hakan"ya Allah kasa ƙanwata ta fito lafiya,i can't bear to lose her " Tafaɗa tana jingina kanta a headrest ɗin kujerar tare da lumshe idanun ta hawaye wasu na bin wasu. Da ace hawayen mutum na ƙarewa Maybe Dana ta sun ƙare.
***********ZA'A KEE***""
Yana fita daga officer ɗin Dr Ahmad directly ta ƙofar baya ya fita daga asibitin saboda yawan ɗin ba mutane dayawa je doesn't like crowded places. A hankali yake tafiya kamar baya son taka ƙasar. Kallo guda idan mutum yayi mashi ,ze ɗauka shi ɗin mutum ne mai girman kai,amma ba haka bane haka Allah yayi shi. The way he walks, the way he does things it's his nature,duk da 25yrs ago ba haka yake ba amma abu buwa dayawa suna faru that made him to become the way he is. Ya na isa motar shi yashiga ya tada sannan ya fita daga asibitin duka. Tuƙi yake a hankali har ya kawo wani wuri inda ba kowa,the Place was quiet and surrounded by trees daga cikin gurin kuma akwai kujeru. The place was clean,baka jin kukan komai se na tsuntsaye ga wasu daga cikin ganyayyakin itace sun fara zama red and orange signifying Autumn lokacin bazara ya kusa. Parka motar shi tay a little away Sannan ya sauko yana taku cikin natsuwa ya je ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun bayan ya goge da handkerchief ɗin dake riƙe da hannun shi. Shiru yay yana jin daɗin kasancewar shi shi kaɗai a wurin. It looked beautiful at the moment ga rana ta kusa faɗuwa the hues of the setting sun ya ƙara ma wurin kyau ga wani gentle breeze da yake kaɗawa . AMREESH YOUSUF ZAKEE ke nan mata shin ɗan kasuwa ne jini ajika. Duniya ga baki ɗaya tasan da zaman shi ba a africa kaɗai ba saboda ƙarfin faɗar shi aside from that shi ɗin ɗan kasuwa ne me gaskiya ba kuma ya jin tsoron kowa se mahaliccin shi. Ya tara dukiya me ɗinbin yawa wadda duk da ɗin bin dukiyar sa hakan besa yazama me girman kai ko ji jida kai ba. hakan yasa yana da NGO nashi nakan shi. Saboda shi dukiya ko wani abu na duniya be dame shiba. business ɗin ma yanay ne cuz it's his passion. Bayan wannan babu wani abu a duniya dake burge shi. And he had no feelings whatsoever besan idan yana farin ciki ko baƙin ciki ba, damuwa ko akasin hakan. Je just doesn't have emotions. Hakan be dame shi ba cuz ya gode Allah ya yayi shi yanda yayi shi ɗin idan badan hakaba da tuni ciwon zuciya ya gama da shi. A yadda yake ɗin nan he doubts idan idea of Dr Ahmad will solve his problem! Ganin da yay magariba ya ƙarato yasa ya miƙe ya koma cikin motar shi ne ignited the engine and left. Tsayawa yayi a wani masallaci yau sallar magariba be tafi ba har sai da yay isha'i. Yana gamawa directly residence ɗin shi ya tafi. Gida ne babba sosai me golden gate. Horn yay mega din gidan ya Masan shine hakan yasa ya buɗe masa gate ɗin kawai. Shiga yay ciki yay parking a parking lot