AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 80

24K to 27K   out of 237.4K words

ne ya amsa masa. Yayinda ita kuma ta zuba musu raunannun idanunta. Da sauri Hameed da Waleed sukayo inda take cike da farin cikin ganin idanunta a buWe. Hannunta duk suka kama suka ri?e suna kaiwa dur?ushe daga ?asa ta yanda fuskokinsu zasu daidaita da tata.
? ? ?  Alhamdullahi Didi ta samu lafiya . Cewar Hameed yana sake ?an?ame hannunta. Shima Waleed cike da Woki ya furta,  ALLAH mun gode maka yau muna cikin farin ciki Daddy Didi ta buWe ido .
? ?? ?aramar dariya Daddy yayi da faWin,  Alhamdullahi shima. Maanal cikin magana a hankali tace,  ?an turai kamarku daban . Dariya duk suka ?yal?yale da shi. Itama saita maida kallonta ga Yazeed dake tsaye kawai yana kallonsu fuskarsa ?awace da murmushin farin ciki. Kallon da take masa ya sashi ?arasa ?arasowa gaban gadon sosai. Sai kawai ta lumshe nata idanun a hankali ta kuma sake buWewa duk a lokaci guda.
? ? ? ? ?  Alhamdullahi. Sannu Maanal ALLAH ya ?ara lafiya yasa kaffarane kinji .
? ? ?? Murmushi ta sakar masa a karo na farko, murya can ?asa ta ce,  Amin Yaya nagode .
? ? Amsa mata yay cike da farin ciki, jiyake tamkar ya rungumeta a jikinsa sai dai babu damar hakan. Balle ma ga Ammie a wajen ga Daddy. Suna a hakan dai kuma sai ga RK. Tunda ya shigo idanunsa akan Maanal Win ne shima, itama dai shi Win take kallo da Wunbin mamaki. Yayinda zuciyarta ke raya mata (shi wannan duk inda naje sai ya bini ne shin?) Rashin mai bata amsa yasata janye idanunta a zahiri daga kansa. Shima sai dai janye nasan yayi tare da ?arasowa ya gaida Daddy da Ammie cike da girmamawa. Maanal ta sake shan mamakin ganin yanda duka amsa masa da kulawa da alamar sanayya sosai kuma. Dubansa ya maida a kanta yana mai Wan kashe mata ido, hakanne ya sakata yimasa ?aramar harara. Murmushi ya saki mai faWi da ?o?arin Waukar file Winta dake a drower Win gefen gadon yana faWin,  Gawa ta?i rami yaya jikin? .
? ?? Dariya Daddy da su Waleed sukayi, yayinda Ammie tai Wan murmushi kawai. Yazeed kam fuska ya sake tamkewa kamar bai san minene dariya ba. Yayinda Maanal ta Wan tsuke fuska itama tana hararar RK Win yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya mi?ama Yazeed hannu cike da sha?iyanci yana faWin,  Babban Yaya barka ?anwa ta mi?e. ALLAH ya ?ara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba .
? ?? Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK Win ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin RK fa bawai yasan ainahin ala?arsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba Waya yake masa kenan. Daurewa yay ya Wan sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa da,  Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ?o?ari ai sai fatan alkairi a gareku .
? ? ??  Doctor! .
?? Manaal ta faWa a hankali cikin suSutar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yun?urin bata amsa Waleed yabata amsar da  Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya baki lafiya ko warke gaba Waya ki daina wannan ciwon  .
? ?? Sake dai kallon RK Win Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a ?irjinta da sauri-sauri kamar ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai shiru dan ita kam bata kuma san abin faWaba bayan hakan. ?oyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta buWe idanunta a kansa dan yanda yake magana can ?asa-?asa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko Waya tayi da baki, sai jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turni?e Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai. Rai a Sace ya Wan du?o shima gareta murya can ?asan ma?oshi ya furta,  Kina son cin wani abu Miss? .
? ?? Idanunta ta Wan maida garesa,  Yaya su Didi na zuwa da abinci ai . Ta faWa a hankali dan muryan baya fita sosai. Cikin jinjina mata kansa ya ce,  Na sani, ko Wan fruit haka ba?ya so? Ko wani abu bayan abincin? .
? ??  Zanci apple to, amma green .
??  An gama Baby . Ya faWa cikin raWa ta yanda ita kaWai taji sai RK dake kusa da su sosai. Saurin kauda kanta tayi, sai kuma ta kalla sashen da Ammie da Daddy suke. Ganin hankalinsu na kan su Waleed yasa ta sauke ajiyar zuciya. RK ta Wan kalla, sai taga shima yay wani kicin-kicin da fuska yanata rubutu a file Win ta. Tana ?o?arin janyewa ya Wago nasa idanun sai caraf a nata. Wani miskilin murmushi ya sakar mata tare da sake du?owa kusa da ita gab, cikin raWar shima ya furta,  Apple yana cikin abinda bazaki ci ba a yanzu wife to be, dan haka kada ki ma wahalar da Yayanmu . Ya ?are maganar da kashe mata ido Waya sai kuma ya kalla Yazeed ya sakar masa wani Wan iskan murmushin rainin hankali.
? ? ? ? (Nikam mike damun waWan nan?) Maanal ta faWa a zuciyarta dan tama rasa yanda zata masalta al'amarin nasu. Tana fama da kanta sunzo sun sakata tsakkiya da shirmensu ya ilahil alamin. Shigowar su Shahidah ne ya taimaketa. Cike da farin ciki sukazo suka rungumeta suna hawayen daWin ganinta. Itama farin cikin take ji a ranta matu?a. Nanfa suka shiga nan nan da ita. Sai kawai Daddy da Ammie suka fita tare da su Waleed. Dan ba'aso suyi yawa a Wakin sam. A hakan ma dan RK najin nauyinsu shiyyasa baiyi magana ba. Ganin Yazeed bashi da niyyar fita a Wakin RK ya dubesa cikin danne kishinsa ya furta,  Yauwa babban yaya inama son magana da kai. Dan akwai alluran da za'a mata zuwa 6pm naga kamar babu shi anan ya ?are, ko zaka samo mana shi a pharmacy please? . Yayi maganar ne idanunsa a kan takardun hannunsa yana kuma Wan tafiya, dan haka baka isa gane ainahinsa ba kai tsaye. Bin bayansa Yazeed Win yayi batare da yace komai ba. Maanal ta bisu da kallo ?asa-?asa.
? ?? Da taimakon yayun nata biyu ta Wan ci abincin, nurse Win dake kula da magungunan ta ta shigo ta bata. Babu wani jimawa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Dama haka doctors Win suke bu?ata ta dinga barci isashe dan zuciyarta da brain Winta su samu nutsuwa.........
'?


_>?q?Team RK & Team Yazeed ina mi?o gaisuwar ban girma=? ?=?L?._
? ?

('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......A Sangaren Yazeed da RK kam suna fita Yazeed ya tsaya cak. Kallonsa RK ya juyo yanayi, sai kuma ya saki lalataccen murmushi yana dawowa da baya inda Yazeed Win yake.  A'a babban Yaya yaka tsaya kuma? Ya kamata muje ko .
? ?? Murya a sar?e Yazeed ya amsa masa da,  Rubuta sunan alluran ka bani anan. Sannan ka daina wani kirana Babban yaya dan ban san ala?ar data maidani yayanka ba .
? ? ? Hannu RK ya kai ya shafo bayan ?eyarsa yana murmushi irin na ?an duniya shi a dole irin yaji kunyar nan.  Haba bazan iya kiranka da sunanka ba gaskiya. Ko a bayan ma kafin na fahimci kai Yayan Maanal ne yasa nake kira. Yanzu kam dana sani sam bazan iya hakan ba .
? ? ?  Ni ba yayan Maanal bane kawai mijin da zata aura ne . Yazeed ya faWa a gadarance. Wani irin mugun dukan zuciyar RK furucin yayi, amma sai ya dake cike da basarwa ya furta,  Irin wannan wasan ai saika saka zuciyata ta buga babban yaya, kona Wauka baka son aura min ita ne. Please mubar zancen haka ga sunan allurar .
? ? Yana mi?a masa ?ar takardar da yay rubutun yabar wajen da sauri dan baya bu?atar sake jin wani furuci daga Yazeed Win bayan wanda yaji. Shifa wlhy san Maanal yake. Kuma baya jin zai iya barma Yazeed Win koma mi za'ayi. Sai dai suyi ya?i mai rabo ya Wauka. Babu ruwansa da ?arfin ala?arsu kowa ya iya allonsa kawai ya warke.
Da wani irin kallo Yazeed ya bisa kawai batare da ya sake cewa komai ba shima yabar wajen...

_________&

? ?? Ganin jikin Maanal Alhamdullah Ammie ta matsama Yazeed komawa kan saboginsa. Shima Daddy ta damesa da ro?on ya koma Kaduna kada su shiga hakkin sauran matansa.?Yazeed dai ya jitane kawai. Dan ya ?udura a ransa bafa zai tafi ya bar Maanal a hannun wannan kuren likitan ba RK. Dan haka ?afarsa ?afarta idan ta samu lafiya. Shi kam Daddy sai da sukai ?ar rigima sannan ya yarda zai wuce Kaduna Win, amma kuma dole sai tare da ita, yace nan da kwana biyu ta dawo ta sake dubata tunda dai ga Nene gasu Shahidah. Ita dai Ammie tace hakan yafi mata duk da bata so hakan ba, dan tana son kasancewa da Maanal Win itama amma babu yanda ta iya haka ta ha?ura suka tafi bisa shawarar Nene dan itama tafi son yaje ga sauran matansa kar abin ya zama wani daban kuma. Yazeed dai ya nuna mata akwai aikin da yake anan Win dan gobe ma zaiyi zama da masu Companyn Mawaad ne.. Wucewar Daddy da Ammie kamar ya buWema Yazeed da RK wani filin TAKUN SA?A ne, dan kuwa kowa ya ri?e wuta yana baje kolin hajarsa. Yayinda ita kuma take nuna bama ta fahimci inda suka dosa ba su duka. Tun suna abin a kaikaice har ya fara bayyana kansa sosai, dan takai da Yazeed ya shigo duba Maanal tsalam zakaga RK a Wakin ya shigo kamar wanda aka jeho. A wajen su Amal taji duk yanda akai aka kawota Abuja. Nan ta fahimci RK yaje gidansu ne sai ya kasance a dai-dai lokacin da take a halin taimako. Hakan ya kwaranye mata mamakin ganin nasa anan. Sai dai kasancewarsa likita bai bar bata mamaki ba. Dan har sukai zamansu a Jos suka gama bai taSa nuna musu ga aikinsa ba. Kai ita tama sha yin gulmarsa da jifansa da kalmar mara aikinyi, sannan a tunaninta shi Win Wan Jos Win ne ma ai.
? ? ? Yau Nene ta Wan tashi da ciwon kai, dan haka ta wuce gida dan ta Wan huta. Dama itace ke kwana da ita anan, da safe zuwa goma sai ta wuce gida idan su Amaal sun zo, sukuma suke yini da ita anan har sai dare idan Nenen ta dawo sukuma sai su wuce. Daga Nene har Amal suna a gidan Shahidah ne yanzu, dan bayan wucewar su Ammie sai itama Nene ta koma can gudun karta zauna ita kaWai anan Win duk da ma ?arfin zaman nata a asibitin ne dai. Bayan wucewarta Maanal ta tashi a barci, da taimakon Nurse tai wanka, kafin ta fito an gyara Wakin, tana ?o?arin zama a bakin gado take tambayar Nurse Win,  Nene fa? .
? ? ?? Amsa ta bata da,  Doctor Rafeeq ya kaita gida ta huta kanta na ciwo .
? ? Shiru kawai Maanal tayi, mamakin RK na sake kasheta, gaba Waya fa yabi ya kanainaye mata ?an uwa kowa ya sanshi. Yanzu haka kullum Waleed da Hameed na manne da shi har sai da suka wuce aka samu lafiya. Haka idan su Didi sunzo zaizo ya zauna wai yazo gaishesu duk hararar da take masa baya ma nuna ya gani. Itako yaya zatai da wannan bawan ALLAH. Babu ma abinda ke damunta sai zaman marina da suke tsakaninsa da Yaya Yazeed, hatta gaisuwa sama-sama sukeyinta yanzu ma ta rasa mike damun kawunansu haka.... Shigowarsa Wakin shi da Doctor Ranjet ya katse mata tunaninta, da sauri taja hulanta ta saka tana Sata fuska. ?auke kai RK yay kamar bai ganta ba yama hau duba magungunanta. Shi dai Dr Ranjet matsowa yay kusa da ita yana tsokanarta, haka yake mata dan shi mutum ne mai wasa sosai. Dole ta daure ta Wan masa murmushi dan turancinsa na sata nishaWi, kullum gaya mata yake ita Win mai sa'a ce. Ruhunta nada tauri sosai, saboda da wahala kaga mai irin matsalarta ya shiga irin yanayin data shiga kuma ya tashi ya cigaba da rayuwa, dan shi kansa a randa aka kawota asibitin baimayi tunanin zata kai washe gari a raye ba. Dai-dai Dr Ranjet na ?o?arin mata wata allura da kullum a irin wannan lokacin ake mata RK ya ?araso wajen. Kujera yaja ya zauna yana mai zuba mata ido dan sai Sata fuska take tana kallon allurar. Amma tana juyowa suka haWa ido da shi sai ta Waure fuska ta fiske abinta. Kansa ya kauda kawai yana murmushi baice komai ba. Allurar akai mata, ana gamawa ta kwanta saboda jiri take sakata. Idonta a rufe har fin mintuna biyar Doctor yay mata sauran abinda ya rage har ya fice da kusan mintuna biyar sannan ta iya buWe idanunta da suka kaWa sosai. A kansa ta saukesu, sai kuma ta janye da sauri ganin shima ita yake kallo.
? ? ??  Nifa bana son haka, azo a tasa mutum gaba ai haramunne ma wannan .
? ?? Murmushi ya saki mai faWi yana mai janye idanun nasa daga gareta. Sai kuma ya furzar da huci kaWan a hankali ya furta,  To amin afuwa sarauniya. Sonki ne kawai ke neman zubar dani amma ke kina Waukar komai wasa .
? ? ?? Shiru ta masa bata tanka ba. Shima sai ya bar zancen ya kama wani daban.  Ni kam banga Zizaah da Aneesa ba, ko basu san baki da lafiya bane? .
? ? Kansa ta jinjina masa alamar eh.
?  A gaskiya ya kamata su sani. In sha ALLAHU anjima zan kirasu na sanar musu kuwa .
? ? ??  Ni dai ban saka ba .
?? Idanu ya Wan waro waje.  Saboda mi? .
? ??  Ba saboda komai ba, kawai dan mutum na ciwo sai anta talla da shi. Yanzu miyyasa ka kai Nene gida ma? .
? ??  Saboda taje ta huta. Ba su Didi na zuwa ba .
?? Hararsa ta Wan yi, kafin tace,  To idan kuma ina bu?atar wani abu fa kafin su suzo? .
? ? ?  Ba gani ba sai ki sakani nai miki. Ai shiyyasa nazo nan na zauna a madadin Nenen. FaWi mi kike bu?ata gimbiyar Rafeeq? .
? ?? Baki ta buWe zatai magana tsulum sai ga sallamar Yazeed. Kafin ma su gama amsashi ya riga ya shigo. Kallon kallo sukaima juna shi da RK Win sai kuma kowa ya janye cike da basarwa.?Takowa yazeed Win ya ?arasa yi ta Wayan side Win. Saboda neman magana sai ya zauna a bakin gadon kusa da ?afafun Maanal. A hankali ta matsar da ?afafun nata dake cikin bargo, dan RK ya wani zubama ?afafun nata ido kamar mai kallon television duk da a lulluSe suke a bargon. Cikin dauriya ta gaida Yazeed. Ya amsa mata idanunsa kafe a kanta....
? ? ??  Yaya jikin naki? .
??  Na samu sau?i Yaya. Ya aiki? .
 Alhamdullahi. Tunda kin samu sau?i sai sallama kenan ko? .
? ? ? Maimakon amsa saita sakar masa Wan murmushin ya?e kawai. Abinda ke hannunsa ya mi?a mata.  Ga abinda kikace kina so, shine maimakon ki sanar min kika kama faWama su Shahidah ko? Bana gaya miki duk abinda kike bu?ata yanzu ki sanar min ba. Domin nine da hakkin yimiki shi ai, kwana nawa ya rage mana zama ma'aurata .
? ? ? ? Kanta kawai ta jinjina masa da faWin,  Nagode . Yayinda RK ya saki wani Wan iskan murmushi yana sake yin balance a kujerar. Sai kuma ya wani laSe baki yana kauda kansa. Duk Yazeed na lure da shi, dama kuma yayi furucin domin shi ne.
??  Ina Nene? .
 Taje gida bata jin daWi .
 Ayya ALLAH ya bata lafiya. Ai tana ?o?ari ma ga jikin girma. Su su Shahidah fa? .
? ??  Basu ?araso ba, suna hanya dai sukace .
??  Okay yayi .
Ya faWa yana zaro wayarsa da ake kira. ?agawa yay tare da kaiwa kunne, sai kuma ya mi?e saboda masifar da Mamma ke masa daga can, dan har ita Maanal Win taji furucinta na farko ma. Sassanyar ajiyar zuciya Maanal ta sauke ?asa-?asa dai-dai Yazeed Win na fita. Hakan yasa RK tuntsurewa da wata dariyar wula?anci. Kallonta ta maida garesa cikin mamaki. Shiko ya wani Wage mata gira cike da neman rigima ya ce,  Amma dai kina matu?ar tsoron wannan yayan naki fa. Irin wannan sauke ajiyar zuciya haka .
? ?? ?in kulashi Maanal tayi, sai dai maimaita kalmar tsoron daya ambata tanama Yazeed Win take a zuciyarta. Shima bai sake cewa komai ba ya kawo hannu zai Wauki abinda Yazeed Win ya bata tai saurin Waukewa tana Sata fuska.
? ??  Wai kai idan baka shiga rayuwar mutum ba da abinda ba'a sakaka ba baka jin daWi ne halan? .
? ??  Oh haka kike fassarani ashe? .
??  Hummm .
Kawai tai shiru. A ransa yace miskilatu kenan. Magana fal cikinta amma bata son yi. A fili kam zaiyi magana sai ga Yazeed ya dawo. Bai fasa ba ya cigaba da faWin,  Birthday na ya kusa mi zaki

9 / 80