AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 80

78K to 81K   out of 237.4K words

sannan ta rufe book Win ta Wauki spoon Win. Shine kuma taketa faman juya abincin, ta kuma zuba masa idanu kamar mai irgashi ko tantance abinda aka dafashi da shi. Ita Oum ta fahimci abinda ya saka Maanal Win komawa hakan game da abincin, shiko RK sai ya Wauka ko bata sonshi ne ko kuma dai hankalinta na gida... KaWan yay gyaran murya tare da kiran sunanta. A hankali ta Wago manyan idanunta da kalarsu ta sauya kaWan, a mamakinsa sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi dake narkar da shi. Hakan kuma yayi dai-dai da isowar AA dining area Win, kuma a kanta idanunsa suka fara sauka dan haka yaga murmushin data sakar ma RK Win. Cak ya tsaya kamar wanda akama tsawa. Shiko RK sam baima gansa ba, dan haka ya maidama Maanal Win murmushinta cikin Wan ran?wafowa gareta ta yanda ita kaWai zata ji abinda zai faWa ya furta,  Gimbiya irin wannan murmushi haka ai sai kisa na Sace Sat. Dan ALLAH kici abinci nan fa gidanku ne. Kin san kowa na cikinsa kafin ki sanni ma. Idan kuma ba?ya sonshi a canja miki da wani? .
? ? ??  Oum gani! .
?? AA ya faWa cikin kaushin muryar data fargar da kowa kasancewarsa a wajen. Sai kuma yanda yay maganar da zafi-zafi ya bama RK mamaki dan abune da bai saba gani ba. AA bashi da yawan hayaniya, amma kuma baida faWa. Barshi dai da fushi da ba?ar maganar tsiya kamar jikan banbaWawa. Oum ko data fahimci inda fushin ya dosa sai tayi murmushi kawai da faWin,  Yauwa Autana maza zo ga abinci kada yay sanyi, dan favorite Winka akayi . Tai maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Maanal kam ko Wagowa batai ba balle ma ta kalla inda AA Win yake, kai bama ta nuna tasan da zuwansa wajen ba sam. Hakan kuma sai ya ?ara ba?anta masa rai, koda Oum ta zuba masa abincin ma ya Wau kusan mintuna biyu kafin ya fara ci, sai da ma ta sake masa magana da taSashi.
? ?? Maanal ma dai ta fara tsakurar abincin. Duk da kuma yanda ta share kamar bata san da zuwan AA Win ba tana satar kallonsa ne ta gefen ido. Yayinda RK ke mata magana lokaci-lokaci, sai dai maimakon amsa Wan murmushi kawai take masa da jinjina kanta ko girgizawa. Sai yanzu ne maganar Barrah ta sakata Wagowa, sai idanunta caraf cikin na AA. Wani shegen kallo ya zuba mata data fassara dana tsananin tsana da ?yama. Babu wani yanayi data nuna ko a fuska ta janye nata idanun zuwa kan Barrah Win. Daga haka bata sake yarda ta kalla inda yake ba ma har suka kammala. Itace ta fara barin dining area Win, hakan yasa RK tashi ya bita shima.
? ? ?? Da wani kalar yanayi AA ya lumshe oily ayes Winsa, batare da ya lura ba ya hankaWe glass cup Win ruwan da aka ajiye masa. Tarwatsewar kofin da ruwan cikin saman ?ya?y?yawan farin tils Win ya saka hankalin kowa dawowa wajen. Oum ta mi?e tana mai kamo hannun nasa da sauri ta ce,  Subahanallahi Auta bakaji ciwoba dai ko? .
? ?? Idanunsa dake lumshe har yanzu ya buWe, sai kuma ya girgiza mata kansa batare da yayi magana ba. RK da tuni ya ?araso wajen shima ne yay kiran masu aiki ta landline, kafin ya juyo ga AA Win yana masa sannu. Ko kallonsa AA Win bai yi ba, shima kuma sai bai damu ba. Dan halinsa babu wanda bai sani ba a gidan dama dangi baki Waya. Maanal dai na zaune daga inda take tana kallonsu kawai, amma bata da niyyar tasowa ma. Haka masu aiki suka gyara wajen kamar komai bai faru ba, shima sai ya mi?e.
? ? ? ? Oum ce dake binsa da kallo ta ce,  Abincin fa? .
? ? ?  Oum na ?oshi, zanje na kwanta sai da safe .
? ??  Kwanciya da wuri-wuri haka? Gobe fa babu office .
?? RK ne yay maganar yana binsa da kallo. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaje ?ofa batare da ya juyo ba ya furta,  Anan zaka kwana ne? .
? ? ? ? Kallon agogo RK yay,  No zan wuce dan inada aiki a asibiti ma zuwa nine. Dan har ma sun fara kirana. Zanyi sallama da Maanal kawai .
? ?? A ta?aice ya ce,  Okay yay ficewarsa. Shima RK wajen Maanal ya koma, yayinda Oum tai shiru kawai zuciyarta na mata kaikawo a ?irji. Batare data sani ba ta zubama RK da Maanal idanu. Abubuwa ne da yawa ke cuWa kansu a zuciyarta fiye da yanda take nazarinsu tun Wazun. Sai dai bata da wani abincewa a wanan gaSar gaba Waya....

? ?? & & &

Wanka yake son shiga yayi, sai dai haka kawai ya samu kansa da tsayawa jikin window Win falonsa ya zubama harabar gidan ido ko nace flat Win Oum. Shi kansa bai san ma'anar tsaiwar tashi ba, amma ya cigaba da tsayawar. Hannunsa Waya a aljihu Wayan kuma yana faman Wagosa ya kalla agogo alamar duba mintuna. Mintuna ashirin ya Wauka cif a wajen kafin abinda zuciyarsa ke jiran gani duk da yana faman ?aryata hakan su fito. RK ne gaba Maanal a bayansa, sai dai suna gama fitowa RK Win ya dai-daita tafiyar tasu kafaWa da kafaWa, tare da Wan ran?wafowa gefen Maanal yana magana fuskarsa da wadataccen murmushi hannayensa duk biyu goye a bayansa. Gani yay Maanal Win ta tsaya cak, tare da hararar RK Win, amma shi sai hararar ta juye masa zuwa kallon soyayya ne, musamman daya ga yanda RK Win yay wata irin dariya cike da nishaWi yana kuma maganar da shi sam baya iya jiyowa daga nan. Da ?arfi ya rumtse idanunsa tare da datse laSSansa da ha?ori tamkar zai hudashi. Haka yake idan har abu zai Sata masa rai ko zaiyi magana yanada Wabi'ar rufe idanu.
? ? Kamar wanda aka zabura ya wani irin buWe idanun tare da fara takawa cike da nitsuwa da ?asaitarsa yayo waje. Kai tsaye sashen gaban Oum ya nufa tamkar wanda ake ingizawa, dai-dai nan motar RK ta gama ficewa a gidan, yayinda Maanal dake tsaye har yanzu ta yun?ura zata koma sashen Oum Win tana sauke ajiyar zuciya. Haka kawai yau kuma sai abubuwan RK Win ke mata tasiri a zuciya. Duk da dai tasan a tsakanin nan tabbas bata jin zafinsa kamar sanda suna a Jos.
? ? ?? Da sauri taja da baya tare da tsayawa cak ganin mutum a gabanta gingirin. Sai a lokacin ni'imtaccen ?amshin turarensa ya wani bulala mata cikin hanci saboda yanda iska ta kaWo mata shi sosai. ?an lumshe idanunta dake a cikin gilashi tayi sai kuma ta buWe a lokaci guda tana ?o?arin daidaita kanta. A dakenta, a kuma nutsenta ta Wago manyan idanuntan ta sauke akan ?ya?y?yawar fuskarsa dake a tsuke, sai dai tsukewar tata bai hana kwarjininsa da mutumtaka da gizagonsa bayyana ba. Shima idanun nasa dake cikin fari tas Win eyeglasses Winsa dake matu?ar sake ?awata fuskarsa da gwarzantashi akanta suke. Hakan yasa suka zubama juna ido, kallo irin na tsakkiyar idanun nan. Sai dai sam Maanal bazata iya jurewa ba, dan haka ta janye nata a hankali tare da rissinar da kanta. Cikin sabon yanayinta dake ba?anta masa zuciya da ?ona masa ita ta furta,  Kayi ha?uri sir, ban san kataho bane . Tai maganar ?asa-?asa da ?ar muryarta mai zurfi tana sake jan jikinta baya, tare da raSawa ta gefensa zata zagayesa ta wuce.........
'?




('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* =?%?=???=??? Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya=??=??? Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....=?%?P+P+=?Q? Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram=?
?=?
? P+=?Q? Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau P+=?Q? Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta P+=?Q?royal jelly na fidda shape din mace...=???=???P+=?Q? Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh P+=?Q? Yanasa mace yayi looking under age dinta=???=???=???kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa=?%?=?%? P+=?Q? Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido =?%?P+=?Q? Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly =?%?=?%?P+=?Q?=???
__________


........Babu shiri taja ta tsaya cak, sakamakon jin an cafke tsintsiyar hannunta. Idanunta ta lumshe da ?arfi sosai, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa tamkar zata faso ?irjinta ta fito. Sai dai me wannan Maanal Win ba Little Maanal bace ta shekarun baya. Wannan Maanal ce, Maanal cikakkiya Wiyar Ammien ta. Wadda taga jiya taga yau take kuma fata da ganin gobe. Maanal Win data iya Wauka da shanye abubuwa masu nauyin gaske da ko namiji sai jarumine zai iya zama irinta. Tuni ta saita kanta cikin dakiya da jarumta. Batare da ta juyo ko yin magana ba tai ?o?arin fisgar hannun nata. Sai dai me wannan rikon bana rago bane, ba kuma na sakaran namiji bane. Dan ri?one akai mata irin na manyan sadaukai. Ta fahimci hakan ta yanda koda ta fisgi hannun nata duk da da ?arfi tayi shima bai ko motsa daga yanda yake ba, bai kuma juyo ya kalleta ba balle yin magana.
? ?? Sosai zuciyarta ta fara hasala, hasala irin wadda har take jin Wacinta a ma?oshi. Cikin bayyanar Wacin a harshenta ta furta,  Minene ma'anar hakan da kake yi? .
? ? ? Idan ginin gidan ya tanka shima zai tanka kenan, maimakon yin maganar ma sai fisgarta yay da ?arfi yay sashensa da ita. Tana ?o?arin tirjewa amma hakan bamai yiwuwa bane gareta. A haka ya bugi ?ofar sashen nasa da ?afa tare da tura kai ciki. Da wani kalar salo ya jefa Maanal saman lallausar kujerar falon, kafin tai wani yun?uri ya rufu a kanta ta hanyar Waura ?afarsa Waya a kujerar ya dogare, Wayar na a ?asa.
? ? ? ?? Wani irin matsewa da matu?ar takura Maanal taji da tsaiwar tasa a haka, tuni jarumtar tata ke neman suSucewa, dan yanayin neman tuno mata da babban al'amarin daya shuWe yake a rayuwarsu ta baya amma tana fisgo dakiyarta da tsiya-tsiya. Komai ta haWiye daga fuskarta da harshenta idanunta a rissine dan bazata iya kallonsa ba ta furta,  Sir minene kake yi haka ne?......
? ? ?  Oh you're still pretending? .
?? Ya faWa cikin wani irin kaushi da Wacin murya mai razanarwa. Dan ita kanta Maanal Win sai da taji kayan cikinta sun kaWa. Amma da yake itama yanzu gwanarce. Ta karantu daga kowanne irin salo da taku sai ta zuba masa idanunta, wani shegen murmushi mai saka yin kamar zaka lumshe idanu ta sakar masa. A nutsenta tana mai sake tsatstsaresa da idanu ta ce,  Pretending?! Dan mi zanyi pretending? Akan me kuma? YallaSai .
? ? ? Wani kalar taune laSSansa yay da rufe idanu yana dun?ule hannunsa. Kamar zai kai mata duka sai kuma miya tuna ya fasa. A maimakon hakan sai ya nunata da yatsansa manuniya.
? ? ??  Na fiki zafin kai .
? ? Yanda yay furucin yana wani wara mata manyan oily fararen ayes Winsa masu girma da cikar gashi dake cikin gilashi sai ta sake jin tsoro na mamayeta. Amma dai tai ?o?arin sake dakewa yanzu ma ta taSe bakinta ta dauke kanta kawai. Cikin ?un?uni ta ce,  Ina ruwana to da zafin kan naka . Hannu ya kai zai cafko fuskar tata, a zabure ta matsar da jikinta tayi ta gefen daya ajiye ?afarsa, dan gaba Waya ji take kamar an sakata a wani kurkuku dama. Hatta da iska bata sha?a yanda ya kamata saboda kusancin nasu. Haka ta mi?e ta nufi hanyar fita cikin sassarfa. Wani irin juyowa yay tare da sanya mata ?afa sai gata a saman kujerar ta sake zubewa.
? ? Hannayensa duka ya zuba a cikin aljihun wandonsa yay wani irin tsaya mata bisa kai ya zuba mata idanun sa tamkar zai haWiyeta da su.  Ni kike ma ?un?uni? .
? ? ?? Baki ta Wan tura gaba, sai kuma ta kauda kai gefe,  Ni yaushe na maka ?un?uni? .
? ? ? ?wafa yayi cike da sake ?uluwa, cikin kakkausan lafazin da bata san ya iya ba ya furta,  Na baki nan da kwanaki uku kacal ki fito ki faWama Rafeeq gaskiya. Idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki .
? ? ? A karo na farko ta zuba masa wani irin kallo tana mi?ewa akan ?afafunta, a gabansa ta tsaya sunama juna kallon ido cikin ido, cikin kausasa masa harshen itama ta ce,  Oh mamaki? Ai ba yau na fara shan mamaki daga gareka ba daman. Gaskiya kuma bismillah ai ban hanaka sanar masaba kai, maza sanar masa kafin iska ta rigaka. Ina dai iyaka yace ya janye daga aurena ko, sai me? Nace sai me idan yayi hakan? Ko hakan sabon abu ne daga cikin rayuwata balle ya daman. Ba shi kaWai ne namiji ba, dubu bayansa biye suke dani kuma in har na basu dama tamkar ?yaftawar ido zasu amsa da rawar jiki har suna shelantama duniya samuna cike da murna da farin ciki. Balle nayi imanin ko ?a?a goma na haifa a duniya Rafeeq zai amsheni ni da su da hannu biyu ya godema ALLAH saboda soyayyar da yake min ta dabance, SO na yake, tsananin SO da wani mahaluki baitaSa min kwatankwancinsa ba a wannan duniyar.....
? ? ?  ?arya kike yi!!! I said you are lying!!!!! .
? ?? Ya faWa cikin wani irin ?araji idanunsa da suka kaWa jazur na firfitowa tamkar zai mareta. Matu?ar tsorata tayi, dan ta gama yarda marin nata zai yi kawai, sai da taji shiru sannan ta buWe idanunta data rumtse. Suma sun kaWa sunyi jazur kamar nashi. Cikin dakiya da sake tsatstsaresa da idanun ta ce,  Kai ka Wauka ?aryar ne, amma ni da yake nunama soyayyar zan bada labari. Zan kuma tabbatar maka da hakan nan da ?an?anin lokaci. Wata Waya kacal zuwa biyu zan zama MATARSA, MALLAKINSA ta har ABADA in sha ALLAHU . Ta raSashi tai wucewarta fuuuu.
? ? ? ? Baiyi wani yun?urin dakatar da ita ba a yanzu, dan bai ma motsa daga yanda yake tsayen ba harta gama ficewa. Sai lokacin yay wani irin kai hannu ya hankaWar da flower base Win dake ata bayan kujerar mai tsananin ?yau da ?ayatarwa. Jikake tatsatsa ya tarwatse a ?asa komai ya zama pieces.
? ? ??  I will teach you lesson .
?? Ya faWa da tsananin kaushin murya dake bayyana dukkan fushinsa. Daga haka ya juya zuwa cikin bedroom Winsa. Kayan jikinsa ya fara zarewa kawai yana wulli da su, kafin ya wuce cikin closet Winsa ya ratsa ya shige bathroom. ?aton gaske ne shima. An kuma tsarashi da kayayyakin toilet masu ?awa tamkar ba banWaki ba. ?ar?ashin shower yaje kawai ya buWe duka ukun ruwa suka fara saukar masa a jiki shaaaaa!! Tamkar irin ruwan samar nan mai zuwa babu zato. Hannayensa kawai ya dafe a jikin glass Win da aka zagaye wajen wankan da shi ruwan na cigaba da saukar masa. Yafi mintuna talatin a haka dan har numfashinsa ya fara fisga alamar ruwan ya masa yawa sannan ya kashe, a haka ya cigaba da tsaiwar ruwan daya saukar masa na kwararewa musamman na cikin sumarsa dake lashe kuWaWe da shi kansa bai san adadi ba. Ada shi ba ma'abocin tara suma bane, amma wasu dalilai suka sakashi fara tarawar harta zama Wabi'arsa. Ba tara sumar kawai ba, abubuwa da yawa ya Wabi'antu da su ne daga baya bisa wasu dalilai. Kuma a yanzu sun zama halittarsa kuma jinin jikinsa da shi kansa bai taSa tunanin raba kansa da su Win ba...
? ? ?? Ya jima a hakan, dan sai da zuciyarsa ta koma ta kwanta cikin ?irjinsa luf kafin yayi wanka kamar yanda ya saba da brush ya fito, idanun nan sunyi matu?ar juyewa da komawa jajaye. Gaban mirror ya tsaya yana goge jikinsa, kafin ya shafa mansa mara hayaniya ya feshe jikinsa da sprys Winsa masu ?amshin tsiya da saka zuciya nutsuwa. Ya kuma gyara kansa da kwantaccen gashin dake lafe a kumatunsa, ya sama bakinsa ?amshi. Tausasan kayan barci farare tas ya sanya, ya sake feshe jikinsa da turarurrukansa na barci tamkar ba kwanciya zaiyi ba sannan ya nufi katafaren bed Winsa dake a wani kalar dun?ule waje guda tamkar zero. Zama yay ya jingina da gadon tare da kai hannu ya rage fitulun Wakin ya maida mai duhun haske sai bed side lamp kawai dake kunne itama ta gefensa. Sai da yaja lallausan duvet Winsa ya rufe ?afafunsa zuwa ?ugu sannan ya Wauki eyeglasses Winsa dake ajiye kusa da novel Winsa dake a bed side drawer Win ya saka, novel Win shima ya Wauka. Alamar daya saka a inda ya tsaya ya sashi buWewa kai tsaye ya fara karatu cike da son kauda komai dake cinkushe da zuciyarsa.....

? ? ___________&

? ? ? ? Kamar yanda ta saba damunsa a kowanne dare da sakwanni yau ma tsaf ta kammala shirin barcinta ta faWa saman gado. Jinta take wani free yau ita kaWai a Waki babu Maanal. Sai hakan ke sakata nishaWi tun Wazun. Yayinda tuni ta kaima uwarta gulmar fitar Maanal Win da saurayi da

27 / 80