AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 80

12K to 15K   out of 237.4K words

yasa ta kasa magana. Dole ta buWe motar ta fita dan shi in baiso wasa ba dole kaji shakkarsa. Bai bar wajen ba har saida yaga ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da jingina jikinsa da kujera yana mai lumshe idanunsa. Ya jima a hakan dan yaci kusan mintuna biyar kafin ya tada motar yabar wajen yana mai danne abinda ke tsikarar zuciyarsa game da ita.....

? ? ? &&&

? ? Yanda Maanal ta samu tarba a ciki zai tabbatar maka akwai sha?uwa da sanayya sosai tsakaninta da mai gyaran. Dan duk miskilancintan nan sai murmushi take da Wan maidama mai gyaran hiranta dan tana mata tambaya ne akan Jos. Basu wani jima ba aka fara gyaran saboda tun jiya ta sanar mata. Kafin tazo ta haWa komai. Gyara sosai jikinta ya sha. Ga turarruka kamar wata amarya. Hatta kanta da ?afafunta zuwa farce an musu ?al. Haka Maanal take akwai son gyara jiki, ?ar gayuce sosai da son kwalliya, sai dai yanzu yanayi yasata Sarar da kwalliyar gefe gyaran jikinta da tsafta ne dai tana nan da abinta akoda yaushe. Sun gama a ?urarren lokaci, dan har Ammie na kiranta a waya ma. A gurguje ta bata ta cire kuWin aikinta tare da amso kayan ?amshin data haWa mata suka fito zata mata rakkiya. Turus taja ta tsaya da ganin motar Yaya Yazeed a ?ofar gidan, kafin ma ta samu abin faWa ya buWe mata gefensa alamar ta shigo. Ganin fuskarsa babu wasa sam yasa batai magana ba ta shiga kawai. Sallama sukai da mai gyaran bayan ta gaida shi ya amsa mata ciki-ciki yaja motar suka wuce. Shiru motar har sun Wan yi nisa a tafiyar cikin ?arfin hali ta ce,  Yaya dama baka wuceba ne? .
? ? ??  Mi kika gani? .
?? Ya faWa cikin wata irin kasalliyar murya data bata mamaki. Gashi ya?i kallonta sam a yanzu. Itama sai kawai ta ce,  Ba komai .
? ? ? Bai sake magana ba, itama tai shiru har suka iso gida. Sai da ya gama parking ta mi?a masa atm Win tana godiya. Kansa kawai ya Waga mata batare daya kalleta ba ko tankawa yanzu ma. Itama sai kawai ta buWe motar tai ficewarta. Da Hajiya Yaya dake daga can ?ofar sashensu da wata ba?uwa suka haWa ido, ganin irin kallon da suke mata yasa duk ta tsargu, amma sai ta dake ta nufesu badan taso ba, sai dan mahaifiyarta ta mata tarbiyya na girmama duk wanda ke gaba da ita. Sannan kodan Yaya Yazeed dake iya ?o?arin sa na girmama Ammie zata iya shanye komai daga mahaifiyarsa itama.
? ? ?  Tofa, kice agola kafi Wan masu gida an dawo kenan? .
? ? Matar da suke tare da Hajiya Yayan ta faWa cikin yamutse fuska idonta akan Maanal dai-dai tana isowa inda suke. Wani harbawa zuciyarta tayi har tsakkiyar kanta. Ba wai yau ne karo na farko da aka fara kiranta da sunan AGOLA gidan ba, amma har yanzu ta gagara sabawa. A duk sanda aka kirata da shi kuma tana jin matu?ar Waci da zafi a ranta. Har takanyi yunkurin son barin gidan, sai dai yin?urin nata baya zuwa ko'ina take komawa tai la?was saboda wasu dalilai. Hawayen da suka cika mata idanu ta haWiye, tare da dai-daita kanta sannan ta Wan risina fuskarta da murmushi ta ce,  Barka da gida Mamma. Aunty ina yini .
? ? ? ? Kafin Hajiya Yaya ta amsa wadda ta kira da aunty Win ta sauri ta cafe zancen cikin masifa,  Oh kaji wani Wan iskan gaisuwa wai barka da gida sai kace wasu sa'oinki? .
? ? ?Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce,  Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba, Amma wai a haka Alhaji ke neman ?a?abama jinina ita .
? ??  Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed Win zasu barsa ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba Waya . ta faWa tana mai ballama Maanal wata shegiyar harara.
? ? Tsamm Maanal ta mi?e kafin Hajiya Yaya ta bama ?anwar tata amsa. Cikin Wan sassarfa tabar wajen tana mai jin Waci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare musu a gidan da su duka basa ?aunarta...?

? ? ?? Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar ?arfi. Kai bazai yiwu ba, dolene ya zigirgiWi Daddy azo ayita ta ?are a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali, da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma ya?i komawa Wakkota. ?an buga glass Win saitinsa da akai da Wan ?arfi ya sashi Wagowa. Sai da ya Wan saisaita kansa kafin ya sauke glass Win. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin kaWawar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce,  Yazeed miye haWinka da waccan yarinyar? A ina ka Wakkota? .
? ? ? ?an gyaran muryarsa data koma can ?asa yayi, kafin ya furta,  Mamma anan ?ofar gida ne mai napep ya ajiyeta shine nace ta shigo na ?araso ciki da ita. Wani abu ne ya faru? .
? ? ? ? Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta,  Yazeed! Yazeed wlhy ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko....
? ??  No Mamma ba hak....
Hannu ta Waga masa cikin tsawa,  Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan . Tana gama faWa ta juya ta bar wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya buWe motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin Soye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ?ar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa dake wani binsa da kallon ?urilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa gaisuwarsa ba ta ce,  Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu ?an uwanta a gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi? .
? ? ? Sai da ya Wan haWiye abinda ke masa yawo a ma?oshi sannan ya furta,  Aunty Please mun wuce maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai .
? ??  An?i a bari Win dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana sha ba?ar wahalar rainon ciki ka da na?udar haihuwarka da shayar da kai. Asiya dai ta fini muhimmanci a wajenka ko? Shike nan kaje kayi duk abinda kake ganin dai-dai ne agareka. Amma ka sani ko mutuwa nayi kurwata bazata barka zaman aure da yarinyar can ba. Dan na riga na maka mata kamar yanda na faWa maka. Garama ka shirya tun kafin takaimu da bakanta a cikin gidan nan. Amma bari shi Alhajin dake Waure maka ?ugu ya dawo gidan ina dai-dai dashi wlhy .
? ?? Kasa iya furta komai Yazeed yayi, sai wani irin haWiyar zuciya yake acan ?asan ransa dan mutum ne mai zuciyar tsiya dama. Haka suka cigaba da masa masifa bai iya sake cemusu komai ba har sai da ALLAH ya taimakesa Daddy yay kiran wayarsa sannan ya tashi ya fita domin amsawa. Daga haka bai koma wajen su ba ya gudu sashensa dan ya shirya gashi har yana neman makara....

? ? ________

? A Sangaren Manaal bata sanarma Ammie komai ba. Sai ma ?an uwanta ne da suka zagayeta suna yaba irin ?yawun da gyaran yay mata. Daga haka Ammie ta korata dan ta shirya kada su makara. Saboda tasanta da nauyin shiri. Aiko bata kammala shirin ba sai da Ammie tai mata tsiya-tsiya. FaWan Ammien yasa ta fito Wauko da Wan box Win da take ajiye kayan ?an kunne da makamantansu ciki a hannu tana neman agogon da zata saka da zobe. Su Amal ne dake musu dariya suka amsa suna duba mata. Dai-dai fitowar Ammie tana faWin,  K muje ai ba dole sai kinsa wani agogo can ba bana son shiririta .
? ? ?? Jin hakan ya sata mi?ewa dan tasan kaWan daga aikin Ammien ta maketa ma saboda bata ?aunar jira, da sauri Shahidah da takamo hannunta ta Waura mata wanda ta zaro kalar silba kawai ta shiga Waura mata batare da su duka sun maida hankali akansa ba. Daga haka suka fice hannunta ri?e da ?ar bag Winta sai gwangwanin maltina data Wauka saboda yunwan da take ji kasancewar bawani break Win kirki tayi ba ta fita gyaran jikin, yanzu kuma Ammie tace bazata zauna cin abinci ba aiba itace ta hanata ci Wazun ba sai dai ta bari idan sunje gidan bikin taci. Itako tasan bazata taSa iyawa ba cin abinci a gidan biki koda na wanda ta sani ne balle wannan, duk da kamar gidane can Win ma saboda ala?ar dake tsakanin mai gidan da uban amaryar mai matu?ar ?arfi ce, ta wani gefen ma za'a iya cewa akwai zuminci. Koda yake su sai dai suyi kara saboda Ammie kawai amatsayinsu na ?a?anta...........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


Lady's collection and more

Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko

08169307477

Address bayan gidan drugs katsina State. Kayanmu nada inganci da zasu birge mai saye fiye da yanda yake zato. Maza ku garzayo kada ayi babu ku.

_______________


.........Tunda suka fito ya zuba mata ido daga inda yake tsaye jikin mota. Itakam sam bata lura da shi ba tana ta? ?o?arin gyara kayan data zubo a handbag Winta data?i rufuwa. Sai da suka iso gab da shi ta tsinkayi muryarsa yana gaida Ammie. Yayinda Amrah ta taSota itama tana gaida Ammien. ?agowa tai ta dubi Amrah Win, suka sakarma juna murmushi, harta maida kanta sai kuma ta Wan Wago dan sai yanzu hankalinta ya kai garesa sosai. A take ta shanye murmushin saman fuskarta ziciyarta na takurewa waje Waya a ?irjinta. Tabbas da tasan tafiyar nan tare zata kasance musu ALLAH duk yanda zatai da sai tayi ta zame kanta a masu yinta. Amma yanzu babu yanda ta iya dole ta dake. Ganin su Ammie sun shige itama ta fara ?o?arin shiga kusa da su amma sai Amrah tai saurin rufe murfin tana faWin,  Kije wajen Yaya mana gashi can ya buWe miki .
? ? ? Tsaye tai kawai tama gagara cewa komai, koda ta saci kallon Ammie sai taga ta Wan harareta, dole ta shiga kusa da shi Win tana faman sauke ajiyar zuciya. ?an karkatowa yay inda take kaWan kamar zai Wauka abu a ?asan ?afafunsu. Cikin raWa ya furta,  You look so good dear . Kasa cemasa komai tayi, sai ma takurewa data Wanyi jikin kujerar, yayinda shi kuma ya Waga yana gyara zamansa tamkar bashi yay maganar ba dan fuskarsa sam babu wani walwalan kirki.
? ? ? Sun fara tafiya shiru motar babu mai magana. Sai da suna gab da barin titin anguwar gaba Waya kamar ance ta kalla hannunta idanunta suka sauka akan agogon da Didi Shahidah ta Waura mata. Ba ?aramin bugawa ?irjinta yay ba har kana iya ganin yanda ma?oshinta ke kaiwa da komawa a wuyanta. Ta ?urama agogon ido wani abu mai shegen nauyi na sake saukar mata a dukkan illahirin jikinta. Bata masan wani ?arfi yazo mata ba tasa Wayan hannunta ta fincike agogon, kamar zatai wurgi da shi waje sai kuma ta daure ta Salle bag Winta ta jefashi ciki batare data zuge zip Win ba ta maida kanta ta nannaWe cikin ?afafunta data Wage gaba Waya zuwa saman kujerar. A take wasu hawaye masu zafin gaske da raWaWi suka fara zirara mata. Yanda tayi Win sai sukai tunanin ko barci take, musamman Ammie da tasan bawani barcin kirki ta samu ba a safiyar yau dama daren. Shima Yazeed daya Wauka barcin tayi sai kawai ya farama Ammie hira. A haka har suka iso Zaria kasancewar tafiyar ba wata mai yawa bace ba. Da yake Yazeed yasan hanya basu wani sha wahala ba nan ma suka iso. Sun sami anguwar kanta da mutane sosai balle ?ofar gidan daya kasance masha ALLAH dan har Ammie na faWin,  Anya Yazeed zamu iya keta mutanen nan zuwa cikin gidan kuwa? .
? ?? Amsa ya bata da faWin,  Ammie zaku iya shiyyasa ma nai parking tanan ganin yafi ?arancin mutane. Zan bidaku ta baya ne akwai wata ?ofa dana sani Uncle na amfani da ita nasan zata kasance buWe yau kodan ba?insa .
? ? ? ? Cikin gamsuwa Ammie ta ce,  To Alhamdullah hakan ma yayi .
? Sun firfito yayinda a kallo Waya Ammie ta fahimci Manaal tayi kuka duk da gilashin dake a idonta. Sai dai ta fassara kukan nata da zaman gaba da aka sakata yi ne dole. Dan haka ta watsar da ita tama haWe fuska. A wannan yanayin suka shiga gidan ta inda Yazeed Win ya faWa. Aiko sai suka samu sau?i jama'a anan sai falon Uncle Win ne ma da mutane dan akwai takalma kusan ?afa bakwai a wajen masu ?yau. Wucewarsu sukai zuwa cikin gida dan itama Ammien ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hakama Amrah. Maanal ce dai bata taSa zuwa ba dama sai yau Win. Amma ta Wan san yaran gidan saboda suna zuwa can gidan nasu lokaci-lokaci...

? ? &-----------

Babu jimawa da shigewar su Maanal tawagar ango da abokansa suka iso ?ofar gidan. Cikin tsari da nutsuwa tarin motocinsu suka layantu dai-dai inda Yaya Yazeed yay parking motarsa. Firfitowa duk suka shiga yi, kowa ka kalla shar da shi cikin dakakken yadi mai shegen ?yau da tsada, wasu kuma shaddoji. Sai shima ango dake sanye da shadda fara ?al tanata mai?o da Waukar idanu. Sun gama firfitowa sai motar dake kusa data Yazeed ce kawai wanda ke ciki baida alamar fitowar, sai da angon ya juya yana Wan kalle-kalle da faWin,  Wai Uncle fa? .
? ? ? ? Duk motar suka kalla. Kafin wani a cikin abokan yace,  Bai kai ga fitowa ba kamar ma suna magana ne da Uncle Nass .
? ??  Oh ai fa an haWu. Ni dai suyi su fito kar a fara neman waliyyai aga duk basa kusa. Bara ma na taSa su Uncle Fawzan suma .
?? Dariya abokan nasa suka sanya masa da sha?iyanci. Yayinda yay gefe yana dariya. Wanda dai ya ambata da Uncles basu fito a motar ba sai kusan bayan mintuna talatin, suma Win dai ba tsoffi bane, matasane da shekarunsu ya haura talatin kaWan, Waya ma zai iya girman Wayan. Wanda bai kai shekarun ba dake sanye cikin yadi milk ne ya fito ta sashen da motar Yazeed take. ?an jingina yay da motar yana amsa waya kansa a sunkuye ta yanda ko fuskarsa ba'a wani gani da ?yau. Yaci fin mintuna biyu a haka kafin ya katse wayar yana mai kai wa du?e ya Wauki abinda idonsa ya sauka a kai tun fitowarsa dake yashe a ?asa. Agogo ne silver na mata mai ?yau sosai, juyawa yay ya kalla motar daya jingina batare da yayima agogon wani kallon tsaf ba. Har ya kai hannu zai aza agogon saman motar da tunanin maybe masu motar ne suka yadda sai kuma ya fasa. Tunanin ajiyewa yay a hannunsa dan maybe su haWu da masu motar sai ya basu, kada ya ajiye kuma wani ya Wauka dan a Wan kallon fisha da yay ma agogon ya fahimci mai daraja ne da za'a iya sayensa da kuWi masu yawa. Motar da suka fito ya buWe ya jefa agogon sit Win mai zaman banza daya zauna dan Wayan ne yayo driving Win.? Daga haka ya juya abinsa kawai....

? ? ______________&

?? Duk da yawan taron jama'a bai hana ai musu tarba ta musamman ba da girmamawa da mutuntawa. Dan can ?uryar Wakin amaryar gidan aka kaisu tare da musu sauka ta musamman da abinci da kayan ciye-ciye irin na biki. Sai nan nan Hajiya Majdiya keyi da Ammie dan tuntuni take son su jone su zama ?awaye Ammien ce dai bata maida hankali ba. Ita kuma ba komai yasa hakan ba sai sanin uwargidanta jone suke da Hajiya Yaya 5&6, ko bikin nan ma dan na yarinyar matar tsakkiya ce shiyyasa Hajiya Yayan bata zo ba saboda suna matu?ar adawa da juna. Ita kuma aminiyar Hajiya Basariyya ce dan ita tun sassafe ma tana nan Zaria Win da duka yaranta kuma kwana zasuyi dan har Abuja inda za'akai amarya zasuje ma.
? ? ? ? ?orafin da take tayi yasa Ammie bama su Maanal umarnin cin abincin. Amrah ce ta zuba ma Ammie sannan ta zuba musu. Maanal na cewa ta ?oshi Hajiya Majdiya tace,  Haba Wiyata kada kimin haka mana, idan kuma ba?ya sonshi na canjo miki wani ko na dafo miki yanzun nan .
? ?? Da sauri ta Wauki spoon ta saka cikin abincin, hakan ya saka Amra kwashewa da dariya. Sunci abincin Ammie da Hajiya Majdiya na hira sai ga wata budurwar yarinya ta shigo Wakin. Zasu iya zama sa'anni dasu Maanal, tayi ?yau cikin lass da nake ?yautata zaton ankonsu kenan dan ?ammata da yawa na dashi a wajen bikin. Tafawa suka Wan yi da

5 / 80