AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   36 / 80

105K to 108K   out of 237.4K words

mata batun ?arin aurensa, a Sangarenta mace ce mara ha?uri da iya shanye abu, dan haka tun a daren sukaci uwar watsi ?arshe kowa a part Winsa yay barci. Dan ya tabbatar mata akan Maanal fa zai iya saita mata hanya ne shi ba damuwarsa bane. Dole taja bakinta ta kulle dan tasan kaWan daga abinda zai iya aikatawar kuwa.....

? ?? _Ikon ALLAH miya faru a Giro>?q? to?._

_____________&

? ? ?? Yanayin da take jin jikinta Alhmdllh yasa ta ce Shahidah taje gida kawai ta huta yau zata kwana da nurse. Da har Shahidah Win ta?i Dr Ranjet yace karta damu taje Win. Dama asibitin bawai suna barin masu jiyya bane ba ai kawai dai sune oga ke bari. Zuwa yanzu Shahidah ta fahimci asibitin nan mallakin RK ne. Duk da yanata dojewa bai son su sani. Dan haka koda Dr Ranjet ya ce ogan ta fahimci RK Win yake nufi.
? ? ? ? Mijinta ne yazo ya Wauketa, basu tafi ba sai da ta tabbatar ta mata duk abinda take bu?ata duk da jikin nata Alhmdllh sannan. Bayan tafiyar tasu Maanal Win na zaune tana karatun novel Win data Wauka na AA ranar a office Winsa, dan yau ta matsama Shahidah ta kawo mata shi asibitin tare da glass Winta. Sosai take zumuWin karatun book Win saboda labarinsa da aka bata. Tayi matu?ar zurfi a karatun dan tana jin daWinsa, bata damu da shigewar lokaci ba dan kusan 11 ma da rabi. Sai can ?asan zuciyarta dake Wan kawo mata tunanin ina RK, rabonta da shi tun safe da ya shigo ya dubata a gaggauce ya fice. Tana son tambaya tana tsoron kar Didi tai mata wata fassara daban dan haka taja bakinta tayi shiru. Sai dai lokaci-lokaci yana zuwa mata a rai.
? ? ? KaWan-kaWan wani irin daddaWan ?amshin turare ke shigo mata hanci, tun tana fuskewa da cigaba da karatunta har dai yanda turaren ke sake ?arfi a Wakin ya addabeta. Cikin nutsuwarta da rashin rawar kai ta Wago idanunta kaWan tana bin Wakin da kallo, dai-dai saukarsu inda ?ofa take ?irjinta yay wani irin motsawa alamar zuciyarta tayi zallo. Sosai ta zuba masa ido tana masa kallo irin na? mamaki ko ruWani zamuce oho. Sai dai fuskarta a dake babu alamar wani shock a kanta. Sai ma janye idanun tai a slowly ta maida ga littafin kamar bataga komai ba.
? ? ? ?? Gently shima ya lumshe nasa oily idanun da ke a Wan kumbure kaWan da kuma Wan sirkin ja a cikinsu dan har yanzu basu komai dai-dai ba saboda ciwon kai ya?i barinsa. Sai dai da Wan haskensu fiye da jiya da yake a halin ciwo sosai. Sake buWesu yay a kanta yana mata wani irin kallo mai wahalar fassara. Fin mintuna biyar suna a haka baka jin komai a Wakin sai sanyin ac da aka saka mata kaWan daya gauraya da ?amshin mayataccen turarensa mai kashe garkuwar jiki. Gaba Waya kallon ya gundiri Maanal, dan jinsa take har cikin Sargon jikinta da magudanan jini. Tuni ta daina karatun kallon rubutun kawai take, sai dai fuskarta ta sake tsukewa.
? ? ? ? ? A cike da ?asaita ya mi?e daga jinginar da yay a jikin ?ofar hannayensa duka zube cikin aljihun farin jeans Win sa, daga sama ma ba?ar rigace mai hi neck data Wame masa murWaWWan jikinsa, sai dai ya kawo jacket mai ?yau ba?a da adon fari kaWan a jikinta ya Waura. Kasancewar zip Win gabanta a buWe yake har ?asa ne ya bayyana rigar cikin da faffaWan ?irjinsa zuwa lafaffen cikinsa. Yanda yake takowa takalman ?afarsa masu ?yau da Waukar hankali na bada ?ara haka zuciyarta ke motsawa a ?irjinta da ?arfi. Cike da izza ya tura kujerar gaban gadon gab da gadon sosai da ?afa, kafin ya matsa gab da gadon har Maanal najin tamkar zai faWo mata akai sannan ya kai zaune. Yanda ya Wan rankwafo a kanta sanda zai kai zaunen yasa hucin numfashinsa dakar fuskarta, yayinda ?amshinsa ya gama mamaye illahirin iskar da take sha?a. Dole ta ambaci sunan ALLAH a zuciyarta.
? ?? Anan Win ma zaman ?asaitar yayi, dan ya wani harWe ?afafu Waya kan Waya tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar hannayensa duk biyu dafe da hannuwan kujerar. A har yanzu Win ma idanun nasa na'a kanta ne sai faman lumshesu yake da buWewa daga cikin fari tas Win gilashinsa dake sake ?awata masa fuska. Rumtse idanu Maanal tayi tana mai danne dukkan abinda ke yun?uro mata. Batare data sake ko kallon sashen da yake ba a kausashe, a kuma tsiwace ta furta,  What are you looking for here? .
? ? ? ? Maimakon bata amsar data bu?ata sai kawai ya zuba ma lips Winta idanunsa har adams apple Winsa na Wan motsawa a ma?oshinsa. Wani irin takaici ne ya sake ratsa Maanal. Tai wani irin juyowa da rinannun idanunta da suka juye lokaci guda ta saukesu a kansa. Slowly shima yaja nashi dake kallon lips Winta ya daidaitasu a cikin natan. Kallon cikin tsakkiyar idanu sukema juna. A hankali a hankali na Maanal suka fara ?yalli alamar taruwar hawaye. Wani Wan iskan murmushin gefen baki ya saki yana sassauta girman idanunsa dake cikin nata. Tamkar wanda akama dole ya motsa lips da Muryar nan nasa can ?asa-?asa kamar abin dole ya furta,  Because you need me .
? ? ??  Never! Har abada kai baka cikin abinda rayuwata take bu?ata Ajwaad .
? ? ?? Wani Wan killer Smile ya saki yana mai janye idanunsa gefe, fin sakan biyar sannan ya sake juyo da idanun nasa a kanta.  Really! You don't need me in your life? .
? ??  Kana tantamar hakan ne? .
? Ta faWa a zafafe.
 Sosai ma kuwa? Inda har ba?ya bu?atata in you life kuma da baki cigaba da ajiye wannan ba . Ya ?are maganar yana buWe tafin hannunsa wani sliver agogo ya bayyana. Kallon agogon take zuciyarta na bugawa da ?arfi a cikin ?irjinta, agogonta ne fa, agogon da ta saka a randa zasuje Zaria ita da Ammie da Yaya Yazeed da Amrah. Tabbas tasan ta ciresa a hannunta, daga haka bata sake tuna ina yake ba. Kai hankalinta ma sam bai kai garesa ba sakamakon haWuwa da RK da tai acan ya harmutso ta.....
? ? ?  Hyy .
?? Ya katse mata tunani cike da son tunzurata. Harararsa kuwa tayi ta Wauke kanta gefe batare da ta ce komai ba. Murmushin sake samun nasara ya saki kaWan yana wani ?an?ance idanunsa a kanta.
? ? ? ? ?  Wannan pretending Win naki ya isa haka. K Bestyn AA ce har yanzu, ko ki yarda ko karki yarda idanunki na nuna hakan ga kowa......
? ?? Wani irin wurgar da littafin hannunta tayi, a bazata kawai ta ganta a gabansa ta dirgo daga gadon. Wani irin lumshe idanu yay ya sake buWewa sakamakon shigar ?amshinta mai daWi cikin hancinsa. So yana matu?ar son traditional perfumes, zai iya cewa ma itace ta koya masa amfani da su ita da Oum..........
'?






('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


........Akan ?yawawan ?afafunta da ?umbunan ke a gyare fes-fes suna ?yalli ya saukesu. Kafin ya tafi da kallonsa har saman ba?in wandon data saka irin mai manne jikin nan, yana gab da gwiwarta rigar asibitin ta bayyana, itace har zuwa sama fara da Wigo-Wigon jaa, tsabar neman magana da salon iskanci ya wani sauke a saman ?irjinta ya kafe wajen da ido tare da Wan datse lips Winsa. Da sauri ta koma saman gadon taja bargo ta lulluSe jikinta gaba Waya tana furta,  ALLAH ya isa wlhy da mun kallon da musulunci ya haramta .
? ? ? Murmushi yay mai fidda Wan sauti sai dai sam ha?waransa basu bayyana ba. Sai kuma ya taSe bakinsa cikin halin ko in kula ya furta,  Daga baya kenan. Idan kin manta bari na tuna miki na san komai A to Z tun kan ki zama abin kallo. Ko kin manta wannan hannun ya miki wanka, ya wanke miki pupu, ya share miki majina, ya wanke miki pants, ya wanke miki blood na period. Ya.....
? ??  That's enough malam. Kuma ka bar Wakin nan tun kafin na maka ihu wlhy.
? ? ? Murmushi ya sake yi yana taSe baki da wani Wan Wage gira. Babu alamar zai ma motsa balle yayi abinda tace Win. Saima cikin tsareta da idanunsa da suka kaWe ga jijiyoyin kansa duk sun sake fitowa. Muryarsa can ?asa ya ce,  Ke baki gajiya da faWa? Why are you being stubborn ne? .
? ? ? Harara ta balla masa da faWin,  Anyi faWan da taurin kan, in baka????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? son a maka ka fita rayuwata mana .
Sai da ya Wan lumshe idanu ya buWe akanta. Yanda yake mata wani shegen kallo tamkar idanunsa zasu narke a kanta ya saka tsigar jikinta tashi, kauda kanta tayi gefe da sauri, shi kuma ya Wan ciza lips Winsa yana wani jan numfashi a hankali.
 Nima ki fita tawa rayuwan mana. Kinbi duk kin hanani sukuni, kin hanani aure, kin sa duk nabi na tsani yaran mutane babu hujja .
Ai bama tasan sanda ta wara manyan idanunta a kansa ba tana harararsa, rasa abin cewa yasata faWin,  ALLAH zai saka min sharrin nan da ka min . Sai kuma ta sake sakkowa a gadon tare da fisgan hijjab Win sallarta ta saka. ?ofa ta nufa fuuu dan gara dai ta bar masa Wakin kawai sai yaci kansa yasha ba?in ruwa. Sai dai me ?ofar gam alamar saida ya rufe sannan. Ranta ne ya sake Saci, har takai hannu zata bubbuga sai kuma ta fasa saboda tunawa a asibiti suke kada ta shiga hakkin sauran majiyata. Dawowa tai inda yake cikin da tsantsar masifa da tsiwa ta balbalesa da masifa.
? ? ?? Yanzu kam gaba Waya dauriyarsa ?wacewa tai, dole ya kai hannu saman kansa dake wani irin sara masa da masifar ?arfi ya dafe, dama tuni dauriya kawai yake yi, shi kaWai yasan azabar da kan nan ke masa, dan shi dama a ciwonsa ciwon kai yafi yawa. Sam masifa ta rufema Maanal ido, sai cigaba da zazzaga masa take,  Please Besty my head ki daina min ihu .
? ? ?  An?i a daina, tunda baka so ka fita mana, waya kawo ka nan Win? .
? ? ?  Ya ALLAH ya faWa da wata sassanyar murya yana kai Wayan hannun ma ya tallafe kan gaba Waya. Dan da gaske ji yake kamar kwalwar ciki zata zazzago.
? ? ? A karo na farko gaban Maanal ya faWi, dan yanda ya kira sunan ALLAH Win da tallafe kan sai kuma hankalinta ya tashi. A hankali ta fara haWiye masifar tata tana kallonsa. Yayinda shi kuma ke cigaba da jujuya kansa a cikin hannayensa yana cigaba da kiran sunan ALLAH, sai kuma ya koma faWin,  Please Besty my head, kaina Besty zai fashe ki ri?e min, dan ALLAH ki ri?e min .
? ? ? ? ? Ai tsabar yanda jikin Maanal ke rawa batama san takai hannunta saman nashi ba, ta ture ta maye gurbinsa da nata tare da du?awa a gabansa tana le?en fuskarsa da faWin,  Na shiga uku mike damunka? Miya samu kan naka? Ka tashi muje wajen likita na ro?eka . Sai hawaye sharrr.
? ? ?? Bai iya ya motsa ba, sai hannunta dake a saman kan nasa da sanyinsa ke wani ratsashi ya sake dannewa da nasa da ?yau. Yayinda ita kuma zafin kan da yanda jijiyoyin ke harbawa ke ratsata. Matu?ar firgici ta shiga, dan tun tana hawaye har kukan nata ya fara fidda sauti. Da ?yar ya Waga idanunsa da suka gama kaWewa ya kalleta, cikin motsa lips Win da ?yar tare da Wan jujjuya kai ya ce,  Stop crying, bafa da yawa bane .
? ? ? ? ? ? Kukan ta sake fashewa da shi da faWin,  Hakanne bada yawa ba, kaga yanda idonka yay ja kanka yayi zafi? Nidai ka bari naje na kira maka Rafeeq... tai maganar tana ?o?arin mi?ewa da son cire hannunta dake a saman goshinsa. Da sauri ya ri?o Wayan hannun nata yana jujjuya kai, sai kuma miya tuna ya saki hannun yana faWin,  Am sorry . Itama kamar wadda ya fargar sai tai saurin janye Wayan dake a saman kansan, ta Wan ja jikinta baya. Murmushi ya Wan yi, sai kuma ya mi?e still dai hannunsa dafe da kan nasa ya Wan raSa ta gefenta ya zauna a gadon jiyyarta yana faWin,  Help me naWan kwanta anan ko zai sauka .
? ? ? ? Batace komai ba ta matsa masa, kwanciyar yay rigingine ya lumshe idanunsa hannunsa dafe da kan nasa. Tun tana kallonsa daga tsayen harta kai zaune a kujerar daya tashi dan itama sai taji kawai tana wani irin jin jiri, yayinda baya data shuWe ke son maimaita mata kanta a zuciyarta. Haka suke ita da shi, da wahala Waya ya kwanta ciwo Wayan bai kwanta ba shima. In ko ba haka ba dukkan hidimar mai ciwo Wayan ne zai yi. Zata iya cewa fara kaiwar AA Win lokacin balaga ne yasa Oum ta fara saka idanu akan al'amuransu, harma takan kasance tare da su batare data barsu keSewa su biyu kawai ba. Sai dai duk da haka ?addara bata barsu ba. (?addarah!) Zuciyarta ta maimaita kalmar da amsa kuwwa. Rimtse idanunta tayi da masifar ?arfi sai kuma Zuciyarta ta fara zafi, (Eh tabbas batace ?addara kawai ba, harda ganganci da son zuciya daga AA Win, eh son zuciya, koma tace zalunci......) Hawaye suka shiga solalo mata masu shegen zafi. Zaram ta mi?e daga gaban nashi ta nufi window jikinta na rawa. Yanda ta tura kujerar da ?arfi harta faWi ya sanya AA buWe idanunsa da ?yar. Kallo ya bita da shi, sai kuma yay saurin rumtsewa jin abinda take faWa cikin kuka mai tsanani daga inda take....
? ? ? ?  Dan ALLAH ka tafi, ka tafi nesa dani bana son ganinka. Ka barni naci gaba da rayuwata cikin salama. Namaka alkawarin zan bar aiki a companyn ka. Bana son tuna komai, bana so, ka daina kusantoni, ka barni,?dan ALLAH ka barni na ro?e ka Ajwaad....
? ? ??  Besty! ya faWa a can ?asan ma?oshi daga bayanta batare data san sanda ya baro gadon yazo wajen ba. Kuka ta sake fashewa da shi tare da dur?ushewa a wajen,  Ka daina kirana da wannan sunan, ka tafi kawai, ka tafi Ajwaad....
? ? ??  Zan tafi, amma ki saurareni kona minti biyar ne .
? ?  Bazan iya ba, baka da sauran space na lokacina, sam baka da shi. sai kuma ta juyo tana daga dur?ushen ta haWe hannayenta waje guda alamar ro?o=?O?.  Na ro?eka ka barni Ajwaad. Ka yi nesa dani, bana bu?atar jin komai daga gareka, bazan iya baka komai ?an?antar lokacina ba a yanzu .
? ? ? ? Da ?yar ya iya haWiye abinda ya ri?e masa ma?oshi, ya lumshe idanunsa da sukai mugun kaWewa mai ban tsoro daban tashin hankali ya sake buWewa a kanta. Cikin wani irin murya mai matu?ar laushi da sanyi ya ce,  Kin fi son mu cigaba da kasancewa a wannan matsayar kenan? Mu cigaba da Satama waWanda ke bibiyar rayuwarmu lokacinsu. Yes muna Sata musu lokaci ne kema kin sani, dan in har bani ne MIJINKI ba, wani bai isa ya zama ba!!. ya ?are furucin ?arshe a kausashe.
?ago kai tai da sauri tana kallonsa da jajayen idanunta. Shima Win kallonta yake da wani mugun kallon tabbatarwa. Amma ta dake a kausashe ta ce,  Mi kake nufi Ajwaad?! .
Shima a kausashen ya ce,  Abinda kikaji na faWa shi nake nufi. In dai ni Ajwaad Aliyu Darma ina numfashi a doron wannan ?asar, wani banza wofi bazai taSa aurenki ba Maanal. Dan haka tun kafin dare yay musu ki sanar da su suje su nema matan aurensu. Ki kuma sani ko mutuwa nayi kika auri wani in sha ALLAHU sai na hanaku zaman lafiya da fatalwata. Idan kuma kinji wasa bismillah, ga fili gamai doki . Ya ?are maganar yana mi?ewa da kaWa mata yatsarsa manuniya a saitin fuska tamkar zai tsokale mata idanu.
Mi?ewa tai itama a gabansa tana huci ga hawaye na zirara mata da gudun tsiya. Cike da tsiwa ta ri?e ?ugu da duka hannayenta biyu tana kallonsa babu ko gezau.  A tunaninka kana da wani ?arfin yin duk abinda ka faWa? Ka lalata min rayuwa sannan kai tunanin hanani auren wani? Shike nan mu zuba, nace mu zuba ni da kai dan ALLAH Wan halak ka fasa, ka saka a ranka ni kuma Maanal Habib Umar Giro zanyi aure, kuma zan auri wanda kake da kusanci da shi wato Rafeeq. Ka fara shiri nan da wata biyu kacal, wata biyu.... ta ?are maganar tana karkaWa masa yatsarta itama da raSashi zata wuce. Ai a wani irin fusace a kuma bazata taji an dam?o hijjab Winta an fisgota baya. Babu zato ta jita manne a jikin bango, duk da ko kaWan jikinsa bai taSa nata ba yanda yay mata rumfa da ingarman jikinsa saboda ya fita tsaho da cikar jiki nesa ba kusa ba, babu ta inda zata sha?i iska ya masifar sake hargitsata. A kausashe a kuma faWace, dan gaba Waya taswirar ?ya?y?yawar fuskar sa ta canja.

36 / 80