AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   74 / 80

219K to 222K   out of 237.4K words

kwana Waya na jiya kacal. Wannan al'amari ne da bai taSa faruwa da kamfani ba. Wasu kuwa na ganin Maanal Win tama cancanci fiye da hakan ai, duk da ba'ita kaWai tayi aikin ba, hasalima ita nata zane ne kawai. Amma dai ta taka rawar gani ai. Dan da batai zanen da ?yau ba suma masu ?erawar da basu yi yanda ya kamata ba. To ita dai bata cema kowa komai ba, iyakaci wanda ya tayata murna tayi godiya. ALLAH sarki Yaqub da kansa ya taimaka mata ta kwashe tarkacenta zuwa sabon office Winta. Dan zuwa gobe ma zata fara aiki a ciki.
? ? ?? Aiko hakan ce ta faru, washe gari Maanal a sabon Office Winta ta zauna. A kuma ranar ne batun bikinta da RK ya fasu a kamfanin, tare da auren boss Win su da duk shima za'ai rana Waya. Kowa dai ya sake fahimtar kusancin Maanal da boss tunda dai RK Wan uwansa ne na jini kowa yasan wannan. Sai ko ?ananun magana ta tashi akan shiyyasa akai saurin bata matsayi kenan. Sarai zantukan na dawo mata amma tai kunnen uwar shegu. Washe gari laraba ma ta Wauki hutu, sai kuma bayan biki zata dawo bakin aiki. Alhamdullah duk da Wan munafunce-munaguncen dake kai kawo haka suka taru sukai mata fatan alkairi, tare da tabbatar da zuwansu duk da shagalin ya zama biyu gana boss a gefe. To ita dai ta musu godiya da tabbatar musu tana saka idon zuwansu....

? ? ? ? A ranar suka wuce Kaduna. Dama Shahidah nata masifa akan gyaran jikin da akema Manaal Win kullum yana bin iska ne saboda galauniyar da take na zuwa aiki kullum. Suna kuwa isowa Kaduna Nene ta tisa ?eyarta zuwa gidanta. Wani irin gyaran jiki mai ban mamaki Nene ta fara mata Wan gaske. Tunda ta shiga kuryar Wakin Nene ko falo an haramta mata fita, hakama wayarta an kwace gyara kawai take sha ciki da waje, ita kanta abin har tsoro yake bata. Abubuwan da ake danna mata tana sha kuwa har kamar zasu sanyata amai take ji. Shiyyasa data faki ido sai ta zubar. Ga wani irin mahaukacin ?amshi da ko yaya ta motsa sai kaji waje ya buWe. Fatarta yayi wani irin ?yau na tashin hankali. Sau Waya Nene ke bata damar yin waya da RK a rana. Shima na minti goma kawai. Duk wani abu ta bashi damar yaje su tattauna da su Aneesa, ga Najma, ga Amrah duk da ma ita Hajiya Yaya ta hanata sakewa...

? ? _______&

? ? ? Tunda fa su Hajiya Yaya suka tabbatar bikin za'ai da gaske sai kuma sabuwar hassada ta tashi. Kullum cikin habaice-habaicen suke da gugar zana. Hajiya Yayan ta saka Yazeed Waukar amarya Nazeefa akan dole sun tafi honeymoon. Ammie kuwa ta tattarasu ta bama banza ajiyar su. Hakama Sangaren su Hajiya Basariyya shirin biki ake na garari da kece raini. Rashin zuwan ango sam ba damuwarsu bace. A cewarsu adai Waura koma minene zasuyi maganinsa ne. Itama danginta sun cika gida tab, dan wannan ne karo na farko da zata aurar.
? ? ?? Ranar talata aka kawo lefen Huznah, lefen da su Hajiya Basariyya aka dinga iyayi da gwalangwaso da shi har ana sakarma su Ammie habaici. Laraba akai kamu, amma na iya Huznah. Dan ita Maanal tace bata bu?ata. Sai kawai akai mata feshin turare normal dai na mutanen da shike nan. Tako ci kuka a Soye, gashi dama dannewa kawai take yi, amma ?irjinta gaba Waya a kwanakin nan jin gim yake da nauyi na tsiya. Amma tanata daurewa dan bata son kowa ya fahimci halin da take ciki har ?an uwanta da Ammie......

? ? ? ________&

? A Sangaren su Oum gasu nan ne dai, kowa ka gani babu wani karsashi ko Wokin auren a tare da shi. An dai kwashe gaba Waya kayan sashen AA ana masa gyara duk da kuwa komai fes yake babu wani damuwa. Bayan an canja komai anyi sabon fenti suma sauran sassan gidan an Wanyi gyaran. A Sangaren Mamy kuwa cike take da farin ciki mara misaltawa duk da ita Nuratu sai wani satin za'a Waura nata auren kamar yanda aka tsara. Amma tun yanzu cikin shirinsu suke suma tunda za'a kawo suruka Waya Huznah. Tsaff Mamy ta gama shirya yanda zata tarwatsa Oum. Duk da a yanzu ma damuwar da take kallon Oum Win a ciki wani kalar nishaWi da farin ciki yake sakata. Amma tanata ?o?arin dannewa yanda ta saba.
? ? ? Ranar Laraba suka tarkata suka wuce Kano suma. Dan za'aje can a haWe bukukuwan ne gaba Waya. Idan taro ya tashi lafiya sai su taho da tasu amaryar. Amma na wani satin anan Abuja za'ai komai basai sun je Kano ba, shiyyasa Mamy tafi shiryama bikin Nuratun fiye dana Huznah. Kwanaki fin biyar kenan babu wanda a cikinsu zaice yaga AA da idonsa, sai ta waya shina Oum ce ke naci kiransa. Dan yayi tafiya zuwa Lagos ta kwanaki biyar Win. A Kano ma zasu haWu da shi bazai dawo tanan Abuja ba. Sunyi tunanin zuwa su sameshi a can Win kuwa. Amma sai suka samu bai iso ba. Suna isa da yamma ?an kawo lefen Maanal Kaduna suka wuce. Ta mota aka tafi da kaya, su kuma suka bi jirgi bayan sallar la'asar. Dan haka Oum suna sauka ko zaman hutu batai ba ta bisu su dan tana son ganawa da Ammie. Sai Nibras data ma?ale domin zuwa taci uban Huznah a cewarta. Sai uwar gulma Saheeba, tunda basuga lefen ba sanda aka taho da shi basu isa Kano ba yasa ta biyo mutane dan ganarma idonta ko lefen RK Win dai-dai yake da wanda suka kai na Huznah. Itama Mamyn taso zuwa Mah-mah ta janye hankalinta da wani abun acan...
? ? ?? To lefen dai Maanal ya iso cikin garin Kaduna, gidan Alhaji Usman Chalawa. Gida fa cike da ?an gulma musamman ta fannin Hajiya Yaya da Hajiya Basariyyar ma tunda danginta duk suna cike fal a gidan ranar suke mothers event Winsu. Itako Ammie komai tace bazatayi ba sai yinin biki a wuce da amarya Wakinta. Lokacin da aka faka dalla-dallan motoci ?an gaske har guda biyu, Waya kuWinta ya tasarma naira miliyan 90 matsayin gift wa amarya Maanal, hakama ta biyu zata iya kaiwa miliyan ashirin da biyar, ai gaba Waya gidan sai da ya gigice. Dan motar 90m Win sabuwace dal a ledarta da ba'ako kware ba, itama kuma Wayar haka. Gashi an ?awatasu da ribbon. Hakama akwatina jerarru na kece raini da ?ar gata kawai ake kaiwa tuni sun cike waje set-set. Ai sai kaji bakin kowa ya mutu musamman lokacin da aka sanar da cewar motar 90m fa gift ne daga Yayan Amarya AA Darma. ?ayar itace ta kayan lefe daga ango.
? ?? (=?)?=?)?ALLAH matan novel sunji daWi, ?yautar motar 90mil fa, ni mai rubutawa ina nan sagadede da baki banda ko keke=?-?=?-?, dan ALLAH azo a haWa ?arfi da ?arfe a saya min mota mutanena=?%?=?%?>?z?)
? ? ? ? Babbar bala'i kenan inji Hajiya Basariyya jin wai ?yautar motar 90mil daga AA Darma wanda zai auri ?arta. Amma ita ?ar tata kota miliyan biyu ba'a sakko mata ba dan ita babu mota. Hajiya Yaya da su kam ba ?aramin girgiza zukatansu sukayi ba. Ita kanta Saheeba sai da zuciyarta tayi masifar girgiza. Jikinta har rawa yake ta turama Mamy text massage. Nibras ma dai sumar zaune tayi. AA Winta ne da ?yautar irin wannan ?atuwar mota haka. Oum kuwa wani irin sanyi ne ya shiga ratsa mata zuciya. A take ta kira Abah ta sanar masa dan babu wanda yasan AA zai yi wannan ?yauta. Su kansu masu kawo lefen a hanya suka haWu da motar. Sai da sukazo cikin Kaduna suka fahimci cikin tawagar su take saboda ganin Modibbo ne ya tu?o ta. Bayan Oum ta yanke waya da Abah AA ta kira, sai dai ya sanar mata yana airport ne zai baro Lagos, idan ya sauka zai kirata...

? ? ? ?? Ammie ta matu?ar shiga ruWani ita kanta da wannan ?yauta t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a AA, sai ma taji ta rasa abin faWa dan mamaki.? Ga wannan uban lefe na girgiza hazo kamar za'a buWe wani ?aramin kanti. Kasancewar guri ya ?ure yamma tayi su Oum basu wani jima ba suka wuce. Duk da akwai tattaunawa sosai da Oum da Ammie ke son yi babu isasshen lokaci. Haka suka rabu akan zasu ?arasa a waya tunda dama dai sunatayin na kullum tunda aka fara kaikawon bikin nan.......

? ? ? Har su Oum suka koma Kano babu AA babu labarinsa. Dangi sai tambayarsa akeyi dan sauran anguna sunata kai-kawo amma shi babu shi babu alamarsa. Zuwa bayan isha'i dai Oum ta kasa ha?uri ta nemo su babban Yaya a waya. Shine ya tabbatar mata suma mamakin rashin isowar tashi suke. Dan ranar mazan family Win suke partyn su, ga shi har za'a fara shi babu shi babu alamarsa. Kuma ya ce musu zai baro Lagos suma tun Wazun...........
'?

? ? ? Jama'a kar dai Yayan su o'e ya gudu ne=?2?9&?.
? ? Ashema matsoraci ne, da Uncle RK Winmu ne babu inda zai je=? ?>?#?

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.......Sai ?arfe kusan goma AA ya iso gidan baba Sardauna. Dan anan gaba Waya ake shagalin bikin. Hankalin Oum yayi mummunan tashi da ganin yanda AA yay masifar zabgewa a tsaye. Duk mai hankali yay masa kallo Waya yasan baida isashiyar lafiya sam.?Jiki na rawa Oum ta kama hannunsa suka shige bedroom Winta, Dan suna a tsohon sashensu ne na gidan baba Sardauna Win da suka zauna a can shekarun baya.
? ? Muryarta har rawa take wajen tambayarsa,  Ajwaad baka da lafiya ne? .
? ? ? ? Hannunta ya kama fuskarsa Wauke da murmushi mai sanyi ya zaunar da ita a kusa da shi. Kafin ta kwantar da kansa a kafaWarta. Idanunsa a lumshe hannunsa cikin nata ya ce,  Oum ki kwantar da hankalinki lafiyar Autan ki ?alau. Zirga-zirga ce kawai taimin yawa a kwanakin nan. Tunda naje Lagos ban zauna na huta ba saboda kayan nan namu da gaske Sata suka so yi. Amma Alhamdullah ALLAH ya kiyaye haka dan yanzu haka har sun sauka Abuja suma. Yaya hidimar bikin? .
? ? ?? Hawaye ne suka zubo a fuskar Oum. Tasa hannu ta share, kafin tace,  To Alhamdullahi ALLAH ya kiyaye gaba. Amma Ajwaad har yanzu kana akan bakanka na?in amsa kana son Maanal daren yau fa kawai ne da mu .
? ? ? ?? A hankali ya tashi daga kan kafaWarta, fuskarsa da wani ?ayataccen murmushi ya ce,  Oum maimaita zancen nan bashi da wani alfanu. Bara naje na Wan watsa ruwa na kwanta na huta a gajiye nake matu?a .
? ? ? Kai kawai ta jinjina tana ?o?arin haWiye ?wallar data cika mata ido. Har ya kai kofa zai fita ta katseshi da faWin,  Munga mota tayi ?yau ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci .
? ? ?? Guntun murmushi ya Wan saki kawai, kafin a saman laSSansa ya furta,  Amin . Ya fice. Ta ?ofar baya ya fita, dan sam baya son haWuwa da Mamy. Kai tsaye daga nan masauki ya nufa, inda duk samarin family dama masu auren kan zauna in har ana biki. A hannun Uncle Mahmud ya amshi key Win nasa Wakin, dan shine da alhakin hakan dama. Shi kansa Uncle Mahmud Win ya tsaresa da tambayar baida lafiya ne. Amma yace masa shi ?alau yake, yayi busy ne kwana biyu akan wasu injinansa da suka nema Sacewa a bakin ruwa Lagos shiyyasa kawai. Badan Uncle Mahmud ya yarda ba ya ?yalesa kawai. Shima yana samu ya shige Waki ya kulle kansa. Duk wanda yazo ya buga sai yace su barsa barci yake son yi ya gaji ne. Dole kowa ya ?yalesa tunda dare yayi.
? ? ? Dole sai a washe gari kowa ya iya ganinsa a Sangaren mazan dai. Aiko suka tasashi gaba akan sai yaje an masa gyaran fuska dan ya tara uwar ?asumba ya?i yay gyaranta. Da farko ?i yay, sai da Uncle Mahmud ya sashi gaba. Dan adai cikin iyayensu maza daga Abah sai Uncle Mahmud Win (ina fatan baku manta da Wan gwaggo Khadijah da itama ta baiwa Baba Sardauna ba bayan Abah da Oum. To shine Uncle Mahmud).
? ?? An masa gyaran fuska mai ?yau yana kumbure-kumbure yana jin haushi. Sai kuma gashi yayi ?yau sosai duk da ramar da yayi ta sake bayyana kanta. Gaba Waya an haWe Waure-Wauren auren anan Kano ne. Dan shima Daddy tuni shi da tawagarsa sun kama hanyar Kano. Anyi haka ne domin sama ma mutane sau?in, tunda shima dai Daddyn asalinsa bakanon ne. Danginsa duk a can suke, daga can suke zuwa Kadunar duk wani biki...
? ? ? Tunda sha biyu tayi kowa yake ?arasa shirinsa a gaggauce, musamman anguna da bakunansu suka kasa rufuwa. Sai dai banda AA da tunda suka dawo daga aski shi da Uncle Mahmud da Babban Yaya ya shige Waki ya kulle kansa. Ba'a farga da rashin fitowarsa ba sai da suka Wauki hanyar tafiya massallaci. Babban Yaya ne ya Waga waya ya kira shi, tare da tambayarsa yana ina? Sai cewa yay gashi nan zai biyo bayansu wani abokinsa ne ya tsayar da shi. Babban Yaya bai kawo komai a ransa ba dan AA yay masifar saita kansa kafin ya Waga wayar. Wayar na yankewa ya kasheta gaba Waya yana mai kai hannu ya shafo jinin dake ziraro masa ta hanci. Murmushi ya saki tare da saurin dafe bango jin jiri na neman zubar da shi. Tun yana bin bango domin kai kansa cikin toilet harya gaza, dole ya zube a ?ofar bayin saboda wani irin nauyi da ?irjinsa yay masa, idanunsa suka fara juyewa duhu ya fara mamaye ganinsa. Duk wani motsi ya fara nisa da kunnuwansa. Kafin cikar abinda bai wuce minti biyu ba ya nema kansa ya rasa, sai damshin Wumin jinin dake fita masa ta hanci kawai yake iya ji a fatar jikinsa kafin a hankali komai ya koma masa Wiffff....
? ?
? ? _________&

?? A massallaci su Babban Yaya suka haWe da Abah, koda Abah yace ina AA sukace yana nan tahowa, wani abokinsa daya iso ne ya tsaida shi. Kamar Abahn zai yi magana sai mutane suka Wauke masa hankali. Ga shirin fara sallar juma'a anayi, dan har an fara khuWuba. Daga can itama dai Oum hankalinta na akan AA Win, dan tun safe da sukai waya bata sake jinsa ba. Garama Babban Yaya dake sanar mata sun tasashi gaba sun kaisa aski shi da Uncle Mahmud har taita dariya. Duk yanda take ?o?arin samunsa a waya hakan ya gagara, ga mutane sai Waukar hankalinta suke yi, dole ya tattara wayar ta ajiye ma ta maida hankalinta garesu...
? ? ? Bayan idar da sallar juma'a aka fara gabatar da Waure-Wauren aure. An fara Waura auren Uncle Najeeb Umar Ishaq Darma da amaryarsa Raihana Kabeer Yola. Sai na Rafeeq Kasheem Kura da amaryarsa Nuwaira Kabeer Yola. A rikice Babban Yaya da Fawzan har ma da Abah suke kallon RK da su Baba Sardauna. Amma duk sai sukai murmushi kawai, Abbu ya sake bada sadaki ga Daddy matsayin na AA. Ana jira aji an ambaci sunan Huznah sai akace ga sadakin Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, ga Maanal Habib Giro. Babu wata damuwa ko gargada ga Daddy ya amsa fuskarsa da murmushi aka ?ulla auren. ?aurin auren ?arshe shine na Sageer Ahmad Isa Chalawa, da amaryarsa Huznah Usman Isa Chalawa...
? ?? Kan babbar buta, ai a rikice Abah yace,  Alhaji Usman nifa ban gane ba. Baba kun sakani a ruWani, yaya duka aurarrakin suka canja kansu? .
? ? ? Murmushi Baba Sardauna da Baban Yola da Daddy da Abbu duk sukayi, hakama RK hankalinsa kwance sai ma murmushi yake saboda kallon da Babban Yaya da Fawzan suka zuba masa. Baba ne ya bama Abah amsa da,  Dama can a haka suke. Kai ne dai kake kallonsu ba'a haka ba. Kowa an bashi matarsa ne . Daga haka ya juya aka ?arasa addu'oi ga ma'auratan da fatan alkairi da zaman lafiya na har abada.
? ?? Ai sai hawaye suka shiga zuboma Yaya Fawzan. Kasa hakuri yay a take ya Waga waya yay kiran Oum shima kuma babban Yaya Oum Win yake nema. Sai ALLAH ya bama Fawzan sa'a tashi ta fara shiga. Tana Wagawa ko sallama baiyi mata ba cikin muryar kuka ya ce,  Oum ALLAH ya mallakawa Autanki Maanal. Maanal ta zama mallakin Ajwaad Oum an Waura Oum an Waura..... sai hawaye. Gaba Waya daburcewa Oum tayi, ai bama tasan tayi wani kalar tafiya jagwab ta zube a kujera wayar hannunta ta suSuce. Hannayenta gaba Waya a saman fuskar ta ta fashe da kuka da ambaton sunayen ALLAH a bayyane, tare da mi?a godiya da kirari ma UBANGIJI mai hukunci bisa hukuntawarsa da rahamarsa...
? ?? Kafin kace mi mutane sun zagayeta ana tambayar lafiya-lafiya. Ta kasa cewa komai ila amfaton UBANGIJI. A haka ?an Waurin aure suka fara dawowa gida. A take zancen Waurin aure da yanda ya kasance ya fara bayyana a cikin gidan....

? ? ? ? ? Mamy na tsakiyar ?an uwanta da suka zo wani dake matsayin kamar Yaya a wajenta na kusa kuma, dan da babansa da babansu uwa Waya uba Waya suke suka shigo domin yimata ALLAH ya sanya alkairi dan zasu wuce, daga Jigawa suka zo shiyyasa. Tanata faman washe baki bata san mike faruwa ba sai da suka gama jerama ma'auratan addu'oi sannan wanda ke kamar yaya a wajen nasu ke faWin,  Ai ni na shiga ruWani ma a wajen Waurin auren. Kuma naji mutane nata mamaki suma har wasu na tambaya .
? ? ? ? Cike da isa Mamy ta dubesa, dan haka take musu daman saboda akaf dangin nasu itace mai auren

74 / 80