AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 80

30K to 33K   out of 237.4K words

?ofa ya juyo yana kallonsu.  Kutashi kuje ku kwanta zuwa da safe koma miza'ai sai ayi. Ku kulle nan Win .
? ? ?? Wasu sun amsa masa da to, wasu ko da hararar ?asan idanu suka rakashi dan sun san babu damar yi a zahiri mutum yaci dukan banza a daren nan balle ma babu Mamma.....

? ? ?&&&

Washe gari koda Yazeed yazo ganawa da Daddy sai ya samu har ya fita. Sashen Ammie ya nufa, inda ya taddata zaune jihum alamar tana tare da damuwa harma da Sacin rai. Gaisheta yay da girmamawa kamar yanda ya saba. Itama ta amsa masa cikin kulawa tana danne damuwarta.
? ??  Yanzu ka iso ne? .
??  A'a tun da daddare. Around eleven na samu kunyi barci shiyyasa na ha?ura har sai da safe. Yanzu kuma naje sashen nashi naga alamar a rufe yake .
? ? ?  Nima nazo na haWa masa breakfast na koma naga yabar gidan. Ka ganni tun Wazun nake kiransa yana rejecting daga ?arshe ma ya kashe wayarsa gaba Waya.
? ??  Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un . Yazeed ya shiga ambata yana mai dafe kansa da dukka hannayensa biyu.
? ? ?  Yazeed nikam da zakaji daka ha?ura da batun auren nan na Maanal. Dan idan zamu duba gaskiya duk batunsane tushen wannan matsalar. Kayima Hajiya biyayya ALLAH sai ya baka wadda tafi Maanal .
? ? ?  Amma Ammie ina sonta, wlhy matu?ar so nakema Maanal dan ALLAH kar kice haka, ke da Daddy ne ?warin gwiwata. Sannan shima Daddy ai yanada hakki a kaina kuma yana son auren. Miyasa Mamma bazata fahimta ba. Miyyasa bazata fahimci Aunty Sabuwa tana zugatane kawai saboda ta samu biyan tata bu?atar na auri tata ?ar bane? .
? ? ? ??  Amma Yazeed ?ar uwartace fa, uwa Waya uba Waya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.
? ?  Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma Win ce kawai ta kasa fahimta .
?? Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana matu?ar son Maanal ta auri Yazeed kodan ?yawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed shi kaWai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ?an uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta basa so sam.....

? ?? ________________&

??  ALLAH nazata wasa kikeyi da kikace min gaki nan tahowa Zaria fa.
? ??  hhhh aina fahimci hakan a muryarki. Bazaki ganeba fitowar ta dole ce. Gidanmu ne keci da wuta na gasken gaske kwana biyun nan .
? ??  Tofa wuta kuma Aminiya tami? .
?  Uhhm ke dai bari, tushen matsalar daga auren agolar gidanmu ne da maigidan yace zai ?ulla kusan shekara uku kenan.....
? ?  Kar kice na katseki wai ?ar amaryar ku? To da wa? .
??  Ita fa, dawa kike tunani idan ba Wan sonsa Yazeed ba. Tunda fa akai maganar dama uwar tasa tace bata yarda ba. Shi kuma Daddyn Huznah bai maida kai ba yarinyar dai tana cigaba da karatu, shi kuma Yazeed yana manne da yarinya. Bayan ta kammala karatun akaso tada zancen bansan miya faru ba dai kuma aka dakata ta wuce service. Indai ta?aice miki batu ta gama service Win ne yanzu zancen ya sake tasowa shine aketa dam-barwa. Ita uwar Wan tace bafa za'ai ba, kwana takwas da suka shige sukazo itada ?ar barikin ?anwar nan tata sabuwa suka cima uwar ?ar mutunci randa muka bar nan kenan shine itakuma yarinyar ta yanke jiki ta faWi ta kama aman jini .
? ? ??  Aman jini kuma? .
??  Uhm kin san sunce wai ai tana da ciwon zuciya .
??  Tir?ashi, eh lallai dole kice gidanku naci da wuta. Ke nan yanzu yaya ake ciki kuma? .
? ?  Yarinyar na asibiti a Abuja yanzu haka. Ba shine nake faWa miki nakoma Abuja ba nima harma naga ?anin Majdiya .
??  Oh ?warai anyi haka. Ko shiyyasa itama taje Abujan ita da yara duka dan gulma shine suka wuce gidan Yaseerah wai ganin Waki. Aiko sai da na mata tujara daga ita har mijin nata data dawo .
? ? Dariya sosai suka kwashe da ita suna tafawa. Hajiya Basariyya ta ce,  Ai kinmin dai-dai wlhy. Kinga gobe ai ta kiyaye .
? ??  Karma ta kiyaye na koya mata hankali. Mu munafuncin kishiya wanne bamu sani ba kuma .
??  Wlhy kuwa. Sai dai wanda kuma aka Soye a zuciya. Yanzu kin san miya sani zuwa Zaria Win? .
? ??  A'a sai kin faWa .
??  Jiya uwar gadaran gidan namu ce ta wuce gida harda kaya cike da akwatina. Dan ya hanata girki a gidan sai mu biyu mukeyi, shine jiya girkin ita shegiyar ne ita kuma taje ta samesu tai musu Wibar karan mahaukaciya. To ban sani ba ko sakinta yayi shine ta kwashi kaya ta tafi, dan naga Wan ma ya dawo jiya da dare su kuma matan sunata kuka. Yau kuma tunda safe mai gidan ya fice rai a Sace matar son nasa itama dai duk ta koma sukuku. Dan haka malam nakeso ki kira mana nan ina son a ?arama wutar fetur ne ya sake birkice musu. Sai kuma batun Huznah da yaron nan da suka haWu a Abuja. Na fahimci kamar itace ta damu da shi, dan sai ta yini kiransa a waya bai ma amsa mata ba sai ya gadama. Ina son a ri?e masa wuta gaskiya san bana son nima ta rasashi. Nayi binciken yaron shi kansa bama ubansa ba wani shege ne. Dan Companys ne da shi na abubuwa. Ga shima uban nasa sune ?asar. Hakama ?an uwansa biyu kowa ?waron kansa ne duk da dai shi ?anin ya fisu komai.
? ? ??  Humm wato ?awata kina matu?ar birgeni, sam ke baki da wasa akan abu. Sha yanzu magani yanzu kikema komai shiyyasa da wahala asha gabanki .
? ??  Yo ai babu zama ?awata. Lamarin rayuwar nan kana sakaci sai a tafi a barka a ?arshe bare mu dake zagaye da shegun kishiyoyi, tako ina da hari ake kawo mana mune na tsaka. Kinga ko dole mutum ya nemo garkuwa da takobin kai nasa harin ai.
? ? ? ??  Wannan gaskiya ne. Yanzu dai bara nasa Zaituna ta kira mana shi ta falon baya. Kin san gidan namu dai cike yake da ?an sa ido. Damma maigidan baya gari ne jiya da yamma yay tafiya.
? ?  Ato ai ansha hidima dole a koma nema kuma. ALLAH ya taimaki ?an baya suma haka dai dan wlhy rashin auren yaran nan ya fara tada min hankalina. Rigi-rigi sai samari sunzo kamar za'ayi sai ki nemesu ki rasa .
? ??  To ke kuwa ma?iya cike da gida za'a barsu haka ne. Ke dai kin san ya?i da gwagwarmayar da nasha Kafin auren nan na Yaseerah ya yiwu. Yanzu saura Zaituna itama dai wani ya biyota a ?an bikin so nake na huta gajiyar nan na fara aiki a kansa. Dan babu wasa .
? ?? Dariya suka kwashe da ita su duka suna mai taSawa. Hajiya Basariyya ta ce,  Haka nake fata a nawa gidan. Dan sai yaran nan sun gama aure kaf kafin yaran Wakin gadararriyar can suyi sa. Na riga na shirya ya?arta ta wannan fanin .
? ?  Wlhy ina bayanki. Shegu ai idan sunce su mugunta suka iya gidan suka taras....

? ?? _________&

? ?? Kwanakin Maanal goma sha shida a asibiti sannan aka bata sallama. Dai-dai da cikar Hajiya Yaya kwana tara a gidansu. Daddy dai tun wannan fitar da yay daga gida a washe garin zuwan Yazeed bai koma ba. Sai daga baya suka fahimci yama bar ?asar ne sabgar gabansa. Dan kwanansa biyu da tafiya yasa Hajiya Basariyya tabisa can. Komai Ammie batace ba akan hakan, damuwarta fushin da yake da ita da batasan laifinta ba. Gefe kuma ga yaran Hajiya Yaya sun tasota da rashin kunya da rashin mutucin a gidan. Sai idan Yazeed na gidan ne take samun sau?in su. Dai-dai da su Hameed sun takurawa da zagi da duka. Wannan dalilin ya saka yau koda su Shahidah suka kirata akan sallamar Maanal tace Maanal Win ta zauna anan gidan Shahidah kawai. Nene sai ta biyo su Amaal ta dawo. Hakan yayma Maanal daWi dan dama bata son komawa Kadunan. Sai dai ita Nene ta fahimci akwai matsalane amma batace komai ba ta shanye a ranta har sai ta koma. Dama tanata mamakin abinda ya hana Ammie sake dawowa Abujan. Kullum sai dai suyi video call safe da yamma. Takance suyi ha?uri da rashin daowarta akwai abinda take yi ne.
? ? ? Badan Maanal tasoba ta yarda RK yay musu rakkiya har gidan Shahidah. Cikin farin ciki su Munaya sukazo suka rungumeta. Itama haWasu tai ta rungume tana mai jin kewarsu dan sau Waya sukaje dubata asibiti aka hana zuwa dasu saboda bata son hayaniya a lokacin. Har cikin falo suna manne da ita. Kafin su fara rige-rigen zuwa Wakko mata gift da kowa ya tanada mata.
? ? ?  I love you yarana .
?? Ta faWa a hankali tana rungumesu....
 Kina da son yara kamar haka, amma kiketa Sata mana lokaci . RK dake gefen kujerar da take ya faWa a hankali ta yanda itace kawai taji. ?ago yaran kawai tai daga jikinta batare da ta kallesa ba. Shima sai ya basar saboda isowar Amal Wauke da ?aramin tire ta haWo masa abin sha. Godiya yay mata hankalinsa kwance ya Salle ruwa ya tsiyaya a kofi ya hau sha. Ita Maanal ma sai ?arfin halin nasa ya Waure mata kai. Kasa jurewa tai sai da ta Wan zuba masa ido. Yanda take kallon nasa ne ya sashi sauke kofin daga bakinsa shima yana kallonta. Sai kuma ya wani Wan ?ya?y?yafta idanunsa. Nata idanun ta Wauke tana Wan yamutse fuska da faWin,  Kai ko kunya baka ji? ..? ?
? ? ?  Ikon ALLAH kunyar mi zanji?. Gidan yayata nake fa. Idan kuma so kike na fara jin kunyar ki bani damar sakaki a gidana na miki al?awarin ko'ina naje aka bani ko miye bazanci ba sai naki .
? ? ? ? Kallo ta jefa masa mai kama da harara sai kuma ta girgiza kai kawai ta mi?e. Harta gama hayewa upstairs idonsa a kanta, sai da takai step Win ?arshe itama ta Wan juyo dan tana jin kaifafan idanunsa na yawo a kanta. Da sauri ya Wauke kansa ya basar. Ita kuma taja ?aramin tsaki ta ida hayewa. Daga haka bata sake sanin sanda yabar gidan ba. Dan wanka ta samu tayi a Wakin Shahidah tai kwanciyarta sai barci. Dama sunce zata dinga samun isashen barci yanzu hakan ne zai dawo da kuzarinta data rasa...

? ? ?? Bayan sallar la'asar Nene dasu Amaal suka wuce. Sai suka koma daga ita sai Shahidah da mijinta da yaranta biyu a gidan kawai. Sai kuma masu aikinta guda biyu. Jitai kuma duk babu daWi, dan tana matu?ar son ta gansu su duka a waje Waya hakan na sakata a farin ciki. Sai dai yaya ta iya aure ya rarrabasu. Hira suke da Shahidah, koma ace Shahidah ke hiran dan Maanal dai daga guntun murmushi sai eh ko a'a ne nata. Muneff ne ya shigo da Wan gudunsa, autan Shahidah, dan daga shi dai har yanzu bata sake ba ko tana hutawane ko ta tsaya oho mata.
? ??  Muneff ban hanaka wannan guje-gujen ba wai nikam? .
? ? Shahidah ta faWa cikin taka masa birki. Yaron bai damu ba ya ce,  Mamy Uncle Yazeed ne yazo .
? ? ? ? ?  Uncle Yazeed na kd? .
? ? ?  Eh Mamy. Yana waje ma .
?? Kallon Maanal Shahidah tayi. Itama Maanal Win ita take kallo.  Kije ki shigo da shi .
? ??  Ni Didi ?afata ke ciwo .
?? Kai kawai Shahidah ta girgiza tana mi?ewa. Hijjab Winta da takan ajiye a falo saboda ba?i irin haka ta Wauka ta saka sannan ta fita.? Babu wani jimawa sai gata ta dawo Yazeed biye da ita. Yana shigowa idonsa akan Maanal ya fara sauka. Itako ta ?urama television ido kamar bata san da shigowar tasa ba.........
'?

?

('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??


.......Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta Wan kallesa ta ce,  Yaya Yazeed ina yini .
? ? ?? Sai da yaja kusan minti Waya kafin ya amsa da,  Lafiya lau. Yaya jikin naki? .
? ?  Alhamdullahi .
 Masha ALLAH . Ya faWa yana maida kallonsa ga Shahidah.  Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai da naje asibitin yanzu akace kuna gida .
? ? ?  Kayi ha?uri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu.
? ? ?  ALLAH ya ?ara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen? .
??  Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba Waya .
? ? ? ?  Kai da sauri haka?. Ita Nene ko Wan hutawa bazatayi ba .
? ?  Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake kwana a garin nan ba .
? ? ? ? ? Murmushi kawai yay da faWin,  Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam . Ya ?are maganar idonsa akan Maanal.
? ? ?  Ni Ammie tace ai na zauna anan .
?  Anan kuma? To saboda mi? .
Shahidah ce ta bashi amsa da,  Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta Wan ?ara murmurewa ne dan suma likitocin sunyi gargaWi sosai akan ta huta a waje mai ?arancin jama'a da hayaniya. Amma tana ?ara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed .
? ?? Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce,  Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi .
? ? ??  ALLAH ya taimaka ya bada nasara . Shahidah ta faWa cike da girmamawa. Dan suna matu?ar giramam yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya taSa musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can ?asa ya ce,  Baki jin komai dai zuwa yanzu? .
? ? ? Kanta ta jinjina masa alamar eh.
?  Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko? .
? ? ? Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce,  Ni ALLAH babu ruwana.
? ? ?? Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya Wan murmusa tare da du?o da kansa kaWan murya ?asa-?asa ya furta,  Adana shagwaSar nan ba yanzu ba .
? ? Kanta ta du?ar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a ?irjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yun?ura zata tashi. Cikin bada umarni ya ce,  Koma ki zauna . Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna Win tana Sata fuska....

?? _______________&

? ? ? ?  Da alama wannan karon mijinki yana son nai matu?ar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya ?arama .
? ? Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da du?ar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce,  Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da wannan zaman ?uncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ?ar?ashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan al?awuran da girmana agaban ?a?ana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba'a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace faWa a gabana Baba . Ta fashe da kuka.
? ??  Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan Wauka jeki kwanta .
? ?? Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana mi?ewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce,  Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa.

11 / 80