AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 80

66K to 69K   out of 237.4K words

yake ba ya bashi amsa a ta?aice.  Fara ajiye ta .
? ??  Okay sir. Sister ina muka nufa? . Ya maida akalar tambayarsa akan Maanal. Shiru bata amsa ba sai da ya sake maimaita tambayar sannan ta dawo hayyacinta. Cikin ?o?arin danne komai da yanayin nan nata na kamewa ta furta,  Samu waje kawai zan sauka na ?arasa a taxi .
? ? ? Kallon AA Darma drivern yay ta mirror Win gaba da tunanin ko zaiyi magana. Amma sai yaga ko kallon inda wani cikinsu yake bai yiba ma. Dan haka sai ya kalla AS cikin marairaicewa. Murmushi AS yayi tare da juyowa saitin inda Maanal Win take,  Please Sister Maanal bafa zamu ajiyeki ko'ina ba sai gida .
? ? ? Rasama mi zatace tayi, sai kawai ta faWa masa sunan anguwar a ta?aice. Bai gaji ba ya sake tambayar street, nan ma kamar bazata kula shi ba sai kuma dai ta faWa. Daga haka bata sake magana ba ta maida idanunta ta rufe. Cikin ?an?anin lokaci suka iso abinka da lafiyayyar mota a saman lafiyayyar kwalta. Shigowarsu cikin street Win ya sa AS sake mata tambayar inda za'a sauketa. A ta?aice ta ce  Nan ma yayi . Shi dai driver tunda ta?i faWar no Win gidan da zataje ai sai kawai ya samu waje ya tsaya abinsa. Itako ta kama handle Win motar ta buWe da nufin fita. Sai kuma ta Wan juyi domin Waukar kayanta da AA Darma ya amsa a Wazun akai rashin Sa'a shima ya kawo hannu kan kayan da nufin Wauke file Win daya Wora kawai ta ri?e masa hannu. Da sauri ta jiyo jin ta kama abu, dai-dai shima yana kallon hannun nasa da yaji an cafke. A tare suka dubi hannun sai kuma suka kalli juna. Maanal ta saurin yarfar da hannun tamkar wadda ta kama wuta, yayinda shi kuma ya wani irin dun?ule hannun nasa waje guda tare da dimtse lips Winsa da hakori tamkar zai kai naushi. Sauka Maanal Win tayi tare da zare kayan nata ta ajiye masa file Win batare data sake gigin kallon ko inda yake ba taima AS godiya da driver tai gaba abinta ko waiwayen motar bata sake yi ba. Shima driver sai kawai ta tada motar suka wuce.
? ? ?? Tunda suka tafin AA Darma hannun nasa kawai ya zuba ma ido tamkar mai karanta wani abu a jikinsa ko cigaba da ganin hannun Maanal Win. Kamar ance ya kalla inda ta tashi idonsa ya sauka akan Wan abin hannunta da alama wajen yarfar da hannu da tai sanda ta kama nashi ya cire batare data kula ba. Hannu ya kai a hankali ya Wauka Wan hannun ya juya. Mai ?yau ne sosai kalar golden, an masa kwalliya da fararen stones, da gani ba wani mai tsada bane, amma yayi ?yau sosai. Yanda ya tsirama Wan hannun ido yana kalli da jujjuyashi haka su AS ke kallonsa zuciyarsu cike da gulma, suna ganin zai Wago suka kama kansu. Shi ko a cikin aljihun jacket Win suit Winsa na ciki ya cusa Wan hannun kawai ya gyara zamansa......

? ? ? Ni dai nace,  Hummm. Idan tayi wari dai maji>?*?
_____________&

? ? ? ?  Wai ni wannan yaron zaima gadara? Ni nan! Ni a garin Abuja .
?? Abokansa uku da suka zuba masa ido cikin mamaki Waya daga cikinsu ya ce,  Sen.. Bukar wai kai da waye haka? Ka shigo kamar wanda aka wancalo kuma kanata kai kawo da zantukan da bamu gane ba .
? ?? Tsaki mai ?arfi ya sake ja, sai kuma ya Wauka bottle na ruwa ya Salle murfin ya hau kwankwaWa. Tas ya shanye yay jifa da robar, kafin ya dubi abokan nasa Waya bayan Waya yana furzar da huci.  Wannan yaron Wan gidan Darma mana, lokaci yayi da zan koya masa darasin rayuwa. Saboda na fahimci tashen balagar iskanci ne ke Wibarsa da giyar ?an kuWaWen da yake gani ya tara kamar yaje dai-dai da kowa....
? ? ??  Halan AA!? Dan nasan shine tsageran cikin ?a?an Darma . ?aya daga cikin abokan nasa ya faWa shima cikin Sacin rai.
? ?  In ba shi Win ba sai wa? Wato wannan yaron shifa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu a garin Abuja. Haka ranar Alhaji Badamasi yace min ya masa rashin mutunci. Wai yaje masa da business amma ya?i ?arSa harda gaya masa ba?ar magana. Tsageran cin yaron kullum sake ?aruwa yake yi .
? ? ? ?  Kufa daina Sata bakin ku, wannan yaron duk abinda yake Waurin ?ugu ya samu, ba daga kowa ba kuma sai Mr president, tunda ya Wauki mu?amin nan ya bashi yake jin kansa dai-dai da kowa. Sannan kaima kayi ganganci, da girmanka da mutuncinka a ?asar nan bama garin Abuja ba minene na sauka yima yarinya magana. Ko ?ar uban waye zaka aika a Wakko maka ita har gidane balle nasan bai wuce karuwan dake tsayawa a wajen bane ba. Na gaya maka kana gidanka kwance duk ?ar da kake so za'a kawo maka amma ban san miya kaika wannan kwamacalar ba haka .
? ? ? ? ?  Karka Sata min rai kai kuma, ai na faWa muku yarinyar tafiya kawai take ina zaton daga cikin wani Companyn ta fito ne, kuma a yanda nake cikin Sadda kamar nan kaima kasan babu yanda za'ai wani ya ganeni, koshi bana tunanin yasan nine akwai dai wata tsakaninsa da yarinyar shima Wan iska, saboda naji wannan shegen yaron daya maida kamar bindinsa ya kira sunanta wai Sister Maanal .
? ? ?  Eh to da gaskiyarka akwai ala?a kam, amma bincike ya kamata muyi .
?? Duk sun gamsu da yin hakan, daga nan suka saki zancen suka fara wanda ya tarasu a wajen. Dan dama meeting ne zasuyi daya shafesu. Su duka biyar Win manyan ?an siyasa ne kuma ?an kasuwa a bayan fage, a wata fuskar kuma dattijan ?asa wai....

? ? Wai.... Ne ma kenan ba manyan ?asar bane
_________&

? ? ? Maanal kam data shiga gida tamkar wadda aka koro har ta bama maigadi tsoro waje ta samu a harabar gidan ta zauna, sai da ta huta taci kukanta sosai ta Wan samu nutsuwa sannan ta mi?e. Wajen fanfo da ake bama flowers ruwa taje ta wanke fuskarta sannan ta shiga ciki. Turus taja ta tsaya tana kallon Huznah dake zaune a falo tana cin abinci. Yayinda su Barrah dake homework sukayo kanta da gudu suna mata oyoyo.....
? ? ? Rungumesu tai idanunta na kan Huznah Win da itama ita take kallo, dai-dai nan Shahidah ta fito daga kitchen.  Aini yanzu nake tunanin zuwa na biki kafin Daddynsu Barrah ya dawo gidan nan .
? ? Shahidah ta katsema Maanal da Huznah kallon-kallon da sukema juna da furucinta. Dan murmushi Maanal Win tayi da kaiwa zaune tana faWin,  Didi ai nima kaWan ya rage na kiraki a waya, ashe wajen nan haka ake wahalar taxi .
? ? ??  Ai dolene, waje duk ma'aikatu ke kuwa. Ya aikin? .
??  Alhamdullah ya naku? .
?  Yana can mun baro sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Bakiga ba?uwa ba ne? .
? ?? Sam Maanal babu ruwanta da Soye-Soye dan ita ?ar sak ce, sai ta Wan kalli inda Huznah take da faWin,  Na ganta Didi. Mamaki ne ya kasheni ai na kasa magana. Sannu da zuwa .
? ?? Cikin Wan basarwa Huznah ta ce,  Yauwa sannunki kema . Daga haka ta maida kanta ga abincinta. Itama Maanal sai bata sake magana ba ta mi?e.
? ??  Didi bara na Wan watsa ruwa, ina Linda dan ALLAH ta dama min kunun gyaWa kafin na fito, Barrah jeki gaya mata ..
? ? Amsawa Barrahn tai tare da mi?ewa ta nufi kitchen Win da Wan gudu tana jiran Linda, ita kuma tai hanyar Wakinta.........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



......Da mamaki Maanal ta dinga bin akwatin Huznah da aka kai Wakinta da kallo, sai dai batace komai ba ta tuSe kayanta ta nufi bathroom. Wanka tayo da alwala, sai da ta gyara jikinta tsaf tai sallar isha'i sannan ta dawo falon. Kunun da ta saka Linda ta haWa mata kawai ta Wan sha, sai magungunanta da Shahidah ke bata da kanta dan ma kada tai wasa. Suna nan suna ?ar hira ita da Shahidahn dan Huznah ba saka musu baki take ba sai ma latse-latse take a waya kamar bata falon mai gidan ya dawo...
? ?? Dalilin dawowar tasa yasa Shahidah shigewa part Winsa, aka bar su Maanal kawai. Sai itama ta mi?e ta taimakawa Linda suka kwashe su Barrah da sukai barci a falon. Daga haka tacema Huznah ita zata shige ta kwanta. A ciki Huznah ta amsa mata, Maanal bata damu ba tai wucewarta. Ita kuma ta rakata da harara. Maanal na shiga Wakin kiran RK ya shigo mata, bata Waga ba sai da takai kwance, ta gaisheshi a mutunce kamar yanda ta saba, daga haka ta fara mata hira da albishir Win gobe in sha ALLAHU yana hanya. Ganin yanata jan hirar ta fara masa hamma, dole yay mata sallama. Kamar jira sai ga Yazeed shima ya kira, jitai kamar zatai kuka, haka dai ta Waga.
? ? ?  Dawa kike waya haka Maanal? .
?? Furucinsa na farko kenan maimakon amsa mata sallamar da tai masa, muryarsa a cinkushe. Sai da ta Wan yi jimm kafin a nutsenta ta bashi amsa da,  Rafeeq ne! .
? ? ?  Rafeeq!? .
? Sai da ta Wan lumshe ido saboda yanda ya maimaita sunan RK Win a kausashe yanzu kafin ta ce,  Uhhum! .
? ? ??  Okay yayi ?yau . Ya faWa yana yanke wayar. Shiru tayi na mamakinsa, Yazeed mutum ne mai nutsuwa da fahimta, sannan yana da ha?uri, zata iya cewa tunda ta haWu da RK bai taSa tunkararta akan al'amarinsa ba sai dai can a tsakaninsu. Amma yau minene ya hasalashi haka? Kai ita kam taga takanta. RK ya nuna fushi idan ya ganta da Yazeed ko tana waya da shi, yanzu shima kuma ga Yazeed Win zai fara nashi. Ita kam dan ALLAH karsu rikita mata lissafi mana, suma barta da abinda ya dameta...
? ? ?? Tana cikin wannan yanayin Huznah ta shigo, bata mata sallama ba dan haka itama tai kamar bata san da shigowarta ba. A gadarance ta jefa wayarta saman gadon, fuuu ta wuce bathroom, ita dai Maanal binta tayi da kallon mamaki, bata jimaba ta fito, ta buWe akwatinta ta canja kaya sannan ta hawo gadon. A mamakin Maanal dai taji Huznah na jera fillos a tsakkiyarsu, sai kawai abin ya bata mamaki ta saki murmushi. Bata kulata ba tai addu'a taja barko.
? ? Barci take son yi saboda gajiya da tayi ga gobe ma dole ta fita aiki, amma Huznah ta hanata sai charting take, kuma voice note. Tun Maanal na dauriya har dai ta mi?e tsam a gadon ta koma saman sofa doguwa dake a Wakin, kwanciyar bata mata wani daWi ba amma ta ha?ura anan Win duk da nan Win ma ba tsira tai ba tana jin Huznah Win da bata fasa abinda take ba harda su SaSSaka dariya kamar ba dare ba. Daga ?arshe bata san sanda tayi barci ba ita dai, dan itama ALLAH ya taimaketa barcin yay awon gaba da ita. Da asuba kuma koda ta tasheta ?in tashi tayi, sai kawai ta ?yaleta. Har gari ya waye tai shirin fita aiki Huznah ta?i tashi salla. Sai kawai ta fice abinta tana nema mata shiriyar UBANGIJI.

? ?? Yau ma Shahidah ce ta ajiyeta a office sannan ta wuce nata aikin, tun a harabar companyn suke gaisawa da mutane har ta shigo. Dama dai tsakaninta da kowa gaisuwar ce, rashin yawan fara'arta da yawan magana ma kesa mafi yawansu ke kiranta da sunan mai girman kai. ?an rukuninsu mutum uku ne kawai sukazo, ta gaisa da su taja kujerarta ta zauna. Dama ita kaWaice mace a cikinsu, shiyayasa daga gaisuwa sai zancen aiki ke haWata da su. ALLAH kuma ya taimaketa kujerarta itace farkon shigowa, suma ganin yanda take haWe fuska da kame kanta yasa suke shakkar shige mata duk da wasunsu na kwaWayin hakan tun ma a ran farko da tazo. Aikinta ta kamayi kawai kamar yanda ta saba, a haka sauran suka iso, kowa yazo zata Wago su gaisa daga haka ta maida kanta ga aikinta. Kusan eleven ta tashi zuwa office Win Director Mustapha.?Duk da kallo suka bita, wanda ke zama kusa da ita cikin yin ?asa da murya yace ma na kusa da shi,  Wato yarinyar nan akwai girman kai wlhy Ema.. .
? ?? Caraf Yaqub da ke facing Winsa ya ce,  Ba wani girman kai wlhy, ta dai san kanta ne. Idan mace ta cika faran-faran ace ma ballagaza, idan ta kame kanta ace girman kai. Kufa lura ita kamar yanayintane ma haka, miskila ce kawai .
? ??  Tab ai ni kuma bana son miskilar mace gaskiya. Ita mace ko yaya da sau?in kai tafi daWin rayuwa .
? ?  A wajenka ba.....
 Oh to kodai santa kake yine wai Yakub .
? ? ??  To laifi ne idan na sota Zaharadeen, naga dai namiji ne ni. Kuma Win inda zata amsa muku son nata kuke shiyyasa kuke gulmarta. Yarinya na girmamaku amma bakwa gani. Yanzu da sakewa take cikinmu da surutu da fara'a sai kuma ace ta saki kanta a tsakkiyar maza. Ta kuma kama kanta kunzo kunayi da ita mtsooww! .
? ? Ya mi?e ya bar musu wajen. Duk da kallo suka bisa, sai kuma suka kalla juna cikin yamutse fuska.  Wannan guy Win na kula fa son yarinyar nan yake .
? ? ??  Oh kai sai yau ka gane, ai na jima da fahimtar hakan. Kuma banga laifinsa ba dan koni ALLAH na ?yasa .
? ?? Dariya suka sanya a tare harda tafawa.

? ? Maanal kam da bata ma san sunai ba kanta tsaye office Win Designer Director Mustapha ta nufa. Tana shiga Elevator massage ya shigo wayarta, ?o?arin dubawa ta fara yi sai taga Yazeed ne. Nutsuwa tai a karanta sa?on, sai ya zam har elevator Win ta tsaya hankalinta nakan wayar, a haka tai ?o?arin fitowa batare da duban gabanta ba. A dai-dai lokacin da CEO AA Darma ke isowa ga elevator Win Assistant Winsa biye da shi. Ya riga ya kawo jiki, kamar yanda itama ta riga ta taho gashi hankalinta ba a wajen yake ba balle taja da baya kawai sai jitai ta bugi abu. A Wan razane tayi baya, wayarta ta suSuce ?asa hakama gilashin idanunta da document Win duk suka tarwatse kasa.
? ?? Sosai ta Wago cikin Sacin rai dan ganin wanene da wannan aikin bayan ta gama bin kayan da kallo Waya bayan Waya. Shima sai hakan ya zam dai-dai da tashi Wagowar bayan ya gama bin kayan da kallo musamman zanen agogon da yay masifar Waukar hankalinsa. Wani kalar zubama juna ido sukai kowanne fuskarsa a matu?ar tamke, sai dai na Maanal Win ya Wan cika da ruwan hawaye dan har ?yallinsu ya nuna. Yanda tai masa ?iri da idanu sai ka Wauka zata fara zazzaga masa ruwan bala'i ne, dan tuni AS Winsa da wasu da suka zo wajen bayan faruwar accident Win duk sunyi kasare cikin Wunbin mamaki suna son suga mizai faru. Amma mi, a mamakin kowa sai suka ji cikin sanyin murya Maanal Win ta furta,
? ? ?  I'm sorry Sir .
? ? Ta ?are maganar da rissinar da idanunta harma da kanta cikin nuna girmamawa. Shi kansa wani irin rumtse idanu yay da masifar ?arfi, sai kuma ya zagayeta ya shige cikin elventor Win batare da yace komai ba. Wannan abu ya bama kowa mamaki, hatta da AS Winsa daya gama tattaro ma Maanal kayayyakinta. Wannan shine abu na biyu daya faru tsakanin Boss da Maanal ko yace na uku harda kaita gida da sukai jiya. Shi sai ma ya rasa kalar tunanin da zai yi akan al'amarin.
? ?? Sauran ma duk sun ma Maanal sorry, kanta kawai ta jinjina musu da Wan yin murmushi ta wuce zuwa office Win Director Mustapha. Bayan tayi knocking aka bata iznin shiga. Ta gaishesa da girmamawa kamar yanda ta saba yima kowa. Shiko ya amsa fuskarsa da murmushi tare da nuna mata kujera. Kanta ta Wan girgiza masa da ajiye document Win hannunta saman desk Winsa.
? ? ??  Sir dama na kammala ne shiyyasa nace bara na kawo maka sai ka duba .
? ??  Yauwa sister Maanal dama kamar kin san yanzu nake shirin nemo ki, dan ban jima da baro office Win CEO ba akan batun. Woow ai sai naga ma kamar waWan nan sunfi ma wancan Win ?yau .
? ? ? Ita dai Maanal komai batace da shi ba kanta a ?asa, sai da ya gama santinsa sannan ya sallameta akan ta zama cikin shiri koyaushe za'a iya nemansa a conference room. Koda ta koma saita samu har gulmar abinda ya faru tsakaninta da CEO Win taje can. Dan ta wuce wasune nayi batare da su sun farga da ita ba. Kowa bata kula ba har abokan zamanta da wasu ke Wan ?us-?us ta zauna ta cigaba da aikinta.

? ? Bayan anje break daga massalaci Maanal ta dawo kan aikinta, dan tunda tazo companyn bata taSa zuwa kitchen cin abinci ba. Kullum da abinda zata ci take zuwa daga gida, dan haka bata taSa maida hankalinta ba. Tana cikin aikin ta samu kira daga head of

23 / 80