AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 80

63K to 66K   out of 237.4K words

hannu ya rungumota tare da ?o?arin haWe bakinsu. Da sauri ta kauce tana dariya, sai ma ta zare jikinta gaba Waya ta mi?e daga kusa da shi. Fuska ya Sata da mata nunin ta dawo amma ta ma?e masa kafaWa.
? ? ??  Shike nan ni kike ma rowa ko? .
?? Murmushi ta masa kawai.
Ya Wan ?ara jinjina kansa da nufar ?ofa yana faWin,  Zan rama . Ya fice. Nan ma murmushin kawai tayi, sai da taji ficewarsa daga sashin gaba Waya ta koma jagwab a saman gadonta zuciyarta na wani irin harbawa. _(Jiya Huznah da uwarta sun sameni wai tana son zuwa wajen ?ar uwarta Shahidah tai sati Waya)_ kalamansa suka shiga dawo mata cikin kunne da amsa kuwwa. A bayyane cikin dafe kanta ta ce,  Ya ilahil'alamin Basariyya mi kike shirya min kuma? Ni nasan dole wannan zancen akwai wata a ?asa . Rashin mai bata amsa yaa sata yin shiru ta cigaba da zancen zuci. Ta jima a haka kafin hankalinta ya dawo jikinta ta mi?e ta shiga kitchen haWama su Waleed abincin breakfast dana tafiya makaranta. Tana aikin tana tunani nan ma harta kammala. Tana cikin haWa musu suka shigo sanye da uniform Winsu. Duk gaisheta sukayi suna mai rungumeta, tai musu murmushi tana amsawa.  Har an shirya ?an makaranta? .
? ? ? ? Kawunansu duk suka shiga Waga mata. Sai kuma cike da shagwaSa irin ta autoci Waleed ya ce,  Ammie mikika dafa min? .
??  Oh tama dafa maka bata dafa mana ba, kuji min Wan iya . Cewar Hameed yana hararsa da kai dankali bakinsa. Murmushi Ammie tai da faWin,  Ni dai kunga kuyi ku wuce bana son surutu yau Win nan. Kowa ya duba abinda yake so shi aka dafa masa .
? ? Murna suka shiga yi, sai kuma suka Wauki wanda zasu ci suka koma work table dake kitchen Win kowa yaja kujera sukai zaman ci. Ammie kuwa ta fara Wan wawwanke kwanikan data Sata dan bata son taga ambar kaya da datti, duk da tasan yanzu mai aikinta zata zo ta fara aikin ta gwammace ta tsaftace waWan nan Win kafin ta iso. Tana kammalawa suma suka kammala. Sallama sukai mata kowa ya Wauka lunch box Winsa suka fice. Sai kuma six dan makarantarsu tana tare da islamiyya ne...

? ?? Koda ta koma Waki saita gagara shiga wankan datai niyya, zama tai ta Wauki waya ta shiga kiran Nene. Ba'a wani Wauki tsawon lokaci ba Nenen ta amsa kuwa. Sai dai suka gaisa da tambayar juna gida kafin Ammie ta ce,  Nene yau zan sameki a gida? .
? ? Daga can Nene ta ce,  Eh bazanje ko'ina ba. Dama nina naso kiran naki ai sai kika kirani, zaki shigo ne? .
? ? ? ?  Eh Nene indai ya bari zuwa anjima kaWan zan shigo .
? ?  To shike nan sai kinzo Win ina saurarenki .
? Daga haka sukai sallama kowa ta yanke.....

? ?? & Sai kusan sha biyu Ammie ta samu damar barin gidan. Dan da ?yar Daddy ya barta dan ma tace masa kitso zataje. Da yake yasan tana zuwa kitson kuma bai kawo komai a ransa ba. Shi irin mutanen nan ne da sam basa son yawan fitar iyalansu, sunfi bu?atar ko yaushe kina gida, shiyyasa a cikinsu babu mai fita aiki ko wani business. Ammien ce ma taga bazata iya wannan kashe kan ba komai sai abinda namiji ya baka tuni ta fara kasuwancinta a gidan Nene. Kuma Alhamdullah komai yana tafiya dai-dai.
? ? Gidan Nene gida ne a matsayin family house. Dan kuwa ita da duka matan ?a?anta suna a cikinsa. ALLAH yayima mijinta rasuwa tuni, ita ta cigaba da gwagwarmaya da yaran har suka girma. Yanda ta horesu yasa duk suna da sana'o'in su, dan babu mai zaman banza. Badai kuWi garesu ba amma ci da sha gwargwado da sutura irin ta gidan mai rufin asiri sun wuce da wannan kam. Sashen Babban Wan Nenen ta fara shiga, matansa biyu, yaso auren Ammie a baya matarsa nata zuba rashin mutunci akan hakan sai ALLAH ma bai ?addara ba, to ashe kishiyar dai na bibiyarta, dan bayan Ammien tayi aure ya auro budurwa gal a leda yanzu haka haihuwarta uku a gidan itama. Wannan dalilin ne yasa sama-sama suke da Ammien. Koda ta shiga a kitchen ta samu Maman Salima kamar yanda suke kiranta, ta wani zubama Ammien ido zuciyarta na bugawa, tuni murmushin fuskarta kuma ta Sace. A yanzu kam ba kishin Ammie ne ke damunta ba hassada ce. Ko'a jikin Ammie ta gaisheta da tambayarta yaranta. Daga kitchen Win ta amsa a da?ile, sai dai idonta na'akan suturar jikin Ammie.
? ? ?  A'a Aunty Asiya ce a gidan namu? .
? ? Amarya dake le?owa daga falonta ta faWa. Murmushi Ammie tai mata da faWin,  Aiko nice Amarya .
? ?  To sannu da zuwa Bismillah ki shigo .
Babu musu Ammie ta shiga, falon ?al an gyara shi sai ?amshin turaren wuta yake kamar bamai ?ananun yara ba. Gashi da gani tana fama da laulayin wani cikin ne ma. Cike da girmamawa ta gaida Ammie kafin ta fita sai gata da ruwa.
? ? Ammie ta ce,  Amarya ai da baki wahala ba ma. Ina yaran nawa ko duk an wuce makaranta? .
? ? ?  Duk sun wuce shiyyasa ai muka samu lafiya Aunty, sai Ameen kawai yana barci ne .
? ?  A'a ai shima ko ya kamata a sakashi makarantar tunda naji bakinsa akwai surutu .
? ? ?? cikin dariya Amarya ta ce,  Sosai kuwa Aunty .
? Bayan Ammie ta sha ruwan ta fito, amarya biye da ita har Wayan sashen. Nan kam mace Waya ce, itama ta amshi Ammie da girmamawa da mutuntawa, bayan sun gaisa ta fito ta shiga wajen sauran suma su biyu. Daga haka ta shiga wajen Nene. A falonta ta sameta zaune ta baje kaya tanata lissafi. Sai wata dake gefenta tana tayata. Da mamaki Ammie ta furta,  A'a Saratu yaushe a gari? Nene shine baki sanar min munada da ba?uwa ba? .
? ?? Murmushi wadda aka kira Saratun tayi, yayinda Nene ta Wan taSe baki da faWin,  Zuwan nata ne dama ya sani nemanki, tunda ita dai fitinar gidanta bata ?arewa .
? ?  Tofa wani abunne kuma ya faru Nene? .
? ?  Humm Asiya ke dai cire mayafi a kawo miki abinci, ga waina can nasa tun Wazun aka sayo miki gidan Hajiyayye ALLAH yasa ma bata huce ba. Saratu Wakko mata .
? ? Kasancewar Ammie na son wainar sosai ta zauna taci, sai da ta ?oshi sannan suka fara maganar Saratun. Sosai ran Ammie ya Saci, tace bako zata bar gidan ba har sai sauran ?an uwanta sun dawo ai zama akan al'amarin Saratun, wannan karon dole su Wauki mataki akan mijin nan nata mara mutunci, dan bazasu yarda da auren duka ba. Bayan sun gama tattauna wannan suka koma batun nasu gidan, ita kanta Nene ta jinjina batun zuwan Huznah Abuja. Amma sai ta kwantarma Ammie da hankali akan ta barta taje Win, amma sun kira Shahidah sun gaya mata komai, sun kuma mata gargaWin ta sanya ido sosai. Ammie dai bata bar gidan nene ba sai bayan magriba da sauran ?a?an Nene huWu ringis suka dawo kasuwa suka tattauna batun Saratun. Da zata tafi sai ta wuce da Saratu can gidanta akan zata huta kwana biyu.

_________&

? ? ?? Washe gari ?an Dubai suka wuce domin haWo kayan lefe dana shagalin biki harma da kayan Wakin amarya. Itama Huznah ta wuce Abuja, sai dai abinda ya sake tabbatar ma da Ammie akwai wata a ?asa ko sallama Huznah batai mata ba. Sai bayan ta tafine uwar ta shigo tana cema Ammien tayi hakuri wai driver ne ya azalzali Huznah Win shiyyasa bata shigo ba. Murmushi kawai Ammie tai ta ce,  Babu komai ai ALLAH ya tsare hanya ya kaisu lafiya . Daga haka bata sake tofa komai ba dole Hajiya Basariyya Win ta fito tana taSe baki, dan taso ne Ammie ta biye mata su Wan yi gulmar ?an tafiya Dubai. Itama Ammien kuma ta ganota shiyyasa ta mata haka...

? ?? Maanal bata san wainar da ake toyawa ba. Da safe dai sanda Shahidah zata sauketa ne a office take gaya mata zuwan Huznah Win. Dan yanzu itace ke kaita, wani lokacin ta dawo a taxi. Tun randa AA Darma yay mata wannan gargaWin ta so yima RK magana, sai kuma wani ikon ALLAH ma a daren ranar RK Win yay tafiyar gaggawa har yanzu bai dawo ba. Dan itama a waya ya kirata ya sanar mata. Busy kuma da yayi sosai yasa ba koyaushe suke waya ba sai ya samu lokaci. Amma ya tabbatar mata bazai wuce kwanaki biyar ba. Yau kuma kwanansa huWu kenan gobe idan ALLAH ya kaimu take saka ran dawowarsa. Yazeed dai ne da yake yana garin yanzu kullum da dare sai yazo gidan Shahidah Win, dan da farko yaso ya mata fushi akan batun aiki wai bata sanar masa ba sai Daddy ya gaya masa, ha?uri kawai ta bashi da nuna masa ai Daddy Win dan ya isa da su ne su duka shiyyasa. Ya dai ?yaleta kawai, amma a ransa ya gama ?udirar wannan aikin sai ta barsa duk da yanada planing Win anan Abuja Win zata zauna ita ko anyi bikin su.
? ? ? A gajiye ta fito daga office Winta zuwa office Win Designer Director Win dake kula da aikin nata, har yanzu dai suna akan project Win nan daya haye mata. Bayan tayi knocking aka bata izinin shiga. Ganin yana haWa kaya alamar zai tashi ne a sanyaye tace,  Director badai zaka tashi bane ba? .
? ? Kallonta yay fuskarsa da murmushi, dan yanzu kam ta fara sabawa da su. Yanda kuma take girmamasu da bawa kowa hakkinsa da kame kanta yasa su jin ?aunarta a rayukansu.
? ? ??  Lallai ba?ya kallon agogo, bakiji yanda company yay tsit ba kusan duk an wuce ai .
?? Agogon ta kalla kafin ta sake dubansa, dan tabbas magrib tama kusa.  Ayya ALLAH ban lura ba. Dan ALLAH ka samun hannu a document Win nan, so nake yanzu na mi?asa office Win CEO idan ALLAH ya taimakeni da safe sai ya duba shi da wuri kafin zaman meeting .
? ? ?  Wayyo ba?ya jin tausayina ALLAH, kinji bayana kuwa ga Madam nata kira na yau birthday Winta. Amma kawo nayi sauri .
? ? Godiya ta masa tare da matsawa ta ajiye masa file Win, tana daga tsaye ya shiga dubawa. ?agowa yay ya dubeta cike da tsokana ya ce,  Anya ba kwanan nan zan baki kujerar nan ba Manaal Giro? Ke Win ?uruwace fa. ?an murmushi kawai tai masa kanta a ?asa dan iyakarta da su kenan, shiyyasa duk da yanda take girmamasun wasu ke mata kallon mai girman kai da faWin rai. Wasu a cikinsu duk sun ?yasa, sai dai kamewarta na zame musu barazana, ga kuma RK da kowa ya tabbatar budurwarsa ce a companyn yanzu duk da kuwa yau ne take cika kwanta na takwas a Companyn. Bayan ya saka mata hannun ta karSa tana masa godiya. Sallama ta masa ta fice, haka ya bita da kallo zuciyarsa na zallo. Tun ranar farko da sukama Maanal interview yarinyar tai masifar shiga masa rai. Abinda ya faru tsakaninta da Boss yaso taka masa birki, amma daga baya sai yaga kuma komai bai sake faruwa ba, sai sabon soyayyarta a zuciyarsa ya dawo fil, sai dai kuma Maanal babu sakin fuska........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? *_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......Ita kam koda takai file office Win Boss ta ajema AS office Winsa ta koma ta cigaba da aiki, dan akwai abinda take son kammalawa kafin ta wuce gida. Kiran sallar magriba ya sata ?arasawa sauri-sauri sannan ta tashi tayo alwala ta haWa kayanta ta kashe komai ta fito dan su Yaqub tuni duk sun wuce sai ita kaWai. Shiru babu motsin kowa duk an wuce. Sai offices Wai-Waine ?an over work irinta koma wanda suka fita ke'a buWe. ?ananun ma'aikata ma ta wuce kusan mutane huWu basu wuce ba, koda ta?fito harabar companyn ma motoci biyar kawai ta gani sai mashin biyu alamar na wanda suka ragene. Idanunta suka sauka akan motar boss. Janyewa tai tana taSe baki, shi dama ai yafi kowa iya over work, dan kullum shine ?arshen barin office. Masallaci ta nufa domin gabatar da magriba. Bayan an idar koda ta fito bata koma ciki ba, hanyar gate ta nufa abinta a ?afa. Street Win shiru babu yawaitar mutane a ?afa sai motoci, sai dai ko'ina akwai haske kamar kana wata ?asa ba Nigeria ba. Taxi nada wahalar samu a wajen kasancewar duk manyan ma'aikatu ne ata wajen, sai gidajen cin abinci da suma ba laifi suke da yawa ta wajen da shopping malls guda biyu dake can farkon shigowa. Tsoron kar dare ya sake mata ya sata cigaba da tafiya a ?afa tana jin nadamar kaiwa haka bata tafi gida ba, har Shahidah cewa tai zata aiko a Wauketa idan ta gama tunda tace ita karta biyo Waukarta yau tana da aiki amma tace mata a'a zata hau taxi. Tayo tafiya babu laifi zuciyarta ta fara karaya, dan ?afafunta sun fara gajiya. Mamakine ya kamata ganin ?ammata tsaitsaye kamar masu jira azo Waukarsu, amma abinda zai baka mamaki suna da yawa duk da kowanne yana tsaye ne shi kaWai ko su biyu. Cigaba tai da tafiyarta dai tana Wan kallonsu sai taji ana horn, da sauri duk hankalin ?ammatan ya koma wajen motar, wasu ma duk sun nufi motar ne, sai dai kuma mai motar bai tsaya ba ya cigaba da bin bayan Maanal ne ana kuma horn Win dai. Da sauri ta Wan ja da baya sakamakon shan gabanta da akai da motar, cikin wani irin Sacin rai ta Wago dai-dai mai motar na sauke glass Winsa. Babban mutum ne da a shekaru ma zai iya haihuwar su Shahidah bama ita ba, yana daga baya kwance driver Winsa a gaba, cikin tsareta da ido ya sakar mata murmushi. ?auke kanta tai da sauri ta raSa ta wuce wani irin Sacin rai na mamayeta. Jin an ?ara biyo bayanta da mota ana mata horn again ta tsaya cak, cikin matu?ar fusata da harzu?a ta Wago dan ta gama shirya yima tsohon banzar nan zagin ?are dangi, amma sai kawai taga motar boss ba wancan bane. Kafin ta iya haWiye abinda ke bakinta AS ya fito daga gaba, kai tsaye inda take ya iso, furkarsa da murmushi ya furta,  Sister Maanal bismillah ki shiga . Yay maganar yana mi?a mata hannu da nufin amsar kayan hannunta. Kai ta girgiza masa tare da janye hannun nata tana faWin,  Karka damu na gode .
? ? ? ? ?  Idan shi bai dace ba, inaga ni kamar zan dace tunda dama ni na fara tayawa . A bazata taji muryar tsohon nan cikin kunnenta daga bayanta. Jitai gaba Waya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta Waga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya ri?e mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. ?o?arin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaWa, shima kallon nata yake cikin ido. Kusan minti Waya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa lips Winsa a hankali ya furta,  Get in .
? ? ? ? Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko Wigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya Waya side Win ya shiga mazauninsa ya Wauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matu?ar Sace ya sake takowa inda Maanal take. Ai yana buWe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji fuska da murmushi ya furta,  Bye bye grandpa . Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja suka wuce.
? ? ? Da wani irin kallon Sacin rai dattijon yabi motar da kallo, sai kuma ya jinjina kansa tare da cije lips da ?arfi ya koma tashi motar. Da sauri driver Winsa ya buWe masa ya shiga ya maida ya rufe suma suka bar wajen....

? ? ? ? Sosai Maanal ta takure jikinta waje guda, yayinda idanunta ke'a lumshe bugun zuciyarta kuwa gaba Waya ya sauya daga normal bugu. Ambaton sunan ALLAH kawai takeyi tare da ?o?arin danne kukan dake son kufce mata.
? ? ? AA Darma dake a gefenta kam tunda ta shigo bai ko kalleta ba. Gaba Waya ya tattara hankalinsa ne ga document Win hannunsa da dama shi yake dubawa kafin suga Maanal Win, koda yake bama shine ya ganta ba, AS ne ya ganta cike da mamaki ya furta (kai wannan ai Sister Maanal ce Alhaji Bukar ya tsare a hanya halan bata sami abin hawa bane har yanzu). Driver na tambayar AS wacece ita Win AA Darman ya daka masa tsawa akan su dakata, shine dalilin tsayawar tasu.
? ? ? ? A yanzun ma driver ne cikin Wari-Wari ya furta,  Sir! Zamu fara saukeka ne kafin a kaita? .
? ?? Shiru bashi da alamar amsawa. Sai da ya mula dan kansa batare da ya bar abinda

22 / 80