AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 80

72K to 75K   out of 237.4K words

jinjina girma da tsaruwar gidan Daddy, hakama gidan Didinta Shahidah gidane mai ?yau da ?awa. Sai dai gidan nan ya matu?ar disashe mata waWan can da take tunanin babu kamarsu. Hatta da parking space a tsare yake anan.
? ? ?? Tunda suka fito su kansu yaran ke bin ko'ina da kallo baki a buWe, Haneeff dai daya kasa ha?uri matsowa yay kusa da Maanal cikin raWa ya ce,  Mie-mie! Uncle R house ya haWu kamar ba'a Nigeria ba .
? ? ? ? Kasa cema yaron komai tayi, sai hannunsa daya ri?o nata ta Wan matsa kaWan. Dai-dai nan RK dake tattaro kayan tsarabar da bai san ko minene ba ya juyo garesu. ?aramin murmushi ya mata ganin yanda take binsa da kallo, batare da yace komai ba ya nuna mata hanya alamar suje, tare da kama hannun Barrah. ?auke kanta tayi kamar bata fahimta ba, sai ya sake sakin murmushi yay gaba, dan wannan yana Waya daga cikin halayenta dake matu?ar birgesa. A gidan sassa ne har kusan shida. Kuma kowanne da tsarinsa, sannan tsakaninsa da Wan uwansa akwai ?ar tazara ta yanda baka isa sanin mi nacan keyi ba, ko shi yasan mi kakeyi a naka part Win.
? ?? Part na tsakkiya a hannun dama suka nufa, RK ya danna bell tare da Wan juyowa ya kalla Maanal.  Ni dai kar aje ana fushi dani a gaban Aunty na . Yay maganar yana kashe mata ido Waya. Harararsa ta Wan yi kawai, tare da Wauke kanta. Shi kuma sai ya sake sakin murmushi. Zaiyi magana aka buWe ?ofar. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce sa'ar Maanal ba, cike da girmamawa ta Wan rissina tanama RK Win sannu da zuwa. Duk da jikinta fes yake cikin tsafta a kallo Waya zaka fahimci mai aiki ce, sai dai masu aikin ma irin wanda ke samun kular nan dan babu wani nakasu a tare da ita. Kayan hannun RK Win ta amsa, yayinda shi kuma cikin dakewa kamar bashi ba yake tambayarta  Aunty fa!? .
? ? ??  Tana upstairs....
?? Kansa kawai ya jinjina mata, batare da yace komai ba suka ?arasa shiga cikin falon da yasha black & golden color na kujeru da labulale, sai wani irin ?amshin turaren wuta ke tashi mai ratsa zuciya. Ga sanyin ac mai kashe jiki. Gaba Waya jikin Maanal sai ya ?ara sanyi. Bata sake tsinkewa da al'amarin ba sai da ya danna wani maSalli ?ofar glass Win dake kamar bango guda ta zuge kanta suka shigo wani falon, nan kam komai golden yellow & white ne, shima dai babu kowa sai ?amshi dake tashi, wayar da yake dannawa ya kai kunnesa, ba'a wani jima ba aka Waga.
? ? ?  Aunt mun iso . Ya faWa cike da girmamawa. Maanal dai data zama kamar wata gunkiya bata san amsar da aka bashi ba taga ya juyo ya kalleta da murmushi, sai kuma ya furta,  Okay gamu nan . Yana yanke wayar.?
? ??  Sorry muje tana sama .
Ya sake faWa idanunsa akan Maanal Win. Kanta kawai ta jinjina masa batare da tace komai ba. Sai dai tana mamakin ta ina kuma zasu bi zuwa saman dan bataga hanya ba sam anan. Amma a mamakinta sai ya nufi wata ?ofa da su, anan ne taga ?afar benen da shima aka ?awata matu?a, dan hatta a ?asansa ma wasu kujeru ne guda biyu aka tsara da gani wajen zaiyi daWin hutawa. Haka dai suka haura upstairs Win Maanal na sake jinjina jin daWin da masu hannu da shuni keyi a ?asar nan. Dole su manta da talaka, dole talaka yasha wahala dan bataga ta yanda za'a iya tunawa da rayuwarsa ba anan. A sama ma wani tsararren falon suka samu, wanda aka ?awata da ash color na kujeru dama labulalen, nan Win ma dai ?amshin turaren ne yay musu sallama da sanyin ac kaWan, sai kuma nutsatstsiyar muryar dattijuwar dake musu lale marhabun cike da ?asaita. Kasancewar RK ya rufe Maanal yasa bata ganin dattijuwar itama bata ganinta, sai dai muryar ta wani irin dakar mata ?irji.
? ? ?  Rafeeq ?aniyarka, dalla gyara ka wani rufe min ?anwar tawa bana ganinta .
? ?? Dariya RK yayi tare da matsawa gefe yana faWin,  Oh Aunt ni yau baki son ganina kenan? .
? ? ? ? Baki ta buWe zata bashi amsa amma sai ta gagara hakan, sakamakon saukar idanunta akan Maanal da ita nata idanun ke kallon ?asa, dan RK Win na matsawa daga rufetan da yay ta rissinar da idanunta saboda yanda bugun zuciyarta ke ?ara ?arfi. Ga wani irin yanayi mai wahalar fassara dake ratsata. Hakama zuciyarta ta mata nauyi matu?a a cikin ?irjinta.....
?? Gaisuwar Barrah da Haneeff ce ta katse dattijuwar daga kallon Maanal, ta saki ajiyar zuciya da sakin murmushi tana mi?ama yaran hannu da faWin,  ?anwata kinga ?araso mana, Bismillah zo gareni .
? ?? Sake motsawa zuciyar Maanal tayi a karo na babu adadi, dan Muryar nan tana mata wani irin amsa kuwwa ne da maimaita kanta a matsayin wata murya da amonta ya faru ya kuma shuWe a duniyarta ta baya. Amma sai ta dake, cikin yanayinta na nutsuwa ta cigaba da taka lallausan carpet Win dake tsakkiyar kujerun zuwa inda dattijuwar take zaune, dan tana zaune ne daga ?asa abinta duk da tima-timan kujerun dake falon. Cak Maanal ta tsaya yayinda take gab da kaiwa inda dattijuwar take, bakomai ya sakata tsayawar ba sai murya ta biyu data daki tsakiyar kunnenta tayi amsa kuwwa a cikin kanta. Sam batai zaton akwai wani bayan dattijuwar a cikin falon ba duk da taji wani ?amshi bayan na turaren da aka saka a gidan da wanda ta tabbatar dattijuwar keyi. Sai da RK ke faWin,  Wai dama da gaske kake daga massallaci gida zakayo ashe? .
? ? ??  Kaje nemana ne? .
? ? AA dake kishingiWe a saman lallausan carpet Win kusa gab da dattijuwar dan filo ne kawai ya raba tsakaninsu gabansa wasu document ne barbaje, sai dai a hannunsa shi novel ne yake karantawa, a maimakon shaddar Wazun yanzu kam ?ananun kaya ne ba?a?e a jikinsa. Amsar da RK ya bashi yana nuna Maanal da faWin,  No naje Waukar Maanal ne kawai dai ya sashi wani kallar Wago idanunsa ya sauke a kan Maanal Win data kasa gaba ta kasa baya. Dai-dai nan itama Dattijuwar da hankalin ta ke akan su Barrah ta Wago tana maimaita sunan.
? ? ??  MAANAL! Sai kuma ta mi?e zaram.  Rafeeq da gaske Maanal Wina ce kamar yanda zuciyata ta ayyana min yanzu-yanzu ko suna ne yazo Waya, to amma akwai kamanni mafa ta kai ?arshen maganar tana ?arasowa inda Maanal take. Lallausan hannunta mai Wauke da zabba masu ?yau da Waukar idanu, tare da bangles takai kan haSar Maanal data lumshe idanunta da suka cika da ?walla ta Wago. Sosai take raba idanunta akan fuskar Maanal Win, sai kuma ta juyo ta kalla RK da shima ya mi?e cike da mamaki, janyewa tai ta maida ga AA da ya maida idanunsa ga book Win hannunsa sai dai tuni abinda yake karantawar ya suSuce masa.
? ? ? ?  Auta gane min nan, wlhy Maanal ce ko? Ko Auta Manaal Wina ne dai ba wata ba. Ajwaad taso, taso dan ALLAH ka tayani gani ko idanun nawane dai ba Baby ba bace....
? ?? Da wani irin ?arfi AA ya rumtse idanunsa batare daya Wago Win ba, ko motsima baiyi ba daga yanda yake. Sai RK ne ya ?araso wajen cikin sassarfa yana faWin,  Aunt da gaske kin san Maanal Wina? Maanal Please! Da gaske kema kin san Aunty na? . Duk ya ruWe da farin ciki shi kam.
? ? ? ? ? Cikin rawar muryar kuka Maanal da tausayin yanda dattijuwar ta rikice ya sake mamayeta, a hankali ta shige jikinta tana faWin,  Oum nice, Maanal Winki ce Oum. Dama baki manta dani ba, dama zan sake ganinki? Ashe muna da rabon sake haWuwa kafin na koma ga ALLAH . Wani irin kuka mai ban tausayi ya suSuce mata, sai dai hakan bai hana muryarta fita cikin nutsuwa da sanyi ba. Sanyin dake bayyana tasirinsa a jikin AA, duk yanda yake sake kamewa da dakewa abin na neman fito da kansa. Dan Barrah da kukan Auntyn tasu ya sakasu yin narai-narai da idanu suma zasuyi kukan ta matsa gab da shi tana faWin,  Uncle kaga Mie-mie na kuka ita da Grandma . Amma ina baiji yarinyar ba, sai da ta Wan girgiza shi sannan firgigit ya buWe idanunsa da suka kaWa matu?a tare da Wagosu ya sauke akan yarinyar. Dai-dai kuma Barrah ta mi?e ta nufi inda Maanal take ta rungume mata ?afafu tana kiran sunanta.
? ? ? ? ?ago Maanal Oum tai daga jikinta itama tana share nata hawayen ga murmushi ya?i barin fuskarta. Hannayenta duka biyu tasa tana sharema Manaal hawayenta da suka gagara tsayawa, dan gaba Waya ma ta kasa cewa komai saboda ita kaWai tasan irin kalar farin cikin da take ciki. Juyawa tai ga RK da ke kallonsu cikin ruWani, murmushi ta sakar masa shima.  Rafeeq ALLAH yay maka albarka kaji, yau kam kayi mun babbar ?yauta daka kawo min Wiyata har gida.....
? ? ??  Aunty duk kin ruWar dani wlhy, wai kin santa ne daman? .
? ??  Sosai kuwa Rafeeq, zan iya cemaka kusan nice na raini Maanal ma .
? ??  What!? Raino fa? .
?  ?warai ma kuwa. Haihuwar Maanal ne kawai ba'ayi a gabana ba. Kunga bismillah kumuje mu zauna .
? ? ? RK dai da ?yar ya kai zaune, sai dai idanunsa akan Oum da Maanal kamar mai tsoron su Sace masa. Waya Oum ta Wauka tare da bada umarnin a kawo ruwa. Babu jimawa kuwa sai ga yarinyar nan data buWe musu ?ofa Wauke da tray wata da bazata wuce sha huWu ba biye da ita. Cike da ladabi da girmamawa suka ajiye kayan a saman Centre table, sai kuma suka shiga gaishe da su RK. A dai-dai nan Oum dake ri?e da hannun Maanal kamar mai gudun a ?wace mata ke tambayarta,
? ??  Ina ?ar uwata Maanal? Ina su Shahidah da Abban ku? .
? ? ? ??  Oum Ammie na nan lafiya Lau, hakama su Didi, wannan ma yaran Didi Shahidah ne .
? ??  Masha ALLAH! Masha ALLAH! Yanzu yaran Shahidah ne wannan? Kai jama'a ALLAH mai alkairi. Kuzo nan kuyi ha?uri ganin ?ata ya Wauke min hankali . Tai maganar tana kamo su Haneeff da sukai ?wale-kwale saboda kukan Maanal Win. Cikin Wari-Wari bakamar Wazu da farko ba suka ?araso wajen Oum Win, sai da Maanal ta kallesu da sakar musu Wan murmushi ta ce,  Itama Grandma ce ku gaisheta ku faWa mata sunayenku .
? ? ? Karo na farko yaran suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka shiga gaishe da Oum Win. Barrah ta faWa mata sunanta, da sauri Oum ta kalla Maanal. Murmushi Maanal Win tai mata da jinjina kanta.  Eh Oum sunanki aka saka mata, Ammie ce taso sakawa tun akan su Waleed, sai kuma suka kasance maza. Shine Didi na haihuwa aka saka .
? ? ? ? ? Wani irin rungume Barrah Ammie tayi a jikinta, ?auna matu?ar ?aunar Ammie na ratsa ?ashinta da Sargo. Muryarta na Wan rawa ta ce,  ALLAH sarki ?ar uwata. Ashe Asiya bata manta da ni ba .
? ? Murmushi mai ciwo da ?una Maanal ta saki batare data iya cewa komai ba. Sai wasa take da yatsunta kawai. Oum ta juya ga AA tana faWin,  Auta kaji fa ashe Asiya bata manta dani ba. Sunana aka sakama Wiyar Shahidah .
? ? ? ? ? ? Karo na farko ya saki wani irin murmushi mai ban mamaki, irin mai ma?alewa a gefen bakin nan da sai kana kallon mutum kake sanin yayi, sai kuma ya yun?ura a hankali ya ri?o hannun Barrah, matsota yay jikinsa kawai ya rungumeta. A mamakin kowa dake falon sai ji sukai ya furta,  I love you so much tunda kikaci sunan Oum na, ALLAH ya albarkaci rayuwarki .
? ?  Uncle ni banda ni? .
Haneeff ya faWa babu zato. Dariya Oum da RK da masu aikin nan sukayi, yayinda Maanal tai Wan murmushi da girgiza kanta. Shi kam AA idanunsa ya buWe sosai a kan yaron, sai kuma shima ya sakar masa murmushin da mi?a masa hannu ya ri?osa, cikin maganar nan tasa ?asa-?asa ya ce,  Kaima ALLAH yay maka albarka .
? ?? Cike da farin ciki Haneeff ya amsa masa. Shima RK da Oum duk suka amsa............
'?

? ??>??Nayi tambaya ko nayi shiru wai???.. kai Bara dai na haWiye kayana>?q?. Idan kuma akwai mai irin tunani na mu haWu a comment


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-090331810




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



........Sosai zuciyar RK ke yin kaikawo a ?irjinsa matu?a akan wannan al'amari. Ba komai ya kawo hakan ba mamakin Maanal da AA da koda wasa basu taSa nuna masa sun san juna ba. Sannan miyyasa AA Win bai sanar da Oum fara aikin Maanal a companyn sa ba kusan sati uku kenan. Ko shima dai bai san Maanal Win bane? Ala?ar iya Oum Win ce kawai da su Maanal Win?. Zuciyarsa na ?o?arin gamsuwa da hakan sai ga sallamar yayan AA Win, da'alama ma yanzu ya shigo gidan daga wajen aiki.
? ? ?? Zama yay a kujera yana sauke numfashi. Oum dake kallonsa cike da tausayawa na jera masa sannu. Amsawa yay fuskarsa da murmushi sai kuma ya Wora da gaisheta. Sai kuma ya juya ga RK yana faWin,  Barka da juma'a Uncle .
? ? ?? Amsa masa RK yay shima yana murmushin.  Wai sai yanzu kake dawowa gida? ?arfe biyar fa? .
? ??  To ya muka iya Uncle. Bakaga shi Autan Oum da yake Wan shagwaSa ne ya gudo wajenta da wuri ba . Dariya RK yayi ganin yanda AA ya dallo musu harara su duka ya maida idonsa ga novel Winsa batare da yace komai ba. Sai da suka tsagaita Maanal da kanta ke ?asa ta shiga gaisheshi ita da su Barrah. Kallonta ya Wan yi, sai kuma ya Wauke idonsa ya maida gasu Barrah yana amsa musu da murmushi. Kasancewarsa mutum mai barkwanci idonsa akan RK yake faWin,  Uncle R kodai Momyn tamu ce ne wai? Dan Wazun Oum ke sanar min zaka kawota yau .
? ? ?? Kallon Maanal RK yayi yana mai jinjina kansa fuska Wauke da murmushi.  Gatanan ai na kawo muku .
? ?  Kai kai Masha ALLAH, Momyn mu ai ban san ke bace dana dur?usa har ?asa. Matar Uncle Rafeeq fa. Bara kiga na taso ki saka min albarka ga Wanki yazo gaisheki .
? ?? Dariya Oum da RK sukayi, yayinda Maanal ta Wan Wago ta kallesa a karo na farko. Dai-dai yana ?o?arin sake yin magana amma sai maganar tasa ta ma?ale a saman harshe saboda saukar idanunsa akan Maanal. ?an wara idanunsa yayi na rikicewa, sai kuma ya maida kallonsa ga Oum dake sakin murmushi itama idonta a kansa. Ai da wani irin sauri ya mi?e ya ?arasa kusa da Oum Win ya zauna, tare da kai bakinsa saitin kunnenta ya ce,  Oum idona ne kokuwa dai kaina ne ya kwance da gajiyar aiki? Wai kin san wa nake gani kuwa? Little fa, Bestyn Auta? .
? ? ?? Kai Oum ta jinjina masa fuskarta na Wan komawa damuwa, itama a hankalin ta ce,  Itace Fawzan, Maanal ce. Itace kuma Rafeeq ya kawo mana matsayin wadda zai aura .
? ?? Ai zaram sukaga Fawzan ya mi?e yana faWin,  What!! gaba Waya idanunsa a waje sosai, sai kuma ya juya yana kallon AA daya wani share kowa yana sauraren surutun Haneeff, idanunsa kuma nakan novel da tunda su Maanal suka shigo ya daina fahimtar labarin. Sake Waukewa yay daga kan AA Win ya maida ga Maanal daketa ?o?arin saisaita kanta. Murmushi ta sakar masa mai sanyi, cikin muryarta mai zurfi da rashin son hayaniya ta ce,  Yaya F .
? ?? Maimakon amsawa sai yakai zaune jagwab a kujera yana faWin,  Ya ilahil'alamina da gaske Little Win ce dai Oum. Ni abin ma sai yake min kamar mafarki wlhy .
? ? ? ?  Bakai kaWai ba Fawzan, ni kaina kallon komai nake kamar a mafarki, yau Rafeeq ya haWa zuminci sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi. Kalla yaran nan yaran Shahidah ne su duka, macen sunana aka saka mata ma .
? ? ? ? Kallonsa ya maida ga yaran, sai kuma ya kalla Maanal.  Little! Su Shahidah duk sunyi aure kenan? .
? ?? Kan Maanal a ?asa ta ce,  Eh yaya. Itama Didi Amal yaranta biyu .
? ? Wani murmushi ya saki mai kama dana damuwa, sai kuma ya jinjina kansa,  ALLAH sarki rayuwa komai sai kaga yana faruwa kamar a mafarki. Oum jiba dai Autar ki duk ta canja, komai na Little ya canja kamar ba ita ba. Ji yanda ta zama shiru-shiru, ba surutu yanzu, komai nata ya canja, ta girma ta ?ara tsayi .
? ?? Murmushi sosai Oum tayi itama idonta akan Maanal datai ?asa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta.  Sosai kam Auta ta canja Fawzan, badan fuskar na nan ba ma sai nace an canja min ita gaba Waya. Girma yazo .
? ? ?  A girma yazo kam Oum, ko'a mafarki akace min little zata koma shiru-shiru haka za'a kwana gardama dani ban yarda ba. Little ina Ammie da Abbah fa? .
? ?

25 / 80