AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   75 / 80

222K to 225K   out of 237.4K words

mai kuWi, itace ke raba musu kayan azumi dana salla, duk da ba wani na kirki bane ba hakan bai hana su girmamata ba. Kuma su babban Yaya ne da Abah ke badawa duk shekara amma sai ta sayi ?ananun atamfa da yaduka ta manna musu. Hakama abincin bawani na kirki ba. Fuska a yamutse ta ce,  Wani abu ne ya faru a wajen Waurin auren? .
? ? ??  Eh to bana ce ba. Akan dai canji da mukaji ne ga ita sunan matar shi Ajwaad da kika sanar mana ne da farko.
? ? ?  Kamar ya canji Yaya Lurwanu? .
?? Kafin ya bata amsa Saheeba ta iso kamar an jehota tana ?wala kiran Mamy! Mamy!. Idanu sosai Mamy ta zuba mata, haka suma sauran mutanen dake wajen. Bata jira amsar Mamy ba ta mi?a mata waya tana faWin,  Abah ne keta kiran wayarki, shine na Waga yace na kawo miki .
? ? ? Amsa tayi, dai-dai nan kiran ya ?ara shigowa. Sai kawai ta Waga takai kunne cike da kissa tai sallama. Cike da fara'a Abah ya ce,  Ina kuka shige haka ke da Fateema sai nemanku nake a waya babu wanda ya Waga min, ki sanar mata ina mata albishir da cewar an Waura auren Autan ta da da Autarta Maanal....
? ? ? Wani irin dimmmm Mamy taji a kunneta kawai, tamkar an Waga irin curarren ?arfen nan an bugama mutum a tsakkiyar kansa babu zato babu tsammani.......

? ?? >?#?>?*???
? ? ??
? ________&? ?

? ? ? ? Acan massallaci kuwa mutanene cikin Wunbin mamaki. Musamman ma'aikatan Mawaad Company da mafi yawansu suka halarci wannan aure. Tuni musu ya kaure akan batun. Wasu suce Maanal ta kamfani wasu suce ba ita bace ba. A gefe kuma suma kansu su babban Yaya harma da Abah a rikice suke. Ga mutane, dole suka danne dan daga nan an Wunguma ne ?aton hall Win da aka shirya walimar cin abinci ga mahalarta wannan Waurin aure. Sai dai kuma hankali ya fara komawa akan rashin ganin AA a wajen. Dole aka fara neman layukan wayarsa, amma duk switch off. Hankali tashe Babban Yaya da Uncle Hussain suka koma can gidan dan dubawa. Sunko iso Wakinsa a gar?ame har yanzu. Tun suna bugawa da kiran sunansa har suka fara ?o?arin Salle ?ofar amma sun kasa. Ga su Abah nata kiransu a waya. Ai kafin kace mi su Aban suma dole sun iso. Nan fa aka taruma ?ofa da ?yar aka ?aryata.
? ? ? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kowa ya faWa ganin AA yashe a ?asa babu alamar rai a tare da shi sai uban jini dayay masa kaca-kaca, ga alamun zubarsa nan ta baki ta hancinsa. Gaba Waya babban Yaya ya Wagosa jikinsa na rawa, hawaye tuni sun gama wanke masa fuska, da wani irin ?arfi yake girgiza AA yana kiran sunansa, amma ina gaba Waya jikinsa ya gama saki. Babu alamar akwai sauran numfashi a tare da shi.
? ? ?? Wani irin baya Abah da jikinsa ke rawa ganin yanda AA Win yake yarab yayi, sai da aka taresa dan kaWan ya hana ya zube ?asa. Baba Sardauna ne ya samu ?arfin halin faWin a Waukesa zuwa asibiti. Haka kuwa akayi duk da duk wanda ya kalli AA zaice yama rasu basu fidda rai ba, Uncle Najeeb da Alhaji ?arami suka kamosa. Daka gansa kaga gawa kawai. A haka suka fita da shi aka saka a mota, suma duk suka shiga aka wuce.....

?? =?-?=?-?=?-?>?r?>?z?>??

? ? ? ___________&

? ? ? ? ?? A Kaduna duka amare biyun sunyi ?yau, sai dai Maanal kwance take zazzaSi ya mata rijib, tun su Aneesa na Waukar abin wasa har suka fuskanci gaske take dan rawar sanyi ma take yi bana wasa ba. Da sauri Najma ta lulluSeta da ?aton duvet. Kafin ta fice tai kiran Amaal. Hankalin Amaal ya tashi, amma ta daure cikin hikima tayi kiran Shahidah dan bata son su Wagama Ammie dake a tsakiyar mutane hankali. Ganin halin da Maanal Win ke ciki ba wasan yara bane ba Shahidah ta bada shawarar su sanarma Nene. Aikuwa haka akayi, da taimakon Nene aka bama Maanal magani, sannan ta zauna ta dinga tofa mata addu'oi. Ga ?awayen Hajiya Basariyya sun cika gidan da kiWa na hauka dan sifiku suka warware a harabar gidan saboda duk mazan sun wuce Kano sai mata kawai a gidan.
? ? ? ?? A dai-dai wannan lokacin kiran Oum ya shigo wayar Ammie. Kasancewar wayar tana a hannun Amaal sai kawai ta Waga. Ko sallamarta Oum bata amsa ba tace,  ?ar uwata . Muryarta na rawar kuka. Cikin faWuwar gaba Amaal tace,  Oum ba Ammie bace nice, wayar tata na hannuna ne ai. Amma Oum mike faruwa kamar fa kina kuka? .
? ? ??  Dole ne nai kuka Amal dole ne. Yau ALLAH ya tabbatar da Maanal a matsayin matar Ajwaad .
? ? ? SuSucewa wayar ta nema yi, sai da ?yar Amal ta tarota, da wani irin mamaki ta ce,  Oum! Kina nufin Ajwaad aka aurama Maanal? .
? ? ?? Ai da wani kalar sauri kowa dake a Wakin ya juya yana kallon Amal. Manaal dake kwance tana faman rawar sanyi a bargo tai wani irin yakice duvet Win itama ta tashi zaram kamar wadda ke amfani da magic sai gata a gaban Amaal. Wayar kawai ta fige jikinta da muryarta na mazari ta ce,  Oum wace Maanal Win? Badai ni ba? Dan ALLAH kada kuyimin haka ni Rafeeq nake so, shi na zaSa, da shi nake son rayuw.......
? ?? Batare data karasa ba kawai ta sulale ?asa yaraf wayar tai nata waje. Ai da gudu kowa yay kanta ana ?wala mata kira....

?? A dai-dai lokacin da Maanal ke sulalewa acan a sume anan sashen su Hajiya Basariyya itama ?aninta ne ya kirata cike da mamaki yake tambayarta yaya haka, yaji Waurin aure ya juye akan Sageer Wan ?anin Daddy maimakon AA Darma data sanar musu. Shi kuma AA Darma Win sunji an aura masa wata wai ita Maanal Habib Giro.
? ? ? ? Gaba Waya Hajiya Basariyya ta saki wayar dake a kunnen nata ta faWo ?asa ta tarwatse. Ita kuma tai baya sai gata jaSar a saman gado ta zube...........
'?
? ??
? ? ??
? ? ? ??9&?9&?=?%?=?%?>?r?>??


09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.......Isowar labarin halin da AA ke ciki ya saka komai tsayawa cak ta kowanne Sangare. Cikin ?an?anin lokaci mafi rinjayen manyan family Win suna a asibitin. Yayinda tuni RK, Abbu, da wasu likitoci suna a kansa anata ?o?arin ganin an ceto rayuwarsa.
? ? ? Sosai Oum ke kuka, kuka mai ban tausayi, dan dole Abah ya dake tashi zuciyar ya kasance da ita. Dama yaranta Babban Yaya da Fawzan suna manne da ita. Abin mamaki a farko Mamy bata asibitin, sai dai ?an uwanta suka tausheta dan da neman birkicewa tai zata tonama kanta asiri suka janyeta zuwa Waki. Sun nuna mata cewar tada hankalinta fa babu abinda zai janyo sai rushewarta a wannan zuri'a, amma idan ta cigaba da dannewa komai ya lafa sai ta ribantu da cikar burinta, saboda tabbas suna zargin akwai abinda ke faruwa tunda har Waurin auren yay wannan juyewar, gaba Waya kuma laifin sun maidashi ga Oum ne, acewarsu dama itace ta tura RK jikin Maanal Win domin hakan ta kasance ita a yaudare ta. To dan haka saita kwantar da hankalinta amarya ta tare a kumayi bikin Nuratu wani satin daga nan sai su san matakin Wauka. Dan ko zasuyi yawo tsirara suma sai sun bata taimako na kashe wannan aure, acewarsu Nuratu bazatai rayuwa da kishiya ba. Da ?yar dai suka tausheta ta ha?ura suka shirya suka tafi asibiti, sai kuma da suka iso suka tarar da tashin hankali yafi wanda ma suke hasashe. Domin kuwa awanni sai shuWawa suke babu wani bayani a game da samuwar AA Win.
? ? ? Karo na farko da hankalin Mamy ya fara tashi, zuciyarta ta dinga raya mata kadafa ace rasa Ajwaad zatayi. Kai ina bata fatan haka, dan soyayyar da takema yaron daban take akan ta sauran yaran. Sai dai kuma abinda ya ?ona mata zuciya ganin yanda Abah da Babban Yaya da Fawzan keta dama-dama da Oum. Hakama sauran manyan kowa dai hankalinsa nakan Oum, ita aketa tausa da tunatar da ita tai masa addu'a. Dan ita ko kallonta kowa baiba a matsayin wadda tasha wahalar rainon cikin Ajwaad da na?udarsa, da gaske dai ta tabbata sun ma manta da cewar itace mahaifiyarsa tarihi ya goge hakan....

? ? ? Sai da su RK suka kwashe awa Wai-Wai har bakwai kafin su fara fitowa. Zuwa lokacin har anyi sallar magrib. Amma sai ?alilan ne suka samun ?arfin zuwa yinta. Kusan gaba Waya akai ca akansu, ALLAH sarki Abbu ga tsufa. Kaida ka gansu kasan su kansu sun jigata. Dan tuni babbar rigar saman kayansu duk sunyi fatali da su shi da RK. Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya bayan yace su sameshi a office. Bayan duk sun zauna a ?aton haWaWWen Office Win nashi cikin nutsuwarsa da Oum suka gado ya ce,  Kowa ya kwantar da hankalinsa tun awa biyu da kasancewar mu da shi aka samesa, bugun zuciyarsa ne ya?i dai-daita tun Wazun sai yanzu Alhamdullah. Amma duk da haka yana bu?atar addu'a, yaron nan ya jima a cikin ciwo, zuciyarsa ta kumbura a shirye take da komai ya iya faruwa. Amma Alhmdllh tunda har ankai ga wannan matakin muna fatan iyakar wahalar kenan dan gaskiya ya auna arzi?i. Yanzu za'a canja masa Waki domin hutawa, muna saka ran nan da awannin talatin numfashinsa zai dawo a gangar jikinsa in sha ALLAHU .
? ?? Sosai kowa ya dinga sakin ajiyar zuciya da jerama UBANGIJI godiya. Harga ALLAH bayanin Abbu ya daki zuciyar Mamy matu?a. Bayan kamar mintuna biyar aka fito da AA, babu wanda bai ji sabbin hawaye ba, wato Wan adam ba'a bakin komai yake ba. Wlhy duk iskancin da muke ji a rayuwa da ciwo ?alilan idan UBANGIJI ya so nuna ba komai bane mu a cikin sakan sai mun bayyana a ba komai Win ba. Cikin ?an?anin lokaci AA ya canja, kamar ba Wan gayu Wan kwalisar nan shugaban Mawaad Company ba ya arrahaman.....

? ?? ________&

? ? ? A Kaduna kam ai gidan gaba Waya ya hargitse, kafin kace mi dangin Hajiya Basariyya sun cika sashen Ammie. Wani irin harmutsi ne na tashin hankali daban mamaki. Dan faWi kawai suke sai sun daki Ammie. Yayinda Huznah ke Wauke da kakkaifar wu?a tana rantsuwa da UBANGIJI sai ta kashe Maanal. Dole aka rufe Ammie da Maanal har ma da su Amaal a Waki. Kafin Nene ta kira Daddy ta tabbatar masa fa akwai matsala ya dawo Kaduna. Hankalin Daddy ya tashi matu?a da jin abinda ke faruwa, dole yay kiran CP na Kaduna yace a tura ?an sanda gidansa. Wannan fa dabara itace ta kawo sassaucin al'amarin. Dan dole kowa ya nutsu kaf dangin Hajiya Basariyya aka korasu sashenta, saboda Daddy ya bada umarnin hakanne kawai bawai a Wibesu zuwa station ba, sai idan sunyi gardama be. Sai a wannan gaSar Huznah ta yanke jiki ta faWi wai ita ta suma. Nan suka rufu a kanta Hajiya Basariyya na kukan idan har ?arta ta mutu sai ta Waure Ammie. Dan sun tabbatar ba?in asiri taima AA Darma dan ya auri karuwar Wiyarta ragowar wani...

? ?? Oho su Ammie bama su san anai ba. Dan su nasu hankalin na nan akan Maanal da aka samu ta farfaWo a bisa taimakon likita da sukai gaggawar kira, abokin Yaya Yazeed kenan. Dole akai mata allurar barci mai ?arfi domin samun nutsuwarta, Alhmdllh cikin ?an?anin lokaci barcin kuwa ya bugeta. Da wannan damar suka samu sukai zaman jimanta al'amarin, dan Ammie tayi matu?ar ?agara Daddy ya iso, yace ya taho, saboda dole ya baro kano, ALLAH ma ya taimakesa ya samu jirgi. Suna isowa Kaduna yake samun kira daga Kanon akan halin da AA ke ciki, sai kuma hankalinsa ya ?ara tashi matu?a. Dole yana isowa yace su Ammie su fara shirin wucewa Kano Win. A Sangaren Hajiya Basariyya ma yace a shirya Huznah dan yau bazata kwanar masa gida ba a gidan mijinta zata kwana, Kanon kenan. Hajiya Basariyya ta birkice zatai masa hauka Yayanta ya wanke mata fuska da mari dan shi dama baya Waukar wargi. Ya kuma rantse mata idan ta sake cewa tak sai ya saka Daddy ya saketa. Wannan fa yasa dole ta nutsu, sai kukan ba?in ciki tana jin zuciyarta kamar itama zata fashe Win. Tana ji tana gani wasu dangin Daddy duka shirya Huznah dake kuka na fitar hankali. Tana rantsuwar bata son Sageer AA take so, itama Win dai Kawu Sani Win ne yay mata jan ido dole tai tsit. An gama shirya amarya Huznah tsaf, ashe abokan ango ana gama Waurin aure dama sun Wakko hanyar Kano domin Waukar amaryar su. Zancen dinner Win da Hajiya Basariyya ta shirya anan Kaduna tasha ruwa kenan. (Sageer dai ya jima yana son Huznah tun tana ?arama, sai dai Hajiya Basariyya na taka masa birki ganin ubansa bai kai Daddy arzi?i ba. Shi kuma sai kawai ya janye jikinsa ya barta ya cigaba da dabgarsa. Kwatsam sati uku da suka wuce Daddy ya samesa har kano ya zaunar da shi tare da masa tambayar har yanzu yana son Huznah? Sosai ya daburce a lokacin, dan harga ALLAH yana sonta har yanzu, kawai dai ya kama kansa ne dan ya fahimci uwarta da ita kanta sai a hankali. Da ?yar ya iya jinjinama Daddy kai, aiko a take yace ya bashi ita, yaje kawai ya hau shiri biki nan da sati uku. Amma yana son yay shiru da bakinsa har sai ranar Waurin aure. Mamansa da Babansa ma sun sake kwakkwafarsa akan ya kame bakinsa ko a cikin dangi ba'ason kowa ya sani sai ranar. Amma zasuyi shirin biki normal sunan amarya ne kawai bazai fito ba sai ranar. Sauran ?an uwa ma zai ce musu Daddy ne yakai kuWin aure da kansa. Lamarin Soyewar ya bama Sageer mamaki, sai dai bai iya ya tambaya ba dan baya iya musu da iyayensa. Sannan yana matu?ar ganin girma da kimar Daddy a rayuwa, bazasu manta da halaccinsa ba, shine ya tsaya tsayin daka akan iliminsu da ginuwar iyayensu da dukiyarsa. Ai ko baya son Huznah akace gata zai amsa da hannu bibbiyu. Balle ma yana son abarsa).
? ? ? ? Sai da aka fara wucewa da amarya Huznah da tawagar dangin Hajiya Basariyya da babu yanda suka iya, dan ?a?ansu Sani yace kowa ya shirya a wuce da shi akai amarya, wanda bazasu je ba anan cikin Kaduna suke su koma gidajensu biki ya tashi anan gidan Daddy ba'a bu?atar ganin kowa. Hakan kuwa dole sukayi, aka bar Hajiya Basariyya na faman kwasar kuka, sai manya da basu wuce biyar ba aka bar mata akan su ?arasa haWa kayan Huznah Win kafin gobe a bita da su. Kayan Waki dai dama kai tsaye can Daddy ya tura aka shirya a gidan Sageer, na Maanal kuma aka kai Abuja gidan su AA, ita kuma Hajiya Basariyya ta saki baki Abuja na Huznah aka kai, dan ko kaWan Daddyn bai basu wata ?ofa ta fahimtar komai akan auren ba....

? ? ? A Sangaren Ammie tana son ?arin bayani daga Daddyn itama amma babu fuska, dan ya haWe gabas da yamma yace su shirya kawai, zasuje can Kanon sai a ?arasa bikin acan ya tanadar da gidan da zasu zauna. Ita mai biyayya ce akoda yaushe a gareshi, dan haka ta fara shiryawa ita da kaf ?an uwanta. Wanda zasubi mota suka fara yin gaba. Musamman ?wai da ?arkwatar iyalan Nene, tunda dama dai sune dangin kawai, sai abokan arzi?i da ake gaisawa daga haka sukai addu'a suka kama gabansu. Wanda kuma zumuncin yay ?arfi sosai suka shiga tawagar ?an wucewa a mota.
? ? ? ? ?arfe biyar Ammie, Shahidah, Amaal, Nene, sai Maanal da aka tada da ?yar daga barci aka shiryata tana faman layi suka wuce airport dan su jirgi zasu bi, harda shi kansa Daddy Win. Wannan abu ya ?ona ran Hajiya Basariyya da sauran danginta. Dan haka suka bata shawara itama ta shirya gobe duk su tafi Kanon gara a ?arasa komai akan idonta, dan sun fahimci wai Daddy na fifita agolarsa sama da ?arsa. Haka kuwa akayi, a daren suka fara shirin komai daya dace acewarsu fitar sassafe zasuyi....

? ?? Kuce min ina uwargida ran gida Hajiya Yaya. Ai tana sashenta ita da ?a?anta da su Aunty Sabuwa na kwasar dariya. Dan su tun farkon faWan daWi yay musu. Acewarsu ai Hajiya Basariyyar ce dai-dai da Ammie. Zuwan ?an sanda a gidan ne ya su nutsuwar dole suka cigaba da gulmar daga ciki. Koda Daddy ya dawo kuma Hajiya Yayar tazo domin bugar cikinsa sai yay mata banza, dan dama haushinta yake ji akan tura Yazeed honeymoon Win dole da tayi. Itama ganin yanda yay matan sai tai zuciya wai ya dizgata saboda bata da muhimmanci a garesa. Bai kulata ba taja ?an matan ?afafunta ta koma sashenta cikin ?an uwanta suka sake buWe babin zagin Ammie da Hajiya Basariyya Win ma. Koda za'a wuce da Huznah babu wanda yay niyyar bi a cikinsu, sai kuma Daddy yasa aka tattaro masa kaf ?a?an yace su shirya su bi masu tafiya Kanon. Babu yanda suka iya suna tura baki da ?un?uni dole sukai shirin tafiyar. Ganin haka sai Aunty Sabuwa ta zuge Hajiya Yaya akan ai ta shirya kawai suma subi ayari dan ayi komai akan idonsu. Dan Jaraba da masifa Hajiya Yaya fa bata jurar doguwar tafiyar mota saboda ?iba amma haka ta shirya Win suka wuce batare da ko sanin Daddy Win ba......

? ? ? __________&

? ?? Su dai su Ammie kasancewar tafiya ce ta jirgi

75 / 80