RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 30

24K to 27K   out of 87.6K words

DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*




*RM*
13


***Washegari da wuri Hajiya ta aiko masu aikin ta da abinci, tace zata shigo anjima. Karba umma tayi ta zuba ma Asma'un da tace kadan da k'yar, itama da dan ci sannan ta taimaka mata ta gyara jikin ta kafin likitan yazo, tun bayan fitar Adam be sake dawowa ba, gida ma ya wuce daga nan yana kokarin shigar da motar sa ciki Hajiya Mama ta kirashi tana son ganin sa, fasa shiga yayi ya ajiye motar a waje ya shiga gidan nasu in da ya tarar da ita zaune ita kadai a falo tana sakawa da warwarewa, tana ganin shi ta mike daga kishingidar da tayi, ya zauna kusa da ita daf ya dan matsa mata kafar ta, janye kafar tayi alamun tayi fushi ta tsare shi da ido cikin bacin rai irin wanda be taba gani ba tace

"Ka kyauta kwarai da watsa min k'asa a ido."

"Mah! Me kuma akace nayi?"

"Yanzu ka kyauta ka bar matar ka ita kadai ta kwana, bayan magiyar da kayi ta min akan na kyale ka, dama kawai ka shirya wulakanta ni shiyasa kayi haka ko?"

" Comman, yanzu mah kin yarda da maganar ta? Wallahi sharri tayi min, baki zo kin same ni a dakin ba? Bafa muyi bacci ba sai wajen asubah fa, ina zaton dai zafin ciwo me ko kuma kiyayyar da take min ce har yanzu bata hakura ba."

" Kiyayya?" Tace tana kallon sa

Juyar da fuskar sa yayi kamar wanda yake cikin yanayi yace

" Kwata-kwata bata kauna ta wallahi, babu yadda ban yi da ita ba amma tun auren taki sakewa dani, haka nake hakuri dan ko hakki na bata bani, wannan tsautsayin ma wai dan kawai nazo dakin ta shine ta tashi ta fita garin sauri ta zame a kafar bene ta fadi, amma kinga yan uwanta da kowa kallon ni ne me laifi, saboda ni aka sani me matsala."

" Haka take dama Asma'un? Ikon Allah!"

"Saboda ni ne me matsala shiyasa kowa laifi na yake gani, amma itama bata san ya kamata ba. "

" Bansan haka take ba, kallon mutuniyar kirki nake mata, ashe itama kwalla kanta ce, ai shikenan, duk da na zata laifin ka ne, ko wahalar musu da ya kake. "

" Ko daya, ni me ma zan mata na wahalar da ita? Ko fa gaishe ni batayi balle tayi min magana, dan dai ma Ina da hakuri ne wallahi. "

" Ah gaskiya bansan bata da hankali ba sai yau, amma babu komai zamuyi magana."

" Shikenan, amma dan Allah kar ayi mata fad'a, ni ba dan kin matsa ba da ba zan ma fad'a ba. "

" Sai ka zauna a haka? Bayan anayin aure ne saboda a samu nutsuwa da kwanciyar hankali. "

" Zata daina ne. " Yace yana mikewa

" Har sai yaushe? Zan same su ita da mahaifiyar ta ta dana lura itama haushi na take ji, zan fada mata komai sai ta fad'a min idan haka ake zaman aure a garin su. "

Kada kansa yayi, ya fice ransa fes, yayi shigewar sa gida yayi kwanciya sa sai wajen tara ya sake shiryawa ya fice abun sa. Da kwarin guiwar ta, ta isa asibitin dan tayi alkawarin yi wa umman magana ko ita da ita ne idan yaso sai ta nuna wa yarta gaskiya dan idan ba irin Adam ta samu ba babu me hakuri da hakan da tuni anji kansu. A yadda ta shigo dakin kadai ya saka Umma tunanin akwai wata a k'asa, ba kamar jiya da ta kasa sakewa ba, daga tsaye ta duba Asma'un ta fita wajen ta samu kujera ta zauna tana kallon masu shige da fice a asibitin, ta dade a wajen har aka soma zuwa, umman ta fito wajenta ta saka musu carpet babba tace Maman ta dawo, ba musu ta dawo ta zauna ta dubi umman da take hade kan kwanukan abincin jiya waje daya tace

"Magana nake so muyi dake ta fahimta."

Barin abinda take tayi, ta zauna kana tace

"Ina ji, Allah yasa dai ba wata matsala bace."

"Kusan hakan, amma dai ko kin tambayi Asma'u yadda akayi ta fadi?"

"Tsautsayi ne ai da yake kan kowa, ban tambaye ta ba gaskiya dan ban ga dalilin tambayar ba."

"Aikuwa akwai dalili, ya kamata ace kin bincika kinji, nidai na binciki Adam, kuma dai har ga Allah maganganun babu dadin ji, ban tsammaci hakan daga wajen asma'u ba. "

" Me ya faru? "

" Eh toh, Adam dai yace min zaman nasu babu dadi dan ko magana bata masa, gashi bata bashi hakkin sa na aure, wannan tsautsayin ma ya faru ne sanadiyyar yazo wajenta tayi niyyar barin dakin sai ta gamu da tsautsayi! "

" Kinga ai ba'a haka, miji daraja ce dashi duk kuwa da halin sa, ki hango ace da ba Adam din bane, da tuni ba zancen da ake kenan ba."

A tunanin ta umma zata ce wani abu, ko ta nuna rashin kyautawar Asma'un amma sai tayi kamar bata gane ba ma, tace kawai

" Allah ya rufa asiri."

Hakan ya kular da Hajiyar, ganin Umman na niyyar mikewa tace

" Iyakar abinda zaki ce kenan?"

" Toh me zance Yaya? Yaran yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba, kuma dai kinga halin da Asma'un take ciki ya kamata a daga mata kafa har ta samu sauki kafin a tuhume ta, a gani na hakan ya dace."

Shiru ya biyo bayan maganar Umman, Hajiyan ta rasa me zata ce,da n ta gane sarai magana Umman ta gasa mata me zafi, ganin bata ce komai ba ya saka ita kuma Umman tashi ta bar ta a wajen. Kwafa tayi cikin jin haushin ta bar asibitin, ba zata lamunci sakarci ba dole ta takawa abun birki.
Sosai umma taga son zuciyar Hajiyan fiye da ada ma akan batun auren, ko makaho ya shafa Asma'un ya shafa Adam din zai gane komai, amma saboda tsabagen son zuciya har mutum na kwance a gadon asibiti amma kazo da irin wannan maganar.
Tun ranar da hakan ta faru, Hajiyan bata sake lekowa ba, tana dai aiko da abinci kullum sau biyu a rana, Nadeeya ce kawai take zuwa kullum ba fashi amma shi kansa gogan sai ya ga dama yake dan lekowa fisha yayi gaba abin sa yana sake rura wuta a wajen Hajiyar tana jin zafin umma sosai tana ganin da saka hannun ta Asma'un tayi duk abinda tayi ma.
Satin ta uku a asibitin aka cire cast din da aka saka mata a hannun sannan aka sake mata x-ray aka tabbatar da yana healing sosai kuma very fast, gentle hand therapy aka cigaba da yi mata wanda aka fara tun kafin a cire cast din, hakan ya sake taimaka mata wajen samun karfin hannun har tana iya motsa shi sosai. Sallamar su akayi sannan aka basu appointment, Hajiya na jin an sallame su ta kira Abba ta sanar dashi gidan ta za'a kawo ta ba gida za'a wuce da ita ba, Abba yace toh ya kira umma ya fad'a mata a wuce da Asma'un gidan ta ko mijinta ya dauke ta kawai su tafi ba sai sun je ba, shiru umman tayi masa ya gama ya kashe. Dama ita bata ce zata tafi da ita gida ba tun da dai da mijinta. Gidanta suka fara kaita wanda Maman ta saka aka gyara shi kafin su dawo, shine zuwan umman na farko suka dan zauna zuwa azahar sannan suka tafi gida ita da Ya Hadiza da Abbati.
Suna tafiya ta tashi ta lallaba ta hau saman tayi wanka ta shirya, tana kokarin shinfida sallaya ne taji alamun an shigo kasan saboda babu motsin komai shiru gidan, ajiye sallayar tayi ta fito sai ta tarar da Hajiyar da kanta zaune a falon tana dan kallon gidan.

"Sannu da zuwa." Tace tana kasowa falon, ta tsuguna ta gaishe ta amma yadda ta amsa ya saka ta jin wani iri,

"Lafiya." Tace a yangace tana kalle kalle a falon, tayi zaton ko duba jikin ta, ta sake yi tunda ta jima bata zo ba sai aike amma sai taga akasin haka.

"Fad'a nazo yi miki tunda ita umman taku ta kasa ba zata iya ba, ni da kaina zan miki kuwa, kinsan hakkin miji akan matar sa kuwa?"

" Naam!? "

" Kin jini sarai, daidai gwargado ai kunyi karatu both na addinin da na bokon, kuma dai ke ba yarinya bace gasu Hidaya nan ai gaba kike dasu, amma ace ba zaki iya yiwa mijinki abinda yake so ba? Har sai yana binki kina butsarewa, duk da irin rokon da nayi miki na ajiye girma na? Ban zaci haka daga gareki ba. "

" Hajiya wani laifin yace nayi? "

" Laifi ? Laifufuka dai, babban laifi wanda ko a wajen ubangiji kin yi babban laifi, dan gayun nan dan tarairayar nan ace duk baki iya ba, kamar wadda ta fito daga kauye, kauyen ma kayau, lallai ki gyara kanki, ba zan lamunci shashanci ba. "

Sai ta mike tsaye

"Dole kiyi wa mijinki biyayya kiyi masa kuma duk abinda yake so, batun hakkin sa kuma ke da Allah wannan idan kika ki bashi. "

Daga haka tayi hanyar fita tana sababi, kan Asma'un gaba daya ya kulle, ta gaza fahimtar in da Hajiyar ta dosa kai tsaye, hawaye taji na neman zubo mata, ta maida su da sauri tana girgiza kanta, ta mike ta haye saman ta rufe kanta ta shinfida sallayar da sauri ta tada sallah tana kokarin hana wa kanta tunanin maganganun Hajiyan balle har suyi tasiri a ranta.
Bayan ta idar ne maganganun suka dinga mata amsa kuwwa a cikin kunnenta, ta danne kanta a saman gadon tana runtse idon ta.
Har dare yayi wajen goma na dare be dawo ba, ta shirya ta kwanta tana karfafar kanta da zuciyar ta, tana shiryawa zama da Adam da selfish mahaifiyar sa, tunda har Hajiyar ta soma irin wannan zantukan toh tabbas ta shirya kuntata mata a zaman su, zata kuma goyi bayan Adam din a komai, bata san me yaje ya fad'a mata ba, sanin ma bashi da amfani tunda ba damar kare kanta za'a bata ba, ita mace a kullum itace a k'asa, ita ake bawa laifi a komai babu kuma wanda yake sauraron korafin ta, idan ta bud'e baki zata fadi damuwar ta sai a dakatar da ita, ace mata rayuwar aure yar hakuri ce, tayi hakuri kawai.
Ta kuwa shiryawa hakurin da ko kashe ta Adam da Hajiya zasuyi ba zata taba ce musu dan me ba, zata kare rayuwar ta a haka har zuwa lokacin da Allah zai yanke mata.
Da safe ta tashi da kwarin jikin ta, ta dan sake gyara gidan da abinda take bukatar ya kasance a wajen da take bukatar sa, sannan ta hada break fast me sauki ta ajiye a dining din da ba wanda ya taba zama akai. Ta dauki nata ta koma daki taci ta dauko al'qur'an me girma ta shiga tilawar sa.
Be kwana a gidan ba, da safen ya dawo ya wuce daki ya hau ramakon baccin da yake kansa, kasancewar weekend ce babu in da zashi, sai wajen sha daya ya farka ya fito falon idon sa ya sauka akan dining din, ya isa wajen ya bud'e yayi murmushi wanda shi kansa be san dalilin sa ba, komawa yayi ya fara wanka sannan yazo yaci abincin ya koshi sannan ya nufi dakin nata. A tunanin sa zai tarar dashi a rufe amma sai yaga akasarin hakan, tana zaune kyem ya shigo ta dan dube shi ta cigaba da karatun ta, rabon shi da ya karanta alkur'ani me girma yayi mugun jimawa, ganin ta tana karantawa ya tuna masa, ya k'asa karasawa ciki ya tsaya yana sauraron ta, tayi kamar bata san da zaman sa a wajen ba har ta kai karshen shafin, ta rufe ta ajiye a bedside ta mike tace

"Ina kwana?" Bata jira amsar sa ba tayi gaba zuwa hanyar toilet, tayi shigewarta ta barshi a wajen, abinda yayi niyyar yi mata sam sai yaji bashi da karsashi, yaji tayi masa kwarjini dalilin karatun da yaji tanayi, juyawa yayi ya bar dakin, ya bar gidan baki daya ma.

_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍


***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_


_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*


*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.



*_TEAM ZAFAFABIYAR_*



RM
Β Β  14

***Tun daga ranar kullum zatayi duk ayyukan da tasan son zama wajibi akanta na sauke hakkin sa sannan zatayi girki kuma yana zama yaci wani zubin ma har ya cinye tas musamman na safe da na dare dan baya zama da rana a gidan daren ma sai late yake dawowa dan sai da safe take jin motsin sa mafi yawancin lokuta, babu wanda hajiya ta sake aikowa gidan tun bayan ranar da ta shigo din, Nadeeya ce dai duk sanda ta samu dama ta kan leko su gaisa ta sake dubata sannan ta tafi. Ranar da ta shigo ne take ce mata ya kamata ta dan dinga lekawa tana gaida Hajiya, ta amsa da toh a ranar kuwa bayan ta gama komai ta shiga gidan sai dai tarbar da ta samu wajen Hajiyar yayi masifar daure mata kai, tamkar ba jinin ta ba, a wulakance ta amsa gaisuwar ta, ta kuma share ta, ta ma yi shigewar ta daki daga karshe ta fito ta bar gidan ba tare da ko magana ba, haka ta karaci zaman ta daga ita sai masu aiki ta koma gida.
Washegari sai ga kiran Hajiyar, hijab kawai ta rufa tabi bayan yarinyar, ta same ta a tsaye a tsakar gidan an jibge kayan miya masu uban yawa da su kabewa da alaiyahu. Masu aikin ta ne da wasu mata su biyu akan kayan. Gaishe ta tayi ta amsa sama sama, ta nuna mata kayan miyar da hannu

"Aiki ne gashi nan, a gyara a dora kafin na dawo, baya za'a je akwai murhu da itace, sauran aikin sai na dawo za'a fara."

"Toh!" Tace a sanyaye ta ja kujerar tsugunnun dake gabanta, ta zauna ita kuma Hajiyan ta koma ciki. Aikin suka shiga yi ka'in da na'in har wajen azahar kafin su ga raguwar sa, ta gaji sosai ga wani ciwon kai da ya matsa mata kwana biyu, babba daga cikin masu aikin ce taga yanayin ta, tace ta koma baranda ta zauna zaasu karasa, ki tayi dan bata son abin magana, suka hada baki wajen rokon ta da ta huta amma taki, ana haka sai ga Nadeeya da Adam din sun shigo a tare, wani irin kallo yayi mata na cikin ido, ta dauke kanta tana maida shi wajen Nadeeya da mamaki ya cikata

"Asma'u har dake a aikin!? Ke da ba ishashiyar lafiya ba?"

Yake tayi, suka gaisa tace ta taso, ba musu ta tashi ta bita ciki shi kuma ya take musu baya, suka yada zango a falo.

"Daga kin shigo kin ga ana aiki sai ki hau yi, duk dauko su akayi biyan su Hajiya zatayi, wannan aikin yafi karfin ki ai."

Murmushi kawai tayi, dama ta san da biyu Hajiyan ta saka ta aikin bayan ga masu aiki nan bajaja, har da hayar wasu ma, duk da bata san taron menene ba amma kuma bata ji komai ba a aikin da ta saka ta, a rayuwar ta aikin gida da duk abinda ya shafi girki baya mata wahala sam, dan ma bata dan jin dadi ne, da ba zasu ma fahimci gazawar ta ba.
A kusa da ita daf yazo ya zauna, ya dan bige ta a kafadar ta ya harare ta

"Ba zaki min magana ba?"

Tabe baki Nadeeya tayi ta sungumi jakar hannun ta, tayi hanyar bedroom dinta

"Na lura kunya ta maka karanci Boy."

Dariya ya saka tamkar bashi ba, tana shigewa ciki ya juyo yana matsawa daga kusa da ita,

"Baki san waye Adam ba har yanzu."

"Bani kuma da bukatar sani." Tace tana matsawa itama, murmushi ya saki ya janyo hannun ta, tayi kara kad'an ya saka hannu ya dalle mata baki

"Sai kin gane baki da wayau, amfanin ki ya kusa karewa a waje na, daga nan zaki gane waya Adam!"

Tsam ta mike, yafi mata kwarai ta koma wajen masu aikin ko aikin zai kasheta da ta zauna inuwa daya da Adam, tana kokarin fita Mama na shigowa, dan saura kadan suyi karo ta matsa baya da sauri

"Amma ina miki magana shine zaki tafi? Magana ta bata da muhimmanci ko?"

Muryar sa ta daki kunnenta ta hanata daga kafarta da take shirin yi ta bar falon, da sauri ya juyo, ita yake kallo irin kallon cikin idon nan

" Mijin ki yana miki magana amma shine zaki kada kanki Asma'u, anya?"

" Hajiya wallahi ba haka bane. " Tace cikin son kare kanta dan bata san makircin Adam din ya kai haka ba

" Kin karyata mijinki kenan?"

Girgiza kai tayi da sauri

" Yayi kyau. " Hajiyan tace tana wucewa ciki, ya tashi ya karbi Jakarta

" Welcome Mah, ai ban ga shigowar ki ba sai maganar ki kawai naji. "

" Ka cigaba

9 / 30