Author : RANO Category : African Stories & Novels
ya ji su ne kawai amma ya riga ya san umma ce ta kira su akan maganar.
Bayan sallar magriba Yaya hadiza ta samu Abban da maganar, ya nuna mata babu fashi su dai kawai su tayata da addu'a, haka ta baro dakin jikin ta a sanyaye bayan ta roke shi ya barta su tafi da Asma'un ya amince amma iya sati daya kawai dan sati uku ya saka bikin tunda babu wani shiri da za'a yi dan kowanne bangare a shirye suke dama.
Mijinta ne yazo ya dauke su wajen tara, a hanya take bashi labarin abinda ya faru, ya dan juyo yana sake bawa Asma'un baki yana tsokanar ta, ta dan yi murmushi kawai amma ita kadai ta san yadda take ji a ranta.
***Washegari bayan an makaranta sun tafi umma ta shirya Abbati ya kaita chan Mandawari gidan su ta samu Hajiyar su da maganar auren Asma'un da lokacin da Abban ya saka, duk basu ji dadin hukuncin Abban ba, da kuma rashin bawa Asma'un dama ta fadi ra'ayin ta dan kawai ana ganin kamar ko an barta ma ba wani ne zaizo neman auren nata ba.
"Toh yanzu dai ya riga ya gama yanke hukunci, namu kawai shine mu bi ta da addu'a, Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina."
Hajiyan tace bayan sun gama magana da Umman.
"Amin, ni na rasa ta ina zan fara ba, sai a aika su miko su sanar da su umman Asiya da su Aunty Falila da gidajen su kawo muntari."
"Eh yana shigowa zan aika shi, sati uku kamar yau ne ai, duk sai a sanar da dangi, Allah ya basu zaman lafiya."
"Amin." Tace a sanyaye.
***Bangaren gidan Hajiya Mama shiri take na ban mamaki, tuni zancen ya karade dangin su bangaren Abban da kuma bangaren Baban su Adam din, mutane da yawa suna tausayawa Asma'un saboda dai sam babu hali na nagarta da zai saka ka dauki yar ka, ka bawa Adam din, ciki kuwa har da yan uwa makusantan su Abban dan wani kawun su sai da yayi wa Abban magana kasancewar kowa ya riga ya san nutsuwa da kamala irin ta Asma'un dan kaf yan uwanta babu kamarta, duk da su ma basu da matsala amma kuma ita din daban ce, magana da koman ta a nutse take yin sa, bata da rawar kan yan mata dan ba zaka taba tunanin ta je jami'a ba ma, bata dauki duniyar da zafi ba haka kuma bata da son kyale kyalen duniya. Haka ya saka mutane suke ganin kamar akwai zalunci a dauke ta a hada ta da Adam wanda ake tunani hatta giya yana sha bayan mugun halin sa na neman mata da yayi shura akai, amma yadda Abban yayi biris da duk wannan ya saka kowa ya shafa ma kansa lafiya aka shiga bin su da addu'ar fatan alkhairi.
Zuwan Adam din uku tare da zugar abokai baya samun ta karshe dai ranar da yazo ya tarar da Abban nan yake gayawa Abba ai yazo baya samun ta, nan fa Abban ya shiga dakin Umma yayi ta mata fad'a sannan ya dauki waya ya kira Yaya hadizan yace ya fasa sati dayan gobe gobe ta dawo gida. Jiki a sanyaye ta amsa masa da toh, bayan ya kashe sai kuma yaga kamar ya zafafa da yawa, sai ya sake kiranta yace ta kyale ta zuwa satin amma zatayi bako gashi nan zaizo yanzo. Nan ma dai toh din tace ya kashe ya koma ya samu Adam din ya yi masa kwantancen gidan Yaya Hadizan sannan ya bashi number wayar Asma'un da ta Yaya Hadizan yace idan yaje ya kira. Bakin sa tamkar gonar auduga ya karba suka dauki hanyar gidan Yaya Hadizan baka jin komai a motar sa ife ifen su irin ma gogaggun yan duniya, burin sa kawai ya nuna musu kalar matar da zai aura ya san ba karamin taya shi farin ciki zasuyi ba, hutu kam zai huta a wajen sosai, yadda yake ji ma kamar sati ukun yayi masa mugun yawa amma haka zai hakura ya lallaba ya cigaba da maneji da su Fido kafin ranar da zai gwangwaje.
Gidan bashi da wahala suna zuwa suka gane, ya dauko wayar sa zai yi kira sai kuma ya fasa ya fito da kafar sa ya karasa gate din gidan ya kwankwasa da dan karfi saboda karar Gen, be jima yana bugun ba mijin Ya Hadizan yazo ya bud'e masa, ya bashi hannu suka gaisa sannan yace ya shigo ciki
"Owk tare muke da guys suna mota bari nayi musu magana."
"Owk." Yace ya wuce ciki ya bar musu kofar a bude, ya samu falon ba kowa an gama jera ruwa da lemo akan dan centre table din, ya dauki remote ya rage volume din tv daidai lokacin da suke shigowa, su hudu ne dukkan su sanye da kananan kaya daya ma daga ciki wandon sa da kad'an yafi guiwar sa, askin kansu kuwa kai kace gobara akayi a wani gefen kan nasu babu kyaun gani, hannu ya basu suka gaisa sannan ya wuce ciki cike da al'ajabin dalilin da zai sa Abba amincewa bayan ya san waye Abban da nagartar sa.
Da k'yar da ban baki Ya Hadiza ta sakata fita dan bata son fushin Abba akanta zai iya hadasu daga ita har Asma'un yayi musu tatas. Hijabi ne burmeme a jikinta har kasa, ta dauko facemasks ta dora akan fuskar ta sannan ta tura kofar falon kanta a k'asa ta shiga. Wata iriyar kunya ce ta kama Adam din da ya ganta da shigar, shi da yaso suga kalar matar da zai aura amma shine zata je ta burma uban hijabi kamar wadda zata zaman makoki.
Dariyar shakiyanci suka fara yi suna kallon sa, ya hade rai sosai yaki kallon ta, a k'asa chan ta rakube ta gaishe su suka amsa cikin dariya dan su basu ga abinda yake ta musu kozozoto akai ba.
"Our wife kina lafiya?"
Daya daga ciki yace yana kunshe dariyar sa.
"Lafiya lou."
Ta amsa a takaice kanta still a k'asa ba zata iya cewa ga adadin su bama balle kamar su, uban gayyar kawai ta gani sanda ta shigo taga ya wani diririce kamar wanda yayi karya aka gano shi, bata kuma kallon sa ba ta zauna. Tana jin su suna ta shakiyan ci suna tsokanarshi amma ko uffan be ce musu ba, sai da suka gama suka fita, ya taso yazo daidai kanta, ya saka hannu ya fuzge facemask din, ta kalle shi da sauri
"Wannan wane irin wulakanci ne na kawo guys dina su ga matar da zan aura shine zaki sako wannan buhun sannan ki wani toshe fuskar ki dan tsabar iskanci."
"Kamar ya? Me yasa zasu ganni ko su din muharramaina ne?"
"Shit! A 21th century dama akwai mata villagers irin ki? Ke baki san civilization ba? Ko baki ga alamar mijin da zaki aura wayayye bane?"
"Ban san duk wannan ba, abu daya na sani shine abinda addinin musulunci ya koyar dani."
Ta murguda masa baki tana jan facemask din zata mayar ya fuzge da karfi sannan ya buge mata baki
"Karki yarda kice zaki min rashin kunya wallahi, dan zan taimaka miki na aure ki, naga ma ai neman kai ake dake na taimaka nace zan aura, so watch your mouth wallahi, kuma na sake zuwa kika zumbulo min irin wannan Hijab din sai na cire shi ta karfi wallahi. Nonsense!"
Ya juya da sauri ya bar falon har da buga kofa, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, bakin ta da ya buge na mata zafi sosai, sai kuma maganganun sa da suka yi mata mugun ciwo, da gaske taimaka mata yayi? Kuma neman kai ake da ita shine ya tausaya mata zai aure ta. Wani kuka ne yazo mata, ta gwammace ta mutu ba aure akan ta auri mutum irin Adam, jinkirin aure ai ba shine zai saka mutum yayi wrong choice ba, gwara ma ace ka aura baka sani ba, amma wannan kowa ya san halin sa.
Ta jima a wajen tana kuka sosai, kafin ta tashi da k'yar bayan ta goge hawayen ta shiga ciki.
RAYUWAR MACE COMMENT GROUP LINK. Meson comment group sai ya shiga link din nan
https://chat.whatsapp.com/EcH31iWkbGnD9DWC8SsuL
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
*RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (3)
***
Tun da suka dauki hanya suke masa shakiyance be ce dasu uffan ba, ya riga ya san dole suyi yadda ya dinga kuranta musu ita, ba karamin bata masa rai tayi ba ta kuma maida level dinsa baya a cikin abokan sa, ba dan ya kwallafa rai akanta ba babu abinda zai sa ya aureta dan shi baya son mace me duhun kai. Tsaki ya dinga ja har suka zo in da zasu rabu, ya sauke su ya fizgi motar kamar zai tashi sama sai gida.
A falo ya tarar da Hajiyar da tarin akwatunan lefe tare da sisters dinsa su uku da suka je hado kayan, suna zaune suna dubawa ya shigo ransa a bace zai wuce Nadiya ta dakatar dashi
"Boy baka gammu bane?"
"Na ganku mana." Yace yayi wucewar sa ya haye sama ya barsu da wagaggen baki.
"Ina ga dai an batawa boy rai, yadda yake zumudin auren nan ai ya tsaya ya ga komai."
" Gaskiya dai, abun ya motsa."
Fadila tace tana dariya
" Bari naje naji ko menene ya faru." Nabeela ta mike Hajiya ta dakatar da ita
"Ku rabu dashi kila shi da abokan sa ne, zai sauko anjima kadan idan ya watsa ruwa."
Komawa tayi ta zauna suka cigaba da maganar auren suna hada kayan da lissafin abubuwan da za'a siya kuma, Hajiyar na jin su tana amsa waya akai-akai Adam din ya sauko ya zauna a kusa da Nadeeya ya tankwashe kafar sa yana kallon kayan.
"Have a look, kayan wife din ka ne."
Dan wara idon sa yayi akan kayan sai kuma ya dauke kai yana kallon Hajiyar
"Mah ba zai yiwu a dawo da bikin nan next week ba?"
"Next week kuma? Ai kamar yau ne upper week din Adam, hakuri zakayi a samu ayi shirye shiryen komai a nutse."
Shiru yayi be sake cewa komai ba, ya ja baya ya jingina da kujera ya ciro wayar sa ya shiga chatting da yan matan sa, hakan ya saka shi manta abinda ya faru, har ya sake suka shiga hira da su kafin su tattara su tafi akan zasu dawo gobe saboda wasu kayan da basu gama siya ba.
***Tsaye Ya Hadiza take a kanta tunda ta shigo take kuka ta ki fad'a mata abinda ya faru, ita kanta ji take kamar tayi kukan dan ta san yanayin da Asma'un take ciki wanda ta taba shiga kusan irin sa Allah ya kiyaye Abba ya sakko aka daidaita, shiyasa take matukar tausayin ta dan mutum irin Adam ace shine mijinka ba karamin tashin hankali bane.
"Ki fad'a min abinda ya faru dan Allah, hankali na ba zai kwanta ba kuma wannan kukan sai ya saka miki ciwo."
Bayan hannun ta, tasa ta share hawayen sannan ta hau ciro hijab din jikinta saboda zafi da hucin da jikin ta ke fitarwa. Duk Ya Hadizan na tsaye akanta har ta cire ta ninke sannan ta hau kokarin kakalo murmushi ta dora a saman jar fuskar ta.
" Wani abu yace miki?"
Da ka ta amsa mata tana jin wasu hawayen na neman zubowa.
" Karki yarda ki biye wa maganganun sa dan irin Adam xasu iya karar miki da hawayen ki tas babu abinda ya dame su. He's not worth your tears, ki nutsu ki shiga kai wa Allah kukan ki, sai kiga komai yazo da sauki ta inda bamu zata ba."
" In sha Allah." Tace tana kwanciya.
Fita Ya Hadizan tayi bayan ta kara bata baki, ta barta tana sakawa da warwarewa, ta riga ta san rayuwar ta tazo karshe, dan tana jin komai zai iya faruwa a zaman ta da mutum kamar Adam, bata san yadda zata kasance ba amma tana da yakinin zaman ba zai taba dadi ba.
Shirye shirye ya kankama sosai a baangarorin biyu, ita Umma dai tana yin komai ne domin ya zama dole amma ba wai don son auren ba, sai dai bata da damar nunawa saboda Asma'un da Abba dan ba zata yarda ta bata kofar da zata bijire wa mahaifin ta ba. Satin ta guda ta dawo gida a lokacin ne aka shiga yi mata yan gyararrakin mata na al'adah duk da ba wani zafafawa akayi ba amma kuma dole dai zaka yi auren 'yarka ka dan tabuka wani abu ko yaya.
Komai baya mata dadi duk abinda ake mata kawai tana bi ne don babu yadda zata yi, saukin ta ma tun da yazo gidan Ya Hadiza be sake dawowa ba, sai magana da yayi mata a whatspp akan abinda take bukata tace babu, sai missed video calls dinsa da ta gani sau biyu bata bi ba, shikenan shima be sake bin kanta ba dama Nadeeya ce tace masa ana tambaya shiyasa ma ya tambaye ta, abinda tayi masa ranar yayi masifar bata masa rai shiyasa ya tattara ya watsar da ita ya cigaba da shirye shiryen sa dan babu fashi a auren dan yadda yake ji idan be aure ta ba akwai matsala.
Saura sati daya bikin suka kawo lefe, akwatuna goma cif masu kyau da tsada, tun daga nan hankalin ta ya kara tashi sosai, ta yarda da gaske dai auren babu fashi, babu abu daya da ya burgeta a kayan dan bata son duk wani abu da ya danganci Adam din, sosai take jin tsanar sa. Bayan an karbi lefen kowa ya watse su Ya Hadiza suka zauna zaman yi mata nasiha dan idan aka shiga satin bikin babu me sukunin zama yayi mata, jin su kawai take dan duk abinda suke fad'a bata jin zata iya yin guda daya, ita dai kawai ta riga ta san zatayi aure ne dan biyayya ga mahaifin ta.
Da daddare kafin duk su watse sai gashi ya zo, gabanta ne ya fadi da taji Areef yace yazo, duk suka zuba mata ido tayi saurin zamewa daga zaunen da take ta kwanta kuka na taso mata.
"Tashi zakiyi kije, kiyi hakuri." Ya Hadiza tayi maganar tana mikewa, tashi tayi daga kwanciyar, ta ja hijab dinta dage gefe zata saka ta girgiza mata kai
" Musulunci ma ya halatta mishi ganin wani abu sashe na daga gareki, ki saka mayafi dan Allah, sai ki dauki Hibba kuje."
Bata yi mata musu ba, ta ajiye Hijab din ta karbi mayafin dake jikin kanwarta Rauda ta yafa, ta rik'e hannun hibba din suka fita, already ya shigo yana falon Abba shi da Abbaty da Yaya Ibrahim. Da sallama ta shigo duk suka juyo suna kallon ta, sannan suka amsa, murmushi yayi mata tayi kamar bata gani ba, ta samu gefe chan ta zauna sai suka tashi suka fita ya zama daga ita sai shi sai Hibba da ta makale a kusa da ita dan tana da kiwa. Tsam ya taso daga wajen zaman sa ya dawo kusa da ita, har tana jin kanshin turaren sa sosai, bata dago ba ta gaishe shi ya amsa yana bin ta da mayen kallon sa, riga da skirt ne a jikinta simple dinki amma tayi kyau sosai, fuskar ta fayau babu hoda sai yar rama da tayi akan ranar da ya ganta a kitchen.
"Fine baby, ya sunan ki?" Ya mika ma Hibba hannu ta noke yayi murmushi
"Madam ya gida?"
"Madam?" Tace a ranta
"Lafiya lou." Ta amsa tana mummuraza yan yatsun hannun ta. Kallon hannun yayi, ya kai nasa hannun ya kama tayi saurin janye wa a tsorace ta kalle shi, a lokacin ta lura da shaddar dake jikin sa an masa karamin dinki iya guiwa kansa babu hula ya rage gashin sa sosai.
"Menene haka? Kamar kin ga wani dodo." Ya tambaya cike da mamakin ta
"Ka daina taba ni." Tace kai tsaye tana kokarin tashi daga kujerar yayi saurin fizgo mayafinta yana zaro mata idon sa.
"Me kike nufi? Aure fa zamuyi? Me yasa kike behaving kamar baki san yadda rayuwar ta zama bane, bana fa son kauyanci."
Kallon sa tayi cike da mamakin sa, ta lura akan rayuwar da yake so yake ganin daidai ce nan da nan zaka ga fushin sa, ita kuwa ta gwammace duk abinda zai fad'a ya fad'a fushin sa ba komai bane akan fushin ubangiji. Tana jin sa ya cigba da gaggasa mata magana san ransa, tayi biris kamar ba da ita yake ba, tana da yakinin zafin zuciya ce dashi, kuma bakin sa bashi da control wejan gasa magana. Sai da ya gaji don kansa yayi shiru yana jan tsaki. Ya zaro wayar sa ya hau kira yana cigaba da huci akan kawai ta hanashi taba jikinta.
"Babe where are you?" Yace bayan an daga wayar
"Ok I'm on my way." Ya kashe kiran ya mike yana kallon ta
"Ba zan yi tolerating kina hana min abinda yake nawa ba, ba zan sake dawowa ba idan an kawo ki gidan zaki ga yadda zanyi dake."
Daga haka ya juya yana taku dai-dai yayi ficewar