RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 30

81K to 84K   out of 87.6K words

kula shi ba ya cigaba da shiryawa bakin sa na bitar suratul bagra, agogo ya daura a tsintsiyar hannun sa ya kafa hular yana gyara mata kari, nan da nan MD din ya shirya ya zo ya tsaya kusa dashi yana budawa.

"I'm ready, muje ko?"

"Shuganan yan naci da sa ido." Ya wuurga masa car key din yana ficewa daga dakin, dariya ya saka ya bishi suka jera gwanin sha'awa.


Afwan pls, yau nayi baki ne.


RM
   42-43

****Cikin gidan suka nufa kai tsaye maimakon su tafi, MD na gaba yana bin bayansa, babbar rigar ta zauna a jikinsa, yayi kyau ainun sai kamshin turare ke tashi daga jikinsa masu dadi kamshi. Gud'a su Anty Faty suka saki suna shigowa, yayi murmushi yana zama a daya daga cikin kujerun dake falon, su ya su ne yan gidan a falo ya kalli wajen da su Amira suke zaune, daya bayan daya suka zame daga falon sukayi daki cike da tsoron abinda zai biyo baya, tunanin su ko zai fadawa su Anty Faty abinda sukayi, duk sai suka tsure suka kasa zama a dakin da suka koma suna tsoron yadda zata kasance.

"Dauko amaryar tamu za'a tafi ne!? Wannan wanka haka."

"A'ah, zance zan rakashi kinsan ya kyello wata fa, biyu zai hada."

"Banda sharri Mudan, wai haka Abuya?"

"Indirectly yake fad'a muku aure yake so ba wani abu ba."

"Haka nace maka oga?"

" Action speaks louder than voice, action dinka ya nuna."

" Naji, is it a crime? After all ai na girma ko Anty Asy?"

" Ba ruwana a cikin wannan maganar, ni team Abuya ce."

" Duk bakwa sona kenan?"

" Gaskiya, ga latest ango wa zai bi bayan gauro."

"Ni kuma potential ango ba, ku jira IV."

" Kamar gaske, muje karka cinye time Malam."

Yace yana mikewa

" Ina munafukan yaran nan suka shiga?"

" Su Amira wai?"

" Su, ko kafar su na gani a part dina ku shaida sai na kakkarya su na zubar."

" Me sukayi maka?"

" Sunfi kowa sani, muje bari mu dawo Anty Faty."

" Ok Ango, muna nan muna jiranku."

" Wai moctail din ne? Ba za'a hakura ba?"

" Ai har na kira tribes din, sun gyara mana wajen ma, we just eat and snap, nothing more, tunda ka hana mu biki sosai."

" Shikenan, zan fada miki idan mun kusa isowa. "

" Owk sai kunzo, zamu shirya muma kafin nan. "

" Ki fad'a ma su Mom. "

" Owk. " Tace tana mikewa

***Wanka tayi da ruwan turare me kamshi cikin kayan da Amaryar Kb ta aiko mata dasu na tafiya gidan aure, ita kanta tasan ta sauya ta zama wata ta musamman, ga fatar ta da ta zama kamar ta jarirai dan taushi. Kayan da aka turara su da turaren kaya wani material ne me sulbi da akayi masa dinkin doguwar riga fitted, daga kasa ta dan bud'e, ta saka ya kamata sosai daga sama, wuyan sa me v shape hakan ya sake fiddo da kyawun dinkin da kuma zaman da yayi a jikinta das kamar ma material ba. Mayafi madaidaci ta yafa a saman kanta tare da taimakon ya Hadiza ta gama shiryawa, ta kama hannun ta, ta kaita dakin Abba, sannan ta fito ta barsu a ciki yana yi mata nasiha me ratsa jiki, kuka ta samu kanta da yi wiwi, sai ga Abbati ya shigo yace wa Abban Abdallan ya karaso, cewa yayi ya shigo dashi ciki, ya koma yayi masa iso suka shigo a tare, har zuwa dakin Abban wanda shine karon sa na farko na shigowa har ciki sosai haka, zama yayi ya tankwashe kafarsa cike da girmamawa ya gaida Abban kansa a k'asa, amsawa Abban yayi sannan ya cigaba daga in da ya tsaya

"ABDULLAHI kaine shugana, kai Allah ya dora ma nauyin kula da hakkin iyalinka, sannan dole ne sai kayi hakuri da sha'anin mata ka dauke kai a abubuwa masu yawa sannan zaman ku zai yi dadi, ga Asma'u na amana ce a gareka, dan Allah karka ci amanar ta, ka kula min da ita duk da bani da haufi akan tarbiyyar ka, na gamsu da kai dari bisa dari."

"In sha Allah Abba."

"Madallah ke kuma Asma'u, ABDULLAHI mijinki ne, wanda aljannar ki take karkashin kafafunsa, ki bishi kiyi mishi biyayya kamar yadda Allah ya hukunta a gareki, kar naji ko na gani, kiyi koyi da halin mata na gari ki zauna da mijn ki lafiya da yan uwansa, kiyi hakuri ki ji kiki ji, Allah yayi muku albarka, ya baku zaman lafiya ya kade fitina a zamantakewar ku. "

Abdallah kadai ya amsa da Amin a ciki, ita kuma kuka kawai take wanda yake jin kukan har cikin ransa, shi Abban ya fara sallama ya fita ya tsaya a wajen su umma ya gaishe su sannan ya fita waje yana jiran ta, MD na zaune a mota yana danna waya ya fito ya jingina da jikin motar maganganun Abban na dawo masa, lallai aure wani girma ne da Allah ya bawa namiji wanda idan be yi wasa ba tsaf zai iya kaishi wuta, dole ne ya jajirce wajen ganin ya sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansa ko dan samun rabauta. Kamar me kirga taurarin dake sararin samaniya haka ya daga kansa yana kallon hasken farin watan da yafi kama da dan kwana goma sha biyar saboda hasken sa, iska ya shaka ya fesar dai-dai lokacin da suka fito da ita kanta a lullube da mayafi, da sauri MD ya bud'e musu kofar, ta saka kafarta bakin ta dauke da Bismillah ta shiga, Ya Hadiza ta rankwafo tana fad'a mata wata magana kafin su juya su koma ciki. Bayan ya bud'e ya shiga MD ya juyo bayan yana dariya

"Yanzu shikenan na zama driver ko?"

"Face your front."

" Ai shikenan, Amarya barka da dare, welcome to the family Anty Asmy! "

" Ina wuni? "

" Lafiya lou Anty. "

Murmushi tayi me sauti, ya matso kusa da ita yana leka fuskar ta, har yanzu kunyar nan ta jiya bata bar ta ba, hannu yasa ya janye mayafin da ta rufe fuskarta, tayi saurin sadda kan k'asa ya saka hannu ya dago fuskar tata yana kallon cikin idon ta

"Kunyar ce wai?"

Daga masa kai tayi

"Oh! Toh I'm sorry toh... Bansan me yasa ba, na kasa resisting."

Sai ya dan sosa kansa yayi murmushi, duk maganar da suke MD baya ji dan k'asa k'asa yake maganar sosai ga sautin dake tashi a motar. Shiru ne ya biyo baya sai hannun ta da ya rik'e yana motsa su a cikin nasa, ta lura yana son hakan dan duk sanda suka hadu sai yayi kokarin rik'e mata hannu. Waya taga ya dauka yayi kira, kalma biyu ya fad'a ya ajiye yace

"Mu wuce chan kawai, sun riga sun tafi."

"Ok!" Yace yana juya motar zuwa hanyar tribes din.
 
   Parking yayi ya fita ya bar su a ciki, ya kalli mayafin jikinta ya saka hannu ya gyara mata shi yadda zai sauko sosai, sannan ya cire babbar rigar tasa ya ajiye yace mata

" Ba zamu dade ba, dan sun takura ne ma kawai. "

" Fita zamuyi? " Tace tana kallon sa ta hasken da ya shigo motar

" Eh, ciki zamu shiga, your new family suna ciki suna jiranki. "

Sai ya bud'e murfin motar ya fita ya zagayo wajenta, ya bud'e yana mika mata hannu

" Kunya nake ji. "

" I'm with you, ki saki jikinki kawai kinji?"

" Zasu karbe ni?"

Dan dam yayi yana kallon ta yana hada maganar ta da wani tunani na daban, itama kallon sa take ta kasa motsawa daga zaunen bare ta karbi hannun nasa ta fito,

" Um?" Tace ganin kamar he was lost in thought, murmushi ya sakar mata ya kamo hannun nata ya taimaka mata ta fito, sannan yace

"Duk wanda be karbi Husna tah ba nima ban karbe shi ba, ko waye. So just relax, you are safe! "

Wani gwarin guiwa ne taji yazo mata, ta rik'e hannun nasa kamar yadda ya bukata suka shiga takawa zuwa cikin ginin da ya tsaru, mutane ne birjik a wajen kowa na aiwatar da abinda ya kawo shi, mafiya yawancin su saurayi da budurwa ne sai yan tsirarin mata da miji ko kuma gang din abokai a gefe, sama suka haura hasken fitilun wajen na sake kayatarda ita, yau ne karo na farko da ta fara zuwa irin wannan wajen, su din basu da yawan wayewa duk da daidai gwargado sunyi bokon amma kuma basu da irin wannan exposure din ko dan irin takunkumin da Abban ke saka musu a dukkan stage din rayuwar su, idan basa makaranta toh suna gida suna taya umma aikace aikace, ballantana ita da ta kasance daddawar daka ko yaushe tana manne da gida bata son yawan yawo ko gidan yan uwa ne.
    Suna zura kafarsu a kofar suka ji saukar abu a kansu, sai tafin mutane da kalmomin congratulations dake tashi, gefe wasu maza ne su biyu bakin su rik'e da abun busa suna musu busa me dadi dake dauke da taken aure me dadi, murmushi kawai taga yanayi hakan ya sakata itama yin murmushin suka cigaaba da takawa har wajen da aka tanadar musu na zama, suka zauna sannan aka shiga daukar hotuna da mutanen da bata san kowa a ciki ba, yawancin su yan mata ne sai manyan da ta gani basu fi hudu ba, sai su MD da su uku ne ma kachal maza a wajen, duk abinda yayi itama shi take yi dan bata san yadda ake gabatar da abu irin wannan ba. Komawa sukayi suka zauna bayan an gama hotunan kafin a shiga gabatar da abubuwan ci da na sha dangin su virgin mojito, da dangogin su snacks da wasu kalolin drinks din da bata ma taba ganin su ba, sai gashin nama da kaji da wani abu da ta hanga kamar shrimps ne ko scorpion ce ita bata ma gama tantancewa ba. Nasu daban special aka jide musu a gabansu, ya dauki cup din da aka zuba wani mint drink yayi sipping kad'an sannan ya mika mata, a kunyace ta sha ya ajiye yana kallon sauran kayan, bashi da plan din dadewa a wajen dan su kansu sun san wannan din ba al'adae sa bace sam. Da hannu ya yafito MD yazo ya duka ta side dinsa yace

"Just 10min ya rage mu wuce, we can't stay long!"

"Ok, bari na fad'a ma Anty Faty, nasan dama ba zaka zauna ba, suma sun sani. "

" Yawwa. "

Zuwa yayi ya fad'a mata, ta biyo shi suka dawo wajen Abuyan tace

" Haba Abuya, 10min yayi kadan ina laifin 30min, amarya pls ki saka baki ku dan zauna, dan ku fa muka taru, pls kayi hakuri ka kara mana, yau ne kawai shikenan fa. "

" Mu zauna? " Yace yana kallon Asma'un da taji kamar ta nutse dan kunya, ita mene nata da zai tanbaye ta, kin magana tayi sai ya kalli Anty Faty

" Ta gaji da yawa, kinga kawai gwara mu tafi. "

" Haba amaryarmu, please! "

" Zamu zauna Anty, har a tashi ma."

" Kai yawwa, hakan shine nan da 1hour kowa ya kama gabansa, thank you amarya. "

Sai ta juya ta bar wajen, kallonta yake amma taki bari su hada ido sai ma gefe da ta kalla, MD ne ya bigi kafadar sa cikin sigar tsokana yace

" Woman wrapper. "

Ai be bari ma ya gama tantance kalmar ba, yayi wuf ya bar wajen sai hango shi yayi a wajen su Amira suna magana, girgiza kai kawai yayi ya matse mata hannu da dan karfi ganin taki kallon sa, ta juyo da sauri ya kanne mata ido

"Kinji wai nine woman wrapper, amma gaskiya MD ya yanke ni, anyways yadda kika ce haka za'a yi hajjaju na, your wish is my command, idan ma kwana kika ce muyi anan din so be it."

Dariya ya bata yadda yayi maganar, a daidai lokacin romantic photographer ya dauke su a hoto, tana kallon sa tayi dariya shima yayi dariya, hoton da yayi masifar kyau, shi kansa sai da ya yaba hoton dan ya dade be ga couples din da sukayi masa kyau ainun kamar su ba, cigaba yayi da daukar duk wani motsin su, dan yasan hotunan zasu kawo masa kasuwa sosai.

Kamar yadda tace din kuwa be sake complain ba, sai da aka tashi tas bayan an cika Asma'un da kyaututtuka masu yawan gaske, aka lode musu su a mota hade da take aways dinsu dan babu abinda suka ci a wajen daga ita har shi. Gidan suka wuce dukka har su Anty Faty, kuma a kusan tare suka isa, Anty Faty yayi wa magana yace ta kaita wajen su Mom, shi kuma ya wuce sabon part din nasu dake chan baya.
Rik'e hannun ta Anty Faty tayi suka shiga ciki, su Amira na bayan su suna yaba Asma'un da basu yi tunanin haka take ba, su a tunanin su da aka ce bazawara sun dauka zasu ga wata katuwar mata, sai gashi sun ganta fiye da yadda sukayi tunani. Suna shiga Mami ta taso ta rungume Asma'un, duk suka saka dariya har Mom dake zaune a gefe

"Mami tayi sabuwar 'ya mun shiga uku." Anty Asy tace aka sake yin dariya

"Ya ranku, sannu kinji 'yata, sannun ki da zuwa."

Zamewa tayi ta zube a kasa ta gaishe da Mamin ta amsa a sake tana sake dagota,

"Mike karki zauna a k'asa kinji, tashi."

Tashi tayi a kunyace ta zauna a gefen carpet din dake malale a wajen sannan ta gaishe da Mom ta amsa fuskar ta cike da fara'a, duk da kanta a kasa yake bata kuma kalli fuskar kowa acikin su ba, amma muryar Abdallan ta sak a cikin maganar matar da suka gaisa wanda kai tsaye ta raya ita din mahaifiyar sa ce, nan nan kawai suke da ita har yan matan da ta lura kannen sa ne. Wajen minti talatin tayi a wajen su, sai da Mami tace Anty Faty ta tashi ta rakata shashen ta a barwa gobe, idan yaso ko Baba Alhaji sa gaisa goben saboda dare, an bar mata danta shi kadai yana kallon hanya. Babu wanda maganar bata bawa dariya ba, banda Asma'u ta taji kamar ta haka rami ta nutse, tayi musu sallama Anty Fatyn ta rakata har shashen nasu da yake da yar tazara tsakani, a kofar ta ja ta tsaya tace

"Asubah ta gari amarsu, sai mun shigo gobe."

"Nagode."

Tace ta turo kofar da take half way a bud'e, ya barta ne daman saboda dawowar ta, yana jin an turo ya fito daga kitchen din jikinsa sanye da wando short babu riga a jikin sa saboda yanayin zafin da ake tun rana, duk da akwai AC amma shi mutum ne me matsanancin jin zafi shiyasa da wuya yake zama da cikakken kaya in dai yana dakin sa ne, sai dai idan zai fita ya dora jallabiya yana dawowa ya cire sai dai idan fita zai yayi nisa sosai. Kin kallon sa tayi ta zauna da sauri a kujera, yayi murmushi ya ajiye cup din hannun sa ya dauki singlet dinsa dake ajiye a saman kujerar ya saka sannan ya dauki cup din ya kai bakin sa yana zama a gefenta.



RM

44-45

***Tsaye yake a jikin window yana leka harabar gidan sanda yaji mota ta tsaya, Fido ce tare da Faiza suka dawo a motar sa, kansa da yake masa ciwo sosai ya rik'e da hannu ya dawo ya zauna a gefen gadon tunanin ta na sake bijiro masa, wani irin zafaffen son ta ne yake nukurkusarshi, ga kuma tsoron Fido da ya cika kirjin sa har baya so yayi ko da kwakkwaran motsi a gabanta. Yana jin takun hawowar su saman yayi saurin kwanciya ya dintse idon sa tamkar me bacci, turo kofar tayi tana da kofar ta kalle shi tunanin ta bacci yake sai kawai ta juya suka shige dayan dakin suka rufo, yana jin haka ya lallaba ya fito, ya sauko k'asa duk da jikinsa babu kwari har lokacin dan babu inda yake zuwa yana kunshe a daki, ji yayi hasken ranar yayi masa gau, kamar zai disashe masa ido saboda kwana kin da yayi a daki yana bin umarnin Fido din, kallon kofar gidan su yayi kamar zai shiga sai ya fasa ya shiga takawa a kafa har zuwa titi ya samu napep ya fad'a masa in da zai kaishi. Suna cikin tafiya ne ya lalubi wayar sa yaji wayam ya manta ta a daki gashi be fito da wallet din sa ba, be ma san in da take ba a takaice dan be ganta ba tun da suka dawo daga asibiti, gashi sun yi nisa sosai dan daf suke da gidan Abban ba abun yace su juya ba, tunda ma har yazo this far gwara kawai ya karasa dan be san yaushe zai sake samu wani chance din irin wannan ba.

"Oga idan muka je zan shiga na karbo maka kudin ka, ashe ban fito da wallet dita ba."

" Ba damuwa." Me napep din yace a ransa mamakin Adam din yake dan kana ganin sa kaga wanda yake cikin yanayi amma kuma maganar sa ras sai rashin kuzari da wani uban gashi da ya bari a fuskarsa babu kyawun gani, da fari ma ya dauka ko bashi da hankali dan da ya tsaida shi har da ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya, sai da yayi magana sannan ya fita daga shakku har ya dauke shi ma. A kofar gidan Abban suka tsaya ya sakko ya tura kansa ciki, Abba na tsaye dasu Abbati yana musu magana akan gyaran wajen gidan sai ga Adam, da kallo duk suka bishi ya rissina ya gaida Abban ya amsa yana nazarin yanayin sa

"Dan bani 300 Abbati na sallami me napep na manta wallet dita a gida ne."

"Ungo bashi Abbati, muje ciki Adamu."

Abba ya ciro 500 a aljihunsa ya mikawa Abbati su kuma suka wuce cikin gidan, umma na tsakar gida suka shigo ta dan zabura da ganin Adam din amma kuma sai batayi magana ba suka wuce dakin Abba shi da Umar da Abban, suna shiga Abba yace Umar yaje ya kawo ma Adam din abinci, tashi yayi ya shiga gidan ya karbo a wajen a umma ya kawo masa, Adam da ya kwana biyu ko isashen abinci baya samu yaci ya karba ya hau ci

28 / 30