Author : RANO Category : African Stories & Novels
ran Umman ya sake sosowa ainun, bata taba yi wa Abban bore ba, tun auren su take masa biyayya daidai gwargado, ba zata bijire masa ba a yanzu musamman da girma yazo, amma bata ji dadi ba, kuma shima ya san be kyauta mata ba.
"Allah Umma kina da hakuri sosai, anya akwai wadda tayi hakurin ki kuwa a cikin mu?"
Murmushin umman tayi, sak Asma'un itace, baki daya halayen ta irin na Umman ne shiyasa take tausaya mata, bata da zafi ko kad'an hakan ya saka tun da ma kowa taka ta yake, ballantana kuma ta hadu da miji irin Adam. Har suka isa asibitin ran Umman be saki ba, ta daure dai kawai suka shiga ciki. Adaidai lokacin Asma'un ta farka, zafin ciwon ne ya farkar da ita, babu wanda be tausaya mata ba, dan ma tana da masifar dauriya, gefe umma ta koma ta dinga share hawaye, zata sake lallaba Abba ita dai ya barta tayi jinyar yar ta, ko ta koma gidan ba zata taba samun nutsuwa ba, ba wai kuma dan tana ganin ba za'a yi Asma'un abinda ya dace ba, sai dan kawai dai wani abun dole sai uwa mahaifi.
Ganin su umman ya sakata sake jin ciwon na dawo mata sabo, tun bayan auren bata ga umma ba, dama jiyan take so ta tambaye shi taje ta wuni dan tayi kewar gida sosai, sai ga tsautsayin da ta gamu dashi.
Allura akayi mata da zata rage mata zafin ciwon, hakan ya saka ta dan samun nutsuwa. Kin motsawa nan da chan Hajiya Mama tayi dan tana tsoron ta bar su Asma'un ta fad'a musu abinda ya faru duk Adam din ya rantse mata be mata komai ba amma bata yarda ba, tana kyautata zaton yana da alaka me karfi da abinda ya farun.
Har yamma likis su umma na asibitin duk su Hidaya sun zo da yan uwan umman, Adam ma ya dawo amma be sake shigowa dakin ba tsakanin sa dai wajen zuwa wajen Drs sai idan abu ya taso haka suje da Abbati. Su kansu su Ya Hadiza sai da sukayi mamakin sa, sun ga sauyawar sa sosai har suka yi tunanin ko dama ya chanja bayan auren dan aure na chanja mutane da dama.
Bayan sun yi sallar magriba sun dawo da yaga an ragu sosai a dakin sai ya shigo, da sauri Asma'u ta rufe idon ta Hajiya mama ma ankare da ita, a dan baya ya tsaya ya gaida umman da rabon su dashi tun bikin, ta tambaye shi me jiki ya amsa kansa a k'asa tamkar ma kirki.
"Ya jikin?" Yace yana kallon gadon da take kwance, bata amsa ba ta sake rufe idon ta sosai, umma dake zaune daga gefe ta dan leko ta
"Inaga ta samu bacci."
Juyawa yayi ya fice duk suka bishi da kallo hatta Maman na cike da mamakin Adam din, kamar wanda aka chanjo mata shi da wani daban, shiyasa ta sake tabbatar da sanin sa, fatan ta daya Allah yasa ba turo yar mutane yayi daga benen ba ma, dan babu wanda ya san ainihin me ya faru ya dai ce zamewa tayi ta fadi.
Tana jin ya fita ta saki kuka me cin rai, bata son sa bata kaunar sa ko kad'an, bashi da tausayi bare imani ko na digo, kanta sukayi dukka kowa na tambayar ta menene, bata ce komai ba, ta dinga kukan ta a hankali wanda kusan duk sun dauki hasken dalilin kukan nata, yana da nasaba da shigowar Adam did, kunya duk ta kama Hajiya Mama, ta dinga borin kunya tana so ta dauke hankalin su daga kan Asma'un amma kuma sun riga sun gane komai.
Sanda su umma suka zo tafiya tayi bacci, dan haka bata san sun tafi ba sai chan wajejen sha biyu na dare da ta farka ta ganshi zaune akan kujera yana danna waya, kansa a kasa yana ta murmushi, wurga idon ta tayi zuwa sauran sassan dakin, babu kowa sai shi kadai ya bada dukkan attention dinsa akan wayar.
"Zan sha ruwa." Ta furta tana kallon gefe, dagowa yayi ya kalle ta, ya dauke kansa ya cigaba da danna wayar sa, ta sake maimaitawa a karo na biyu nan ma yayi biris.
Jujjuya hannun ta, ta dinga yi mara ciwon cikin jin ishirwa sosai, ta yi kokarin daukar na ajiye akan bedside drawer din asibitin amma ta kasa, yayi kamar be san me yake faruwa ba, sai da ya gama abinda yake tas, sannan ya tashi ya dauki ruwan ya mika mata. Kautar da kanta tayi alamun bata so, ya dire mata a wajen ya fice gami da jawo mata dakin!
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
RM
12
***Tun da ya fita be sake dawowa dakin ba, har drip din da yake hannun ta ya kare, jini ya soma biyo hannun. Tsoro taji, ta shiga kiran nurses din amma babu wanda ya shigo,akwai yar tazara tsakanin nurses lounge din dakin da aka kwantar da ita, gashi ba zata iys kashewa ba saboda dayan hannun ko motsa shi bata isa tayi ba, cigaba da kallon robar da drip din ke sauka tayi, wani guntun hawaye ya ziraro zuwa saman kuncin ta, ta gaji sosai da zubar da hawayen ta, zuciyar ta zafi kawai take mata, bata san dalilin da ya saka aka barta daga shi sai ita ba, ya kamata ace mace ta zauna ko da kuwa Yaya Hadiza ce idan Umma tana jin nauyin Hajiya Mama, ji tayi duk ta soma jin haushin su, tunda ita bata san abinda ya faru ba, Hajiya Mama ce ya kamata ta zauna amma sai ya nuna mata shi zai zauna, ya dinga mata magiya ganin cewa ai mijin ta ne ya saka kawai ta kyale shi, tana fatan dalilin hakan su gyaro matsalar su kafin wayewar garin.
Wucewa wata nurse tazo yi zuwa wani dakin sai ta duba ta ganta, tayi saurin karasowa dakin ta kashe drip din cike da mamakin ganin babu kowa a dakin sai ita kadai
"Babu wanda zai kiramu? Ke kadai kika zaune?"
Girgiza mata kai tayi
"Fita yayi."
"Ok, idan ya dawo kice ya daina nisa gaskiya ko a samo wata babba ta zauna dake aikin na mace ne ba namiji ba, ko ba a garin nan kuke ba? "
Tayi mata tambayar cike da mamakin idan har yar gari ce ai be kamata a barta da namiji ba, bata amsa ba sai kawai tayi shiru tana motsa yan yatsun hannun da suka gaji sosai, juyawa nurse din tayi ta fita tana mamakin dalilin da zai saka a barta ita kadai bayan dazu cike wajen yake da yan uwanta gal
Baki daya ma baya cikin asibitin dan sai da akayi asubah sannan ya dawo, bata runtsa ba saboda azabar ciwo haka ta dinga kuka me cin rai ita kadai kwal a daki kamar bata da galihu, Fido ce ta matsa masa da kira gashi ya rasa dalilin da ya saka baya iya kana kansa zuwa wajenta idan har ta kira din, sai yaje ya dawo yake jin haushin kansa, ya sha tama yi mata wulakanci amma sam ya kasa, ita kadai take juya shi son ranta duk kuwa da ita din ma wataran yana mata bore idan yan abun suna kusa dashi.
Ganin dawowar sa ya saka nurse din nan dawowa dakin, ta tarar dashi yana kokarin kwanciya akan couch din dake dakin, dakatawa yayi ganin ta shigo a tunanin sa ko magani zata bawa Asma'un
"Be kamata ka dinga nisa ba gaskiya, dan dazu Allah ya kiyaye nazo da wuri, baa so a bar mara lafiya shi kadai ko Yaya ne, idan akwai uzuri babba sai a nemo mace dattijuwa ta zauna da ita."
Wani kallo yayi mata irin na wacece ke, kafin yace a kufule
"Ina ruwan ki? Bana son gulma da munafurci malama."
Tsaye tayi tana duban sa baki bud'e, ya ja tsaki ya kwanta yana rufe kansa har sama da abinda aka kawo wa Asma'un saboda rufa, kallon gadon da Asma'un take tayi, taji tausayin ta ya kamata, ta kuma dau alkawarin in dai ta gane iyayenta sai ta sanar musu da su zauna da yar su gaskiya, yanzu take da bukatar kulawa fiye da kowanne lokaci.
Ana idar da sallah Hajiya Mama ta taho asibitin, ta tarar duk suna bacci shi a kujera ita a gado, murnushin jin dadi tayi , ta saka sallaya a gefe itama ta dan kishingida a wajen.
Duk abin nan a tunanin Nadeeya a asibitin Maman ta kwana, shiyasa daga asibitin su tayo nan din wajen bakwai da rabi dan night duty tayi dama da tabbas ita zata zauna da Asma'un.
Zuwan ta ya tashi Adam din, sai a lokacin ya ga Hajiyar ma, ya mike suka gaisa, Nadeeya ta tambaye shi me jiki ya amsa da sauki tamkar wanda ya san halin da take ciki da gaske. Tare suka tafi gida suka bar Hajiyan yaje yayi wanka ya huta. Wajen tara Umma tazo tare da Abbati da breakfast, jiya bata iya bacci ba saboda tunanin halin da Asma'un ke ciki, ta kuma sake rokon Abban akan ya barta amma sai ya nuna fushin sa sosai, sai kawai ta kyale shi duk a tunanin umman ai Hajiya Maman anan ta kwana, a yadda ta sameta ma da yadda ta amsa dubiyar zaka rantse a wajen ta kwana. Babban likita ne yazo, suka shigo tare da nurses ya duba Asma'un da hannun nata, hakan ya farkar da ita, suka gama suka fita daga nan yace ayi masa hoton hannun sannan sai aga me yakamata ayi.
Matsawa Umma tayi gaban gadon tace
"Ya jikin naki?" Maimakon ta amsa sai kawai ta saka kuka.
"Kuka kuma? Menene kuma na kuka eh? Hakuri zakiyi kowanne bawa da kaddarar sa."
"Dan Allah karki tafi umma, ki zauna."
"Ai dama ba yanzu zan tafi ba, sai anjima."
" A'ah, karki tafi gaba daya, bana son ya Adam ya zauna mugu ne, bashi da kirki."
Da sauri umman ta kalli Hajiya Mama da itama umman take kallo a gigice, sam Asma'u bata san Maman na dakin ba tunda a k'asa take daga jikin bango baa gano ta.
"Karki sake cewa mijinki mugu, bana so kar na sake ji." Umma ta fad'a ranta na sosuwa sosai.
Cigaba Asma'un tayi
"Jiya ficewar sa fa yayi ya barni, drip din ya kare babu kowa, so yake na mutu wallahi." Ta karashe tana sake fashewa.
Shiru umman tayi bata ce komai ba, sai zuwa chan tace mata tayi shiru kar ta karawa kanta wani ciwon ko ta sakawa kanta hawan jini wanda bata ma san ko ta riga ta kamu dashi ba.
Kasa hada ido mama tayi da Umma, ita kuma umman tayi kamar bata san me Asma'un ke nufi ba, har zuwa sanda Abba yazo duba Asma'un, tana ganin shi ta sake fashewa da kuka, sosai yaji tausayin yar tasa, ya kuma san tabbas baa kyauta mata ba. Hakuri ya dinga bata da zai tafi Hajiya Mama ta tashi ta bishi waje, umma ta tabe baki tana ayyana yau ko da auren ta zai mutu ba zata bar asibitin nan ba, kawaici da kara daidai gwargado tayi, kuma babu wanda baya son dansa bare ace ta nuna son yaya, ta shiryawa Abba bore duk abinda zai ce ba zai hanata zama ta kula da Asma'un ba.
Dawowa ciki Mama tayi, suka cigaba da zaman kurame har zuwa sanda yan gidan su Asma'un su Rauda suka zo, da kuma kannen Adam din, hakan ya saka wajen sakewa ba kamar dazu da ko uffan babu me cewa wani a cikin su ba, ita Hajiya Mama nauyi da kunya ta hanata katabus, ita kuwa Umma tana sane ta mata banza dan ta lura bata san kawaici ba, shiyasa zata nuna mata ita ma tana da iko akan yayanta da kuma mijinta, ba dole sai abinda taga dama take so shi za'a yi ba, ko da hakan na nufin cutar da yayan ne.
La'asar likis Hajiya Maman tayi musu sallama ta tafi a zuwan sai gobe da safe, umma bata yi mamakin tafiyar ta ba dan kunya take ji sosai musamman da Umman ta gano ba ita ta zauna da Asma'un ba, kuma taga duk take taken Umman na son nuna ikon ta a wannan karon shiyasa ma ta ce Abban ya bar umman ta zauna ta kula da Asma'un ita sai ta dinga zuwa da safe, be yi musu ba tunda dama ita yake karawa amma dama har ga Allah yafi son umman ta zauna sai dai ba zai iya ce mata ta zauna din ba kar Hajiya Maman taga rashin kyautawar sa. Hakan kuwa da akayi sai yaji dadi, ya tafi kasuwa da yakinin daga umman har Asma'un zasu fi jin dadin hakan. Da yamma sai gashi ya sake dawowa ya sake duba jikin nata yaje ya samu likitan yaji duk bayanan da ya kamata ya sani akan hannun nata.
Adam be dawo asibitin ba sai dare, gida yayi tafiyar sa ya kwanta ya huta ya fito da yamma ya je chan majalisar su sannan ya wuce ya siyo nama da lemuna ya wuto asibitin. Babu wanda ya kulashi a cikin su Rauda shima be kula su ba, umma kawai ya gaida sai Ya Hadiza da ta fito daga toilet bayan ya zubar da ruwan da ta goge wa Asma'un jiki dashi. Kadaran kadahan ta amsa ya dan yi tsaye jim sai kuma ya ajiye ledar hannun sa ya fice.
"Adam baya kyautawa sam, na rasa dalilin da yasa ya amince da auren nan idan har baya son Asma'u."
Umma tace cike da takaici
"Hmm, duk wanda yayi na gari ai kansa ko? Ni dai fatana Allah yasa ba shine dalilin karayar nan tata ba, dan idan har aka tabbatar toh babu amfanin zaman su fa."
"Ni kaina abinda nake zargi kenan, dan dai kinga ba zaka fara tambayar yaro yana cikin wannan halin ba, jira nake ya sake samun karfin jikinta sai mu bi baasi, idan har akwai cutar wa babu amfanin auren."
"Gaskiya dai, ya kamata a bincike ta aji."
" Allah ya kyauta. " Umma tace tana mikewa ta fita wajen Abba suyi magana, ta tarar da Abba ya dawo zai shigo dakin, ta hade rai a tunanin ta zai mata maganar tafiya amma sai taji yace
" Yaran nan ya kamata su tafi haka saboda dare, idan kuma mazajen nasu ne zasu zo daukar su toh."
" Eh sune zasu zo. "
" Toh Madallah, ya jikin nata? "
" Da sauki. "
" Allah ya kara sauki, bari na wuce ni, zan shigo da safe saboda ance babban likitan da safe yake zuwa sai kuma yamma wajen biyar. "
" Ok, Allah ya kaimu. Allah ya bamu alkhairi. "
" Amin summa Amin, sai da safe. "
Ya juya ita kuma ta koma ciki, anan take fad'a ma su ya Hadiza yadda sukayi da Abban. Sukayi dariya Rauda har da kwaikwayon yadda Umman ta fita da nufin ita da Abban ko shi ko ita idan yayi mata maganar tafiya. Dariya suka saka gaba daya har Asma'u da take kwance sai data murmusa. Daya bayan daya suka yaye ya zama daga ita sai Umman, ta sake sosai tana jin kamar bata da saurin ciwo, hira umman ta dinga janta tana son gano irin zaman da take a gidan Adam din duk da dama duk sun yi hasashen irin rayuwar da zata tarar din. Kasa fadawa Umman dalilin da ya sakata faduwa tayi, dan da nauyi sosai, tace mata me? sai kawai tace mata zamewa tayi a wajen sauka daga benen bata fadi ainihin abinda ya faru ba, kamar dai Umman bata yarda ba, amma kuma sai ta kyale ta kurum, ta bita da addu'ar samun lafiya.***
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES