Author : RANO Category : African Stories & Novels
fitar a bada ita ta yadda ba zata taba wani amfanar wanda aka bawa ba."
" Sosai, Allah ya bamu ikon sauke nauyin dake wuyan mu."
" Amin na Ma'u."
" Ka fara kenan ko?"
" Daga magana?"
" Tashi mu shiga wajen ciki, Allah yasa bakayi barin zance ka fadi maganar nan ba."
"Wacce, ta I love you din nan?"
"Kana da katuwar matsala, kaga ka sameni a ciki kawai."
"Allah ban fad'a ba, na dai ji inason na fad'a da na shiga dazu, na daure dai saboda abinda kayi min alkawari."
"Kaji dashi, idan ma ka fada kanka kayi ma ai."
"Ba zan ma fad'a ba." Yace yana zura takalmi a kafarsa, tuni har Abdallan ya kai kofa , yayi sauri suka jera har ciki, Ihsan da Amira na zaune kowacce da waya suna dannawa, suna ganin su kowacce ta nutsu, suka gaishe da Abdallah tunda dama shine be shigo ba, ya amsa yana hararar hannun Ihsan da yake ita ke facing dinta,
"Baku da aiki sai danne dannen waya ko?"
Girgiza kai tayi, ya wuce be sake cewa komai ba, dariya ce ta so kwacewa Ihsan din tuno abinda taji jiya, ta kalli Amira tayi mata signal da ido,dan dama tun a jiyan ta fesa mata labarin, kama bakin ta tayi da hannu tayi mata alamar wallahi babu ruwan ta,
"Gulmar me kuke? Munafuki."MD yace yana duban kowaccen su
"Wallahi Allah Ya Mudan babu ruwa na."
"Nima babu ruwana."
"Sai kun fad'a min, kallon me.kike mata? Ke kuma me kike cewa ba ruwanki?"
"Dama ihsan ce..."
"Amana fa nace miki."
"Toh ni ai ba ruwana, ni bance ki fad'a min ba kika fada min,."
" Wai me? Me ta fad'a miki."
Rage muryarta tayi sosai kasa k'asa tace
" Jiya ne kuna magana da Ya Abuya a balcony ashe isy taji shine tazo ta fadawa Mami da Mum nima ta fad'a min."
" Shikenan kun ja min, yanzu zai dauka ni na fad'a.". Da sauri yayi hanyar dakin Mami da Abdallan ya shiga, ya tarar da shi a zaune kusa da mamin tana masa magana, wani kallo da yayi masa tun kafin ya karaso ciki ya bashi tabbacin maganar Mami take masa, Ashe neman shi da take tayi tun dazu kenan, ji yayi tana cewa
" Naji dadi sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya sa ayi damu."
Kasa amsawa yayi da Amin saboda kunyar da ta lullube shi, ya dinga jerawa MD aiken harara, da sauri ya karaso ciki yana kama bakin sa
"Wallahi Allah bani na fad'a ba, Mami dan Allah ni na fad'a miki?"
"Toh idan kaine sai me? Dama ai dole a fad'a mana tunda abin farin ciki ne."
"Eh amma.dai ai ba wajena kika ji ba? Waccan me bakin akun ce ta fad'a miki ko?"
"Wa?" Tace tana nuna kamar bata san wa yake nufi ba, dan tasan zasu iya takurawa Ihsan akan haka, shiyasa ba ma zata ce ita bace ta fad'a, tsakanin su chan su karata da boye boyen su
"Kai ka fada min dazu da ka shigo ko ka manta, anan su ma yaran sukaji."
"Mami..." Ya fad'a saman gadon ta yana hade hannayen sa waje guda
"Dan Allah ki taimaka min kice bani na fad'a ba."
"Waye ya fad'a toh?"
Ganin da gaske ba zata fad'a ba, ya saka shi bin bayan Abdallan suka shiga dakin Mum suka sake fitowa a tare, su Ihsan basa falon sun tashi, daga gani Mami ce tace su tashi kafin su fito. Zai kama su ne ko zuwa anjima ne, ya ayyana a ransa.
Wayar sa ya dauko kawai daga shashen nasu ya bar gidan ba tare da ya saurari MD din ba, dan so yake ya fara aikin da Baban ya saka shi yau yaga abinda zai iya yi kafin yammacin ranar.
***Wayar sa ya kunna sanda suka isa zariya, ya dubo number wani friend dinsa da sukayi school tare ya yi dialing, yana dagawa yace masa gashi a zariya yana neman masauki shi da madam ne, baya kuma son sauka a hotel, kasancewar yasan yayi aure ya saka be kawo komai ba, ya fad'a masa in da zasu hadu, ya katse wayar yana sauka daga kan main road din,
"Ina zaka kai ni?"
"Auren mu zan nemi wanda zai gyara mana shi, I can't do without you, nasan kuma kema haka ne, so ki kwantar da hankalin ki, duk abubuwan da nayi miki a baya marasa kyau, zan gyara komai,."
"Bana son ka, bana kaunar me son ka, idan kaga dama ka tafi dani daga nan har karshen duniya ba zan taba auren ka ba."
"Ai ba ke dama xaki aure ni ba, ni ne zan aure ki, za kuma ki gani, my baby love." Ya kai hannun sa ya shafi gefen fuskarta, ta matsa da sauri tana hararar sa, ji take kamar ta samu wani abu ta daba masa, ta daina ganin shi kwata-kwata saboda tsanar da take masa.
In da zasu hadu da abokin nasa suka je, ya zo suka gaisa ya shigo motar, suka tafi, bata ce musu uffan ba, tana jin abokin yana tsokanar ta da amarya, tayi masa banza sai Adam din ne yace ai bata jin dadi ne, abokin yace Allah ya kara sauki.
Wani dan madaidaicin gida ya kaisu, ya fito yana basu umarnin su fito
"Ina fatan dai ba zaku takura anan ba, part biyu ne,madam dita ce a daya, dayan kuma na brother dina ne da zai yi aure, an gama komai."
" Ya isa, just kwana biyu zamuyi, wani aike ne ya kawo ni da na gama zamu wuce."
" Owk, muje toh."
" Muje." Ya bud'e mata kofar, ta fito tana masa mugun kallo amma ko a jikinsa, ya sakata a gaba har ciki, dan idan ma tace zatayi masa gardama bata kuma san in da zai kai ta ba.
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
RM
26
***Matar sa na zaune a falon suka shigo, tun a hanya yayi mata text message saboda haka ta san da zuwan su, ta fara'ar ta, ta tari Asma'un, ta dan saki fuskarta kad'an, suka gaisa sannan tace ta taso , ba musu ta bi bayan ta suka shiga dakinta, ta kawo mata ruwan sha da lemo sai abinci, ruwan kawai tasha ta jingina kanta da drawer din da take zaune a kusa da ita. Sake shigowa matar tayi, tace mata zatayi alwala kasancewar wajen karfe daya lokacin na rana, toilet ta nuna mata sannan ta shinfida mata sallaya kafin ta fito, ta koma wajen su Adam din da suke falo tare da mijinta, ta kwashe kayan abincin da suka ci. Fitowa tayi daga toilet idon ta ya sauka akan karamar wayar dake saman mirror, dauka tayi da dan sauri ta saka number Abba tayi dialing. A dai-dai lokacin Abban tare da Abban su Abeed da Umar da wani abokin Abban suna kokarin tafiya police station sai ga kiran, kallon number da be sani ba Abba yayi, wani tunani ya kawo masa, ya daga da sauri yana kiran sunan ta
"Asma'u?"
"Abba nice."
"Kina ina Asma'u? Fad'a min inda kike yanzu gamu nan."
"Bansan ina ya kawo ni ba, gidan wani abokin sa ne dai, yanzu haka ina dakin matar zanyi sallah."
"Ina adamun?"
"Suna falo."
"Ki kwantar da hankalinki, ki zauna a gidan kinji? Tunda bashi da hankali nasan ta inda zan bullo masa."
"Yawwa, zan kiraki yanzu ki rike wayar."
Kallon su yayi da su ma shi suke kallo jin ya ambaci Asma'u
"Wai wani gidan abokin sa ya kai ta, da sauki ma tunda ba wani wajen daban bane."
"Toh Alhamdulillah, yanzu menene abun yi."
"Ba zamu kai maganar wajen yan sanda ba musamman tunda tana hannu na gari, idan mukayi haka kamar mun daba ma cikin mu wuka ne, bamu san yadda mutane zasu juya labarin ba, sai kaga an juya masa maana kuma dai kaga mace ce gidan wani zata nan gaba. "
" Gaskiya ne." Abokin Abban yace, sai duk suka yi shiru kowa yana saka yadda za'a bullowa al'amarin.
Ajiye wayar tayi ta tada sallah, lokacin matar ta sake shigowa taga tana sallah sai ta juya, ta same su a tsaye zasu fita, dama Adam din ne yace tayi mata magana,
" Sallah take." Tace masa, dan jim yayi kamar yana tunani sai kuma yace
"Dan Allah ki kula da ita, kar tace miki zata wani wajen babu in da ta sani."
" In sha Allah." Fita sukayi ta rufe kofar falon ta koma ciki, ta zauna tana jiran ta idar da sallar, su kuwa dama fitar da sukayi wajen wani malami zai raka shi, zaman da sukayi suka ci abinci ne ya bashi labarin dalilin zuwan su nan din, amma ya boye masa da ainihin abinda ya raba su din, kuma ya nuna masa suna matukar kaunar junan su dashi da ita, shiyasa ma ya yarda zai taimaka masa suje wajen malamin ko Allah zai sa a dace a maida auren nasu kawai, idan yaso sai su koma gidan da auren su.
Murmushi tayi mata ganin ta idar, ta maida mata itama,
"Mijinki ya aiko na kiraki, amma sun fita ba dadewa zasuyi ba."
"Ok." Tace a gajarce,
"Sunana Aisha, kefa."
"Asma'u."
"Lallai, kamar ma baku dade da auren ba ko? Dan kamar nasan lokacin da dear yaje bikin naku."
"Eh... Bamu dadi ba."
"Allah sarki, Allah ya sanya alkhair."
Maimakon ta amsa sai tace
"Garin ku me kyau, na dade ina jin labarin garin wajen wata kawata mijinta dan nan ne, sai yau Allah yayi zanzo."
" Kice baki taba zuwa zariya ba, ah lallai kinyi missing, ba laifi kam garin namu."
" Gaskiya, ita wannan unguwar taku fa, ya sunan ta."
" Anguwar zariya."
" Ok su kamar a limancin kona suke."
"Owk na san unguwar sosai, akwai wasu yan uwan mu a can ina zuwa."
" Lallai."
Tace tana jinjina kai, ta lura gwanar hira ce Ayshan, ta sake da ita sosai kamar sun saba, daurewa take tana tayata hirar tun da ta ji in da take, ganin lokaci na tafiya yace tace
" Kinga na bar wayata a mota, dan Allah bani aron taki."
"Owk ba damuwa, ina na ajiye wayar ne?"
" Itace wannan?" Ta dago mata wadda tayi kiran daxu
" Yawwa eh, yi amfani da wannan din, bari na dubo dayar ko a kitchen na barta."
" Owk."
Text message ta turawa Abba
" Muna zariya, cikin birnin zariyan."
Reply yayi mata da
" Gamu nan. "
Goge komai tayi ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya, rashin wankan da batayi ba yafi komai damun ta, gashi bata da kayan da zata chanja da har wanka sai tayi, hijab din dake jikin ta ne kawai ya rufa mata asiri dan dogo ne har ya kusan rufe mata kafarta. Tana zaune suna hira sama-sama har su Adam din suka dawo, basu samu malamin ba sai anjima zasu koma, dan haka sai suka zauna a falo suka cigaba da hirar su, bata fito ba tun da suka zo, gashi yana son ganin ta, ji yake kamar ya shiga dakin yaga halin da take ciki amma dole yayi taka tsantsan dan ba zai yi wasa da wannan damar ba. Be kawo zata karbi waya ta kira ba, dan shi a tunanin sa itama tana son shi kamar yadda yake son ta, shiyasa ma yaga batayi wani abu da zai nuna damuwar ta ba, tun wanda tayi bayan sun dauko hanya, hakan ya kara bashi tabbacin komai zai zo musu da sauki. La'asar sukayi suka sake fita dan shi a son samun sa ma ace yau komai ya tabbata, daga nan ya koma gida su tattara kayan su, su bar garin gaba daya tunda be san da maganar Fido ba. A daidai lokacin su Abba sun riga sun kamo hanya har sun yi nisa ma, dan ba zasu bari sai gobe ba. Umar ya taba rashin mutuncin da zai wa Adam din idan suka isa, dan ya gama gane mahaukaci ne na gaske tunda har zai iya take abinda yazo a addinance saboda shegen son kansa.
***Kasa zama mama tayi a gidan ta tafi gidan Abban, ta tarar da Umman da yaranta, kadaran kadahan kowa yayi mata har Umman da take bata girma sosai amma sai taga akasin haka, zuwan nata ya taimaka mata wajen samun saukin tashin hankalin da take ciki tunda ta samu labarin an san in da Adam din yake, ta dauka da gaske Abban zai kai karar Adam din, bayan tahowar ta Faiza ta rako masu motar kayan furnitures da kayan kitchen, sun samu labarin an daura auren bayan Fido din ta koma, aikuwa suka hau shiri gadan gadam sauran kawayen Fido din da ta yarda dasu suka bi Faizan su zasuyi jere, ita kuma ta nufi salon daga nan zata wuce kunshi, ita a dole amarya, fadar irin farin cikin da take ciki ma bata baki ne, shi gogan bata san ko labarin auren be sani ba, kamar ma ya manta da maganar wata Fido kwata kwata. Babu izinin kowa suka shiga gidan maigadi ya bud'e musu cike da mamakin yanayin su, kasancewar gidan yana nan a sabon shi babu abinda yayi, sukayi jeren su da uban kaya, har yamma suka yi ganin ba zai gamu a ranar ba yasa suka bari su dawo gobe su karasa, Fido bata so ma, dan ma tayi kiran Hajiya da shi kansa Adam din duk bata shiga, hakura tayi goben amma idan har be kira ko yazo ba zata kai kanta ne, su Faiza sun rakata idan yaso ya dawo ya sameta a chan tunda dai aure ya riga ya dauro hatta sadakin ta yana cikin acc din ta.
Sai wajen magriba sannan su Abba suka isa zariyan, ya kira number da Asma'un ta kirashi, ta dan jima tana ringing kafin a daga, wayar na hannun matar abokin Adam din ita kauma Asma'u tana sallah, jin namiji ne ya kira wayar ya sakata katse kiran cike da mamakin waye, ajiye wayar tayi ta karasa abinda take ta fito, ta samu ta idar, wayar ta mika mata ganin kiran na sake shigowa
"Ko number da kika kira ce?"
Da sauri ta karba, ta daga tana mikewa tsaye
"Eh abba, bari na baka tayi maka kwatance."
Sai ta mika mata
"Dan Allah kwantancen gidan nan zaki ma abbanmu."
Karba tayi ta gajshe shi cikin girmamawa sannan tayi masa kwantancen, ta bawa Asma'un yace gasu nan, kasa zama tayi dan bata so Adam ya dawo, Aysha na lura da ita, ta kasa hakuri tace
"Zuwa zai yi?"
"Eh, zuwa zai mu tafi."
"Owk." Tace ba dan ta gamsu ba, ta shiga sake sake a ranta, ta tabbata akwai wani abu dan yanayin Asma'un ya sa ta gane labarin ba yadda Adam din ya fad'a bane, basu dade da wayar ba suka iso kuwa, Umar ne ya kira a wannan karon,yace mata sun karaso
Toh." Tace ta ajiye wayar, sannan tace wa Ayshan
" Suna waje, zasu jira Adam din su dawo, dama so nake su zo sai na fad'a miki gaskiya...Mun rabu da Adam bama tare a yanzu, karya yayi wa mijinki, ba da izini na ko na iyaye na ya taho dani nan ba, bayan kuma babu damar da auren mu zai koma saboda saki uku yayi min,. "
" Wayyo, amma be kyauta ba, wallahi ni Ina ganin ki naji kin kwanta min a rai na, dan Allah ki bani number ki ma dinga gaisawa. "
"Toh. " Ta saka mata number ta, tace ta kira idan ta koma zata gani sai tayi saving, ta kira kuwa a take, sannan ta shiga daki ta hado mata abubuwa a leda ta kawo mata. Shiru su Adam din basu dawo ba, Umar ya sake kiranta yace ta fito kawai, tayi wa Ayshan sallama ta rakota har waje, ta gaida su Abban, motar Asma'u ta shiga, ta sake mata sallama tana tsaye suka bar layin, ta girgiza kanta tana juyawa dan ta koma ciki, ta hango motar su tana shigowa layin amma ba ta in da su Asma'un suka bi ba, ciki ta koma suka shigo, ta fito tana musu sannu da zuwa, wara ido Adam yake ko zai ganta amma ko motsin ta be ji ba, kasa hakuri yayi yace
"Please Madam kice ta fito na ganta, tunda muka zo ake punishing dina."
"Owk." Tace sannan tace
"Dear dan zo kaji." Bin ta yayi ciki, ta fad'a masa komai da komai da Asma'u ta fad'a mata, dama yayi tunanin haka ganin a yadda suka zo garin da kuma yadda Adam din ya damu sosai, gwara da akayi haka ma, komawa yayi wajen Adam din ya tarar dashi yana kaiwa da komowa irin ta wanda yake cikin damuwa sosai,
"Ba zata zo ba?" Yace da sauri
"A ah, she's gone. "
" How? Ta yaya? " Ya fad'a a kidime
" Kayi hakuri kawai, kasan dai babu aure bayan saki uku, ina ganin be kamata kayi kokarin halatta abinda yake haramun ba. "
" Ba wannan nake son ji ba, ka fada min tana ina, ina taje? "
Yayi maganar cikin daga murya da karaji
" Tare da kai muka fita, bayan mun fita aka zo aka tafi da ita, she told my wife everything. "
" Damn it! " Ya daki bangon falon
" Da na sani ban yi trusting naku ba, amma zan dawo..." Ya juya