RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   24 / 30

69K to 72K   out of 87.6K words

ya shiga ya tada motar suka bar layin, ransa ya kai kololuwa a baci amma calmness dinsa na tare dashi, satar kallon sa take, driving kawai yake da hannu dayan dayan kuma yana rik'e da nata be ce uffan ba, be kuma sake kallon ta ba bare ta saka ran zai mata magana.



RM
   34

***Driving kawai yake da hannu daya, dayan kuma yana rik'e da nata be ce uffan, be kuma sake kallon ta ba bare ta saka ran zai mata magana. Yayi kokari sosai wajen maintaining coolness dinsa dan yadda yake ji kamar ya koma ya saka a kama masa Adam a kulle masa shi har sai ya manta da Asma'un da duk abinda ya shafe shi, kishin sa yake ji sosai a yau fiye da kullum,

"Ka... Kayi hakuri.". Ta samu kanta da furtawa cikin rarrabewar kalmomi, kansa a gaba yana kallon titi ya dan matsa hannun ta kad'an amma bai ce komai,shiru ne ya sake biyo bayan motar, hanyar office ya dauka, akwai hadari sosai a area ba kamar baya da suka baro ba, har iska ta soma kadawa kad'an kad'an, rage tafiyar yayi ya shiga layin, har lokacin idanun sa na kan hanya hakan ya kara tabbatar mata ransa babu dadi. Kanta ta daga tana kallon building din dogon gaske, a chan sama ta hangi suna K'AREFA, bata gama karantawa ba aka wangale katoton gate din, harabar wajen cike take da motoci sababbi masu kyau, sai hadahadar mutane daga chan gefe, ciki sosai ya shiga da motar sannan yayi parking ya kashe ta, sai a lokacin ya juyo yana kallon ta, yana kallon mayafin da yake jikinta, babba ne amma kuma ba shi da kauri sosai, har yana iya hango rigar jikinta amma ba tar ba, sai ka saka ido sosai, kusa da ita ya matso sosai ya zura kansa bayan motar, ta sauke numfashi tana jin closeness din nasu na haifar mata da yanayi, rigar sa ya dauko jacket, ya kama mayafin nata yana kallonta cikin ido, dan motsawa tayi kadan ya karasa nannade mayafin ya dora mata jacket din akai, ya balle mata sannan ya maida mata mayafin ta, baya ya danyi yana so ya tabbatar da baa gani yanzu,sai ya fito yana zagayo side dinta ya bud'e mata. Fitowa tayi tana sadda kanta k'asa mamakin sa na cikata, tafiya ya soma yi bayan ya saka hannun sa a nata yabi hanyar baya mara cinkoso da hayaniya, ya shiga ta wata kofa inda suka tarar da mutane uku a zaune kowannen su na duba takardu a gaban su, daya mace ce sai sauran maza biyu, da sauri suka tashi tsaye suna masa sannu da zuwa dan rabon sa da bangaren kusan sati kenan MD ne yake kula da duk baangarorin, hannu ya daga musu kawai ya wuce da dan sassarfa ya danna bud'e kofar lift din ta bud'e ta shiga sannan ya mara mata baya, kus-kus suka hau yi bayan shigewar su, cikin yanayi na ban mamaki dan basu san komai game da maganar auren nasa ba, ba kuma su sanshi a mutumin banza ba. Duk iya hasashen su ba su iya hasaso komai ba, sai suka hakura duk suka koma bakin aikin su, suna masu kyautata masa zato.
  

Binsa kawai take kamar rakumi da akala, har suka dangana da babban office din nasa, ya bud'e suka shiga ciki sannan ya murza key din yana sakin hannun ta, ya wuce gaba da sauri ya shiga toilet din dake cikin office din, tsaye tayi a inda ya barta tana satar kallon office din da yayi masifar tsaruwa, ga wani sanyin dadi da kamshi irin wanda take ji a jikinsa a duk sanda yazo wajen ta, tana nan a tsayen tana more kallon komai a tsanake ya fito hannun rigar sa a nannade, ya kalle ta yana takowa zuwa wajen da take tsaye

"Zo ki zauna."

Ya nuna mata couch din dake gefe da hannun sa, wuce shi tayi ta zauna a dosane tana mamakin sauyawarsa kamar bashi ba, bata san wannan side din nasa ba, sai yau da ya nuna mata shi din miskili ne, na gaske. Iska ce ta taso da karfi, ya rufe dukka windows din, ya rage hasken office din ya zama dim, duk abinda yake tana ta satar kallon sa, aka soma ruwan da karfin gaske, kujerar sa ya hau, ya bud'e system dinsa yana so ya rage abinda yake ji a zuciyar sa, baya so tunanin da zuciyar sa take bashi yayi tasiri akan sa, duk in da ya shiga sai ya fita ba tare da ya iya aikata komai ba, haka ya dinga shiga nan ya fita nan har ya gaji ya ture system din yana jan dan siririn tsaki, baya jin zai iya jure tsawon kwanakin da Baban yace zata tare gaskiya, dan hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in dai har Adam na kaiwawo a tsakanin gidan nasu. Wajen da take ya kalla sai yaji ta bashi tausayi musamman sharentan da yake, yasan ba ita tayi masa laifin ba amma ya rasa dalilin da ya saka shi jin zafin sosai, lura yayi da tana jin sanyi kamar, dan ta dage kafarta sama ta cure waje daya, remote din AC ya dauka ya kashe ta gaba daya, ya ajiye ya isa wajen da take, ya durkusa a gabanta yana kamo hannunta cikin nasa

"Kayi hakuri." Ta sake ce masa a karo na biyu, hakan ya kara masa tausayin ta sosai, ya daga mata kai kafin ya furta

"Baki min laifi ba ai."

"Naga kamar kana fushi dani."

"Um um." Ya sake girgiza mata kai

"Haka nake Husna, ba komai nake magantuwa akai ba."

Jinjina kai tayi, sai ya dauke zancen ta hanyar cewa

"Ya kika ga office din nawa?"

"Yayi kyau."

"Really, taso kiga."

Ya mike tsaye ya kama hannun ta, ya kaita har wajen kujerar da ya taso yace ta zauna, ta zauna ya zagayo ta bayan ta yayi mata rumfa, ya dora kansa a saman kafadarta numfashin su na gogayya da juna, hannun ta ya dora a saman mouse din sannan ya dora nasa akai, ya shiga wajen motocin da yayi order ya dinga scrolling sama. A zahiri idon ta na kan computer din sai dai a badini babu abinda yake ganewa face bugun zuciyar ta da ya karu sosai, shi kansa ya shiga wani yanayi amma ya kanne yana cigaba da scrolling har ya wuce abinda yake so ya nuna mata, sai da ya sake dawowa baya sau uku yana wucewa kafin ya tsaya a inda yake so ya tsaya da k'yar.

"Ki tayani zabe, wacce zan dauka."

Muryar sa very deep cike da kasala yayi maganar a kanta taji shi har cikin kwakwalwarta, kamar bashi ne yayi maganar ba. Motoci ne guda uku akan screen din, dukkan nin su sunyi kyau ainun, har ta rasa wadda zata zaba a ciki, ta dinga kallon sa tuna sakewa, da k'yar ta tsaya a kan wacce MD yace yana so

"Wannan tayi kyau sosai."

"Wannan fa?" Ya nuno wadda ya siya da sunanta,

"Wow, wannan tafi kyau, amma kalar mata ce."

"Tafi wannan kyau?" Ya sake nuno dayar

"Tafi, ita kawai zata fi kyau a mace."

"Kina so?" Yace yana sake zuro kansa sosai jikin wuyan ta, ya rufe system din da hannun sa.

"Na'am?" Tace cikin inda-inda

"Kina so?" Ya sake maimaitawa

Girgiza masa kai tayi,

"Tafi karfi na."

Hannu yasa ya juyo da kujerar ta dawo tana kallon sa, ya sake durkusawa agabanta ya zube hannayensa akan cinyar ta

"Taki ce, bata fi karfin ki ba, duk wani abu da Abdallah ya mallaka naki ne."

Kamar almara haka taji maganar, ta rasa wane kalar farin ciki zatayi, murmushi kawai ta dinga yi me tsada, wanda ya sake dilmeyar dashi a cikin son ta, godiya tayi masa ba dan tana tunanin godiyar ta yi ba, sai dai dan kawai tana tunanin abinda zata iya furtawa kenan, tana jin kunyar sosai, ido ya zura mata yana kallonta, ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta tana fitar da siririn sautin dariya, hannu ya rike ya bud'e fuskar yana marairace mata kamar zai yi kuka

" Na fa biya, a barni na more kallon matata."

Dariya suka saka a tare dan yadda yayi maganar yayi masifar bata dariya, be sake tunawa da wani Adamu ba, zaman su waje daya ya mantar dashi komai har yake jin ba dan kar ace yayi rashin kunya ba, da daga nan sai gida, amma ba zai iya ba, zai dai roki Abba a rage kwanakin a takaita, dan a matse yake kamar yadda MD yake tsokanar sa, be kuma san a matsen yake ba sai da ya gansu a Inuwa daya.
A hankali a hankali ruwan ya dinga raguwa, ya zama sai da da yayyafi kawai, yunwa yaji yana ji sosai, gashi yasan lokacin lunch ya wuce, wayar sa ya ciro zai kira MD ya tarar da missed calls dinsa da na Baba Alhaji, Baban ya fara kira sukayi magana sannan ya kira MD yace ya saka masa order daga 10-10 two pack yana office, zai tsaya tambayar shi yaushe ya dawo ya kashe wayar dan yasan shi da bin kwakwaf.
Kan couch din ta koma ta zauna ya gama wayar yazo ya zauna shima, daf da ita ya cigaba da danna wayar yana so yayi abinda Baba Alhaji ya sakashi, baya wasa da duk abinda da ya shafi Baban, very serious taga ya zama yana ta aika sakonni duk da bata ga me yake rubutawa ba, bata son bin kwakwafi sai kawai tayi baya da kanta dan ta bashi damar gama aikin sa, ji tayi ya jawo ta jikinsa, ya mana sashen ta a jikin nasa shashen ya sakalo hannun sa ta bayan ta,ta shiga jikin sa sosai ta barin sa, cigaba da abinda yake yayi kansa akan wayar tayi luf a jikin sa har sai da ya gama, sannan ya ajiye wayar yana yin baya dasu. Knocking akayi a kofar ya yi jim yana tunanin waye,dan ba kasafai ya ke zama a office din nan ba kuma ya tabbata babu wanda zai biyo shi nan din sai MD, tunowa da yayi da order da yace yayi masa yasa shi mikewa ya nufi kofar ya bud'e kad'an. MD ne a tsaye sai messenger rik'e da ledoji biyu manya masu dauke da tambarin 10-10 restaurant, karba MD yayi ya sallame shi yace

"Matsa na wuce."

Babbake kofar yayi yana hararar sa, ya mika masa hannu alamun ya bashi ledojin

"Bamu taba haka ba, sai na kai maka har ciki sannan nake tafiya idan ba tare zamu yi lunch din ba."

"Time da nake sa'anka ba, yanzu bana cin abinci da tuzuru, bani kayana ana jirana."

" Amarya ce a ciki?" Ya bud'e baki cike da mamakin Abdallan

Tura shi yayi ya rufo kofar ta waje yana mika masa hannu

"Bani nace."


Dariya ya kwashe da ita, ya mika masa yana karkade hannun sa

"Dole ne ma nayi aure wallahi."

"Kanka ake ji."

Ya juya ya shige cike ya sake rufe kofar, sosa kai MD ya tsaya yana yi cikin jin dadi, ya kada kansa yayi gaba yana murmushi a ransa yana ayyana yanayin Abdallah da yadda zai iya tafi da mace, bashi da matsala ko kad'an kuma a duniya yana respecting din mace, yasan zata sha gata a wajen sa, bashi da haufi akan dan uwan nasa dan zai iya bugar kirji yace Asma'u tayi dace da sa'ar miji na gari. Yayi nisa a tunani cike da nishadi yake sauka da steps din masu yawa, be tsaya hawa lifter ba dan yana bukatar ya more tafiyar yana hasaso Abdallah da mace, macen ma wadda ya yarda yake so.

A saman table ya ajiye ledojin ya dauka dan madaidaicin carpet ya ware shi a wajen, ya sakko da kayan ya ajiye sannan yace ta taso, girgiza kai tayi tace ta koshi dan bata san ta yadda zata fara cin abinci tare dashi ba, bayan haka ma ita din ba gwanar cin abinci bace sosai, kuma ba wai tana jin yunwa bane dan sai data ci abinci tare da su Rauda da Hidaya.
Har ya zauna ya taso yana hararar ta a wasance,

"Zaki taso ko sai na dauko ki?

" Allah bana jin yunwa."

"Ban yarda ba, baki san idan aka yi ruwa ciki rarakewa yake ba?"

" Ni nawa bayayi. "

" Comman, taso." Ya mika mata hannun sa, ba dan taso ba, ta mika masa ya taimaka mata ta mike, tabi shi zuwa wajen ta zauna tana tankwashe kafarta, abincin ya bud'e Chicken Mandi rice ce sai hadin salad a gefe sai shredded Beef hade da wata soup me shegen kamshi (abincin da nake kwadayin ci kenan! 😂 Lol) a nutse yayi Bismillahi ya fara ci a hankali kamar wanda baya son ci, juya spoon din ta dinga yi yana kallon ta, ya dan ci sama-sama ya ture yana furta Alhamdulillah, tsattsareta yayi da ido alamun taci, ta marairace masa kamar zatayi kuka

"Allah na koshi."

"Shikenan tam, bari na maida ki gida ko? Ko zaki bini mu tafi namu gidan?"

Murmushi tayi, ta tattare kayan ta hade waje daya, dan dayan ko bud'e shi ba'a yi ba, toilet ya sake shiga ya kuskure bakin sa da mouthwash yayi alwala ya fito, , yace ta tashi tayi alwala dan yana jin ana kiran magriba idan suka fita ba zata samu ba, alwala taje tayi dan dama a matse take da fitsari, ta same shi akan carpet din yana gyara botir din hannun rigar sa, a bayan sa ta tsaya ta gefen sa, ya jasu sallar. Bayan sun idar ne yace su tafi, ta tashi shi kuma ya dauki ledar da ba'a bud'e ba, wanda yaci kuma ya barwa cleaner idan yazo gyara office din bayan sun fita, yanzu ma kamar dazun hannun ta na cikin nasa suka fito, duhu ya samo yi sosai babu kowa a wajen da suka ga mutanen dazu alamun sun tashi aiki, ta kofar bayan ya sake bi da ita, suka tarar an gama wanke masa mota tayi tas, yasan aikin MD ne, murmushi yayi ya bud'e mata ta shiga ta zauna sannan ya koma ya shiga ya tada motar, maimakon taga sun yi hanyar gida sai taga sun baude, bata ce komai ba har ya tsaya yace mata yana zuwa, be dade sosai ba ya dawo ya saka ledojin da ya siyo a baya sannan ya ja suka tafi.
Motar Abba na kofar gida sanda suka iso, amma babu kowa a layin watakila saboda ruwan da akayi ne, juyowa yayi gaba daya bayan ya tsaya ya matso sosai daf da ita, ya dora hacin sa akan nata yana gogawa kad'an kad'an, ba'a son ransa ya dawo da ita ba, ga wani irin feeling dake taso masa musamman yanayin ruwan da akayi, ji tayi ya hade bakin su waje daya, ta dauke numfashi cikin wani irin yanayi ya shiga kissing dinta passionately, yadda yake koman sa a nutse da class haka ma a yanzu, tana jin yanayin nutsuwa a tattare da abunda yake yi, kusan minti daya sannan ya cikata yana yin baya, jikinsa na kare macewa sosai, he can't wait this long gaskiya, dole ya nemi ragin kwanakin, dan yasan zai cutu, musamman da ya riga ya san ita din halaliyar sa ce, daga shi har ita babu wanda ya iya magana, ya daga mata lock din motar ta bud'e murfin ta zura kafarta waje sannan tace masa

"Sai da safe."

Maimakon ya amsa sai ya tsare ta da ido, tayi murmushi tana rufe masa kofar ta zagayo ta bangaren sa, balle kofar yayi ya fito, ya bud'e bayan ya ciro ledojin ya mika mata biyu ya rike sauran, suka shiga takawa zuwa cikin gidan nasu, a ciki suka hadu da Abbati, ya karbi kayan ya shiga dasu, ya dan yi jim kad'an sannan yayi mata sallama ya juya yana tafiya a hankali. Sai da taga ya tafi sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta kutsa kanta cikin gidan nasu tana ayyana kalar kunyar da zata sha musamman idan ta tarar su Rauda basu tafi ba.



*RM*

35

***Da sand'a ta shiga gidan tana addu'ar Allah yasa har ta shige daki umma bata wajen, muryar Rauda ta soma ji tana tambayar Abbati abubuwan da suke cikin ledar, lebewa tayi sai taji Umma tana cewa su daina bud'e mata su bari tazo, kamar ta koma haka taji, ta daure dai ta shiga da sallama ciki ciki, bin ta duk sukayi da kallo, tayi saurin zama daga gefen Rauda ta gaida umman kamar wata bakuwa, dariya ce take cin Rauda amma ta kanne.

"Babu matsala ko!? Abin da Adam yayi masa Ina fatan hakan be zama matsala ba." Umma tace tana mikewa

"Babu komai, ya dai ji babu dadi amma kuma be wani nuna ba."

"Toh masha ALLAH, Adam be kyauta ba, amma dai Abban ku yayi ma tufkar hanci, yace kar ya sake ganin kafarsa har sai kin tafi, idan bakya nan kuwa babu me hanashi zuwa amma yanzu kam kar ya sake ganin sa, ya ma rage kwanakin tarewar yace sati daya sai kawai a siya kayan ko readymade ne, tunda wannan na Hajiya Maman sai da su za'a yi sai ayi miki wasu kawai. "

" Ok. " Kawai tace tana hango yadda Abdallah zai ji idan tace masa an rage kwanakin, tunanin shi ta tafi gaba daya har bata ji sanda Rauda take cewa ta matsu a bude kayan ba, sai data dan taba ta sannan ta wayance tana cewa

" Me kika ce? Bari na shiga ciki. "

" Wai kayan fa zaki bud'e duk na matsu wallahi. "

" Rauda kwadayi." Umma tace tana dariya

" Allah Umma na matsu, nasan kayan kwalam ne, Allah ya taimake ni da na tafi shikenan ba ni za'a kwashi gara. "

" Ki bud'e mana, sai ni dole? Kin jiki. Ni bari kiga ma. " Ta tashi ta shige ciki tana jiyo Rauda da Abbati suna bud'e ledojin suka saki ihun murna.


Jacket dinsa da har lokacin take rik'e da ita ta saki akan gadon ta cire kayan jikinta ta saka wasu riga armless da dogon skirt sai ta dora rigar tasa akai saboda garin da dan sanyi dan ma taga alamar ruwan da akayi a chan yafi yawa sosai.
Rik'e da ledojin Rauda ta biyota

24 / 30