Author : RANO Category : African Stories & Novels
yamma tayi ba, ya tashi gaba daya, ya rufe office din ya fito, a kofa suka hadu da Fazallah, yace
"Yallabai ba dai tafiya zakayi ba?"
"Eh akwai wani abu ne?"
"Gaskiya, kayan da Alhaji ya aiko dasu sun iso, har an yi cleaning nasu da komai gasu chan ma a k'asa, dole sai ka fara dubawa kafin ayi distributing dinsu."
"Ba zasu iya hakuri gobe ba?"
"Eh toh..."
"Ka basu hakuri kace su koma gida su huta, gobe duk sai su dawo kowa sai ya dauki wanda zai kai, yanzu kam akwai important abu da zanyi wallahi."
"Ba matsala, zan sanar dasu."
"Yawwa." Yayi gaba yana take masa baya, wayar sa ya zaro ya kira MD yace ya tashi ya zo gida yana so ya raka shi wajen Baba Alhaji zai masa wata magana, toh yace ya kashe yana sake daga kafarsa zuwa wajen mota, ya samu driver companyn nasu ya bashi car keys din yace ya kaishi gida dan ji yake kamar ba zai iya taka motar ba, zama yayi yana karo karfin AC motar, ya runtse idon sa yana hasaso abinda zai faru, ya family dinsa zasu karbi maganar, har aka zo gidan be san an zo ba yayi zurfin a tunanin sa, sai da yaji motar ta tsaya sannan ya dago idanun sa da suka dan daga saboda gajiya ya zura wa harabar gidan kamar ranar ya fara zuwa, a nutse ya turo murfin motar ya fito yana kallon motar MD dake ajiye a gefe alamun ya dawo kenan, maimakon ya wuce part dinsu, kai tsaye na Baba Alhajin ya nufa bayan ya bawa maigadi jakar sa da tarkacen sa ya kai masa chan.
A zaune ya hange shi, daga shi sai yar shara da dogon wando, kansa da ya soma tara farin gashi ya zubawa ido yana ayyana yadda rayuwar take tafiya ba tare da mutane sun farga ba.
"Bawan Allah!" Ya fad'a sanda Abdallan ya shigo, hakan ya kara masa karsashi ya karaso ciki da dan sassarfa, da kallo yake bin sa har ya zauna a kasan makeken carpet din dake malale a tsakiyar falon, ya tankwashe kafarsa dake sanye da safa wadda ta tsaya masa daidai idon sahu, ya dukar da kansa cike da girmamawa irin ta da da mahaifi yace
"Barka da warhaka Baba."
"Barka dai Abuya, an taso?"
"Eh baba, ya hanya? An dawo lafiya?"
"Alhamdulillah wallahi, ya ayyukan? Ina fatan babu matsala."
"Babu." Yace a takaice
"Toh Madallah, kaci abinci kuwa? Ko duk gajiyar ce na ganka haka haka."
"Naci, akwai gajiyar ma ai."
"Toh Allah yasa mu dace."
Dan jim yayi bayan ya amsa da amin, ya rasa ta ina zai fara fadawa Baban maganar, Baban na ankare dashi, ya kuma san me zai fad'a masa dan tun daga airport Mudan ya fesa masa,
"Abuya?"
"Na'am." Yayi firgigit ya amsa
"Yarinyar yar ina ce?"
"Yan Sumaila ne Baba."
"Masha Allah, ka aminta da ita da tarbiyyar ta? Saboda babban kuskuren da mace ko namiji zasuyi a rayuwar su shine zabin abokan zama ba na kwarai ba."
"Nayi bincike daidai gwargado, amma zaku iya sake yi."
"A ah, babu bukatar hakan dan kai da kanka kana da damar da zaka nemawa kanka aure, kuma na gamsu da kai da tarbiyyar ka, nasan ba zaka yi wa kanka zaben tumun dare ba, yaushe kake so aje?"
"Ko yaushe ma, yau dai mahaifin ta yake son gani na,bansan akan menene ba dai."
"Kaje aji menene toh, ALLAH ya tabbatar da alkhairi."
"Amin." Yace a kasan makoshin sa,
"Amma baba, ta taba aure amma bata fi watanni ba, auren ya mutu."
"Ka san me ya raba su da mijin ta?"
"Eh..." Ya kwashe komai ya fadawa Baban, abinda ya sani dan tun a ranar da ya ganta ya yi bincike yasan komai akanta
"Allah sarki, wannan shi ake kira da shikan wawa, irin wanda wani wawa yayi wa mahaifiyar ka har na samu damar aurenta, har kuma yanzu da nake tare da ita ban taba samun matsala da ita ba, mutuniyar kirki. "
Sam Abdallan be taba sanin wannan labarin ba, ya dinga kallon Baban har ya kai karshe a maganar sa sannan yace
" Kaga shikenan tarihi zai sake maimaita kansa. "
Murmushi yayi me sauti, a hankali a hankali ya dinga jin nutsuwa na shigar sa, yana jin kamar ya same ta ya gama ne, dama duk zulumin sa akan yadda iyayen sa zasu karbi maganar ne, amma yanzu da ya samu kwarin guiwa sai yake jin zai iya tunkarar ko ma menene don ganin ya mallake ta.
Cike da karsashi ya sake wanka bayan ya chachakali abinci, ya shirya cikin shigar manyan kaya, shi da MD suka fita a motar MD din, Abdallan na zaune a gefen me zaman banza kamar ko da yaushe in zasu fita MD ne yake jan motar, unguwar su Asma'un suka nufa, gaban Abdallan na cigaba da faduwa dan ya kasa nutsuwa da kiran Abban gani yake kamar zai hanashi Asma'un ne, ko yace be gamsu dashi ba, a waje suka tsaya ya kira wayarta a kashe, sai suka samu yaro suka aika shi ciki, tare suka dawo da Abbati da yaron yace su shigo ciki, yana ta satar kallon su, yan gayu sosai, ga hutu da jindadi ya nuna a jikinsa, satar kallon kafar su yayi ya ganta kamar basa taka k'asa, luf luf, ciki ya wuce bayan ya kaisu har falon ya je ya sanar wa da Abba sun shigo. A zaune ya same su, yana shigowa suka sakko k'asa suka gaishe shi, ya masa musu a sake yana karantar su,
"Abdallah." Ya kira suna ba dan ya san wanne a cikin su ba, dagowa yayi ya amsa kirjinsa na bugawa
"Kai ne kake neman auren Asma'u ko?"
"Eh Abba."
"Toh masha ALLAH, so nake ka turo magabatanka, suzo muyi magana, dan ba zan boye maka ba, akwai dan uwan ta da muka hada su aure, toh dai Allah cikin ikon sa auren be jima ba, suka rabu bayan yayi mata saki har uku, daga baya ya gane kuskuren sa shine ya dawo, bana son sintirin da yake min anan dan nasan hakan zai hana walwalar Asma'un, shi yasa nake so idan da gaske kake ka fito, idan yaso ko auren ne a daura idan har yaji tayi aure zai hakura dole. "
" Haka ne. " MD yace yana jinjina kaie
" In Sha Allah magabatanmu zasu zo gobe, in sha Allah. " MD yace dan yasan Abdallan ba zai magana ba
" Allah ya kawo su, dama shine dalilin kiran. "
" Mun gode Allah ya kara girma. "
" Amin ya Allah. "
Sai ya mike
" Bari tazo, Ku gaida gida."
"Mun gode."
Ta kofar ciki ya koma, ya tarar da Abbati yana bawa umma labarin su, Asma'u na zaune bata sa baki ba, amma deep down tana jin wani irin feelings dangane dashi, shiyasa ko da Abba ya shawarce ta da maganar tace mata ta amince, musamman ganin yadda hankalin umma ya kwanta dashi duk da bata taba ganin sa ba. Abba ne yace taje suna dakin baki, ta tashi a kunyace ta fita tana daukar takalmin Abbati ta saka, bata ma san shi ta saka ba sam, sai da taje kofar, ta cire sannan ta tuna, shiga tayi tana dan rabewa, ta same su dukka a tsaye idon ta ya sauka a cikin nasa, yayi mata murmushi yana jin sabuwar kaunar ta na ratsa shi, a kunyace ta gaida su, MD ya amsa sannan ya fita ya bar su, gabanta yazo ya tsaya, ta sauke kanta tana jin duk ya cika wajen, kunya da kwarjinin sa suka hanata sakat, muryar sa ta tsinta a saman kanta, taji tamkar kafafun ta zasu kayar da ita a wajen saboda yanayin da ta shiga.
"Abba ya amince na turo, kin yarda kin amince zaki bani dama?"
Da kai ta amsa masa dan ba zata iya magana ba, yana tsaye daf da ita kamar zai maida ta ciki, sai yar tazara da bata wuce kamu biyu dake tsakanin su ba, mayen kamshin shin sa da yafi komai kashe mata jiki ya cigaba da huda ta,
"I promise to take very good care of you, in sha Allah together we will meet tomorrow."
"Zan wuce, zan je na samu Baba da maganar, bana so aje lokaci, dan bansan abinda zai faru gaba ba."
"Sai ka dawo." Ta samu kanta da furtawa, hayaniyar da suka ji a compound din gidan ta katse su, muryar MD yaji, ita kuma ta Adam, gabanta ya fadi, tabi bayansa da sauri lokacin har Adam din ya shaki kwalar MD, kamar ma baya cikin hayyacin sa, daga gani yasha wani abu ne dan yanayin sa ya nuna hakan.
*RM*
29-30
****
Umar tare da Abba suka fito da sauri, lokacin har Abdallah ya karasa wajen, fuzgo Adam Umar yayi, ya hankada shi baya da karfi a zafafe,
"Subhallah." Abba yace wata mahaukaciyar kunya na rufe shi, MD ransa yayi mugun baci dan baa taba masa irin wannan wulakancin ba, waya yake be yi aune ba kawai yaji ya shaki shi gami da hada shi da bango, rik'e hannun sa Abdallah yayi yana girgiza masa kai, daga Abban har Umar din sun kasa magana sai girgiza kai kawai da Abban yake yi yana kallon Adam din da yake ta juya idonsa daga gani kasan a make yake,
"Dan Allah kuyi hakuri." Abba ya fad'a da k'yar ya ki bari su hada ido da su sam,
"Babu komai Abba." Abdallah yace yana jan MD din
"Ba komai." Ya sake maimaitawa sannan suka fita daga gidan, MD be ce komai ba, har ya bud'e masa motar ya shiga shi kuma ya zagaya ya zauna a wajen MD din zai kunna motar, rik'e hannun sa MD yayi, yana duban sa
"Are you ready to marry da?" Ya tambaye shi yana tsire shi da ido
"I'm more than ready ma, anything?"
"Ina wayata?" Ya lalubi aljihun sa, sai ya dauke ta a saman kafarsa
"Bani two mint ina zuwa."
Ya balle murfin motar ya fita
"Karka koma ciki pls."
"Waya zan yi." Yace masa yana matsawa gefe, Baba Alhaji ya kira lokacin sun fito compound din gidan shi da Alhaji Muktar da kanin sa Alhaji Tukur, dama duk yammaci indai Baba Alhajin na gida anan suke zama har sai bayan sallar isha'i sannan suke tafiya shi kuma ya shiga ciki, kiran MD ya katse musu hirar da suka akan kasuwancin su,
"Ya akayi Mudan?" Yace bayan ya daga
"Dama akan maganar yarinyar da Abuya yake neman aure ce,idan kayi mana izini a daura auren a yau?"
"Saurin me ake Mudan? Akwai matsala ne? Kuma shi mahaifin nata zai yarda ya baku auren ta daga zuwan ku?"
"In Sha Allah babu matsala, dama Baban nata yace a turo ayi magana."
"Yanzu me kake so ayi kenan Mudan? Ina shi Abuyan? "
"Yana mota, amincewar ka muke nema, idan ka amince sai muga abinda ya kamata ayi."
"Na amince, ka tura min address din gidan yanzu zamu zo mu samu mahaifin nata, ka jiramu kafin muzo."
" Allah ya kara girma, mun gode Allah ya saka da alkhairi."
" Amin. Ina jiran ka."
" Zama me kama ku ba, danku ya dauko aure, yanzu haka so suke wai nayi musu izini su nemi auren, shine nace zamu zo sai ayi magana da mahaifin ta muje matsayar sa, su kuma muji dalilin gaggawar, bamu san me Allah ya boye ba, harkar aure tana bani mamaki sosai kar ka sauwala rabo ya kashe ka."
" Haka ne, idan har yaron ka ko yarinyar ka ya nuna maka aure yake so , toh kayi masa shine mafi aala, balantana Abdallah ba yaro bane, shi da kansa ya isa ya kai ya nema wa kansa aure kuma a bashi, musamman saboda nagartar sa."
" Haka ne." Duk suka hada baki wajen fad'a, suka tashi driver Alhaji Muktar ya dauke su suka nufi unguwar su Asma'un.
Lekowa MD yayi maimakon ya shigo matar, fuskar sa tar kamar an masa bushara da gidan aljanna, kamar bashi ne cikin bacin rai a dazun ba, hannu Abdallah ya daga masa alamar ya akayi? Ya kwashe da dariya yana jingina da jikin motar, horn ya danna masa da karfi, ya sake lekowa yana mika hannu ya zare key din motar
"Mene haka wai? Na tafiya zamuyi ba?"
"Eh akwai sakon da zan karba."
"Bani key din ka taho toh, ko so kake ya fito ya kara kama ka da rigima shi da baya gudun abin kunya?"
"Wuce nan wallahi, dan a cikin gida ne na kyale shi Amma wallahi anan sai na daka shi kuma na sa an rufe min shi wallahi, yanzu ma ai ban hakura ba, zamu gauraya dashi bayan na nuna masa karfin iko na."
Tabe baki Abdallah yayi, cike da kosawa da maganar MD din,
" Sai kayi tayi ai."
" Zan kuwa yi amma sai na fara aurar da kai tukunna."
" Silly boy." Ya zaro wayar sa ya hau dannawa yana share MD din da shirmen sa, Waka yaji yana rarewa, ya girgiza kai yana ayyana abinda ya saka shi farin ciki haka nan da nan, yana zaune cikin motar rabin kafarsa na waje ya zuro su yana rik'e da wayarsa kansa a kasa yana dannawa yaji shigowar mota layi, be dago ba ya cigaba da abinda yake sai yaji an faka a daidai saitin sa, hakan ya saka shi dagowa , mamakin ganin wadanda be yi tunanin gani ba ya cika shi, ya kalli MD da yayi wajen su ya dawo da ganin sa kofar gidan su Asma'un, kansa ne ya kulle ya ma kasa tunanin me yake shirin faruwa ko me yake faruwa, har lokacin yana zaune a motar yana bin su da kallo, Abba ne ya fito daga gidan yana saba babbar rigar sa, cike da girmamawa da mutuntawa suka gaisa sannan ya jasu zuwa cikin gidan, wani kallo yayi ma MD da yake kada kai kamar kadangare yana fatan komai ya kasance kamar yadda ya shirya. Motar Adam na nan kuma be fito daga gidan ba, ya tabbata yana ciki kuma hakan ya sake masa dadi, ya dinga zayaye a tsakanin wajen, fitowa Abdallah yayi ya damko shi yana bata fuskarsa
"What have you done? Me ka aikata?"
"Wait and see, aure zan maka."
"Aure? Ban gane ba."
"Nima ban gane ba."
"Allah sa ka fada min, kai ka kirasu ko? Me kace musu?"
"Eh ni na kira, kana tunanin idan ni ne zan iya barin abinda nake so tare da wanchan mahaukacin? Wallahi ko me za'a yi sai na aure ta na nuna masa iyakar sa, tunda shi jaki ne mahaukaci, kuma ko kusa da ita naga yazo walalhi sai na saka an tsinke min kafarsa daya wallahi."
" Oh innalillah, yanzu da wanne idon zan kalle su? Kamar fa yadda ka nuna I'm in desperate kenan ko? Na shiga uku. "
"Toh gauro irinka dama ai dole a same shi da matsuwa man,. "
" Baka da hankali wallahi. " Yace yana juya masa baya, be san ina zai dauki abinda yake ji ya ajiye ba, farin ciki, tarin fargaba da wani abu kamar tsoro tsoro, a zahiri a nutsen sa yake kamar babu wani abu amma kuma a badini shi kadai ya san luguden da ake a girkinsa, kiran sallar magriba ne ya fito dasu, kasancewar akwai masallaci a daidai saitin gidan, nan suka nufa suna hira cike da raha kamar sun jima da sanin junan su, hakan ya dan kwantar masa da hankali har ya samu kwarin guiwar daura alwala suka bi bayan su.
Ana idar da sallah Abba dama yayi wa limamin magana tun kafin a tayar, dan haka ana idarwa ya bada sanarwar daurin auren Asma'un, kallon kallon Abdallah ya dinga yi yana bin mutanen cikin masallaci da kallo, fit ya tashi ya fice MD ya bi bayan sa da sauri, akan kunnen su akayi siga da komai, Alhaji Muktar ya bada sadaki naira dubu dari biyu, anan take aka daura auren Abdallah da Asma'u. Rungume shi MD yayi yana furta Alhamdulillah, shi kuwa gogan sai ya rasa in da zai saka kansa, ya dinga jujjuayashi yana mamakin yadda al'amarin ya kasance. Wajen su, su Baba Alhaji suka nufo, ya mika ma Abdallah hannu alamun su gaisa, a kunyace ya mika masa ya rik'e shi cikin nasa yana murmushi
"Congratulations my son. In sha Allah kayi sa'ar mata."
"Baba..." Ya fad'a yana shiga jikinsa ya rungume shi, bayan sa ya bubbuga cike da zolaya yace
"Abuyan MD ya girma."
Dariya suka saka a tare su Alhaji Muktar suka karaso, suka bashi hannu suma dukka sannan suka yi masa Allah sanya alkhair, wani iri yake jin sa kamar wanda iska zata dauke tayi sama dashi
"Mahaifin ta ya roki a basu sati biyu kafin ta tare, ganin yanayin yadda auren ya kasance."
"Ba komai, mutum na gari me cike da karamci, naji dadin yabon da ya samu dashi da yarinyar, shiyasa ma ban yi k'asa a guiwa ba, wajen ganin Abdallah na ya mallake ta, ina fatan ta zamar masa sanyin idaniya kamar yadda mahaifiyar sa ta zamar min."
"In sha Allah."
Suka amsa a tare, MD sai rawar jiki yake kamar mazari, shine nan shine chan kamar ya taka rawa, har mota suka rasa su Baba Alhajjn Abba yazo suka sake sallama da yiwa juna murna da fatan alkairi, suna tafiya Hajiya Mama na zuwa ita da Nadeeya a gigice, Nadeeya ce take tukin, Hajiyan ta kasa nutsuwa tunda Abban ya kirata yace zai daura ma Asma'u aure, bata san nan Adam din ya taho ba, yake dai gida ya samu Fido ya nada mata mugun duka sannan yayi ficewar sa, Ashe nan ya taho tana ta kiransa a waya sai Nadeeya ce tazo ta duba Fido din ta bata magani, yanzu haka sun baro ta tare da kawarta Faiza dan har targade yayi mata.
Duk abinda ake da maganar auren har da daura auren Adam be sani ba sani ba dan bacci yake sosai a dakin Abbati saboda cewa yayi ba zai tafi ba, kuma duk alamu sun nuna baya hayyacin sa shiyasa Abba yace su kaishi dakin Abbatin kafin ya dawo hayyacin nasa, ita kanta uwar gayyar Asma'u bata san wainar da ake toyawa ba, tana kan abun sallah tana tilawar alkur'ani me girma, umma ma Umar ne ya shigo bayan sun zo yace mata manyan baki ne suka zo wajen Abban sai kuma sanarwar da taji daga masallaci duk da loudspeaker din bata da kara sosai kwana biyu matsala take