RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 30

18K to 21K   out of 87.6K words

Lion?"

"Me kika gani?" Yace yana zama a inda Asma'un ta tashi. "

"Baka ga me kayi ba?"

Tace cike da kulewa

" Me nayi?" Ya dage mata gira yana baje hannayen sa a saman kujerar

"Menene na wani riko ta kamar irin kayi missing din nan nata."

"Missing? Ni nace miki haka? Warning kawai nake so nayi mata, baki tsaya kin ga komai ba amma har kin yanke hukunci."

", Shikenan." Tace tana zama a kusa dashi, ta kwantar da kanta a kan kirjin sa, ya juyar da fuskar sa dayan side din sabon tunani na bijiro masa.

Dafe kirjin ta, tayi bayan ta shigo daki tayi gaggawr sakala key ta kulle sannan ta zauna tana maida numfashi, macen da ya shigo da ita ta dinga hasasowa a idon ta, lallai Adam ya shahara, tunda har zai iya kawo mace gidan auren sa, ba tare da fargaba ko dar ba. Bata damu ba, idan ma dari zai kawo matsalar sa ce, ba zata dai yadda kuma ta sake hada jiki dashi ba.
Saman taji sun hawo, suna kyalkyala dariya cikin yanayin da ta hasaso a ranta, dakin sa suka shiga gami da murzawa kofar key, shiru bata sake jin motsin su ba.. ishirwa taji tana ji, ta manta bata hawo da ruwan ba na saman ya kare, tashi tayi ta sallalaba ta fita xuwa kitchen din kasan, ta dauko ruwan kenan yana shigowa kitchen din, yi tayi kamar bata ganshi ta, tayi kokarin rab'awa ta gefe zata fita ya tare hanyar yana bin ta da kallo.

"Zan wuce!" Tace a dake

"Ba zaki wuce ba!" Yace yana matsowa

"Sauri nake please ka matsa."

"Anki a matsa din, saboda Sis ta hure miki kunne shine har kike da bakin fad'a min magana, wai tsaya ma, baki san nayi tafiya ba? Baki san ki duba mutum yana nan ko baya nan ba, kin fiso ma idan bana nan ko?"

Wani banbarakwai taji maganar tasa, ta kalle shi a kaikace ta sake kokarin rabawa zata wuce ya kamata ya hada jikin sa da nata, ta fizge da karfin gaske, ruwan ya fadi kasa tayi ficewar ta, ta barshi tsaye cike da takaicin abinda tayi masa, lallai ma yarinyar nan, sai kuwa ya koya mata hankali dan yaga kamar ta manta waye Adam, ko dan taga kamar ya sakko yana mata magana a nutse, tsaki ya ja mayen kamshin turaren ta da ya cika kitchen din ya shigar masa har makoshi, sink ya nufa ya kuskure bakin sa sannan ya dau ruwan ya fito.











_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*



RM*
       10

***Da asubah Fido ta bar gidan bayan ya sauke ta a gidanta da take zaune wanda shine ya kama mata shi yake biyan kudin hayar gidan tsawon lokacin da suka sauka a tare. Gida ya dawo direct ya wuce daki ya kwanta babu batun sallar asubah a lokacin burin sa kawai yayi bacci dan ba wani isashen bacci suka samu a tafiyar da sukayi ba ta bikin abokin sa Chairman shiyasa yake jin tamkar idonsa zasu rufe saboda bacci.
Sallar asuba ta idar ta zauna a wajen tana karatun al'qur'an har gari yayi sha sannan ta tashi ta gyara dakin ta koma ta dan kwanta zuwa takwas ta mike, so take ta shiga gidan Hajiya Mama shiyasa ta ki bari ta koma baccin safen. Wajen goma ta gama abinda take ta bud'e kofar ta dan leka ta tabbatar baya nan sannan ta fito ta rufe kofar a hankali ta fita. A harabar gidan suka hadu da Nadeeya zata fita, tsayawa tayi suka gaisa ta sake tambayar ta jikin ta, a kunyace ta amsa mata tayi godiya ta fice ita kuma ta shiga ciki. Hajiya Mama na zaune a falo tana breakfast, ta saki fuskarta sosai ta hau yi mata sannu da zuwa

"Dama ina shirin yi wa Adam korafi, idan ya fita kiyi tahowar ki nan kiyi zaman ki, chan ai sai kadaita ta dameki."

"Ina kwana?" Tace tana durkusawa k'asa

"Lafiya lou wallahi, zauna mana."

A kunyace ta tashi daga tsugunan ta zauna daga gefe, Hajiyan ya turo mata tray din dake gabanta

"Maza ci abinci, bari na watso ruwa nazo."

"Naci abinci Mama."

"Gidanku, maza dauki ki zuba kici wani abincin kirki kake iya ci ne, Nadeeya ma tace min baki ji dadi ba, ban sani ba wallahi sai yau take fad'a min, ni dai nace Allah yasa addu'a tace Allah ya amsa min."

"Uhumm..." Tace cike da kunyar Hajiyar, fuskar ta cike da farin ciki ta shiga ciki, ta bar Asma'un da tunann maganganun ta, bata jima ba ta dawo ta zauna, ta shiga jan Asma'un da hira cikin sigar son bugun cikin ta ko taji wani abu dangane da zaman nasu, dazu take maganar Asma'un anan Nadeeya take ce mata ai bata ji dadi ba ma, daga haka kuma bata sake ce mata komai ba, shiyasa tayi tunanin ko cike ne da Asma'un, tayi niyyar dama anjima ta shiga gidan nasu sai kuma ga Asma'un ta hutashsheta ta shigo, bata samu amsar dukkan bayanan da ta nema wajen Asma'un ba dan kamar kunyar Hajiyan take ji sosai hakan ya sake tabbatr wa da Hajiyan Asma'un cikin ne.
Har sha biyun rana suna zaune a falon in da Hajiyan ta saka aka ajiye mata abubuwa masu yawa a gabanta duk wani abu da tayi tunanin zata ci sai ta saka an ajiye mata, ita abin ma sai ya dinga bata dariya da mamaki, bata dai nuna komai ba, ta dai jinjinawa kokarin Hajiyan da kuma irin soyayyar da take wa Adam din nata. Cikin shigar dakakkiyar shadda coffee colour ya shigo falon, sosai shigar ta karbe shi ko dan be saba irin ta ba? Kallo daya Asma'un tayi masa ta kauda kai dan ita sam bata ga abun kallo a wajen mutum irin Adam ba, wanda yake da kyawun dan miciji.

"Shine kika taho kika barni ko? Bayan nace ki jirani mu zo tare."

Kallon baya asma'u tayi a tunanin ta da wata yake, sai kuma taga ya nufo ta, yana sake son tabbatar mata da itan yake, yak'e ta hau yi ganin idon Hajiyar na kansu tana ta murnushin jin dadi, dungure mata kai yayi yace

"Punishment dinki kenan na tahowa ki barni, gobe ma kin kara."

"Gidanku Adam, karka kara dungure mata kai, wani ya hanaka tashi da wuri?"

"Toh ai laifin ta ne fa, ita ta hanani baccin jiya, shine kuma ta taho ta barni."

Mutuwar zaune tayi, bata taba sanin akwai maza makirai ba sai yau, kallon sa take shima kuma ita yake kalla idon sa fes a kanta, ya harare ta, ga gefe ba tare da Hajiyan ta gani ba, tayi saurin sauke kanta k'asa mamakin sa na sake girmama a ranta, ya wuce duk in da take tunanin sa. Be sake bata mamaki ba sai da taga ya zo ya zauna daf da ita yana cigaba da tsokanar ta, wanda ta lura ba karamin dadi hakan yayi wa Hajiyar ba.
Anan suka ci abincin rana, ko da tace zata tafi sai Hajiyan ta hanata, ganin su a tare a hakan yayi mata dadi ainun, ta dinga hasaso yadda komai zai daidaita a rayuwar Adam din ta. Sai da akayi la'asar ta barta ta tafi lokacin shi ya ma riga ya fice wai zai raka wani abokin sa neman aure.

***Gidan su take son zuwa, gashi bata san ta ina zata fara sanar dashi ba, tasan haramun ne ta fita bata tambaye shi ba, amma kuma bata san ta ina zata fara tambayar ba, ita kadai take sakawa da warwarewa har tara na dare be shigo ba, ba jiran sa take ba dama, amma kuma tana ankare da duk motsin sa. Bacci ne ya soma daukar ta, ta mike daga zaman chatting din da tayi da su Hidaya ta je ta dauro alwala tayi shafa'i da wutri tazo ta kwanta bayan ta rage kayan jikin ta, ta daga curtains din dakin yadda iska zata shigo sosai.
Bata san yaushe ya shigo ba, cikin bacci bacci taji ana taba ta, ta tashi a firgice, ya rik'e ta gam yana toshe mata baki.

"Hakki na nazo karba, kikayi gardama na sake miki kacha-kacha."

Gumi ne ya shiga karyo mata, tana tuna bakar wahalar da tasha a wajen sa waccar ranar, magiya ta soma masa da hada shi da Allah amma babu alamun zai ji ta balle ya tausaya mata, tunanin yadda zata kwaci kanta ta hau yi dan kuwa idan bar ta amince masa akwai matsala bata gama warkewa ba har yanzu dan kusan kullum sai ta shiga ruwan dumi take jin dadi, dukkan karfin ta, ta tattaro ta hankade shi, ta mike tayi hanyar barin dakin duk da duhun da ya mamaye ilahirin dakin, shaf ta manta gaba daya da kafar benen dake wajen, burin ta kawai ta tsira da ranta, ji tayi kamar ta taka abu me tsantsi, sai kuma taji ta zame ta kwalla kara gami da zamewa ta fadi a wajen, kanta ya bugu da karfin stairs din ya fasa mata saman goshin ta!






*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166



RM
   11

Akan hannun ta ta fadi, tayi kara me karfi, be fito ba, ya tabe baki cike da haushin ta. Kokarin tashi tayj amma sam ta kasa motsa hannu, wani irin zugi yake mata ga goshin ta da yake fidda jini sosai. Kuka take sosai ta shiga kiran sunan sa 

"Ya Adam! Ya Adam! Zan mutu dan Allah ka taimaka min!"

Yi yayi kamar ba zai zo ba, sai kuma wani abu ya darsu a ransa ,ya mike da sauri yayo wajen, a yanayin da ya ganta ne ya saka shi karasowa a guje

"Tashi! Tashi!" Ya hau ce mata a kideme dan be yi tunanin hakan ba, ganin ta soma zama unconscious ya saka shi dagata chak ya sauka da ita da gudu gudu, ya shiga kwala wa me gadi kira,sosai kanta yake zubda jini ga hannun nata da ya tabbatar da ya samu matsala. Direct asibiti ya wuce da ita, bayan ya kira Nadeeya da wayar sa daya da ya bari a mota, a kidime ta amsa masa tace gata nan sannan ta kashe ta kira Hajiya Mama tace mata Asma'u babu lafiya sun tafi asibiti, itama Hajiyan ta tsorata sosai, ta dinga kaiwa da komowa har sai da driver ta da ta aika ya dawo, sannan suka dauki hanyar asibiti .

   Taimakon gaggawa aka shiga bata, aka samu aka tsaida jinin goshin mata amma sai da akayi mata dinki a wajen, sannan aka tabbatar masa da ta samu karaya a hannun da ta fadi a kansa, ji yayi kamar almara, ya dinga kallon ta a karon farko yaji burburshin tausayin ta ya wanzu a zuciyar sa, dakin da aka kwantar da ita ya tura ya shiga, ya tarar tana kwance tana fitar da numfashi daidai na azaba, wayar sa ya daga da Nadeeya ta kirashi, ya juya ya bar dakin yana amsa wayar da kwantancen dakin da suke, kusan a tare suka iso da Hajiya mama dan ita Nadeeya din daga nesa take, dukkan su a rude suke, suka isa dakin Nadeeya ta riga mama isa gaban Asma'un tana kallon hannun ta

"Karaya?" Tace cike da tashin hankali

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun!" Hajiya mama ta fad'a tana kallon Adam din cikin son karin bayani

"Faduwa tayi wallahi mah, a wajen sauka daga stairs bansan dame ta zame ba, wallahi ban sani ba."

Wani kallo Nadeeya ta masa, ta kalli Maman ta fita zuwa wajen Drs din.

"Garin yaya haka ta faru Adam? Garin yaya?"

Girgiza mata kai yayi, yana jin wani iri, abun da be taba ji ba.

"Fad'a kukayi? Ko dama chan har yanzu akwai matsala ne?"

Girgiza kai ya sake yi, ta matsa ta taba jikin Asma'un da ya rure da zazzabi me zafin gaske

"Me zance wa mahaifanta? Waye kake ganin zai yarda da cewa faduwa tayi? Bayan kowa ya san yadda akayi auren nan, sannan kowa ya san halin ka."

Bashi da bakin magana, domin shi kansa be san bakin da zai yi amfani dashi wajen kare kansa ba, adah idan aka ce zai russuna haka har yaji tausayi irin haka zai karyata, amma kuma ya rasa dalili, sosai yake jin tausayin ta musamman ganin irin bakar wahalar da tasha a yanzun, karaya ba abu bane me sauki musamman a wajen wanda ya soma girma ba kamar yara kanana ba, ya taba samun dislocation sanda yana tashen ball ya san wahalar da yasha a lokacin ballanta na ita, yana jin Maman tana ta maganganu be ce komai ba, be kuma bar dakin ba, har zuwa sanda Nadeeya ta dawo da ya lura tana fushi dahsi sosai, har zuwa lokacin da Maman ta kira Abba a waya ta sanar masa.
   A tunanin sa zasu zo a take a lokacin, amma babu wanda yazo, da Hajiya Maman ta sake kiran Abban sai yace mata babu komai su ma sun isa zasu shigo da safe, hakan ya sake karyar wa da Hajiyan guiwa, taji da gaske bata kyauta ba, bata yiwa Asma'un adalci ba kuma ba ta yiwa mahaifin yarinyar hallaci ba, ya dauke ta ne tamkar uwa mahaifiya ya kuma amince mata yana bata dukkan girman ta, son kai ya kwashe ta da aikata abinda ba zata taba yafewa kanta ba.
   Kwanan zaune sukayi saboda yadda hannun ya matsa mata, sun tausaya mata dukkan su, har shi uban gayyar da ya zama so silent kamar bashi ba, sai gabannin asubah sannan ta samu wahalallen bacci ya dauke ta.
   Toilet mama ta shiga tayi alwala Nadeeya ta tsaida shi ganin zai fita, ta tsare shi da ido cikin tuhumar sa tace

"Me kayi mata?"

"Naam?"

"Tsorata kawai tayi ba, shine ta fito da gudu ta fadi, wallahi ban mata komai ba."

Ranta ne ya sake baci sosai, ta nuna masa kofa jin Maman zata fito, ya fice da sauri yana sake rejecting kiran Fido da take ta jera masa shi tun daren.

***Abbati ne yazo tare da Abba wajen takwas lokacin Adam din ya bar asibitin yaje dauko mata kaya, nan fa Hajiya Mama ta saka wa Abban kuka, ya dinga bata baki yaki yarda ya nuna damuwar su ko wani abu, ya kuma sake jaddada mata hakan kaddarar Asma'un ce, babu wani da ya isa ya hanata faruwa. Be jima ba yayi mata addu'a ya tafi, ya bar Abbati saboda ko za'a nemi wani abin tun da Adam din baya kusa.
  
***Waya umma suke da Ya Hadiza ta fad'a mata abinda ya faru, kuma Abba yace ta kyale Hajiya Maman suyi jinyar kar ma tace zata je ta zauna, hakan ba karamin bata mata rai yayi ba, a kalla dai a barka ka zauna da danka dan yafi bukatar ka akan kowa, hakuri Ya Hadizan ta bata tace gatanan zuwa gidan zata kuma kira Abban a waya, ajiye wayar sukayi umma ta cigaba da shirin tafiya asibitin dan ma yace ta jira Abbati ya dawo ya kaita da tuni ta tsufa a chan dan ba zata iya jurewa ba, dama ta san za'a rina ai tunda aka hada Asma'un da mahaukacin miji.
   Har Yaya Hadizan tazo Abbatin be dawo ba, sai kawai umman ta fito suka tafi, a hanya take fad'a mata yadda sukayi da Abban, yana nan akan bakansa be yarda Umman taje ta zauna ba, ya dai amince taje kullum amma ba wai da zuwan zaman jinya ba,

7 / 30