Author : RANO Category : African Stories & Novels
gaishe shi, ya dinga saka mata albarka, sai da MD suka shigo tare da Abuyan sannan suka koma cikin gidan ta zauna dasu Amira a falon suna kallon wani film me kyau.
Sai wajen twelve sannan yayi mata text yace ta dawo, ta tashi tace ma Mami din zata tafi, sai tace mata ta shiga wajen mom ta sameta a daki, ta shiga ta gaishe ta again sannan tace zata tafi ne dama, dadi taji sosai ta saka Ihsan tace ta rakata. Sosai Asma'un ta kwanta mata ta gamsu da ita a matsayin matar Abdallan nata.
Satin sa biyu iyakar sa yar karamar unguwa su fita da MD shima basa dadewa, ba karamin sabo tayi dashi ba a yan kwanakin har takan ware suyi ta hira kamar ba gobe, ga wata irin zazzafar soyayyar sa da ta sake kamata. A dan zaman nan nasu ta gane wanne irin miji Allah ya bata, me cike da tarin abubuwan mamaki, mutum ne me tsananin addini da kankan da kai, baya taba ketare iyakokin Allah yana kums kokari sosai wajen sauke nauyin dake rataye a wuyan sa, ba zata ce tafi kowacce mace sa'a ba, sai dai tana da yakinin zata iya jerawa a cikin matan da sukayi dace da sa'ar miji a wannan zamanin.
Washegari zai koma aiki duk kuwa da shine ogan kansa amma ta lura baya sanya wajen aikata duk abinda yake ganin zai sake kafashi, a hakan ma yana gidan ko yaushe yana kokarin rage ayyukan nasa ne, wanda yake daukar kaso mafi rinjaye a aikin company din nasa, be zauna ya nade hannu da kafa ba, shiyasa har yanzu yake samun cigaba a al'amarun sa.
Da wuri tashi ta shirya masa abin kari ta kuma taimaka masa wajen shiryawa, ya tsuke abinsa a cikin suit ash colour, ya makala necktie ya saka half cover shoe da black socks saboda bakin da zasuyi yau din wannan shigar ita ta dace da zama dasu. Be sani ba, ta dauke shi hoto ya juya yana tattaro wayoyin sa da system dinsa, fuskar sa a kasa ya dan dukar da kan, yayi kyau a hoton ga wani irin haske da ya kara tun bayan auren su, so take ma ta tambaye shi zuwa gida amma ta kasa, gashi yau yace mata zai iya kai magriba be shigo gidan ba, dan ma su Amira na zuwa ko ita taje anan zata dinga rage zaman.
"Kayi kyau."
Ta samu kanta da furtawa bayan ta karbi jakar hannun sa ta rataya a kafadarsa suka shiga takawa zuwa falo. Hancin ta ya lakace mata yana murmushi
"Har na kaiki kyau? Kin ganki kuwa? Gaskiya na iya kiwo wallahi, bul-bul fa ko ina, har nan."
Yace yana pointing din kirjinta, hararar sa tayi a wasance tace
"Dama a haka nake."
"Ummm... Ba wani."
"Allah!"
"Shikenan bani jakar nan kar nayi late, MD na waje yana jirana ba sai kin rakani ba."
Mika masa tayi sannan tace
"Allah ya kiyaye ya bada sa'a."
"Amin my wife, nagode ki kula min da kanki."
***A birkice yake tunda ya tashi a yau din baya jin komai baya ganin kowa sai ita, ga Fido a gefe da ta hana masa sakat idanun ta na kan duk motsin sa, kwana biyu kenan yana bibiyar motsin Abdallan har office dinsa yaje akace baya zuwa, gashi babu damar zuwa unguwar tasu saboda polisawan nan dan ba karamin aikin su bane su nada masa na jaki yanzu bashi da kwari.
Ganin yau Monday ya saka shi son sake komawa yaga ko yazo, ga Fido taki fita dan tun sassafe yake saka ran zata fitan,amma shiru, yana nan zaune bayan ya gama shan tea da slice bread biyu yaji tana wayar zata fita, murna ya hau yi ya labe yana kallo ta shirya, tazo ta sameshi ta ja masa warning, ya amsa da toh tana fita ya saka kai shima ya fice sai K'AREFA MOTORS