RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 30

39K to 42K   out of 87.6K words

waya, zama yayi ta gama sannan ta dube shi

"Za'a je garin su fiddausi neman aurenta."

Kirjinsa ne ya buga da karfi, sai a sannan ya tuna da wani maganar aure, ya rasa dalilin da ya saka Hajiyar damuwa da maganar, yadda tadage akan maganar auren ne zai baka mamaki, kamar bata san wace yarinya bace Fido din,yasan ba tuban gaskiya tayi ba, kawai dai akwai dalilin ta na kafewa sai ta aure shi, wanda shi akaran kansa be san dalilin menene ba.

"Nifa ba zan auri yarinyar nan ba."

"Aikuwa baka isa ba, aure kamar anyi an gama ne."

"Wai Mah kin fi son ta ne akaina? Ko ni yanzu bani da wani amfani."

"Oho, ban sani ba nima, aure ne dai babu fashi, ba zaka sake sani a wata masifar ba, karfin hali kawai nake ba wai Ina jin dadi bane, dan haka kar ma ka fara wata magana wallahi sai ka aureta sai dai idan mutuwa nayi."

Mikewa tayi ta bar shi a wajen a zaune tamkar wanda aka dasa, be san yaushe Hajiyan ta chanja masa haka ba, wanda a baya ita da kanta take bashi zabin duk abinda yake so, ta kuma mara masa baya dari bisa dari, amma be san dalilin da yasa yanzu ta kafe akan lallai sai ya auri Fido din ba, bayan ita da kanta ta san abinda ya hadu ba wai abu bane me kyau. Ita kanta Hajiyar sau tari tana mamakin yadda take jin sam ba zata taba iya nutsuwa ba har sai an daura auren, tamkar ana hura mata wuta haka take ji, shiyasa ta dage kai da fata ko da hakan na nufin shigar Adam din hali na daban ne.
    

*** Waya Faizan ta gama suka kwashe da dariya a tare suka tafa, Faiza tace

"Kin ga abinda nake fad'a miki ko!? Ai ba'a bori da sanyin jiki, maganin uwar kawai shine magana yanzu ba gashi nan ba komai na tafiya daidai, amma da ke kin dauki wata shawarar da ba zata bulle miki ba, hakan kuwa shine kawai maganin irin su, idan suka ki bi sai a biyad dasu, shima Adam din ki kyale shi zai gane bashi da wayo, sai ku zauna su gama daku sannan su ajiye ku su dauko masu kamun kai, ba zata sabu ba."

" Wallahi ni sam hankali na be dawo jiki na ba, sai da na samu labarin yarinyar da yaga min ihun baya so har da barin ciki tayi, ina rashin so anan?"

"Ke ya mayar gaula ai, ki zauna ki kare rayuwar ki a haka babu me kwasar ki, ko shi ba zai kwasa ba, bare wani."

"Haka ne wallahi, toh ba zata sabu ba wallahi."

" Ai da kin tsaya kallon ruwa."

" Ai na dawo hayyaci na wallahi, ko nawa zan kashe, akan na same shi, idan yaso duk abinda zai biyo baya wannan daga baya ne."

" Yawwa yar gari." Suka sake tafawa cike da jin dadin yadda abubuwan suke tafiya.



***Tunda tazo gidan Ya Hadiza ake kiranta da unknown number, da bata dagawa har ta fara dagawa amma sai ayi shiru tayi ta magana ita kadai, daga baya sai ta daina dagawa kawai ko sau nawa za'a kira, gashi na kiran wasa bane sai a jera kira yana katsewa guda goma, data gane idan aka kira ko sau daya ne ta daga ba za'a sake kira ba kuma sai bayan wasu awoyin sai ta cigaba da dagawa amma itama sai tayi shiru idan kuma Abeed na kusa da ita sai ta daga ta bashi yayi ta shirmen sa, har a gaji a kashe.
Ranar juma'a bayan yaran sun dawo daga makaranta sun hutakasancewar da wuri suke dawowa ranar Abban su yace su shirya zai kaisu shopping, suka hau murna da shiryawa, daki Ya Hadiza ta sameta tace ta shirya zasu fita ana idar da sallah, tashi tayi bayan ta ajiye littafin da take karantawa ta shiga toilet din dakin tayo alwala ta fito, ta chanja kayan jikinta zuwa abaya ash colour me kyau, ta yane kanta da mayafin abayarw, very simple and unique, tayi kyau babu komai a fuskarta sai powder da wetlips. Ana idar da sallah Ya Hadiza tace ta fito, ta fito dauke da Abeed a kafadarta.

"Kinyi kyau kanwata."

"Kai Ya Hadiza."

"Wallahi baki ganki ba, son kowa kin wanda ya rasa."

Murmushi tayi kawai tabi bayan ya Hadizan zuwa mota, mamaki duk sukayi ganin motar Adam a kusa da ta Abban su Abeed din, suna tsaye tare kamar magana suke, dauke kai sukayi suka shige mota sai da Abban ya kara wajen minti biyar sannan ya shigo motar yana murmushi

"Mutuminki ne fa, wai yazo wajen Asma'u."

Gaban Asma'un ne ya fadi ta dafe da sauri, dariya taji Ya Hadizan tayi

"Bashi da hankali amma ko?"

"A ah, na raba ki da shiga tsakanin mata da miji fa, sai su shirya su barki da babatu. "

"Ko Asma'u? " Yace yana juyo da kansa baya, bata ce komai ba, har suka bar unguwar kanta na k'asa kuma shi Adam din be tafi ba, sai ma biyo bayan su da yayi.
Wani babban supermarket suka tsaya, yana kallon Adam ya parker daga bayan su Asma'u da ya Hadiza basu ganshi ba sam, ciki suka shiga, Abeed na hannun Asma'u ya Hadiza da mijinta suka hau sama suka bar ta da yaran a k'asa suna daukar tarkacen kayan school dinsu.


Fitowar sa kenan daga office a gajiye ya tsaya ya duba wa Baba Alhaji madarar sa da yake sha Ensure, kullum sai ya manta ya koma gida yau dai yace bari ya shiga kawai ya huta dan kwana biyu be sha ba, suit ce a jikinsa ya cire ta saman, kafarsa sanye cikin bakin takalmi sau ciki, sai siririn glass fari da ya dora akan kyakyyawar fuskar sa, tun da ya doshi kofar shiga supermarket din securities din wajen suke gaishe shi, amsawa yake a sake ba tare da takure kansa ba. Kansa tsaye ya wuce wajen da ya saba dauka, ya dauki iya adadin da yasan Baban zai kwana biyu yana sha be sake nema ba. Wayar sa ce tayi kara, ya zaro ta yana dagawa, yana tafiya yana amsa wayar daidai lokacin da Asma'u ta biyo Abeed da yake ta gudun sa tsakanin wajen, be ganta ba, ita ma kuma bata lura dashi ba, sai ji yayi ya bigi mutum, da sauri ya furta

"Subhallah."

Saura kadan ta kai kasa Allah ya kiyaye, cike da kulawa yake tambayar ta

"Baki ji ciwo ko wani abu ba? Sannu I'm very sorry ban ganki ba, fault dina ne ina waya ban duba ba sosai."

Kallon sa ta danyi, yadda yake faman bata hakura kamar shi kadai ne yayi laifin, girgiza masa kanta tayi a hankali tace

"Ba komai, kayi hakuri kai ma."

"Are you sure you are okay?"

Da kai ta amsa masa,

"Masha Allah." Yace ya cigaba da tsayawa a wajen maimakon ya wuce, kunya taji, tana son barin wajen amma kuma ya tsaya yaki tafiya, kamar wanda aka dasa a wajen haka ya tsaya shi be ce komai ba, be kuma tafi ba

" Sai anjima." Tayi karfin halin ce masa tana jan hannun Abeed din, bata ji me yace ba, dan taga kamar he's lost in his thoughts, tayi gaba abinta ba tare da ta sake waiwayo wa ba, sai dai kamshin turaren sa da ya cika baki daya wajen ya cigaba da biyo ta har saman wajen su Ya hadiza.

Payment Abban su Abeed ya tsaya yi yace su je mota, suka bar shi a ciki suka je mota suka shiga, ya gama payment din kenan ya fito ana saka masa kayan a baya yaji an masa sallama, ya juyo yana amsawa sannan ya bashi hannu suka gaisa

" Sunana Abdallah."

" Sannu Abdallah, ya gida ya aiki?"

"Alhamdulillah wallahi, dama naga wata ne bansan ko matar aure bace, ta shiga motar nan tana sanye da abaya

"Ash ko? Ba matar aure bace, sister din matatace."

"Owk Masha Allah, dan Allah idan babu damuwa inaso ka bani dama na ganta, ba yanzu ba cox yanzu dare yayi kar na tsaida ku, may be kuma sai ka fara neman permission from her Dad, kamar yadda yake, I can wait."

" Ba damuwa in sha Allah, lets exchange number zan kiraka duk yadda ake ciki."

" Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi."

" Amin."

Yace ya bashi number sa shima ya bashi nasa, yayi gaba zuwa wajen motar sa Abban su Abeed din na kallon sa har ya fita daga cikin harabar wajen, dadi ne ya kamashi, dan idan Allah ya amsa addu'ar su toh tabbas Asma'u ta yi miji, miji irin na nuna sa'a, ABDALLAH IBRAHIM K'AREFA. Duk abinda ya faru Adam na makale yana kallon su, duk da be ga fuskar mutumin ba, be kuma ji me suka tattauna ba, amma sai yaji sam hankali sa be nutsu ba.



*RM*

    *21*

***Shigowa motar yayi fuskar sa na bayyana yanayin da yake ciki, Ya hadiza ta dan kalle shi zatayi magana ya rigata

"In Sha Allah Asma'u tayi miji."

Kasa k'asa yayi maganar saboda haka Asma'un dake baya bata ji ba, ga yaran dake faman mata surutu, fuskar Ya Hadizan ce ta fad'ad'a zuwa tsantsar farin ciki tace

"Dan Allah? Waye?"

"Kina jin wani family K'AREFA?"

"Sosai." Ta fad'a cike da zakuwa

"Toh baban dan gidan ne, mallakin K'AREFA MOTORS, shi kika ga muna magana, kuma maganar akan Asma'un ce, very responsible guy ni na sanshi amma shi be sanni ba, nasan har cikin gidan su saboda wani aiki da ya hada office dinmu da Mahaifin sa, mutanen kirki ne wallahi sosai, sai kin ga yadda yazo min, kai Alhamdulillah."

"Alhamdulillah!" Ya Hadiza ta furta tana waigawa baya, ta kalli Asma'un dake kokarin budewa Abeed chocolate, tayi murmushi tana jin zakuwar kiran umma ta fesa mata daddadan labari, ta tabbata Allah ne ya dubi Asma'un yayi mata chanji mafi alkhairi, ko dan hakurin da tayi. Sama sama suka karasa abinda ya fito dasu sukayi takeaway suka yi gida, shi kansa Abban su Abeed din ya matsu ya sanar da Abba maganar, ita kuma Ya Hadiza Umma, suna shiga gidan kuwa kowa yayi dakin sa domin kiran wayar. Umma na tare da Abba a lokacin suna maganar Asma'un, sai ga kira a kusan lokaci daya, umma ce ta fara dagawa sai shima Abba ya daga cike da girmamawa suka gaisa da sirikin nasa sannan ya sanar dashi abinda ya faru da uzinin da Abdallan yake nema, bayan ya gama Abban yace

"Ai kai ma uban Asma'u ne Ali, na baka wuka da nama kayi duk abinda ya dace, abu daya na sani, shine Asma'u ce take da damar zabarwa kanta abokin rayuwa a yanzu, idan har ta amince dashi kuma ka gamsu dashi, shikenan babu damuwa. "

"Nagode Abba Allah ya kara girma. "

" Amin ya Allah, a gaida yaran da matar gidan. "

" Zasuji. "

Jinjina kai Abba ya dinga yi har Umman ta gama amsa wayar Ya Hadizan cikin farin ciki, tana ajiye wayar yace.

"Uwata ce ko?"

"Eh, akan maganar Asma'u ne."

"Alin ya sanar dani komai, Allah ya wuce mana gaba yayi mana zabin alkhairi."

"Amin ya Allah." Ta amsa tana jero addu'ar dacewa a ranta.

***Asma'u na daki Ya Hadiza ta biyo ta da abubuwan da aka siyo nata, a gefen gadon ta ajiye ta tsaya ta idar da sallar isha, ta juyo tana duban ta

"Ga kayanki nan, ga abincin nan a ciki, kici akwai labari me dadi."

"Ai ba zan iya cin abincin ba idan ban ji labarin ba.".

Tace tana mikewa daga sallayar

"Ai na zaci shafa'i da wutri zakiyi."

"Idan nazo kwanciya zanyi, dan Allah fad'a min, labarin."

"Kema fa wasa wasa akwai son jin gulma, toh ai labarin akanki ne."

"Ni kuma?"

"Eh wallahi,Allah ya amshi addu'ar mu, kin samo gallelen miji in Sha Allah, wannan da suke magana daxu da Abban su, kin ganshi?"

Girgiza kai tayi a sanyaye

"Toh dai zaki ganshi ai, dan zaizo gobe."

"Waje na?"

"Emana."

"Wallahi ni dai tsoro nake ji. "

" Babu abinda zai faru sai alkhairi, kiyi istikhara kafin ki kwanta, mu nemi zabin Allah, Abban su dai ya gamsu dashi dari bisa dari kinsan kuma halin shi. "

Shiru tayi jikinta duk yayi sanyi, bata da tunanin hakan nan kusa, tana so ta huta sosai dan ita gaba daya auren ya fita daga kanta, duk da akwai mazaje na kirki na gari amma an ce ruwan da ya dake ka shine ruwa, amma duk da haka zata nemi zabin Allah, ta barwa Allah komai.
   Chachakalar abincin kawai tayi dan duk sai taji bata ma da appetite, ta kwanta bayan tayi nafilar tayi lamo akan gado, bata jin bacci ko na digo, rayuwar ta ce ta shiga dawowa mata tiryan tiryan, tun sanda ta bud'e idon ta, ta ganta a gidan su kawo zuwa lokacin da ta mallaki hankalin kanta zuwa rayuwar gidan Adam da bayan ta, ta tsinci abubuwa da yawa cike da rayuwar tare da kalubale da suke tattare da rayuwar baki daya. Ta jima tana sake-sake kafin barci barowa yayi awon gaba da ita.

***Tunda Adam ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, abin duniya yayi masa mugun yawa gashi ya gama saddakarwa da gaske son ta yake, irin soyayyar nan me zafin gaske, irin wadda mutum yake jin zai iya komai akai, sanda ya shiga gidan su sai da Mama ta dube shi ta sake dan ya rame sosai tamkar bashi ba, abinci tasa aka kawo masa amma sam yaji bashi da taste ko kad'an, a tunanin ta ko akan maganar auren sa ne da ta matso sosai, ba zata fasa ba dan haka ma ba zata bashi fuskar da zai zo da wata magana ba, idan ma akan auren ne duk zai sauke idan akayi auren, su Nadeeya ma sun mata mitar sun hakura sun zuba mata ido dan da gaske abin yafi karfin su kuma ba fasawa zatayi ba dan ta kafe. Gidan sa ya koma ya tarar an kwashe kusan komai na gidan da yake a mazaunin na Asma'un, kamar ya ari hauka haka ya koma gidan su ya samu Maman yake tambayar ta kayan gidan

"Na aikawa Asma'u kayanta tunda da sunanta akayi su, ita kuma fiddausi sai tazo da nata."

"Innalillah, amma Mah da baki aika ba, ina so wallahi."

"Me zakayi dasu? Kai da za'a kawo maka sababbi."

Idan ma yace zai tsaya mata bayani ba zata yarda ba, juyawa kawai ya koma ya shige dakin sa ya rufo, ya dauko album din da Nadeeya tasa akayi musu na bikin ya bud'e ya hau kallo tamkar gaula, idan yazo kan nata sai ya dau dogon lokaci yana kallo yana murmushin, sai yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ya kamu sosai, kamu me wahalar gaske. Be san ta ina zai fara gyara kuskuren da yayi ba, ya riga ya bata komai wanda gyaruwar sa zatayi matukar wahala. Da hoton ta ya kwanta rungume a kirjinsa, yayi mafarkin tana zaune a dinning tana zuba masa daddadan abincinta ya sauko yazo ya zauna, ta shiga bashi a baki tana masa kallon da yake sake narkar dashi, juyi yayi be san yazo karshen gado ba, sai ji yayi ya fado tim, ya mike a zubure yana zazzaro ido, ya sake daukar hoton ya koma tsakiyar gadon ya kwanta, mafarkin da yayi na dawo masa, tsaki yaja da ya gane da gaske mafarki yake, ya dinga juye-juye kafin ya samu barcin ya sake dauke shi.
   

***Tun da suka tashi da safe, suka hau shirye shiryen tarbar bako, ya sanar da Abban su Abeed zaizo da yamma wajen hudu da rabi bayan sallar la'asar, seat room din da yake saukar baki ya gyara da kansa har da daga kujeru da su sharar yana ko ina yayi fes, snacks Ya Hadiza ta saka Asma'u tayi me dadi, sannan ta sakata gyara jikinta tayi wanka wajen uku da rabi, tasan ba gwanar kwalliya bace itama kuma tafi son mace ta fito a natural dinta shiyasa bata ce tayi ba, zuwa hudu komai ya zama ready, sukayi sallar la'asar wajen hudu da rabin kuwa sai gashi yazo, da Abban su Abeed suke waya har ya karaso kofar gidan, ya fito ya taro shi zuwa ciki, ya kaishi har falon bayan ya kunna gen kasancewar babu wuta a garin. Ciki ya shiga bayan sun gaisa yace wa Ya Hadiza ta turo Asma'u, tare suka dawo ta riko hannun ta, yana tsaye ya tsokaneta sukayi dariya, a kunyace ta shiga seat room din bakin da dauke da sallama tana kokarin daidaita kanta da yanayin faduwar gaban da take ciki, ga wani irin bugawa da kirjin ta yake yi zuciyar ta tamkar zata hudo ta fito waje. A bayyane ya amsa sallamar tata muryar sa tar idon sa akanta sai dai ita kasa take kallo har ta samu waje ta zauna sannan ta gaishe shi.

"Ba zan amsa ba, haka ake gaisuwa babu kallon mutum?"

Dagowa tayi kad'an, ta kalle shi sai mamaki ya kamata ganin na jiyan nan ne a supermarket din nan

"Yauwa ko kefa, kina lafiya!?"

"Lafiya lou."

"Masha Allah, ya gida ya komai."

"Alhamdulillah."

Daga nan sai sukayi shiru, shi be san yadda ake magana da mace ba gashi dama ba gwanin magana ba, balle ita kuma, yaso MD ya rakoshi amma yaki yace sai dai yaje da kansa idan yaga kamun ludayinsa sai ya rakoshi gaba, baran baran sukayi akan haka, still yaki biyoshi dan har mota ya rakoshi yana tsokanar sa yayi masa banza yayi tahowar sa bayan ya karfafi kansa akan zai iya, sai gashi ya rasa duk kalaman bakin nasa da yayi ta tsarawa a cikin kansa tun jiya, amma ya nemi guda daya sam ya rasa. Kiransa akayi, hakan ya taimaka wajen rage shirun da wajen yayi

"Kana da matsala wallahi."  Yace

"Ban sani ba, idan abinda ka kira ka tambaya kenan, toh zan kashe."

"A ah tsaya, Mr love karka kashe dan Allah, kira nayi dama na tuna maka da ka bar note din da ka rubuta na abinda zaka ce idan kazo, bani address na kawo maka yanzu."

MD yayi saurin tsaida shi yana danne dariyar sa.

" I have no time to waste, sai anjima malam! "

Ya kashe wayar yana murmushi, idon su ne ya hadu lokaci daya, tayi saurin janye nata gabanta na sake bugawa da karfi, shi kansa sai da yaji wani abu me kaifin gaske, ya sake

14 / 30