RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 30

9K to 12K   out of 87.6K words

yi, dan a kalla ya kamata ace an shirya sosai, basu ji dadin short notice din ba amma kuma babu yadda za'a yi haka za'a je din dan be kamata a bar ta ita kadai ba babu yan gidan su.
   Kamar yadda yake a al'adar Malam bahaushe bayan daurin aure ana zuwa angwaye su gaida iyayen amarya suyi musu godiya, bangaren Adam kuwa da abokan sa suna chan hotel din da aka sauke su, Adam na tare da Fido, dan ko daurin auren be je ba, dan dama yace in dai a Sumailan za'a daura ba zashi ba, sai abokan sa uku kawai ne suka je dama suma duk target dinsu na ga dinner din ba wai daurin auren ba, musamman da aka kaishi har Sumaila ba zasu iya bin hanyar ba balle su sha wahala shiyasa sukayi zaman su har aka dauro aka dawo, aka aiko musu da abinci suka ci sukayi nak sannan suka soma shirin shiryawa dan su shiga gidan su Adam din sannan su rakashi wajen Amaryar tasa bayan ya samu da k'yar ya lallaba Fido ta tafi, jin sa yake yau babu ya shi dan zai gwangwaje sosai, sai kuma yi maganin tsiwa da rainin ta, dan bata kai matsayin da zata gaggasa mata magana anyhow kuma ya zuba ido ya kyale ta, dole sai koya mata hankalin da ba zata sake ba.
    Suna shiga cikin gidan nasu aka yi musu cha ga ango ga ango, yan uwa sai faman tsokanar sa ake, yana washer baki tamkar gonar auduga, da sun san dalilin da yasa yayi auren nan da basu taru haka ba, so yake da gaske ya dauke hankalin kowa daga kansa, ya sheke ayarsa babu me saka masa ido, ya kuma rabu da mitar Maman na kullum yaki aure, shiyasa ma be yi wani dogon tunani akan hukuncin sa ba, dan dai shi yasan ba son ta yake ba, tana dai da abin da yake so a tattare da mace, amma batun kyawun fuska yafi son fara sosai, ita kuma tana da duhu musamman da take cikin fararen tas dan duk yan uwanta sun fita haske hakan ya saka ake ganin har kyau din ma sun fita. Jingina dogon tunanin da ba zai amfane shi ba yayi, suka shiga dakin Mama in da take tare da manyan kawayenta, ai sai kawai ta rungume shi cikin farin ciki, baka jin tashin komai sai gud'a da sambarka, ita kadai tasan yadda take ji da auren nan nasa, a kalla idon mutane zai bar kanshi, kuma tana fatan Asma'u ta shirya mata shi, ya bar duk wata banzar al'adar sa, dan ita a ganin ta ma, idan har mace ta kasa daidaita dabi'u da al'adun mijinta, zuwa nata da take so to tabbas bata kai mace ha, ko tace ma kawai ta rako mata duniya ne. Sun dan jima a dakin sannan suka fito suka rankaya gidan Abban.
   Sanye yake da riga jamfa da wando babu batun babbar riga dan babu ita a tsarin sa, musamman lokacin zafi ne ko da Mama tayi masa magana sai yace mata ai tana mota zai saka idan sun fita, nan kuwa ko dinka ta be ba, hula ma dan dai kawai babu yadda zai ne, amma tabbas yana dawowa zai cire kayan dan ba zai iya ba, saukinta ma a dinner din suit zasu saka da ace manyan kayan zai sake maimaitawa toh da an samu matsala dan shi a rayuwar sa baya son abinda zai zo ya takura masa.
   Sanda suka isa gidan sauran yan daurin auren basu gama watsewa ba, da yawan su ma suna zazzaune ne a kofar gidan an saka rumfa suna shan iska ana hira cike da Raha, yawanci su yan Sumailan ne sai yan tsirari da suke abokan Abba. Shi kansa Abban yana wajen tashi yayi ya amsa waya ya dawo.
    Labarin isowar angwayen ya riski cikin gidan, aka shiga shisshiryawa shigowar tasu, asma'u da taji abun daga sama sai da taji wani ras a kirjinta, tayi saurin dafe shi ta mike tana kokarin neman hanyar ficewa daga gidan, tun dazu umma take sababin su koma gidan Safiyya a aiko musu da abinci amma ya makale a dakin Umman taki fita, sai gashi yanzu tana son fitar amma bata san yadda zatayi ba, dan dole idan tace zata fita sai sun ganta, abinda ita kuma bata so kenan. Ganin take taken ta na son guduwa ya saka Aunty Hauwa ta dakatar da ita, ala dole ta dawo ta zauna tana kudundunewa a cikin mayafin ta.
    Hargowar su ta fara jiyowa alamun sun shigo ciki, tana jin wasu mata da bsta gane su waya ba suna ta tsokanar su,su kuma suna biye musu, irin dai wasan jika da kakan nan, shine a gaba wajen zakewa da amsawa tamkar bashi ba, kamar ba ango ba ma dan babu wata alama da zata nuna a jikinsa da zaka gane ango ne, tana jin sanda suka dungumo suka shigo falon umman, lokacin su Aunty Hauwa duk sun fita falon, nan dai akayi addu'a wanda aunty hauwan ce ta assasa da babu me wannan tunanin a cikin su, sannan suka yi waje suna cigaba da hayaniyar su. Wani ne cikin abokan ya tabo shi, yace

"Ina amarya ne?"

" Ba za'a hadu wajen dinner ba, kyale ta kawai pls."

" Ok."

" Ku jirani a waje ina zuwa." Yayi hanyar dakin su Abbati, suka sheke da dariya, wato ba zasu ga Amaryar ba amma shi zai ganta, ba komai ai akwai anjima. Waje sukayi shi kuma ya shiga dakin ya tarar dasu da abokan su, Abbati yayi saurin tashi suka gaisa sannan yace ya taimaka ya kira masa ita, fita yayi sauran abokan ma suka fita ya zama sai shi kadai a ciki, a tsaye yake be zauna ba, da ba dan ace yana so ya kara jaddada mata maganar dinner din ba , da babu abinda zai saka shi nemanta, tunda dai an daura ai shikenan, duk ma abinda take tunani ko ji dashi zasu gauraya ne, daga shi sai ita yadda zai nuna mata shi din gogaggen dan duniya ne, idan aka ce ta sake gaya masa magana ma ba zata sake ba.
   Sanda kiran ya isketa kusan shidewa tayi, bata hango rangwame wajen Adam ba, shiyasa bata son duk abinda zai hada su waje daya daga shi sai ita, narai narai tayi da fuska, kamar zatayi kuka dan har kwalla ta cika mata ido, ganin yadda ido ya dawo kanta ya sakata tashi ta bi bayansa, duk taku daya da take ji take kamar ta saki fitsari a wando saboda zulumi. A hankali ta tura kofar sai kuma ta tsaya ta kasa shiga, yana kallon inuwar ta, ya ja tsaki ganin zata bata masa lokaci, ya fizgota da hannun sa ta dawo cikin dakin,durkushewa tayi da sauri jikinta na rawa tamkar mazari. Kallon ta yake yana kokarin ganin ko tayi abinda ya sakata, yana nan zanen kamar jiyan babu abinda ya chanja. Dogon tsaki ya ja, sai yayi maganin ta kuwa, yanzu ba wannan ne ya kawo shi ba tukunna

"Ina kayan da na bawa Abbati ya kawo miki?"

Shiru tayi, ya sake maimaitawa bata amsa ba, sai da ya daka mata tsawa me karfi sannan tace a kidime.

"Suna wajen Hidaya."

"Ok." Yace yana matsowa daf da ita, ya daga ta gami da fizge mayafin da tayi lullubi dashi, ya rage daga ita sai tsuran kayan jikinta, riga ce fitted da skirt da yayi daidai da jikinta, bin ta ya dinga yi da wani shu'umin kallo, ya lashe lips dinsa na k'asa yana kallon saman kirjinta, hannu ta sa da nufin karewa ya sa karfi ya murde hannun har sai da tayi kara.

"Baki isa ki hanani abinda na saka kudi na siya ba, karki sake idan ba haka ba, zaki fuskanci hukunci me tsananin."

Yawo maganar ta shiga yi mata akai, siya? Kenan ba auren ta yayi ba ma, siyan ta yayi, da lefen kenan ya siye ta ko da sadaki? Bata gama tunani ba sai jin hannun mutum tayi a jikinta, ta firgice tana kokarin guduwa, hannu daya ya saka ya matse ta kam, ya shiga taba ta duk in da yaga dama, kuka take sosai ta rasa yadda zatayi dan ya hana mata ko da kwakkwaran motsi ne, sai da ya ga dama dan kansa, sannan ya ture ta da karfi tayi baya saura kad'an ta fadi Allah ya taimaka ta tsaya a kafarta, be ko kalleta ba ya juya ya fice yana maida numfashi, ba zai iya resisting ba idan ya tsaya, komai zai iya faruwa.
    Durkushewa tayi a wajen ta saki kuka me cin rai, bata taba ganin aure irin nata ba, duk wata amarya a wannan ranar tana cikin farin ciki mara misaltuwa saboda auren wanda take so yake son ta. Sai dai ita akasin haka ne a gareta, babu digon soyayyar ta a tattare da adam, tun tana yarinya Adam be tana kaunar ta ba, be taba tausayin ta ba, illa ma duk sanda suka hadu ko a gida ko a wani waje sai yayi dwewrieiririwroieoei e pie I i a little more Ta yaya zata iya? Me yasa babu wanda yake hango mata abinda take hangowa a gaba, me yasa? Ko kuma dai suna hango matan kawai babu yadda zasu yi ne, musamman Umma da tafi kowa saninta, ita ya kamata tafi kowa tausaya mata, amma sai taga kamar itama bata damu ba. Cigaba da zama tayi a dakin har sai da yamma tayi likis, sai da Abbati yazo sannan aka san tana dakin, dan har hankali ya fara tashi abna tunanin in da taje, idonta ya yi luhu luhu saboda tsabagen kuka, haka dai aka babbata baki sannan ta wuce dakin Abba, kasancewar daga wajen dinner din za'a wuce da ita ba zata dawo ba, nasiha sosai yayi mata wadda ta sake kashe mata jiki, ta kara volume din kukan ta dan kukan ne kadai yake rage mata radadin da take ji a ranta. Shi kansa Abban duk dauriyar da yake sai da yaji ya karaya, hawayen da ita suka tsaya masa a rai, ya nemi dan guntun farin cikin da yayi saura ya rasa, ya dinga ganin baiken sa, da ya barta zuwa lokacin ta, da be yi gaggawa ba. Shi da kansa ya dinga bata hakuri, tayi shiru tana sauraren sa cikin yanayin karaya, umma kuwa kasa cewa komai tayi, har Ya Hadiza ta shigo ta taimaka mata zuwa dakin ta, sannan ta sakata shiryawa saboda dinner din, bata musa ba, dan musun bashi da amfani tunda aikin gama ya riga ya gama, sai dai tana wanka tana kuka sosai, hakan ya jawo mata dadewa sosai a ciki, sai da Rauda ta kwankwasa mata sannan ta fito, suka taimaka mata ta shirya a cikin gown din da ya kawo, gown din da bata da maraba da ta arna sai dogon hannun net da ke jiki, mayafi fari ta dora akai da ya rufe mata duk wajen da yake a bude a rigar, kirjinta da sangalalin hannun ta, takalmin ne dai ba zata iya sak'awa ba saboda ya mata tsayi da yawa, bata ma iya tafiya dashi ba.
   Duk abubuwan bukatuwar ta sun yi gaba kafin ta iso, hatta kayan sawarta da komai rankatataf an kai mata su, yadda ana gamawa zasu wuce chan gidan, dama duk wanda suke da bukatar ganin gidan Amarya sun gani tuni, shiyasa kawai aka yanke shawarar musamman ganin dare zai yi kuma shi kansa Adam din ya fadawa Mama yau yake so a kawota, har su Nadeeya na tsokanar da yayi rashin kunya, yayi kuwa mirsisi yana jin su yayi gaba abin sa. Ita kuwa Mama farin cikin da take ciki ba zai fadu ba, ta hasaso shiryuwar danta, tunda duk alamun sa sun nuna yana son Asma'un, a kalla zatayi galaba a kansa a wasu abubuwan da yawa.
   Tuni wajen ya cika da jama'ar Adam da kawayen Mama sai su Nadeeya kowa da jama'ar ta, sai bangaren su Asma'un suka tashi yan kad'an, duk suka koma suka darare dan babu ma wanda ya nuna jin dadin ganin su, dama basu da yawa dududu su goma ne kawai, sai Asma'un da Rauda da Hidaya, sai kawarta guda daya, zuwan su ne ma wajen ya saka su Nadeeya nuna sun gansu, aka raka amarya wajenta duk kunya ta isheta, kamar ta tsaga kasa ta shige dan ita ire-iren abubuwan nan tun da ma ba zuwa take ba. Tana zama suna isowa cikin zugar su guda, sun sa suit bakake sai uban gayyar da ya saka fara tayi masifar karbar sa kasancewar shi fari sosai. Nan da nan wajen ya kachame. Baka jin komai sai tashin kida me masifar kara da ya saka haifar mata da matsanancin ciwon kai. Zama yayi a gefenta, daf da ita har tana jin jikinsa a gefen nata, kafarta ya take mata bayan ya zauna, ta kalle shi da sauri ya watsa mata harara, tayi saurin tun k'asa da kanta. Tana jin shi ya lalubo hannun ta, ya matse shi sosai har sai da tayi kwalla, ya sakar mata murmushi yana matsowa daf da ita kamar zai fad'a mata wani abu, ta runtse idon ta da sauri, tana jin sanda ya furta.

"Kinyi kyau matar Adam!" Ya saki murmushin gefen nan, wanda shi kadai yasan manufarsa sai ita da take hasashe!

Rayuwar Mace labari ne daya tamkar da dubu, akwai kalubale a rayuwar asma'u, a rayuwar da yawa yawan mata! Amma sai dai me?
Me zai faru? Wanne irin zama ne zai kasance tsakanin ta da shi? Mata da yawa suna zaune da mazaje masu halin Adam ko fiye, amma kullum magana daya ce, muyi hakuri!
  Akwai haske tattare da RAYUWAR ta a gaba, hasken da zai yaye mata dukkan damuwar ta!
   Soyayya me tsafta, soyayya me tsayawa a kalbi! Ku biyo zafafa biyar dan ganin yadda zata kasance a RAYUWAR Mace! Rayuwar Asma'u


_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*



     *RM*
          6


*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._*
__________________________________

_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_

_(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_

_SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_

_KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_

_AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_

_KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_

_WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_

Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous

*_DA SAURAN SU DA YAWA_*

*_Handles_*
*Instagram* @sakina_vendibles *Facebook*
@Sakina vendible *Tiktok*
@Sakina vendibles_


****Zuwan angwayen ya saka aka shiga gabatar da bikin gadan-gadan. Babu abinda take ji sai faduwar gaba a duk sanda ta tuna abinda yake tunkaro ta, suna nan zaune aka fara kiran amarya da ango su fito fili. Murmushi ya sakar mata ya miko mata hannu, ta kalle shi a tsorace, ya sake sakar mata murmushin sannan ya kama hannun nata ya mikar da ita, suka shiga takawa zuwa filin tamkar tsofaffin masoyan da suka jima da kaunar junan su.
   Sun jima a filin shi da abokan sa na ta tikar rawa, taji jiri kamar zai debe ta, ta daure kanta na k'asa amma tayi matukar gajiya, yana ankare da ita yana sane kuma suka cigaaba da abinda suke, sai da ta gama gajiya likis sannan suka koma suka zauna, ta  kalle bangaren da su Hidaya suke, suka hada ido ta marairace fuska, tasowa suka da Rauda suka zo wajen ta, suka zauna a side dinta sai taji kamar an yaye mata dukkan damuwar ta, hira suke mata k'asa k'asa, hakan ya sakata warewa har tana murmushi, nan fa su ya Hadiza ma suka taso suka hawo wajen, daukar hoto. Tasowar yan gidan su ya sakata mantawa da shi da existence din sa a wajen, ta sake sosai har sai da mc yace ya isa haka su koma sannan suka koma amma ban da Rauda da ta rikewa hannu kam ta hanata tashi, sai kawai ta cigaba da zama a gefenta da yake akwai spare kujera a wajen.
   An dau lokaci sosai har su Ya Hadiza suka fara deciding kawai su tafi, basa son barin ta ita kadai amma dare yana yi musu sosai hakan kuma ba sabon su bane, bayan haka dukkan su da mazajen su, gashi duk ba gidan umma zasu koma ba sai gobe zasu koma. Waya Hidaya ta kira Rauda daga wajen zaman su, ta daga amma

4 / 30