Author : RANO Category : African Stories & Novels
da Abbati, suka baje su a tsakiyar dakin, suka ci sukayi nak, Raudan take ce mata anan zata kwana yaje garin su shima achan zai kwana sai da safe zai biyo su wuce, umma ce ta leko tace Abba yana kiran Asma'un, ta tashi zata dauki hijab dinta sai a lokacin Rauda taga jacket din, ta bita da kallo har ta fice kafin ta tashi ta haye gadon.
Dawowar sa kenan Abban ta shiga da sallama, yana tsaye ko zama be ba a tsakiyar falon, zamewa tayi k'asa ta gajshe shi, ya amsa cike da kulawa irin ta da da mahaifi, sannan yace
"Adam bashi da hankali sam, bansan haukan nasa ya kai haka ba, nayi magana da Alhaji Ibrahim dan dama saboda a samu damar shirye-shirye nace musu sati biyu, yace in dai akan abinda za'a zuba ne na kayan daki su ba'a yi musu, miji shi yake zuba komai, dan haka ko yanzu muka ce Abdallah yazo zaizo ya dauki matar sa, toh amma na shawarci mahaifiyar ki gata nan, tace dai dan Allah a barki ko kwana uku ne ko sati, akwai abubuwan da zasu karasa naku na mata, dan haka ni yanzu magana bata hannu na, tana hannun mijinki idan har ya amince shikenan, idan be amince ba, gobe yazo ya dauki matar sa."
Kamar an buge mata kafafu haka taji maganar ta Abba, ta zauna sosai a dakin ta gaza dago kanta, tana jin Abban ya cigaba da kokarin chanja channel din TV, umma kuma ta fita ta sake dawowa tana nan a zaune bata san me zata ce ba, sai da ya zauna sosai sannan yace
" Ki nemi izinin shi idan har ya amince bani da matsala, yadda kukayi dashi sai naji idan Allah ya kaimu, Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya, ayi hakuri dole baa cin ribar rayuwa sai da hakuri, bani da haufi akanki amma dole sai kin kara hakuri akan wanda kike dashi a dah, Allah yayi miki albarka."
Wani kuka ne ya taso mata, a karo na biyu amma na sake bada ita ga wani tamkar yadda ya faru a farko, sai dai akwai banbancin na farkon da na biyu, kuka ta soma yi ba dan bata son auren ba, sai dan tana jin kamar Abban ya gama mata komai, kamar ita shikenan kuma, tasan zata shiga sabuwar rayuwa ne me banbanci da rayuwar gidan Adam, bata san da wani kalubale zata zo mata ba, amma koma wanne iri ne tana fatan ta samu sassauci a cikin sa.
Tashi tayi bayan tayi ma Abban godiya ta fito, ta samu umma a dakin ta, tana zaune tana jiran fitowar Asma'un, tana shigowa ta ce
" Ki lallabashi ya barki ko satin ne, kinga akwai gyaran da ya kamata ki samu ko? Ki lallabashi dan Allah dan har Yarku ta biya kudi gobe za'ta fara aikinta."
" Umma toh me zance masa?"
" Kice masa dai akwai shirin da baki gama ba."
" Shikenan, zan fada masa."
" Karki kauron baki Asma'u na san halin ki, taimakon ki ne."
" Ba zan ba Umma."
" Yawwa, Allah ya baku zaman lafiya, wai yanzu Abban ku da ya shigo yake cewa Adam na asibiti, kamar wai jininsa ma ya hau a yadda likitoci suka ce."
" Allah ya bashi lafiya."
" Toh Amin."
Tare suka fito da Umman ita tayi dakin Abba ita kuma ta wuce nasu dakin tana sak'a yadda zata tambaye shi dan ta lura zai iya ki musamman yaji cewa Abba ya barshi shi zai yanke hukunci, dakin ta shigo Rauda ta hau waka
"Soyayya dadi, tafi zuma dadi, kinga yadda rigar nan tayi miki kyau?"
Sai lokacin ta tuna da rigar jikinta, ta harari Raudan kunya na kamata
"Yar sa ido, wai me ma yasa ya barki ki kwana ne?"
"Ai dakin umma ma zanje na kwana kar na hanaku more daren."
"Kyaji dashi." Tace tana isa gaban mirror ta dauki wayarta da ke kai ta zauna ta rubuta masa text message ta tura bayan ta goge ta sake rubutawa wajen sau uku, da k'yar ta daure ta tura na karshen, yana shiga ko minti daya baa yi ba, yayi reply
"Ban amince ba, ki shirya gani na."
Saroro tayi rik'e da wayar, ta kalli Rauda ta fara fad'a mata yadda sukayi da Abba, dariya ta saka tace mata
" Ki kirashi Allah, ki marairace masa zai hakura. "
" Zan iya? "
" Sosai ma, kiyi sauri kar yace gashi a waje. "
Tashi tayi da sauri ta koma dakin umma da ba kowa, ta kirashi tana rik'e da kirjinta da yake faman dukan uku uku, sai da ta kusan katsewa sannan ya dauka yana kishingida bayan ya ajiye cup din da yake shan bakin shayi a cikin sa.
" Wife? "
" Umm, dan Allah kayi hakuri kar kazo? "
"Kar nazo? Me yasa? Gani a hanya ma ki shirya kinji? "
" Dan Allah kayi hakuri, na shiga uku. "
" Baki shiga uku ba, kina tare dani wanne shiga uku zaki? "
" Ba zaka zo ba ko? "
" Yanzu kuwa, na ma fito ki shirya ina zuwa sai tafiya, wow I can't wait to have you in my arms, yadda gari yayi dadin nan.... "
Toshe bakin ta tayi da sauri tana ganin tsantsar rashin kunyar sa, magiya ta cigaba da yi masa yana sake biye mata, da gaske ta dauka zuwan zai sai da yace mata wasa yake amma kwana uku kawai, tace dan Allah sati, da k'yar da magiya kamar zata masa kuka ya hakura amma sati daya kawai, ajiyar zuciya ta sauke tayi masa godiya, yace baya son godiya sai dai ta bashi wani abun, shiru tayi tana tunanin me zata bashi, yayi breaking shirun nata ta hanyar cewa
" Sai kin ce I Love you Abdallah sau goma, shine na kara yarda da sati amma idan baki fad'a ba, kwana uku kawai na yarda. "
"Tirkashi. " Ta furta tana rik'e haba,
" Zan kashe, idan kin shirya zan kira dan dai Allah kawai dan an fi karfi na ne, da yanzu zan zo wallahi. "
" Zan fad'a toh."
" Oya, na bud'e zuciya ta, da kunnuwa na. "
" I lo... ve.. ueeew. "
" Ni a hade. "
" I love you." Ta fad'a kamar wdda aka hankada, ta kashe wayar da sauri tana kifa ta, sai kuma ta saki murmushi tana jin wani sabon so da kaunar sa na ratsa ta, so me zafin gaske.
Kyalkyalewa yayi da dariya cike da mamakin ta, kunyar ta tayi masifar yawa, dole sai ya koya mata yadda zata so shi, har ta iya kallon cikin idon sa ta fad'a masa irin son da take masa. Shafa kansa yayi yana bud'e gallery dinsa , ya shiga folder din hotunan da yayi mata dazu, ya dinga zooming dinsu yana karewa dan mitsitin bakin ta da yake tunanin yadda chokali yake shiga kallo. Tunanin moments din dazu ya shiga yi, softness din lips din su suka fi tafiya dashi fiye da komai, ga wani warmness da yake ji duk sanda ya samu close contact da ita.
RM*
36
***Dakin ta koma ta samu Rauda har tayi bacci, cike da tausayin ta, ta gyara mata gefen gadon dan daga gani baccin dauke ta yayi babu shiri, wajen kayan ta, ta nufa ta zauna tana rarrabe su tana hade wanda data hada waje daya, har ta kammala sannan tayi shafa'i da wutri taje dakin umma ta dauko katifa ta saka a k'asa ta kwanta ba dan tana jin bacci ba, tunani ta shiga yi, tana ganin komai tamkar almara, kamar ba ita ba, tasan a aji da komai Abdallah ya fita yayi mata fintinkau, bata taba kawo irinsa ko kwatankwacin sa a irin mijin da zata aura ba, sai dai kuma tasan komai hukunci ne na Allah, duk abinda Ya tsara shine daidai. Wato ita rayuwar baki dayan ta challenges ne, daga wannan sai wannan. Juyi ta dinga yi har ta samu bacci barawo ya kwashe ta, me cike da mafarkan Abdallah.
Da wuri Ya Hadiza ta kira Umma tace Asma'un ta shirya Amaryar Kb zata zo ta fara yi mata idan Abban ya amince, zuwa umma tayi dakin ta tarar da Asma'un a zaune tana tilawa, Rauda kuma na bacci,
"Umma ina kwana?" Ta gaishe ta bayan ta kai karshen shafin,
"Lafiya lou, Rauda bata tashi ba!?
" Komawa tayi, tace bata jin dadin jikinta ma. "
" Yanayin ne, ga watan haihuwar ne kinsan sai a hankalin, idan tana jin ciwo dai tayi magana. "
" In Sha Allah. "
" Ya kukayi dashi? Abban ku yana jiran feedback
"Ya bari, sati daya wai."
"Yayi ai, anjima kad'an Amaryar Kb din zata zo, sai ta fara, idan yaso juma'a sai ayi walima kawai."
Juyawa umma tayi, tace
"Anjima sai kizo ki sanar da Abban dan yanzu be tashi ba."
"Ok tam."
Fita umman tayi ita kuma ta cigaba da karatun ta, sai da tayi daya cif sannan ta ajiye ta fito zuwa kitchen domin taga abinda zai samu na breakfast kafin Rauda ta tashi dan wasu masu ciki akwai saurin jin yunwa.
Wajen tara da rabi Abba ya kirata, ya tambaye ta yadda sukayi ta fad'a masa, Madallah kawai yace ya fita, ta koma daki tana zama Amaryar Kb na zuwa, ta jiyo muryar bakuwa suna gaisawa da Umma ta tashi ta leka ta window. Rauda na toilet tana wanka umma ta kwala mata kira, ta tashi da sauri ta fita, ta gaida Amaryar Kb din ta amsa tana tsokanar ta dan ta gane ita ce amarya, dakin Umma aka kaita Asma'un na zaune a gefe ta hada komai da zata bukata a gefe, Sudanese Scrub/Dilka aka fara mata cike da kwarewa irin ta gogaggun wanda suka san ta kan gyara ciki da waje, ita kanta ta yaba yadda take aikin nata balle ga Rauda a gefe tana sake kurantawa, tun kafin ma a gama na ranar kamshi ya bad'e ko ina na dakin, zuwa gabatowar azahar suka gama lokacin Rauda ta tafi sai Asma'un kawai da Umma a gidan, sallama suka ji ana kwalawa, umma dake zaune a kujerar dake kan hanya ta amsa tana zura kanta waje, Nadeeya ce tare da Fadeela sai wata yar uwar su Abba da take zuwa idan ta bushi iska daga Sumailan take zuwa tayi musu kwana biyu ta tafi, tashi umma tayi ganin masu sallamar tana musu lalle da zuwa, kunya Nadeeya take ji tun sanda adam ya saki Asma'u kamar ita tayi haka take ji shiyasa bata taba iya sakewa da su musamman Asma'un da suke shiri amma yanzu ko doguwar magana basa yi, yanzu ma Hajiya Mama ce tace suzo su kawo Inna balkin daga nan sai ta samu damar magana da Asma'un, ta farko bata so ba amma ganin halin da Adam din yake ciki ta saka ta zuwa, dan akwai hakkin ta sosai akan adam idan bata yafe masa ba haka zai ta shiga masifu dan ta cutar dashi, yanzu ma a kwance yake asibiti tun da ya samu labarin auren Asma'un ya fita hankalin sa har suma yayi.
Tashi Asma'u tayi daga zaunen da take, suna shigowa tayi hanyar fita bayan sun gaisa dasu, dakin ta, ta shige tana jin wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikinta, wayarta ta dauka ta shiga whatspp tana dubawa, yau be kirata ba tun dazu take dakon kiran nasa amma ko da ta dawo dakin ma ta dauka zata ga missed calls dinsa amma sai taga babu komai, gashi ita ba abin ta kirashi ba, kunya ba zata barta ba, cigaba da dakon kiran nasa ta yi tana fatan ya kirata nan kusa, kwala mata kira Umma tayi, ta tashi ta ajiye wayar ta sameta a waje
"Ki shiga wajen su, zakuyi magana da Nadeeya, ashe Adam din ma yana asibiti ba lafiya, Allah ya bashi lafiiya."
"Amin."
Tace tana shiga ciki, ta samu Nadeeya ne kawai da fadeela a dakin babu Inna balkin, tun kafin ta zauna Nadeeya ta soma mata magana
"Dan Allah Asma'u ba dan ni ba, dan Allah ki yafe ma Adam abinda yayi miki dan Allah, soyayyar ki zata haukata shi, he's insane har baya iya tantance daidai da ba daidai ba, nasa yanzu ke matar wani ce, ba kuma na miki fatan sake dawowa wajen Adam a karo na biyu ko da bakiyi aure ba, duk da ina da yakinin ya shiryu, amma bana miki fatan zama dashi. "
" Ba komai fa Allah Ya Nadeeya, ni ban rik'e shi ba, Allah ya bashi lafiya. "
" Ki yafe masa dan Allah,. "
" Na yafe masa duniya da lahira, Allah ma muna masa laifi ya kuma yafe mana, kuma Allah yana son mutum me hakuri da yafiya, ina masa fatan alkairi. "
" Nagode sosai Asma'u, hakika Adam yayi rashin mace ta gari, ina miki fatan nasara a dukkan al'amuran ki, ya baki zaman lafiya da zuria dayyiba, idan na samu time zanzo naga dakin ki. "
" Nagode sosai. "
Tafiya sukayi suka bar Inna balkin anan, daga nan asibitin suka wuce suka tarar da Adam din a cikin mawuyacin hali, Fido ce a dakin kawai mama taje gida ta dawo, bata kula su ba har suka zauna, ta cigaba da danna wayarta dan bata jin ko digon tausayin Adam din musamman da aka ce akan mace ne yake wannan ciwon, jira take kawai ya dawo gida ya fara cin ubansa dalla dalla a hannun ta, dan ta samu tabbacin aikin yayi kuma zai fara aiki ne da zarar ya gama ciwo ciwon son nasa. Turo kofar akayi, ta tashi ta taro su, su Faiza ne su uku, suka hau hayaniya a dakin kamar ba dakin mara lafiya ba, tashi fadila tayi ta fita, Nadeeya ta kalle su tace
"Ku dan rage muryar ku dan Allah, baa son hayaniya musamman shi da jinin sa ya hau, hakan zai hana jinin sauka."
Kamar wadda tayi magana da duwatsu haka suka maida ta, suka cigaba da shewa shewan su da hirar su mara amfani, ranta ne ya baci ta kalli Fido din tace
"Fiddausi ki kaisu waje su zauna baa son hayaniya akan mara lafiya."
"A matsayin ki nawa? Mijinki ko nawa? Ko dan kin tsofe a gida baa da aiki sai gantali a kwararo shine zaki min bakin ciki dan kinga ni nayi auren?"
"Ikonn Allah,."
"Ikon gaske, idan ta miki zafi sai ki kaini gaba. "
" Allah ya kyauta. "
Tace ta bar dakin da ba zata iya dasu ba, tana fita Hajiya Mama na dawowa tare da yar aikinta ta riko kayan abincin, a wajen ta ajiye kayan ita kuma Maman ta shiga dakin, babu wanda ya nuna alamun mutum ya shigo bare su daidaita kansu,
Matsowa tayi tana kokarin duba Adam din amma sai Fido din ta babbake wajen tana tauna cingam ta gefen bakin ta
"Fiddausi ya jikin nasa." Tace bayan ta matsa baya
"Gashi nan ai." Ta sake juya kanta gefe
Dan jim Hajiya tayi a tsaye, sai kuma ta juya ta bar dakin dan mugun shakkar yarinyar take ji, har bata iya yarda su hada ido sam, maganar ta samu Nadeeya da Fadila na yi, taki saka baki sai ma ta saka sallaya daga gefen su tayi zaman ta, su kansu sun gano bata son laifin Fido din ko kad'an, gashi ita kanta bata raga mata bare su.
***Kwana hudu da fara gyaran jikin Asma'u ta chanja, tayi wani irin masifaffan kyau, kamar ba ita ba, ga wani kamshi me sanyin dadi da ke tashi daga jikinta, ko gifta ka tayi sai kaji shi gwanin dadi, tun bayan zuwan da Abdallan yayi be sake zuwa ba dan ya gane zuwan nasa akwai matsala, sai dai waya da chatting da suke kusan raba dare suna yi, a yan kwanakin suka sake shakuwa da juna shakuwa ta ban mamaki.
Da safe yana shiryawa yaji ana danna masa door bell, sai da ya gama fesa turare sannan yaje ya bude ya tarar da Ihsan a tsaye har ta soma kosawa da jiran sa ta kuma san yana ciki dan motar sa tana nan,
"Ya akayi?"
"Anty faty ce tace idan ka shirya ka shigo ciki."
"Tazo ne?"
"Eh dazu tazo ita da Anty Asy."
"Ok zanzo." Ya maida kofar ya rufe, ya karasa shirin sa a tsanake sannan ya fito ya shiga gidan, tun daga shigowa ya hangi manya manyan akwatunan na alfarma a ajiye a gefe, sai wasu yan kwanduna masu kyau da akayi musu ado da purple kyalle, zama yayi yana kallon kayan, suka gaisa sannan Anty Faty tace ya duba kayan ne, anjima zasu je su kai da rana.
Sama sama ya kalla dan ba zai iya tsayawa kallon komai ba, yace yayi kawai suyi duk abinda suke ganin ya dace, daga nan ya wuce ya gaida Mami tayi masa maganar events din da zasuyi idan Asma'un ta tare, sama sama itama ya jita dan ba wani interest yake dashi akai ba dan ma sun kafe dan har sun yi gayyata da komai hatta hall da komai dai sun gama tanada, dakin Mom ya shiga ya sameta a gefen gado me aikin ta na shirya mata kaya a cikin wardrobe din. A k'asa ya zauna ya gaishe ta, ta amsa masa cike da kulawa sannan ta tanbaye shi Asma'u, kamar ya bud'e rami ya shige dan kunya dan tunda aka fara maganar bikin bata ce komai ba, ya zata ma bata sane da komai ashe tana ankare, sai tsabar kara da kawaici irin nata da ta bar Mami akan komai dan tasan zatayi abinda ma yafi natan, hatta Faty da Asy kannen ta ne amma yadda suka shaku da Abdallan zaka dauka ma yayyen sa ne, shima kuma yana respecting dinsu kamar yayyen nasa na gaske. Nasiha ta hau yi masa akan aure da abinda ya dace mutum yayi a matsayin sa na wanda Allah ya bawa shugabanci, sosai maganganun suka ratsa shi, ya kara fahimtar aure ya wuce duk yadda mutane suke tunani ko hasashe,godiya yayi mata ta dinga saka masa albarka sannan ya baro dakin bayan ta bashi dabinon ajwa guda bakwai tace ya cinye su maganin sihiri ne.
Har ya bud'e motar sa zai shiga ya tuna da gift din Asma'un da yake so a tafi mata dashi, komawa yayi part dinsu ya dauko box din me dauke da spare car key din da