Author : RANO Category : African Stories & Novels
zuwa in da yake ba, sai yayi gaba kawai ya je ya samu daki a hotel ya biya kudin sati dan idan ya zauna a gidan su ma surutun Mama da mutane ya isheshi
***Duk yadda Hajiya Mama zatayi wajen boye masa maganar auren Asma'un tayi, ta kuma hana kowa gaya masa idan yayi mata maganar sai tace suna magana da Abban ne komai ya kusa daidai ta, hakan ya sakashi rage damuwar da yake ciki har yake tsayawa yayi wanka ya gyara jikinsa, tsakanin sa da Fido tun ranar da suka saida hali, tasan guduwa yayi, sai ta rabu dashi tana tama shi dan saura kiris ya shigo hannun ta,daga nan ne zai gane shi din karamin dan bariki ne dan sai ta zame masa tamkar rakumi da akala.
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
*RM*
33
****
Rauda ce ta fara zuwa tana kwance tana bacci bayan tayi sallar asubah ta koma sai ji tayi an danno kanta, ta bud'e idon ta tana ayyana Rauda din ce, da sauri ta tashi tana dubata
"Amma Allah Rauda baki da kai sam, wai bakya jin nauyin jikinki ne?"
Turo baki tayi tana dariya
"Farin ciki ne wallahi, babu fa abinda nayi na fito zai tafi office yace nazo ya ajiye ni, yasan ba zan iya zama ba shima."
"Shi yake biye miki ma Allah."
"Ina umma?"
"Wai bata san kinzo ba ma?"
"Ai direct nan nayo, nasan tana dakin Abba luf zan sai ya fito ya tafi kar yayi min fad'a."
"Aikuwa sai na fallasa ki."
Tace tana sakkowa daga gadon tayi hanyar toilet
" Ki rufan asiri dan Allah, kinsan Abba fad'a zai yace na fito na bar shi."
" Aifa sai na fad'a."
Ta shiga ta kuskure bakin ta sannan ta dawo ta zauna a gadon tana fuskantar Raudan
"Yaushe zai zo?"
"Wa?"
"Yaya Abdallan."
"Ban sani ba, kin karya?"
"Banci komai ba fa, me akayi ne yunwa ma nake ji."
"Nima yau umma bata tashe ni ba, bari na dubo mana kitchen din muga."
Mike kafa tayi ta saka pillow a bayan ta bayan Asma'un ta fita, ta dauki wayarta ta shiga call log taga wayar da sukayi da shi, murmushi ta saki tayi saurin ajiye wayar ganin sako ya shigo alamar text kuma shi ya turo, dadi take ji sosai Asma'un ta samu me.sonta da gaske, halin ta na kirki yafi dacewa da miji na kirki na gari, jin ta dawo ya saka tayi saurin kife wayar tana kallonta dauke da flask da cups ta ajiye sannan ta koma ta dauko sauran kayan, kunu da kosai ne Umman tayi hade da taimakon sabuwar me aikinta da tayi bayan bikin Asma'un, sakkowa tayi da k'yar suka yi breakfast din suna hira, sannan Asma'u ta sake kwashe kayan ta maida kitchen, ta wuce dakin Abba dan ta gaishe shi, ta same shi ya shirya yana cin dumamen tuwo da Lipton da ya zamar masa al'ada, fuskar sa ce ta fad'ad'a da fara'a cike da farin ciki ya amsa gaisuwar ta yana dorawa da tambayar babu matsala ko? Be ga wani abu tattare da ita da zai nuna masa rashin amincewar ta ba, hakan ya kara masa karfin guiwa ya bita da addu'ar fatan nasara a dukkan al'amuran ta na rayuwa, sannan ya jawo drawer sa ta falo ya ciro sadakin ta ya mika masa
"Ga sadakin ki nan Allah ya baku zaman lafiya."
Kin karba tayi, ta tashi zata bar dakin yace dole ta dawo ta dauka saboda hakkin ta ne, ganin ya dage sosai ya sakata dukawa a kunyace ta dauka sannan ta sake mika masa
"Abba gashi toh ko za'a yi wani abun dashi, ni babu abinda zanyi dashi."
Girgiza kai yayi yana kin karba
"Hakkin kine, abun da za'a yi miki kuwa hakki na ne, kamar yadda nayi wa kowa a cikin yayana, dan haka ki je ki ajiye anjima Abbati zai karba sai ya saka miki a account zai miki amfani ko gaba."
Bata da zabi illa tayi godiya ta tashi rik'e da kudin ta fito tana juya su a hannun ta, dakin ta koma Rauda ta mika mata wayarta da sauri sanda kiran ya sake shigowa a karo na uku, tsoron haduwar su da Abba ya hanata kai mata wayar dakin Abba shi kuma ogan be daina kira ba, har ma ta yanke shawarar kai matan sai gata ta shigo,
" Ya Asma'u Uncle Abdallah sai kira yake, gashi nan ya sake shigowa ma kiran."
Hannu tasa ta karba sannan ta jefa mata kudin kan cinyarta tana fita zuwa dakin umma dan bata son yin wayar a gaban Raudan. Sai da ta shiga dakin sannan ta daga tana ji ya shaki iska ya fesar, sannan ya amsa sallamar da tayi masa
"Ina kika shiga ne my wife?"
"Wajen Abba naje, ashe ka kira."
"Eh so nake naji muryar matata kafin na tafi office."
"Uhmm."
"Kar naje na kasa aikin Oga ya sallame ni, kinga ai da matsala ko? Abinki da karamin ma'aikaci."
" Ka iya tsokana."
" Ba wani tsokna, da gaske nake, kinsan yanayin aikin kasar tamu."
" Ummm... Haka ne."
" Toh kin gani?"
Ya fad'a yana danne wayar a tsakanin kansa da kafadar sa, ya duka yana saka socks sannan ya saka takalmi ya mike wayar na makale da kafadarsa har lokacin yana magana k'asa k'asa, brush ya dauka ya sake kwantar da sumar kansa wadda tasha gyara,
"Idan na gama daga office din zai biyo, sai muyi maganar abinda ya kamata ko?"
"Tam shikenan.... Sai ka dawo. "
" Yawwa, take care of yourself for me. "
" In sha Allah."
Tarkacen kayan sa ya dauka bayan ya tura wayar aljihun sa, ya rik'e dayar da tab dinsa a hannu ya fito falon, yasan ba zai samu MD ba dan yace masa yana da sakon da zai karba a airport da duku-duku, dan haka shi kadai ya shiga cikin gidan nasu, ya gaida su Mami sannan ya nufi wajen Baba Alhaji, ya tarar ya koma bacci be tashi ba, sai kawai ya fito ya bar gidan dan dama kunyar haduwar su yake bayan abinda MD din ya shuka masa, yanzu yasan duk wani kallo yan gidan zasu dinga masa bayan shi ba haka yake ba, MD ne duk ya jawo amma shima zai rama ne, yana kallon irin kallon da Mom take masa jiyan nan yasan idan ya dawo sai ta zaunar dashi dole ne, be san me zata ce masa ba dai amma yasan bata da zafi da tsawwalar da zata ce bata karbi auren ba. Be sani ba, tun a jiyan suka fara tunanin hada lefen sa bayan Baba Alhaji da kansa ya kirasu ya basu labarin duk yadda al'amarin ya kasance, kuma duk cikin su dama babu me ja da hukuncin Allah, shiyasa ma yayi komai kansa tsaya dan yasan yayi sa'ar mata na gari masu son duk abinda yake so, shi da kansa ya basu kudi yace a hada wa Asma'un lefe, Mami ce ta karba dan dama itace uwar Abdallan, ita kuma zatayi komai ita Mom yar kallo ce kawai. Aunty Fati ta dora itama akai nan da nan aka soma hada kaya na gani na fad'a a daren aka siya wasu online kafin yau da zasu shiga kasuwa sosai dan ma abin yazo a kure da Dubai Mami zata ta hado lefen Abdallan na nuna sa'a, amma duk da hakan ma zasuyi abu me kyau da tsari.
Yana zaune a office din yana duba wasu motoci ya ga MD na shigowa cikin building din ta cikin CCTV din dake cikin office din wadda take nuna duk shige da ficen da ake a cikin compay, tashi yayi ya murda key a kofar tasa ya dawo ya zauna ya cigaba da aikinsa,kansa tsaye ya murda kofar amma sai ya jita a rufe, ya sake murdawa yaji da gasken a rufe take, sai ya juya a tunanin sa ko Abdallan baya nan, murmushin mugunta yayi lokacin da yaga ya juya dan yasan zuwa zai ya isheshi ya hana shi aikin gabansa gashi yana so yaje yaga matarsa kuma baya so aikin ya kai masa yamma sosai dan so yake ya dauki hutu daga satin da zai kama. Sai da ya gama aikin tas wajen biyu da rabi sallah kawai ta tashe shi sannan ya bud'e kofar ya dauki waya ya kira MD din yace yazo ya sameshi a office da yake building din da suke daban daban ne amma duk cikin gini daya, shi yana bangaren karan kansa shi kuma MD na kula da business din Baba Alhaji
"Na zata ko Amaryar ce a office din dana ga ka saka key ai, shiyasa ma ban zafafa ba na koma."
"Ina sane ai, damu na zakayi ban gama aikin ba. "
" Nima fa aikin ne dani da yawa wallahi, ba zan iya zuwa ba gaskiya. "
" Dan Allah kazo, abu zaka tayani dubawa, kayan sun zo suna nan Lagos, kazo mu duba sai ka zabi daya. "
" Dan Allah da gaske? "
" Idan ba zaka zo ba shikenan. "
" Ah wallahi gani nan, jira ni yanzu zaka ganni. "
" Ok kayi sauri kafin na chanja shawara. "
" Yanzu kuwa. "
Yana ajiye wayar yana shigowa, ashe suna wayar ma yana tahowa, murmushin mugunta yayi masa ya tura masa system din gaban sa bayan sun zauna
" Kai ne mayen mota, ga latest nan, sai ka duba ka bani ta wajenka sai naga nawa zaka cika?"
" Dan Allah da gaske? "
" Oho. "
" Wow..bari muga." Yaja system din gaban sa yana dubawa a hankali har yazo kan wadda tayi masa, wadda dama tun da ya saka order su ya kwallafa rai akanta, juya masa system din yayi yace
" Wannan nake so. "
" Banda ita. "
" Why? Haba Abuya kaifa kace na zaba. "
"Eh amma banda ita, it's for my wife. "
"What?! " Ya mike yana kallon sa
" Abinda kaji, ka duba wata dai ina sauri ne, zan tura ma wani Alhaji ya gani, sai na cire su a ciki
"Amma ai this is not fair, kaifa kace na zaba na zaba kuma..."
"Nace banda ita ba, it's for my wife."
"Ai shikenan, tunda ta fini."
"Wait... Wai ka zata daya kuke dama?"
"Na fita ma nake tunani."
"Tab! Zabi kayi sauri, na gaji da magana, ko ka jira next order idan sun sauka. "
" Bari naga, ita din dai wallahi nake so, haba angon Ma'u, haba Alhaji Abdallah Motors, haba Yaya Abdallah me kudin duk Nigeria, pls pls ka bar min ita, ga ta mata nan masu kyau u can choose one for her, dan Allah, inaso na kare yawa da ita wallahi, akwai wata babe dana tama. "
" Ajiye min system, baka shirya ba har yanzu, kuma wai a haka Baba yake cewa kai kayi min aure, wannan ai insult ne babba, idan baka nutsu ka shiga taitayin ka ba, sai dai kaga ana raba alawa da goro. "
" Auren dole? Zaka min? "
" Oho, ka dame ni kasa ina ta bata baki na, tashi zan kulle office dina. "
" Ina kayi daga nan? "
" Gari zan shiga, karma kace zaka bini. "
" Nima garin zan shiga ai, hanyar ina kayi?"
" Baka zo da mota bane?"
" A ah zan dawo nan ai, bana so na fita da ita ne. "
" Toh ba hanya daya zamuyi ba."
" Why are you avoiding me, ko dai chan zaka? "
" Ina? " Ya harare shi yana tura kofar ya rufo ta suka jera
" Chan din, idan ma chan zaka ni ba zuwa zan ba, ba zaa barni a waje a shige ciki ba, kuna chan kuna shan dimi ni an barni waje, nah nima inada gata na. "
Duka ya kai masa yana dariya
" Allah baka jin magana MD. "
" Ai gaskiya ne. "
" Toh yafi maka ai, nima takura min kake. "
" Yanzu sai ka dawo kenan? Ko gida zaka wuce daga chan? "
" Noo zan tsaya zooroad, zan iya dare ma, anyways muyi waya idan akwai wani abun. "
" Ok, safe! "
Ya saki kofar ya rufe masa ita yana ja baya, juya motar yayi ya fice shi kuma ya koma saman dan ya tattare sauran ayyukan da zai kafin time din da zasu shiga meeting, lokacin ma ya taho shiyasa zai yi sauri yaga yayi rounding up idan yaso gobe sai ya fara wasu kawai.
***Siyayyar kayan ciye-ciye ya tsaya yayi, tare da fresh fruits masu yawan gaske sannan ya tura mata message din gashi nan, suna zaune suna maganar me gyaran jikin da Ya Hadiza zata kira wata neighbor dinta Amaryar Kb da tayi bala'in iya gyaran amarya har ma da uwargida, abubuwan da take siyarwa maganin mata na matsi dana ni'ima, turaren wuta, Khumra turaren wankan, vip humra, oils perfume sannan tana gyaran jiki na amare. Bangaren turaren wuta tana saida irinsu Sandal flakes , Kajiji ,Yellow sandal Mufaddal.Senegalese Kajiji Couscous.
Green sandal,Sudanese mix,Shek Bakhur, Sandal coconut.
Dorot , Hadut, Gabgab,Kajiji balls.
Aroosa da sauran su. Ga kuma maganin infection sadidan, su tsumi, zumar chad da sauran kayan gyara na kankaro mutunci, ga hadaddun khumra masu masifar kamshi da kama jiki, turaren wanka da na gashi, ga kuma na carpet da na curtains musamman a yanayin damunar nan. Amaryar kb Global Enterprise dai ta hada komai na gyara da kankaro mutunci 08067558902 shiyasa ma Ya Hadiza taga ya kamata ta kirata, suyi magana ta gyara Asma'un ciki da waje, ana cikin maganar ne sakon sa ya shigo, shine ta zame ta shige daki ta fad'a toilet tayi wanka a gurguje ta fito ta shafa daya daga cikin khumran da Ya Hadiza ta taho mata dashi na cikin kayan da Amaryar Kb take saidawa ta shafa ta dan shafa powder da wetlips, ta sake bin jikinta ta feshe shi da wasu kalolin turarurrukan masu sanyin kashi sannan ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita idan yace mata yazo, Hidaya ce ta biyota ciki, ta ganta a shirye tsaf tana danna wayar ta, basarwa tayi kamar bata ga shigowar Hidayan ba, juyawa tayi ta tseguntawa su Yaya Hadiza, suka yi dariya har Umma da dadi ya lullube ta, fitar hidayan da kad'an zai ga kiran sa, ta daga gabanta na faduwa yace yana waje, a kasalance tace toh ta tashi ta shiga zagaye a dakin ta rasa ta ina zata fita, kunyar su take ji tana jiyo hirar su a tsakar gidan, kuru tayi ta daure ta fito rik'e da flat shoe dinta a hannu, taki yarda su hada ido da kowa tace
"Umma shine yazo."
"Allah ya kiyaye, ki gaishe shi."
Har tayi gaba Ya Hadiza tace bari ta tsokaneta
"Cewa zakiyi Umma angon yazo."
Dariya suka kwashe da, ta daga kafarta da sauri ta fice taji umma na cewa ya Hadiza ya kyale mata yarta.
Bayan sa ta hanga ya juya shi yana facing din kofar shigowa, dogo ne me cike da haiba, ba shi da rama sannan ba shi da kiba jikinsa dai-dai ya dace da yanayin sa, riga da wandon yadi ne a jikin sa ash colour dinkin rigar daga dan ya wuce guiwar sa, kansa babu hula sai takalmin kafarsa sau ciki, duk a dan dakikun da basu gaza goma ba ta gama tantance shi, takun ta yaji ya juyo da sauri yana rik'e da car key dinsa da babbar wayar sa a hannu, murmushi ya sakar mata ita ma ta maida masa tana russunar da kanta ganin ya kafe ta da kallon sa wanda yake kashe mata jiki, a gefen sa ta tsaya ta gaishe shi, maimakon ya amsa sai ya mika mata hannu alamun su gaisa, a kunyace ta mika masa ya kama hannun ya rik'e yana dan motsa shi acikin nasa hannu.
"Kinyi kyau sosai." Ya fad'a yana kallon lips dinta da suke shekin lips balms, kauda kai tayi cike da jin kunyar sa, har lokacin be saki hannun ta ba, kamar ma hakan na sashi nishadi, ciki tace ya shigo ya noke kafada
"Ban gama kallon ki ba, nan yafi haske na more kallon matata."
"Kai..."
"Emana."
"Dallah malam cika mata hannu! "
Ya buga tsawa idonsa na kankancewa cikin tsakanin tashin hankalin ganin hannun Asma'un cikin na Abdallah, tahowa yayi gadan gadan, wani banzan kallo Abdallan yayi masa ya saka hannu ya matso da Asma'un jikinsa sosai sannan yace
" Don't you dare, karka kuskura ka karaso kusa da matata."
" Matar ka? Yaushe ta zama matar ka?"
" Kaje ka tambaya kaji, kuma wallahi ko kusa da ita na ganka wallahi sai na daure ka kaji na rantse, shashasha kawai. "
A karkace Umar yayi parking suka fito shida Abbati a dari suka fado gidan ganin motar Abdallan data Adam a kofar gidan, suna zuwa suka damke Adam din daya fara hauka yana kokarin jan Asma'un, hannun ta cikin nasa ya shiga takawa da ita, ya nufi gate din gidan ya fita da ita, Adam ya birkice ya dinga kwala mata kira su Abbati suka rik'e shi gam, gaban motar ya bud'e mata ya sakata, sannan ya dawo