RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   29 / 30

84K to 87K   out of 87.6K words

babu kakkautawa, tausyai sosai ya kama Abba, tausayin yadda Adam din ya zama a dan kankaninin lokaci wanda yake kyautata zaton matar da ya aura ce baya jin dadin zama dan babu wanda zai kalle shi ya ce yana cikin nutsuwar sa, sai da yaci ya koshi sannan Abban yace ya taso shi da Umar din suka fita ya kaishi shagon aski yace a sama aski, a mota Abban ya zauna ya barsu da Umar da ya tamke fuska tamau dan ba yadda zai da Abban ne amma mutum irin Adam ba abun a tausaya masa bane ba. Bayan an gama ne suka sake komawa gida Abba ya Shashi yayi wanka sannan ne yace ya fad'a masa abinda yake damun sa. Shiru yayi dan bashi da abin fad'a, ba kuma zai yi gigin fadar laifin Fido ba dan yanzu haka ma tunanin sa yana chan dan dadewar nan da yayi yasan ta neme shi, kuma dole ne ranta ya baci idan ya koma sai yasha cin mutunci.

"Zan tafi Abba, dama zuwa nayi na gaishe ku."

"Ka tabbata babu wata matsala? Yaya tace rabon da ta saka ka a ido tun ranar da aka sallame ka, haka ne?"

"Eh." Yace yana kada kansa

"Adamu mahaifiya ce fa? Kasan halin da ta shiga akan hakan?"

"A ah."

"Toh lallai kaje ka ganta ka kuma bata hakuri."

"Toh in sha Allah."

"Yawwa, idan akwai wani abu sai kayi magana, zan fita kasuwa dama zuwan kane ya dawo damu ciki da tuni munyi nisa ma. "

" Da... Dama.. Abba cewa nayi Asma'u fa? "

" Kana da hankali kuwa Adamu? Baka san Asma'u tayi aure bane? "

" Na sani. " Yace a wani yanayi

" Toh ka fuskanci rayuwar ka, bana son shirme. "

" Tashi Umar muje kar Abbati yayi ta zaman jira. "

Ganin sun tashi ya saka shima ya tashi, suka fito a tare ya riga su fita dan Abba ya leka falon umma yana mata magana Adam din ya fice daga gidan. Yana tafiya a kafa suka tadda shi, Abba yace ya shigo su rage masa hanya yace a ah ba komai, kafin ma ya gama magana Umar ya figi motar, nuna shi Abba yayi yana murmushi yace

"Ka ganka ko Umar? Bana so duk lalacewa Adam dan uwanka ne."

Shiru yayi be ce komai ba, yana hango Adam din yana cin tafiya ta cikin mirror din baya, yayi murmushin mugunta ya sake take motar a ransa yana ayyana kad'an ma ya gani.

***Gaba daya Fido ta rikice tana neman sa, har gidan Hajiya Mama ta shiga ta samu Fadeela a tsakar gida ta tanbaye ta ko Adam ya shigo, tayi mata banza dan dama haushin ta take ji, falon ta leka ko zata ganshi ko takalmin sa amma bata ga alamar shi ba, sai ta fice da sauri tana sake komawa saman ta shiga dakin shi anan taga wayar sa a ajiye akan gado da tayi ta faman kira babu amsa, bata son alakar shi da yan uwansa dan hakan zai kawo mata cikas a aikin ta shiyasa take kaf kaf dashi, dama tun da ba aiki yake ba, dukiyar su da mahaifin su ya bar musu ake juya musu anan yake samun kudin sa na kashewa be san wata wahala nema ba, duk kwanan duniya akwai ribar da ake bashi yana daga kwance a gida yanzu da Fido tazo sai ys zama ma ta hannun ta kudin yake shigowa take yin yadda take so itace mijin itace matar be isa tayi magana ya musa ba.
Yasha wahalar napep duk wanda ya tsaida idan yace har ciki za'a shigar dashi saboda babu kudi a jikinsa sai anje zai dauko sai yaki dan sun fison na hanya, wani ne na karshe ya yarda ya dauke shi Amma shima sai da ya zabga masa kudi haka ya shiga a gajiye tiikis ga uwar ranar da ake yi me shiga jiki. Duk yayi wuri wuri kafin ya isa gidan ga kuma Fido na jiran sa dan akan idan ta me napep din ya sauke shi, ta taho wajen napep din tana kallon gyaran da yayi a kansa da fuskar sa,

"Bani 500."

Yace mata yana kallon cikin napep, cikin rigar ta, ta saka hannu ta ciro ta mika masa ya bawa me napep din sannan ya wuce tabi bayansa cikin rashin gansuwa da yanayin sa, na rashin gaskiya. Bata barshi ya shiga falon ba ta tare shi ta hanyar yin sauri tasha gabansa ta babbake kofa

"Ina kaje?" Ta kafe shi da kallo

"Aski naje nayi da gyaran fuska, baki gani ba?"

"Shine ka dade haka, har da hawa napep da tsada haka? Malam karka raina min hankali mana."

"Baki yarda ba? Bayan ga shaida nan kin gani."

"Ban yarda ba kuma ba zan yarda ba , sai ka fada min inda kaje har ka dade haka nayi ta neman ka, baka kuma tafi da waya ba."

"Nace miki aski naje, wajen tsohon me aski na. Akwai layi shi ya sa na dade wayata kuma manta nayi har ma wallet dina, baki ga sai da nazo na karbi kudin ba, hadda na askin zuwa zai ya kaiwa me asken 300 shi kuma ya rik'e 200 na kawo ni da komawa."

Wani banzan kallo tayi masa, bata yarda dashi ba amma for now bata da hujja, matsa masa hanyar tayi ya shige tabi bayansa kamar wata uwarsa.

***Kiran Abba ne ya shigo wayar Maman tana rik'e da wayar bayan sun gama magana da Nadeeya, dagawa tayi ta zauna suka gaisa yake ce mata Adam yazo, sai data zabura kamar bata ji dai-dai ba, ya sake maimaita mata sannan ya fad'a mata yadda sukayi, godiya ta hau yi masa da sa albarka, hadda hawayen ta dan dadi, naka sai naka dai, babu wanda zai iya mata abinda Abban zai mata kaf duniya, shi din mutum ne na gari me matukar zumunci amma idan wani ne ai ko kallo Adam be ishe shi ba, bare ya tsaya ya saurare shi har yayi masa wannan gatan. Ji tayi hankalin ta ya kwanta, ko babu komai taji halin da yake ciki, ta kuma san yana lafiya, hakan ma ya isheta. Nadeeya ta kirawo ta fesawa labarin abinda ya faru, ta tayata murna sannan suka ajiye wayar. Duk abubuwan da ta gujewa Hajiya Maman sai da suka faru, shiyasa kawai komai zakayi kayi shi tsakanin ka da Allah sannan banda son kai, karka wulakanta dan wani ka fifita naka dan baka san wanda zaka mora a rayuwa ba. Ita kanta Maman tasan Asma'u tafi karfin Adam a yanzu amma duk da haka ba zasu daina yi masa addu'ar samun mace ko da rabin Asma'un ce a hakuri da nagarta ba.

***Cup din dake hannun sa ya mika mata bayan ya sha rabi, ta girgiza kanta alamar a'ah, sai kawai ya kafa mata a baki yana kallon cikin idon ta, bata da zabi illah tasha, kunun aya ne me sanyi da dan karen dadi, dan zata iya cewa bata taba shan me dadin sa ba, sai gashi ta zuke shi tas a kunyace ta janye kanta ya kalli cikin cup din ya kalle ta

"Ana so ana kaiwa kasuwa."

Toshe bakin ta, tayi da tafin hannun ta, ta saki dariya, ya ajiye cup din yace ta taso su shiga ciki, shine a gaba tana bin bayan sa har suka dangana da first bed room din da yake tsakanin dan corridor da falon, hasken fitilun dakin daban da na falon hakan ya sake fito da kyawun dakin da yake a share a gyara tas tas kamshin turaren wuta na tashi a cikin sa. Toilet din dake makale a dakin ya nuna mata yace taje tayi alwala, yana zuwa, ya fita ita kuma ta shiga toilet din da shi kansa abun kallo ne ta dauro alwalar ta same shi a dakin ya shinfida babban abun sallah ya sako jallabiya, sannan ya fito mata da dogon hijab a cikin kayanta, mika mata yayi ta saka ya nuna mata inda zata tsaya daga saitin bayan sa.



RM
   46-47

***Nafila sukayi rak'ah biyu sannan ya juya ya kama kanta yayi addu'a, addu'ar da ya manta jiya be yi ba, shi da kansa yaga baiken sa na gaggawa da rashin hakurin da yayi, amma kuma a wani bangaren ba zai iya hana kansa bane musamman sanin cewa abinda ya aikata din ba haramun bane, yan tambayoyi yayi mata dangane da addini ya gamsu kwarai da amsoshin da ta bada ya jinjina kansa yana saka mata albarka a bayyane, murmushi kawai take har suka gama ya mikar da ita yace ta zauna gefen gado yana zuwa, ya sake fita ya dawo dauke da ledojin da akayi musu takeaway, sai plate da silver spoons ya ajiye a gaban gadon kan dan madaidaicin carpet din ya nannade hannun jallabiyar sa ya zauna yana tankwashe kafarsa

"Let me feed my wife, na fara cika duties dina."

Zamowa tayi daga gadon ta zauna a daf gefen sa ya zuba mata abincin ya saka spoon ya debo ya kai bakin ta,

"Oya! Bud'e bakin"

"Zan iya ci ai."

"Ba wani, ba ci zakayi ba nasan, ni ne zan baki har sai kin koshi, muga ma dai cikin ki."

Ya kai hannu ya daga hijab din jikinta, sai a sannan ma abun yazo kansa, ya zare hijab din yana cewa

"Bakya jin zafi?"

Kasa ta kalla da sauri daga ita sai fitted gown din dake jikinta me V shape wuyan da ta kamata sosai musamman da take a zaune, shi kansa sai da yaja numfashi kafin ya daidaita kansa ya shafi cikinta da ya cika ciki sosai yace

"When last kika ci abinci ma wai?"

"Nayi lunch."

"Lallai, kalli cikin ki fa very flat kaman baa taba saka masa abinci a ciki ba. "

" Let me feed you, bud'e bakin."

Budewa tayi bayan tayi bismillah ya bata abincin, a nutse har ta soma jin ta koshi, ta girgiza masa Kai da ya sake nufo bakin nata alamar ta koshi, be yi musu da ita ba, ya ajiye yana siyaya mata ruwa a glass cup tasha kad'an ya ajiye sannan ya tashi zai tattare kayan tayi saurin tashi,

"Zan kwashe!"

"Yau dai ba ranar aikinki bace, zauna ina zuwa." Yace mata yana tattare kayan ya fita dasu, mayafin ta dauka ta sake rufawa ta koma ta zauna a kasan tana nannade kafarta. Wajen mintuna biyar ta zata zai dawo taji shiru, sai ta fad'a toilet din tayi fitsari sannan ta wanko bakin ta, ta fito ta hange shi a saman gadon ya rufe iya kasan kafarsa yana kokarin saita AC din dakin dan shi zafi yake ji. Gaba daya dakin ya dau sanyi har ya soma shiga cikin jikinta amma shi ko a jikin sa, hakan shine daidai yayi mugun sabawa, da hannu ya yafito ta ganin tayi tsaye, ta karaso kusa dashi ya jawota zuwa kan gadon ta saman jikinsa zuwa dayan sashen gadon,

"Wannan kayan ba zai dame ki ba?"

"Zan chanja."

"Ok, chanja kizo kiji." Yace yana sakinta, ta yunkura ta sauka ta dayan side din zuwa gaban wardrobe din ta bud'e tana kallon kayan ciki da ake jera su gwanin sha'awa, da k'yar ta hango wata doguwar riga mara nauyi kuma da dan tsawon ta dan ta wuce guiwa sosai ta kusan kai idon sahu, dauka tayi ta nufi toilet ta saka ta sake yafo mayafin ajikinta ta dawo dakin, dan kallon ta yayi, ya maida hankalin sa kan wayar sa da yake duba sakonnin mutane, gadon tazo ta hau ta kwanta akan dayan pillow din ta kalli dayan barin ta juya masa baya. Ajiye wayar yayi bayan ya saka ta a flight mood ya saka hannu ya juyo da ita suna fuskantar juna.

"Kina jin bacci?"

"A ah." Ta girgiza kanta

"Ok bari na baki labarin mijinki." Ya sake jawota sosai ta shiga jikinsa kanta na saman kirjinsa

"Sunana ABDALLAH IBRAHIM K'AREFA, d'a ga Alhaji Ibrahim, mu biyar ne a wajen iyayen mu, nine babba sai MD (Mudan) sai Ibrahim (Aby baya nan yana karatu a Sudan) Aysha (Amira) sai Khadija (Ihsan). Baba Alhaji shine mahaifin mu da matan sa biyu Mom da Mami, tun da na taso ban san wani abu wai rabuwar kai ba, mun taso dukkan mu cikin so da kaunar juna, ni da Ihsan ne kadai yayan Mom, amma kuma mun fi shakuwa da Mami fiye da mahaifiyar da ta haife mu. Hakan ya kara mana kaunar junan mu kamar yadda zaki gani a tsakani na da MD, bani da aboki kamar sa haka shima bashi da tamka ta, mune koman juna babu wata baraka a tsakanin mu tun tasowar mu kawo yanzu. Mahaifin mu dan kasuwa ne tun da muka taso muka bud'e ido, hakan ya saka mana so da kaunar kasuwanci duk da be barmu mun tsunduma a harkar kasuwancin ba har sai da muka kammala first degree dinmu daga nan muka fad'a harkar, ina kokarin kamalla degree na na biyu Allah ya dafa min har na bud'e company nawa na kaina da nake yin order motoci ina saidawa wanda na fara kamar wasa. Tun daga nan MD ya karbi ragamar kula da harkokin Baba na waje ni kuma nake kula da duk wani abu da ya shafi cikin gida. Wannan shine tarihi na da gidanmu a takaice, bayan boko nayi karatun addini me zurfi har ta kai na sauke al'qur'an me girma kuma na kammala littafai da dama."

" Masha Allah." Tace tana jinjina kai,

" You will get to know me better in sha Allah,

"In Sha Allah."

A gajiye yake ranar, dan haka kawai rumfa yayi mata da hannun sa, yace mata goodnight bayan yayi kissing forehead dinta. Nan da nan bacci ya dauke shi, ta dinga kallon sa ta dan hasken da ya shigo cikin dakin, tana admiring din sa.

Da safe ta riga shi tashi bayan yayi sallar asubah ya koma sai ta sulale wajen bakwai da rabi ta bar dakin zuwa na kusa dashi, sai a lokacin taga dakin, ta cire kayanta ta zuba su a laundry basket din da ta gani a tsakanin toilet da dakin, ta bud'e akwatin da tazo da ita jiya me dauke da tsofaffin kayanta ta dauki wata bakar abaya ta saka ta fito zuwa falon, babu datti babu komai sai kawai ta wuce kitchen ta tsaya tana tunanin abinda ya kamata tayi, ita ba yarinya bace karama bare ta zauna ta shanya baki bata yi musu komai ba, doya ta dauka ta feraye ta wanke ta tas sannan tayi mata yankan da zata soya ta haka ba tare da ta yanka ba, ta ajiye a gefe ta dubo kayan miya da veggies wasu fresh an jera su akan wani abu shima me kyau wanda duk aikin MD ne da Anty Faty, sai dangin su garlic da fresh ginger suma a gefe daya, sauce zatayi da fried yam din sai ta yayyanka tomatoes tayi grating bell peppers da scotch bonnet, ta yanka albasa me yawa, da hada da half green pepper tayi sauce din me dan karen dadi da kamshi, sannan ta soya doyar bayan ta gama miyar. Sai ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta saka a sabon tea flask ta hada komai akan babban tray ta kaisu falon ta jera a tsakiya. Turare ta kunna a cikin bunner sannan ta koma dakin ta shiga wanka, ta shirya cikin wani hadadden lace mint green da touches din golden, cikin kayan lefen ta ne yayi kyau sosai kuma kana gani kasan me tsada ne. A hankali ta tura kofar dakin taga ya sake dunkulewa waje daya, sai ta dauki wayarta a saman mirror ta fito ta sake jawo masa kofar a nutse. Karatun al'qur'an me girma ta kunna a wayar ta ajiye a saman kujera ta koma kitchen din ta dan sake gyara shi ta jawo kofar sai taji ana knocking a kofar shigowa part din, wajen kofar taje tace

"Waye?"

"Mune." Amira tace suna rik'e da warmers din abinci da tea flask,bud'e musu tayi tana fad'ad'a fara'ar fuskar ta, suka gaishe ta a tare suna satar kallon ta dan ba karamin kyau tayi ba, kayan sun zauna das a jikinta sannan daurin yayi mata kyau sosai.

"Sannun ku, Amira da Ihsan ko?"

Dadi ne ya kamasu jin ta fadi sunan su, suka amsa mata da eh, tace su zauna,

"Mami tace karmu zauna wai yayi safiya, zamu dawo anjima breakfast tace a kawo muku. "

" Toh shikenan,mun gode ku gaishe su "

" Sai anjima. " Suka juya ta rufe kofar tazo ta bud'e warmers din taga farfesu ne da chips sai kunun gyada, plate ta dauko ta zuba ta ajiye sauran a wajen da ta jera kayan abinci ya zauna taci sosai, ta gama tasha tea dan bata fiya son kunun gyada ba ita, ta wanke kwanukan ta dawo ta zauna kenan sai gashi ya fito. Idansa fes akanta ya sakar mata murmushi yana nufo ta, tashi tayi tsaye ya karaso ya bud'e hannun sa ya rungume ta.

"Good morning Baby!"

"Ina kwana!?"

"Lafiya lou, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lou."

" Masha Allah, shine kika gudu kika bar ni ko?"

" Bana jin bacci ne."

" Sai kika zo kina bawa kanki wahala maimakon ki huta ko?"

" Ba wata wahala fa."

" Ba wani."

Yace yana zama a wajen kayan abincin

" Wanne ne yaran chan suka kawo wane ne kika girka da hannun ki?"

" Dama kaji zuwan su?"

" Ina jin su, na ganki ma kina zuba loma baki jira ni ba."

" Laaaa..." Tayi saurin rufe fuska da tafin hannun ta, yayi dariya ya bud'e flasks din yace ta zauna, ta zauna ta zuba masa doyar da sauce din kamar yasan shine wanda tayi, yaci sosai da ruwan bunu hakan yayi mata dadi sosai, ya gama ta tattare wajen ta gyara shi kuma ya shiga wanka, sai da ya tsokane ta akan tazo ta tayashi ta gudu kitchen ya dinga dariya shi kadai yana wankan har ya kammala ya fito ya shirya irin shirin da yake weekends yace tazo su shiga cikin gidan. Mayafi ta yafa madaidaci ya fito suka nufi chan part din iyayen tana karewa ko ina kallo.
Tarba ta musamman ta samu a wajensu, musamman Mami da take ta nan nan da ita, duk sai taji tsoron da take ji ya kau, taji wani gwarin guiwa na zuwar mata, har falon Baba Alhajin Mami ta kaita ta

29 / 30