Author : RANO Category : African Stories & Novels
sa, be ko yi sallama da kowa ba ya kama gabansa sai gidan Fido, daga chan ya wuce wajen abokin sa ya karbi wasu kaya sannan ya wuce gida.
Tun ranar da ya tafi bata sake jin duriyar sa ba, Hajiya Mama dai tazo sau daya da maganar yadda bikin zai kasance tunda duk abu daya ne bangaren ta da na Abba, umma dai bata ce komai ba, duk abinda suka tsara suka yanke ita bata da ta cewa dan ko da tace din ma ba lallai suyi amfani dashi ba. Daga haka aka shiga satin bikin.
Ranar laraba aka je akayi kafi, gidan yayi kyau sosai sama da k'asa sai parking space, a jikin gidan Hajiya Maman yake dan katangar su daya, dama tace ko Adam zai yi aure yana tare da ita bata so yayi nisa ko kad'an, balle kuma da zai auri Asma'un sai take ganin ai shikenan ma dama Asma'un ikon ta ce itama. Alhamis aka shiga bikin gadangadan, gidajen biyu ko ina biki ya kankama Hajiya Mama dai saboda yawan mutanen wasu sai dan karamin hotel hotel din dake bayan gidan aka kama musu musamman abokan Adam din da sukayi karatu a turai tare suka zo daga wasu states din.
It's better to marry late than to marry wrong! (Kamar haka dai bature yace, na manta dai.
Don't marry out of desperation dan aure ya wuce duk tunanin me tunani!
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
https://arewabooks.com/chapter?id=628b84d5aed642354ddce302
RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (4)
***Zazzaune suke da kawayenta su biyar wanda sai da Umma tayi mata fad'a sannan ta sanar da su da maganar bikin,sai gasu kuwa washegari da aka yi kafi. Lefe suka kalla suke cin abincin da Umma ta saka aka kawo musu sannan suka me kushin da Nadeeya ta turo ta shiga aikin yi musu kunshin wanda ita dai asma'u kawai bin su take da kallo ta sallama komai musamman da taga an soma yi mata lallen sai ta fad'a kogin tunanin yadda rayuwar ta zata kasance idan ta auri Adam. Duk hayaniyar da suke da tsokanar ta, bata kula sh ba, dan ba ma gane musu take ba. Ana gama mata jan lallen sai kawai ta zame a wajen ta kwanta ta rufe idon ta, tana fatan ace tayi bacci ta farka taga an ce ai mafarki ne babu maganar auren ta da Adam din. Sai dai sam baccin yaki daukar ta, duk abinda suke fad'a na shakiyanci tana jin su.
Sai bayan magriba sannan aka gama musu, suka tafi anan ta samu ta shige daki ganin gidan ya cika sosai da yan uwa, gobe za'a yi kamu dan haka makusantan umman duk sun zo da su Yaya Hadiza da yaran su, dangin Abba kuwa kusan rabin su suna gidan Hajiya Mama, sai gobe zasu taho nan din daga nan kuma sai su raba kansu gida biyu wasu su zauna anan wasu a gidan Hajiya Maman.
Tana kwance Rauda da Hidaya suka shigo, suka zauna suka shiga yi mata hira, sai ta mike ta dan ware a cikin su har tana kyalkyala dariya tamkar bata da sauran damuwa, su kansu sun yi mamaki sai suka ki yarda su bar ta ko na dan lokaci ne suka raba dare suna hira irin ta yan uwa, da tuna rayuwar baya da yarintar su. Sai chan dare suka kwanta suka tashi da asubah daga nan kuma aka shiga shirye shiryen kamu da za'a yi a kangon Abban dake jikin gidan nasu ta baya.
Bata fito ba ta sake gyara kwanciyar ta dan dama ba sallah take ba, ta dai kama ruwa ta wanke jikinta sannan ta sauya kayanta ta koma ta kwanta dan bata san idan ta tashin me zatayi ba, kayan da zata saka a kamun da komai duk su Rauda sun hada mata waje daya, dama tun farko tace musu ba zatayi make-up ba, wanda dama shine yake cinye dukka lokacin shiyasa kawai ta cigaba da mikewa tana jin hayaniyar na tashi ana dora tukunya ana saukewa alamun dai da gaske bikin ake, babu kuma wani abu da zai hana sai dai mutuwa.
Ji tayi ta nemi guntun hawayen da take dashi ta rasa, tana tunanin ma ko sun kafe ne tun yanzu dan ta san akwai sauran kuka a gabanta. Sai kawai ta dinga sauke ajiyar zuciya a hankali tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta.
Breakfast su Rauda suka shigo dashi, kosai ne da kunu sai farfesu da akayi mata daban sai ruwan tea game bukata, bata shan kunu da dangogin sa tun da chan, shiyasa sai Rauda ta hada mata tea ta dinga hadawa da kosan da bread kuma sai taci sosai dan kwana biyu bata samun isasshen cin abinci saboda zulumi. Umma ce ta shigo rik'e da wata Leda a hannun ta, ta ajiye a dakin ta kalle ta, tace
"Ku koma chan gidan Safiyya sai ku shirya a chan nayi mata magana, za'a aiko muku da abincin rana idan an gama nan dakin ma wasu bakin ne zasuyi amfani dashi."
"Dama yanzu muke shirin tafiya." Cewar Rauda tana tattare kayan wajen.
" Kizo daki na."
Tace wa Asma'un tayi gaba, tashi tayi tabi bayanta tana fita akayi mata cha, amarya amarya, ta dinga yake kawai tana gaishe su har suka dangana da dakin Umman inda duk kannen umman suke cike. Gefen gadon ta zauna tana gaishe su, suna amsawa wasu suna tsokanar ta, Aunty hauwa ce ta tabo ta, tace ta dawo ciki sosai, ta matsa wajensu, ta soma mata magana a hankali yadda ba kowa zai ji ba, sai ita da take fadawan, har ta gama bata ce komai ba, tayi godiya idon ta na cikowa da kwalla dan maganganun sun shige ta sosai kasancewar Aunty Hauwan babbar malama ce ta san addini kwarai, duk abinda ta fad'a mata gaskiya ne sai dai bata san ta Ina zata fara ba, ta Ina zatayi yiwa Adam irin biyayyar da Aunty Hauwan take fad'a. Ta dan jima a dakin har sai da su Rauda suka leko sannan ta tashi suka dunguma zuwa gidan Safiyya, amarya ce bata jima sosai a unguwar tasu ba, suna da alaka ta bangaren Umma shiyasa ma umman ta zabi su je chan su zauna saboda gidan zai cika da mutane sosai.
Wajen karfe hudu ta gama shiryawa da taimakon su Rauda da wasu kawayen ta da suka zo tun dazu, kuma suka tursasata dole aka dan mata makeup duk da light ne amma tayi kyau, ta dinga hararar su suna mata dariya dan ita har ga Allah bata son duk abinda ya shafi kwalliya irin wannan ita dai barta da yar powder da kwalli sai lipstick shikenan.
Abbati ne yazo daukar su a motar Abba duk da ba wani nisa bane duk cikin layi daya ne amma ita kunyar fita take a haka shiyasa kawai ta kirashi yazo ya dauke ta da kawarta daya su kuma sauran suka yi gaba wajen kamun suka jira a wajen dan su shiga da ita.
Wajen ya cika sosai, an tsara komai yadda ya kamata, Hajiya Mama da Jama'arta suna bangare daya sun sha kwalliya, su Nadeeya ma sun iso sun sha kwalliya sun yi kyau sosai, kallo daya zaka musu kaga banbancin wayewa fiye da mutane da yawa a wajen, idon su a bude yake sosai sai suka zama daban a wajen.
Amarya na zuwa aka soma abinda ya tara mutane a wajen, nan fa su Hajiya Mama da mukarrabanta suka bud'e bakin aljihu suka dinga zazzaga kudi, baka jin komai sai sunan su da MC ke ambata saboda ya ga ruwan kudi, ita kanta Ummaa uwar bikin gefe ta koma ta zubawa sarautar Allah ido, sun kankane komai hatta wajen Amaryar su Nadeeya ne suna ta aikin daukar hoto, sauki daya da umma take hangowa Asma'un shine ta wajen su Nadeeya din da Hajiya Maman, kamar suna son ta, kamar zata samu sauki a wajen su, ko dan alaka me karfi da take tsakanin su, sai dai kash!
Wajen takwas aka gama, shima da an daka ta tasu ba za'a tashi ba, basu shiga gidan Abban ba, suka hau motocin su suka tafi. Sauri take ta isa daki ta cire kayan dake jikinta dan ba karamin takura mata sukayi ba, tana zuwa dakin su taga mutane ne tsofaffi a cike duk sun kwakkwanta,juyawa tayi zuwa dakin su Abbati, tasan babu kowa kuma basu dawo ba, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya ta hau kokarin zuge zip din rigar da ta kamata sosai dan ma ta saka wadataccen mayafi amma da babu abinda zai sakata, jin hannu tayi a gadon bayanta, ta juyo a razane suka yi ido biyu dashi, ta daddage zata kwalla kara ya rufe mata bakin da karfin sa. Kici-kicin fuzge kanta take ya saka dayan hannu ya rike mata kan sosai, sai kawai ta fashe da kuka me cin rai. Sakin ta yayi da sauri yana mata wani irin kallo. Da sauri ta juya ta fice daga dakin jikin ta sai rawa yake kamar mazari, dakin Umma ta shiga ta wuce da sauri wardrobe din Umman ta dauki hijab ta saka sannan ta fito da sauri, a tsakar gida sukayi kicibis da Abbaty,ya tare ta da sauri
"Dama ke nake nema, Adam yana dakin mu tun dazu yana jiranki."
" Dan Allah kace ya tafi, ni ba zan iya zuwa ba."
Zaro ido yayi
" Abba ne fa yace na zo na gaya miki, babu ruwana wallahi."
"Abba!? Ya dawo ne?"
" Tun dazu ai yana nan, shima Adam din tun kuna wajen kamun yazo Abba yace ya jira shine yayi magana aka tashi ai daga kamun. "
Wani abu ne ya tokare mata a wuya, bata masa magana ba kawai ta bi hanyar dakin nasu, ta tura ta shiga, yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin. Gefe ta samu ta makale ya matso yana kallon hannun ta da kafarta da akayi mata lalle.
"Menene wannan haka?" Ya fad'a muryar sa a dan tunzure, ta masa banza kamar bata ji ba, ta gwammace ya kashe ta idan ma kashe ta zai amma ba zata tanka masa ba, sake magana yayi da dan karfi, ta dago a tsorace taga yana wa hannun ta da kafarta kallon tsana.
"Bana son wannan abun da kika je akayi miki, karki kuskura kizo min gida dashi wallahi, ki san yadda za'a yi ki goge shi."
A wani irin yanayi take kallon sa, mamaki na neman kashe ta, lallen yake nufin be sani ba, ko kuma me? Bata gama dawowa daga tunani ba, taji ya wurgo mata leda akan fuskar ta, tsinin takalmin dake cikin ledar ya buge ta, sosai taji zafi.
"Kayan da zaki saka ne a dinner din da friends dina suka shirya gobe, saura ki zubar min da girma na da aji na da kauyancin ki, ki tabbatar kuma kinje an goge wannan bakin abun na hannun ki, ina laifin ma ki saka nail polish ko kiyi fixing nail din ma , amma kiyi wannan abun irin na yan kauye, bana son shi bana son ganin shi kuma."
Saroro tayi tana kallon sa mamakin sa na neman kashe ta, tashi tayi daga zaman da tayi, ta dire masa kayan a gabansa tace
"Bana bukatar kayan nan saboda ba zan je wajen ba, sai ka dauka ka kaiwa wadda take da wayewa daidai da taka, wadda ba zata baka kunya da kauyancin ta ba. Lalle kuma ba zan goge ba, tunda ba dan kai nayi ba, kuma hannu na ne da kafata ba ta wani ba, abinda naga dama shi zanyi.". Ta murguda masa baki ta juya da sauri ta fice dan tasan tsaf zai iya gaura mata mari yadda taga yana huci. Kasa motsawa yayi daga wajen kamar wanda aka bigewa kafa, ya kalli kayan da ya kashe kudi masu yawa wajen siyansu amma ta watsar masa a wajen, sannan ya gaggaya masa magana yana tsaya har ta fita be fisgota ya nuna mata shi ba sa'an ta bane. Ransa ya kai kololuwa a baci, huci ya dinga yi kamar wani dan karamin zaki, sai ga Abbati ya shigo da yaga fitar Asma'un, kallon kayan dake kasa yayi ya kuma kalli fuskar Adam din, sai ya juya zai fita.
"Tsaya pls, wannan kayan ta manta su ka kai mata, ni zan wuce."
"Owk." Yace ya dawo ya dauki ledar suka fito a tare ya tafi shi kuma ya shiga ciki ya samu Rauda tana waya a tsakar gidan ya bata ya tafi.
***Daren gaba daya bata iya runtsawa ba, bata kara tabbatar da banzar al'adar Adam din ba sai a jiya, hakan ya tsaya mata a rai matuka har ta rasa irin tunanin da zatayi akai, tana jin yar hayaniyar wadanda basuyi bacci ba a tsakar gida suna aikin abinci har ta daina jin su kwata kwata, sai daf da asubah sannan bacci ya dauke ta cikin yanayin da ba zata iya misaltawa ba. Wajejen bakwai aka hau tashin ta kasancewar ranar ce daurin aure, ta tashi idon ta duk sun kumbura saboda rashin isasshen bacci. Shiryawa ya Hadiza tasa ta ta hau yi, babu um babu a'a ta hau shirya war, tana jin sanda su Abba da jama'ar da zasu tafj daurin auren suka tafi saboda a garin su Abban za'a daura Sumaila, ji tayi jikinta ya kara sanyi sosai. Ta zauna rik'e da kanta dake sara mata sosai, ko da aka kawo breakfast din sai ta kasa shi, jiya ma ashe dan ba taga anzo tafiya daurin auren bane har ta samu sukunin ci sosai. Babu yadda su Rauda basuyi da ita ba amma bata da nutsuwar da zata iya saka wani abu a cikin ta, lokaci kad'an sai ta duba agogon wayarta har sha daya tayi, jikinta ya kara saki sosai ta saddakar shikenan, shikenan ta shiga rayuwar da bata da yakinin samun kwanciyar hankalin ta.
Wajen karfe daya da rabi suka soma shigowa, kowanne su cike da farin ciki, farin cikin da yake daidai da bakin cikin ta, tana jin sanda wani kawun ta kanin umma yake fadawa matan tsakar gidan an daura, wata daga cikin su ta saki guda me karfi. A take taji kanta na wani irin juyawa, taga dakin na neman fado mata akai, bata san sanda ta fashe da wani irin kuka ba, su Rauda dake gefenta suka hau tayata dan dama karfin Hali kawai suke da kuma bin umarnin umma!
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Last Free Page (5)
***Babu wanda yake da niyyar rarrashin wani a cikin su har saida Ya Hadiza ta shigo, ta harari Rauda da Hidaya cikin bacin rai tace
"Menene haka? Ku da zaku karfafa mata guiwa sai kuma ko zauna kuna tayata kuka, kukan menene? Akwai wanda ya isa ya kujema kaddarar sa ne? Kowanne bawa fa da yadda Allah ya tsara masa, ku tashi dan Allah kafin hankali ya dawo kanku. "
Shiru duk sukayi har ita Asma'un sai dai ba zata iya fasalta yadda take ji a kirjin ta ba, abu ne dankare me girman gaske, wanda ko hadiyar yawu sai tayi da gaske take iyawa saboda yadda ya tokare mata ko ina.
A hankali gidan ya sake cika sosai bayan dawowar yan daurin aure, suka dinga jerin gwanon shigowa wajen yin Allah sanya alkhair, daga nan kuma aka dinga fitar musu da abincicika kala kala. Sakon gidan Hajiya Mama ne ya iso, katinan dinner ne ta aiko dashi sannan ta aiko da kuloli manya dankare da sinasir da waina, sai a lokacin su Ya Hadiza suka san da maganar dinner din dan babu wanda ta fadawa. Tunanin yadda za'a yi da zuwan suka shiga