RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 30

75K to 78K   out of 87.6K words

ya siya mata sai alkur'ani me girma me kyau da wani littafi akan al'adar mata a musulunci.
Anty Faty ya kaiwa yace a hada shi car key ne, kafin su tafi zai aiko a kawo motar, harda rawar ta, ta taka ya girgiza kai kawai ya fice yana mamakin karamcin su.



_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*


*RM*
      37-38

Barka Da Sallah!


****Jikinsa sosai ya matsa masa,ga effect din shaye-shaye da ya kusan taba masa kwakwalwa ga sam Fido ta hana kowa rabar sa, ita kadai take kula dashi shima ba sosai ba sai zaman hira da shewa ita da su Faiza, duk mama ta rame ta zama abun tausayi a dan kwanakin, ita dama rayuwar duniyar nan baki dayan ta wa'azi ce, tasan tayi kuskure a tarbiyyar Adam in da ta dauki son duniya ta dora masa bata ganin laifin sa, duk da deep down tana jin kamar ba haka ya kamata tayi ba amma so ya rufe mata ido, bata tsawatar masa ba bare har yasan daidai da akasin hakan.
A darare tazo yau ma kamar kullum dan yadda take tsoron Fido ko mutuwar ta albarka, abinci ta kawo masa tana kuma son ganin sa taga halin da yake ciki amma bata iya dogon zama a dakin sai dai ta koma waje ta tsuguna har dare sannan ta tafi gida, a zaune ta hange shi yana kallon kofar shigowa ya rame sosai yayi baki, cup ne a hannun Fido din tana bashi tea yana sha amma be ce mata komai ba, murmushin jin dadi ne ya subuce ma Hajiyan ta karaso da dan saurin ta amma sai taga kamar Adam din be damu da ganin ta ba, sai ma kallon Fido din yake da ta sauke cup din hannun ta, ta tashi ta ajiye a saman dan madaidaicin fridge din dake dakin, maimakon yayi magana sai ya zame ya kwanta yana maida idon sa ya kulle hakan ya daki Maman sosai har taji tana kokarin zubewa a wajen, dafa karfen gadon tayi ta kasa cigaba da tafiyar, sai addu'a da ta shiga karantowa har ta samu sauki a yadda take ji.

"Sannu da zuwa." Fido tace tana karbar kayan hannun ta, ta kaisu gaban gadon daga gefe ta ajiye dan dama abincin gidan Maman take jira ta kwashi girki, dan dama ita ke cinyewa dasu Faiza kullum. Toilet tayi shigewarta bayan ta ajiye ta bar Maman tsaye ta kafe Adam din da ido wanda yake motsi kad'an amma idon sa a kulle kamar me bacci.

"Adam?" Ta kirashi cikin muryar rada rada kamar wadda bata so a ji, motsi yayi ya juya dayan bangaren be ce mata komai ba, rik'e bakin ta, tayi da sauri kuka na kokarin kwace mata, shigowar likita da wata nurse ya sakata daurewa suka gaisheta a mutunce sannan ya matsa ya duba Adam din ya tambaye shi jikin sa, kai kawai ya nuna masa yace ciwo yake? Ya kada kai alamar eh amma be bud'e idon ba

"Zai daina, sake gwada bp dinsa sister."

Likitan yace yana daukar result din test din da akayi masa ya hau dubawa, bp ta sake gwada masa ta fad'a ma Dr din ya daga kai kawai ya chanja masa wani maganin sannan suka fita, sake matsowa Mama tayi ta sake kiran sunan sa, gani tayi ya dame baki alamun ta dame shi, ya yamutse fuska ba tare da ya tanka ta ba

"Sun ce kar a matsa masa da magana saboda ciwon kan nasa."

Kofar toilet din ta kalla dan bata san ta fito ba, da sauri tace

" Toh toh, bari na jira a waje toh. "

Ta juya da sauri ta fita daga dakin, tabe baki tayi ta matsa gaban gadon tana leken sa

" Kice ta tafi bana son ganin ta. "

" Hajiyar ka ce fa. "

" Ita din. "

" Ok oo, nawa ido kunfi kusa. " Ta bar wajen tana jin dadi a ranta, ta samu abinda take so, Adam sai ya raina kansa ya gwammace be wulakanta ta ba.
Zaman kurame Mama tayi ita kadai har su Fadila suka zo sannan ne ta dan saki ranta, suma duk basu dade ba suka tafi dan ba zasu iya zaman takaicin Fido din ba, Nadeeya ce kadai take taya Maman zama idan ta gama aikin ta, sai dare suka komawa gida, tana jin tausayin Maman musamman yadda Adam din ya zama a yan kwanakin nan, kamar be san ta ba, ba kuma ya zancen kowa sai Fido din amma ko su basu ishe shi kallo ba, kamar ma zuwan da suke takura shi sukeyi.
Washegari aka sallameshi Fido bata fadawa kowa ba, suka tattaro suka dawo gida, sai da Mama ta dauki kafa taje asibitin sannan ta san sun dawo, hakan yayi mata ciwo sosai ta dawo gida da takaicin amma kuma ba zata iya magana ba, yadda take ji kamar an saka abu an daure mata baki haka take ji, ko ta yi yinkurin yin magana idan taga Fido sai ta k'asa taji wani bala'in tsoron ta.
Bata shiga gidan nasu ba, sai kawai ta wuce dakin ta, ta kwanta ciwon bayan da ya matsa mata kwana biyu da kafa na sake damun ta sosai.


***Anty Faty, Anty Asy sai kannen Mom su biyu da wata sister din Baba Alhaji sune zasu kai kayan Abuya, MD ne akan komai duk shirye shiryen da za'a yi da duk abinda ake bukata, gidan ya soma cika da yan uwa na kusa da na nesa dan ma katin gida ne ba zaka gane cikar ba saboda ba'a cinkushe waje daya ba, tsayawa wajn fadar haduwar kayan bata baki ne dan basu duba matsayin Asma'un na bazawara ba, komai kamar na auren fari haka sukayi mata dan ban da su na cikin gidan babu wanda ya san da maganar duk yan uwa, kuma su din ma ba zasu taba fad'a ba dan Mami da kanta ta ja musu kunne akan maganar dan ko Baba Alhaji idan yaji zai iya fad'a sosai dan tun ranar farko shi kansa ya tsawatar musu domin ya san halin mata da kananun maganganu akan abinda yake wata al'adah ba addini ba, manzon Allah SAW ma Nana Khadija ya fara aura kuma bazawara ce dan haka ba sabon abu bane ba kuma haramun bane face ya kasance sunna mai kyau wanda hausawanmu suke ganin kaamr be dace ba saboda wata al'adah tamu mara asali da tushe.
Mota biyu sukayi, motar Anty Faty sai ta MD sai guda daya da aka zuba kayan a ciki wanda suka kasance akwatuna bakwai masu kyau da tsari, babu karya ko fariyar akwatuna a ciki amma kuma an kashe kudi daidai da arzikin su dan babu karamin abu a ciki komai me tsada ne da aji kuma na amfani.
Bayan tafiyar su ya dawo gidan a gajiye dan ko magana be samu sunyi da ita ba tun da ya fita, bayan ya bayar an kawo motar ya shiga wata sabgar wadda ta cinye duk lokacin ranar tasa, be zauna ba dan baya jin ko ruwa ya saka a cikin sa, har zai wuce part dinsu ya tuna da kiran da Mom take masa, sai ya juya akalar sa zuwa shashen cikin gidan. Cikin babban falon babu kowa da alamun tafiyar su Anty Faty ta saka aka tashi dan ga alamun kayayyakin su nan a barbaje a falon, wucewa yayi zuwa ciki a daidai corridor din da zai kaishi dakin Mom din Amira, Ihsan da wata cousin dinsu Siyam na zaune suna magana k'asa k'asa, har zai wuce sai yaji kamar an kira sunan sa, sai ya dakata yana tsaye curtains din dake wajen ya dan kareshi

"Ai ya Abuya dai wallahi ya cika abu local, bazawara dai?" Siyam din tace tana tabe baki

"Eh haka mukaji mu ma."

"Kuma su Baba suka barshi?"

"Eh, baki ga ma fad'an da sukayi mana ba, kar suji kar su gani Mom da Mami kuwa har da cewa idan suka ji zancen sai mun gwammace kida da karatu."

"Tab! Amma gaskiya ya kwafsa, zamu ganta ai gobe kuwa ko ta hadu, ni duk kun saka bikin ya fita a kaina wallahi."

" Muma ai, ni wallahi dama Ya Feena ya aura tafi wallahi."

" Wallahi, ga ta yar gayu sosai, kuma har yanzu tana son shi wallahi, cewa ma tayi ba zata zo ba, ga bikin ko dan dinner babu,wai walima kawai kamar wasu malamai."

" Hmm, sai dai bikin Ya MD, amma wannan kam sai dai mu yi kawai."

" Wai kyakkyawa ce!?"

" Bamu santa ba ai."

" Tab!"

"Dan Allah amma karki fadawa wani, ana ji an san ni da Amira ne, kuma kinsan shi zai iya karya mana kafa akan haka wallahi."

"Bama zan fada ba."

"Ku sameni a part dina."

A razane duk suka dago, suka mike a lokaci daya amma tuni ya bar wajen ko kallon su be ba, rik'e kai Amira tayi tana kallon Ihsan da ta fara kuka wiwi, Siyam kuma kamar ta saki zawo a wajen tana wurga ido tana neman hanyar barin gidan.

"Mun shiga uku mun lalace!"

"Wallahi guduwa zan ba zan zauna ba."

"Wallahi karki gudu, kika gudu har gida zai turo Ya MD wallahi, muje kawai." Amira tace zuciyarta fal tsoro amma taurin kai ya hanata nunawa, Ihsan kuwa kuka take har suka isa part din, suka tsaya cikin tsoron wanda zai fara shiga, Amira ce tayi karfin halin bugawa, shiru sai ta kama handle din ta bud'e, suka shiga da sanda amma babu kowa a falon sai takalminsa da ya cire da hular kansa a saman center table, a k'asa suka zube a tsorace.

"Malama ki daina kuka dallah."

Ta zunguri Ihsan tana hararar ta, kin shiru tayi sai dai ta rage sautin sosai. Fitowa yayi ya sauya kayan jikin sa zuwa jallabiya fara kansa sanye da hular da ake kira da tashi kafiya naci alamun sallah yayi, waya ce a sakale da kunnen sa yana magana k'asa k'asa,

"Send me the address, I'll come and pick you."

" Owk, sai nazo."

Yace yana zama a kujera, ya ajiye wayar a gefen sa ya dauki remote ya rage karar tv din, satar kallon sa suke dukka ya tamke fuska babu alamun dariya ko kad'an,

" Dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zamu sake ba. "

Ihsan ta fad'a cikin kuka, be ko kalli in da suke ba bare yayi magana, dama kuma ya riga ya santa da shegen tsoro ga bakin tsiya, takardun da yazo dasu ya karasa arranging tas suna durkushe a wajen sai da ya gama sannan ya juyo yana kallon su daya bayan daya, dududu ba zasu wuce sha takwas ba amma sun iya zama su tsara zance haka kamar wasu iyayen mata, ji yake kamar ya hadasu dukka yayi musu shegen duka amma ba zai iya ba, fushin sa kadai yasan ya wadatar ba zasu sake gobe ba, yara ne yanzu duk sun zama sai a hankali, ba zai bari ire iren maganganun suyi tasiri ba, har Asma'u ta samu matsala da family dinsa, ba ita ta sakawa kanta hakan ba, babu kuma wanda zai ga laifin ta domin ta zama bazawara, Allah da kansa ya halasta saki idan har shine maslaha akan zaman auren.

"Ba zan maimaita abinda naji kuna fad'a ba, naji komai kuma this should be the first and the last da zan sake jin irin wannan maganar a cikin gidan nan, wallahi sai na mugun saba muku, mutanen banza!"

"Kayi hakuri."

Amira da yake kallo tace tana sunkuyar da kanta.

"Ku tashi ku bani waje!"

Da sauri suka mike suka fice, ya maida kansa jikin kujerar yana lumshe idon sa, kafin anjima ya fita, part din da zai zauna yana cikin gidan amma ta baya sosai, an gama gyara komai ko yace MD ya gama gyara komai dan kwana biyu rabon da ya shiga ya duba, so yake idan zai fita ya shiga ya gani ko akwai abinda yake bukata da baa saka ba.

Da gudu gudu suka karasa shiga dakin su, suka kwashe da dariya Amira na kwaikwayan Ihsan da take kuka, duka ta kai mata ta goce tana sake kyalkyalewa

"Shegen tsoro kamar farar kura."

"Ba zaki gane ba, ni zai fi cin uba dan nafi zakewa, ke kuwa taku tafi zuwa daya zai iya daga miki kafa, Siyam kuwa be ce mata komai ba."

"Amma yasin na tsure da naga fuskar sa, wai gumurzu, shi fa dama Ya Abuya baya dariya asalin sa."

"Yana yi wallahi, sai yaga dama amma nasan yana ma Anty Asma'u."

"Hadda su Anty?"

"So kike yaci ubana kenan ko?"

"Ya MD zai hada ka dashi ya sassamaka wallahi,."

"Yayye Maza ko wahala." Siyam tace tana dariya

"Da wuya da dadi, amma ana cin uban ka daidai gwargado,."

" Ni ko da yake bamu da maza manya, bansan wannan ba. "

" Ai ki gode Allah, ta wani bangaren wallahi, mu fa idan suka ga dama kallo ma bamu isa muyi ba, sai kiga ance Ina books din ku. "

" Tabdin, kuna fama. "

" Kin shiga tarko kema, yanzu Ya Abuya ba zai barmu shigar masa gida bama wallahi, ni dama ban saka aka ba, dan zai iya cewa mu daina masa sintiri a gida, da dai Ya MD ne yawwa. "

" Dama gari banza ma hana mu zai, bare ya kamamu dumu-dumu cewa zai gulma muka zo. "

" Allah dai ya rufa asiri wallahi, sai a kiyaye gaba. " Ihsan da sai a lokacin ta dawo daidai daga mugun tsoron da taji tace sannan tace

" Bari naje wajen Mom na dawo. "

Ta fice ta bar su su kadai


****



RM
39-40

***Alwala ya tashi ya sake daurowa domin ance alwala tana wanko zunubai shiyasa baya taba hada alwala daya a salla biyu, masallaci ya wuce na cikin gidan ya hangi motocin da suka je kai kayan a harabar gidan hakan ya tabbatar masa da sun dawo kenan. Bayan sun idar ne suka jero da MD yana fad'a masa yadda zuwan nasu ya kasance, yana jin sa har ya kai karshe kafin yace masa

"Thank you for everything."

"Me akayi!?"

"Ban sani ba."

"Toh shi na gani."

"Muje naga gidan kafin na fita, nasan ma an gama komai."

"Eh an gama gaskiya, console ne kawai ya rage zasu kawo shi gobe, shima ba wanda aka zaba suka kowa ba shiyasa ma da tuni an gama hada komai. "

" Owk, that's good. "

Rage murya MD yayi kamar wanda zai rada yace

" Plate dina ya dawo gidan ka. "

Murmushi yayi yana bud'e kofar,

" Gidan zaka dawo gaba daya da zama kawai. "

" Rufa min asiri, yafi karfi na. "

" Zakayi bayani."

Ya wuce ciki ya barshi a falon yana dariya, duddubawa yayi ransa fes yana jin kamar ya bud'e ido ya ganta a gabansa a cikin gidan, komai yayi kyau sai kamshi ke tashi ko ina, da k'yar ya baro dakin ya karasa dudduba sauran dakunan da toilets sannan suka tafi, ya shirya zuwa kananan kaya riga da dogon wando ya dauki hanyar gidan kunshin da tace masa taje a unguwar gidan Ya Hadizan.
   A hankali yake driving din cikin wani yanayi ya saka wakar Westlife cikin raguwar sauti sosai har ya karasa address din data turo masa, yayi parking daga gefen gidan ya fito daga mazaunin driver ya dawo na gefe ya kwantar da kujerar baya sosai ya kwanta ya ciro wayar sa ya tura mata da text message

"I'm out!"

Karasa mata ake dan yau ne karshen gyaran jikin da Amaryar Kb take mata dalilin masu kawo kayan yasa ta taho nan din, sosai ake mata gyaran yau dan tun safe ake abu daya har da wasu hadaddun turarukan tsuguno da na wanka. Babu in da baya kamshi a jikin ta ga wani santsi da sulbi da fatar jikinta tayi wanda ita kanta da kanta ta san babu karya ta hadu. Kunshin take turarawa yanzu a cikin wani rami aka saka turaren ta zura kafarta da hannun ta bayan kunshin yayi, sai ga text dinsa, reply tayi masa ta ajiye wayar a gefenta. Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Amaryar Kb ta gama hada ta tsaf, dama tun jiya tayi gyaran gashi sai turara su da aka yi yau din. Doguwar riga ce abaya a jikinta baka, ta saka flat shoe dinta ta dauki yar karamar hand bag dinta ta saka wayarta tayi ma Amaryar Kb sallama ta fito tana cike da kunyar sa, hango motar tayi daga gefe chan bayan yaga fitowar ta yayi mata fitila, ta nufi wajen kai tsaye ta zagaya bangaren me zaman banza ta bud'e, duhun da ya mamaye wajen ya hana mata ganin sa, ta sako jikinta sosai sai ji tayi an riko ta, ya jawo ta jikinsa gaba daya kamshin ta na ratsa jiki na jijiyoyin sa, wani irin cool kamshi me sanyin dadi,

"Subhallah!" Ya furta sanda ya ji ya kama hannun ta da ya kara taushi sosai har wani tubus tubus yaji yayi,

"My wife."

"Ashe kana nan, ban lura ba."

"Ina sane na dawo nan din ai, I just wants to hold you, ."

Yayi mata whispering yana dan cizon gefen kunnenta,

26 / 30