RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 30

51K to 54K   out of 87.6K words

cikin sassarfa ya bar falon, ya rasa ina zai kama, ta ina zai fara, ya samu dama me kyau amma yayi wasa da ita, me yasa ma ya tafi ya barta, bayan yasan tana da damar da zatayi waya ta kira gida. Rasa ina tsoma ransa yaji dadi yayi, ya kasa tuka motar ma, baya tunanin zai iya hawa titin nan balle ya kai kansa kano a daren, dole zai jira gari ya waye saboda lafiyar sa, sai da ya bari kafa ta fara daukewa a garin ya samu wani gidan mai da baya amfani, direbobin mota ne yawanci suke kwana a ciki parking yayi a ciki, ya sauke glass din motar ya kwanta a baya, sauro kuwa yace da wa Allah ya hada mu, ya dinga gasa masa cizo babu tausayawa, abinka da farar fata kafin safiya ya fice daga hayyacin sa, babu wanka babu komai ya dauko hanya.


Hafsat Rano -RM
           27

***Lokacin da suka dauko hanya Umma ta kira Abba, ya daga ya sanar mata da gasu nan tare da Asma'un, Alhamdulillah, ta furta sannan ta kashe tana sanar musu da abinda Abban yace, har lokacin Hajiya Mama na gidan, tana jin an ce sun taho ta tashi, tayi musu sallama ta tafi,dan dama zaman jiran da take kenan, Nadeeya ta kirata ta fad'a mata zuwan kawayen Fido gidan, shiyasa take so taje taga me yake faruwa duk da dai an ce sun tafi. Duk suma sai umma tace su tafi gidajen su sun dawo gobe, Ya Hadiza ce kawai ta rage suka zauna da Umman suna dakon zuwan su Abban, sai dare sosai suka dawo, Asma'u ta rungume umman tana fashewa da kuka, ita ma umman kukan ta saka, amma ba kamar Asma'un da duk dauriyar da take jin tana da ita a gaban Adam din ta neme ta a yanzu ta rasa, ta gaji sosai da komai dama rayuwar baki daya, hakuri duk sukayi ta bata, Abba yayi mata nasiha me ratsa jiki, hakan ya sanyaya mata jiki ya sakata yin shiru sai jan ajiyar zuciya take, su kansu sun san tabbas a yanzu ta kai karshe. Da safe ta tashi da missed calls din sa, da text message bayan kiran da yayi mata da ya Hadiza ta fad'a mata da zata bata wayar, ji take kamar bata bukatar sake shigar da kanta wata matsalar a yanzu, amma kuma ba zata iya yi masa wulakanci ba. Wanka ta fara yi, tana shiryawa umma ta shigo dauke da abincin ta, ta ajiye tana kallon ta, shigowar ta uku kenan tana tarar da Asma'un na bacci, tausayin yar tasu suke ji dan sai da Abba yaga da gaske ba a lokacin zata tashi ba ya hskura ya fita, dan da so yayi ya dan kara bata baki kafin ya fitan.

"Umma..."

"Naam Asma'u, kin tashi kenan."

"Eh na tashi, ina kwana!?"


"Lafiya lou, Abban yana ta jiranki, yaki fita da yaga baki tashi ba sai ya hakura suka fita da Abbati."

" Allah sarki Abba, bacci nayi tayi wallahi."

" Ai gwara ki huta sosai, ga abinci nan kici, saura ki tsaya janjani kici sosai."

",Toh umma." Tace tana sauke abincin kasa, ta zauna kenan wayar ta, tayi kara, ta kalli umma kafin ta kalli wayar, shine yake sake kira.

" Shine ko? Ki daga kar yayi tunanin wani abu, jiya ya kira ma."

"Toh." Tace tana dagawa, sai umman ta fita ta ja mata kofar a ranta tana addu'ar dacewar Asma'un

Daga nan tana iya jiyo ajiyar zuciyar da ya sauke, dan shi kadai ya san yanayin da ya shiga na rashin samun ta a waya jiya gaba daya, badan aikin da ya fita ya tsaida shi ba da komai dare sai yazo, shiyasa yau yana tashi ko shiryawa be ba, ya hau kiran ta, be sameta ba yayi mata text message shima shiru shine yanzu har ya zauna a office dinsa yaji sai ya kuma gwada kiran ko zata dauka,

"Ina kwana?" Tayi breaking shirun da yayi ta hanyar gaishe shi, shi kansa be san shirun me yayi ba bayan abinda yayi ta fata kenan yaji ta daga, amma kuma ya lura kamar so yake ta sake magana yaji muryarta tar ya sake tabbatr da ita din ce ta daga a yanzu

"Me bawan Allah yayi aka wahalar da zuciya da ruhin sa jiya? Umm?"

"Babu komai, wayar ce bata wajena."

"Baki san yadda na damu ba wallahi, anyways, hope komai lafiya?"

"Alhamdulillah."

"Ok masha Allah, nazo na ganki?"

"Na'am?"

"Eh? Are you free nazo yanzu, inason ganinki. "

" Owk sai kazo. " Ta samu kanta da hana shi, murmushi yayi wanda har sai da ta jiyo sautin sa, ya ajiye wayar bayan yace mata gashi nan, mikewa yayi ya cire rigar suit dinsa dake rataye a saman kujerar da yake zaune, ya saka yana balle botir din jiki MD ya turo kofar ya shigo rik'e da wasu manyan files, wani kallo yayi masa ganin yana tattare wayoyin sa daga kan table yace


" Don't tell me fita zakayi."

" Fita zan, akwai wani abu ne? "

" Sosai, sai ka duba kayan nan, akwai wajen da zakayi signing kafin su saki kayan. "

" Gaskiya sauri nake, ba zan iya ba, ajiye kawai sai na dawo. "

Dora files din MD yayi a saman table din yana bin Abdallah da kalllo, hanyar fita yayi ya bishi da sauri yana jerawa dashi

"Meeting zaka?"

"A ah."

"Ina toh?"

"Ina ruwan ka? Dole sai kaji duk in da zani?"

"Ahhhh! Yau kuma?"

"Eh." Ya kauda kansa barin kallon MD din dan zai iya ranfoshi nan da nan, cikin lift suka shiga MD nata kokarin sai ya ji in da zaije amma yaki fad'a masa, ya bishi har parking space yana masa magiya, ganin da gaske ba zai fda masa ba, sai kawai ya bud'e motar ya shiga, ya zauna a gefen sa

"Aikuwa sai dai muje tare, nima dama inaso naga Aunt din tamu, taga dan kanin ta itama."

"Mudan wai me yasa kake takura min ne?"

"Toh ai kaine, sai kayi ta boye-boye, yanzu dai muje kawai ko ina zaka sai naji."

" Oya." Ya jefa masa car key din yana balle murfin motar ya fito, sannan ya zuro kansa yana hararar sa

" Kasan ni ba driver ka bane ko? Fito toh."

Ba musu ya fito, ya zagayo wajen driver ya shiga, shi kuma Abdallah ya koma wajen me zaman banza, yaja motar.

Fita tayi ta samu umma a daki, ta dan yi jim kafin ta fad'a ma umma wai zaizo, tashi umman tayi da kanta ta sake tabbatar da falon Abba a gyara yake, sannan tace

" Kin fada masa kina gida? Kar ya tafi chan."

Girgiza kai tayi,

" Kira shi toh, ba dadi sai yaje chan sannan ya taho nan."

Wayar ta dauko, ba zata iya kiran sa ba, dan haka ta tura masa text message na address din gidan, lokacin sun dauke hanyar gidan Ya Hadizan yaga text din, ya saka MD juyawa suka dawo baya, yana bashi direction din gidan har suka karasa, a waje MD ya faka yana kallon unguwar, yana kuma son ya tsokani Abdallah amma kuma sai sun fito, wayar ya ciro ya kirata, gabanta ya fadi ganin kiran sa ,ta mike tana daidaita nutsuwar ta sannan ta daga, toh tace kawai ta ajiye wayar ta fito, umma na ganin ta tasan sun zo, tace taje ta shigar dashi ta kofar gaban gidan. Fitowa tayi ta bud'e kofar gidan ta dan leko, yana zaune cikin mota yaga sanda ta leko, be cewa MD komai ba kawai ya fito, ganin haka ya saka shima fitowa yana ware ido yayi gulma, gaba kawai Abdallan yayi ya bishi a baya, tana tsaye jikin gate din kamshin turaren su me dadi ya riga su isowa, ta yi saurin kallon wajen dan ta tunanin ta basu ganta ba, shiyasa ma daga leko ta koma tana tunanin wanda zata saka yayi musu magana sai gasu, a kunyace ta gaishe su, tayi ciki tace su shigo,

"Nan ma ya isa, kinji?"

Tsayawa tayi, ta dawo duk kunya ta cikata, ta tsaya daga jikin gate din, ya shigo ciki MD na take masa baya

"Auntyn mu." MD uban azarbabi yace yana wuce Abdallan ya shigo ciki sosai

"Yau dai naga wadda ta sace min zuciyar brother na, Masha Allah."

"Kaje mota gani nan"

"Ban gama ba, kina lafiya?"

"Lafiya lou."

"Toh Madallah, sunana Mudassir, amma an fi kirana da MD, kuma ni kanin sa ne, kuma best friend dinsa."


"Allah sarki."

" Kaje mota."

"Zan dawo ni kadai Aunty, tunda yanzu korata yake, bari na je motar bansan me yazo fad'a ba."

Ya juya yana dariyar mugunta, ya fice. Kallon cikin ido yayi mata bayan fitar MD, tayi saurin kauda idon ta tana sunne kanta k'asa,

" Ina office fa, naji kawai inason ganinki, dole na ajiye komai na taho shi kuma wannan uban surutun yazo zai cika miki kunne."

" Ba komai, ai yana da kirki."

" Ko?"

Kanta a kasa ta amsa, hakan ya bashi damar sake more kallon ta, yana admiring kyawunta, da cute innocent face dinta, calmness dinta yaana kara masa sonta

" Pleaseeee...Bari naga fuskarki sosai yadda ko na koma office ba zan kasa aiki ba, sai nayi ta tunawa."

Rufe fuskar tayi da tafin hannun ta, tayi dariya, ita da gaske kunya yake bata dan bata taba experiencing irin haka ba, da yaga da gaske dai kunyar sa take ji sai ya hakura, yace mata zai dawo, amma next zuwan da zai sai ya fara ganin Abba, daga nan sai yaga me ya kamata ayi, ita dai kawai jin sa take yi.
Komawa tayi ciki bayan yayi mata sallama ya tafi, yaje ya samu MD a mota yana waya, tada motar yayi suka bar unguwar har lokacin yana waya, sai da ya gama sannan yake fad'a masa jirgin su Baba Alhaji ya kusa sauka, dan haka yana sauke shi a office din ya wuce airport dauko shi, dan be yarda wani ya dauko shi ba idan ba MD din ko Abuyan ba.
Suna barin unguwar Adam na isowa, duk ya lalata motar sa dan tuki na hauka ya dinga yi baya kaucewa rami ko duk abinda yake hanyar, kafin yazo duk ta kakkarje ga dattin da tayi, Umar yaga sanda ya shigo layin a haukace, ya biyo bayan sa da sauri ya fasa siyan abinda zai siya, kafin ya karaso har ya shiga gidan kasancewar shi a mota yake shi kuma a kafa, a tsakar gidan ya same shi, umma tana tsaye daga kofar dakin ta, Asma'u kuma na cikin daki rufe har da key dan yanzu Adam ya wuce a sashi a layin masu hankali sai dai mahaukata. Sosai umma tayi mamakin yadda ya koma, kamar bashi ba ga uwar kasumba da ya tara na rashin gyara, Umar na shigowa be yi wata wata ba, ya zabga masa mari, ya rik'e shi yana kokarin dukan sa

"Menene haka Umar?" Umma ta daka masa tsawa

"Abinda ya dace dashi kenan umma, duk abinda yake wallahi iskanci ne, dan yaga ana kyale shi ne."

" Cika shi, babu ruwanka dashi duk wanda yayi nagari kansa, ai ko yanzu Adam ya gane cewa ba abu bane me kyau zalunci, idan Allah yaso kamaka sai ya kamaka ta in da baka yi zata ba."

" Toh ai Umma be ma kamata a bar shi ya shigo gidan nan ba, dan zai iya cutar da Asma'u."

" Babu abinda zai iya yi mata."

" Umma dan Girman Allah ayi hakuri, wallahi umma nayi nadama dan Allah Asma'u ta saurare ni, dan Allah magana kawai zan fada mata nasan zata amince."

"Wai Adam baka san babu aure tsakanin ka da Asma'u bane ko yaya?"

" Za'a iya gyarawa umma, dan Allah ki taimaka min."

" Tirkashi! Abun naka babba ne Adam."

Tace tana rik'e baki, jingina yayi da bangon tsakar gidan, Asma'u ta leko ta window ta hange shi a tsaye ya rataya hannun sa ta bayan sa, Umar na gefe yana hararar sa kamar ya kai masa bugu, umma kuma na kofar dakin ta, tana jiran Abba da ta kira yace gashi nan, komawa tayi ta haye gado tayi kwanciyar ta, dan bata da bukatar ji ko ganin duk wani abu da ya danganci Adam din.
Shiru Abban be karaso ba, umma ta shige ciki aka barshi a wajen, a rana amma kamar be damu ba, ya cigaaba da zaman jiran fitowar Asma'un, a daidai lokacin Fido da kawayenta suke isa gidan, Hajiya Mama na tsakar gida tana bawa masu aikinta sallahu dan Abba yace tazo gidan ayi magana, sai gasu sun shigo sun saka Fido a tsakiya ta sha lullubi a dole amarya, turus Hajiyan tayi, jiki a sanyaye ta jasu cikin falon, suka gaishe ta Faiza tace amarya suke kawo, da kanta ta tashi ta rakasu har gidan Adam din, sannan ta fito jikin ta na kara sanyaya, a halin da Adam din yake ciki yanzu bata san yadda zai karbi batun auren ba, wanda ita kanta bata san me ya sha kanta ta amince ba, dan sai yanzu take jin ta tafka babban kuskure wajen amincewa,amma kuma bata san ya zatayi ba, bata da zabi.



_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*


RM

*28*

*****
Yana tsaye a tsakar gidan Hajiya ta shigo, ganin ta be saka shi tashi ba, sai ma sake gyara tsaiwar sa da yayi dan ko sama da k'asa zata hade yau sai yayi magana da Asma'u, yasan zata fahimce shi, yasan zata sake bashi dama,

"Adam!" Ta kira sunan sa tana rik'e bakin ta, sai kuma ta kada kanta zuwa ciki tana kwala sallama, jin sallamar ta ya saka Umma fitowa, tayi mata iso zuwa ciki, ta kasa zama ta tsaya daga tsaye jikin ta duk yayi sanyi

"Be karaso ba amma nasan daf yake da shigowa."

"Assalamu alaikum." Yayi sallama tana shigowa gidan

"Yauwa gashi nan ma."

Waje sukayo tare, suka tarar dashi a tsaye a gaban Adam din yana masa magana,

"Tsaiwar me kake anan Adam?"

Maimakon ya bashi amsa sai kawai gani sukayi ya zube guiwowin sa a k'asa

"Abba dan Allah kayi min rai."

"Tashi maza, tashi." Ya dago shi amma sai ya noke yana cigaba da magiya da hada Abban da Allah, jikin Mama ya kara sanyi sosai tana daga gefe bata ce komai ba, duk abinda yake faruwa bata tanka ba, fad'a Abban ya soma yiwa Adam din cikin sigar lallashi, amma sam ya kasa fahimta shi dai kawai ayi hakuri dan Allah, ganin da gaske ba zai gane ba, ya saka Abban yin gaba yana cewa

"Umar dauki waya ya kira min Ali."

Toh yace yana komawa daki ya dauko wayar sa, ya kira ya taho da wayar ya mikawa Abban, dagawa yayi da sallama ya gaida Abban,

"Kana jina Ali, yaron nan da yazo neman auren Asma'u nake so ka tura min shi, idan zai iya zuwa yanzu toh, idan sai yamma ma dai ina jiran sa."

"Yawwa." Ya katse kiran yana juyawa wajen Hajiya Mama

"Yaya nayi wa Asma'u miji in sha Allah, dalilin sanin cewa babu aure a tsakanin su da Adamu, dan haka nake so gani baki ga mahaifiyar Asma'u, ina so Adam ya kyale Asma'u ya barta tayi facing rayuwar ta, bana son wata matsala ta taso, alakar dake tsakanin mu tafi karfin abinda zai kai mu wajen hukuma, amma tabbas da ba Adam bane ya dauki Asma'u toh sai dai hukuma ta raba mu dashi."

"Na sani." Tace

" Amma kayi hakuri nasan ko ta ina ba'a kyauta maka ba, zan masa fad'a in sha Allah ba zai sake zamar wa Asma'u matsala ba."

"Kai kuma Wuce muje."

Kin tafiya yayi, ya cigaba da magiya, ciki Abba ya shige umma ma haka, ganin yaki tashi ya saka Hajiya Mama fita waje, ta kudura a ranta duk ma abinda zasu masa suyi masa kawai ita ta gaji, tana fita Umar ya fito, ganin babu kowa a wajen yazo da sauri yana kama kafadar Adam din

"Tashi ka fita, wallahi ko zaka mutu Asma'u ba zata ganka ba."

"Dan Allah minti biyu kawai ya isa, dan Allah."

"Ko minti rabi ne wallahi ba zaka ganta ba, kaje chan an kai maka mata, karka zo nan ka ishe mu."

"Mata?"

"Oho idan kaje ai zaka gani."

Cikin hanzari ya mike, yayi hanyar waje da mugun sauri, dariyar mugunta Umar ya fashe da, har da tafa hannu, yana cike da jin dadin yadda abubuwan suka sauya wa Adam din a dare daya, dama chan basa shiri haushin sa yake ji saboda shegen girman kansa. Asma'u na jin duk abinda akeyi, ta sake gyara kwanciyar ta kawai tana jin duk babu dadi.

***Abdallah na office ya samu kiran Abban su Abeed, ya mike tsaye da sauri kafin ya daga wayar, sakon kiran Abban da ya sanar masa ya haddasa masa kasala har ya kasa cigaba da aiwatar da aikin dake gaban sa, duk da dama a yau yayi niyyar zuwa ganin nasa amma kuma sakon yazo masa a bazata, ya kuma saka masa shakku da tsoron Allah dai yasa ba wani abun bane, a daddafe ya karasa abinda yake, be bari

18 / 30