RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 30

42K to 45K   out of 87.6K words

murmusawa yana taba zoben azurfar dake hannun sa. Shigo da tray akayi, Abeeda ce ta ajiye ta gaishe shi ya amsa a sake sannan ta fita, ya jawo tray din ya zuba ruwan yasha hade da Bismillah tana jin shi, sai taji ya burgeta hakan da yayi, ya koma ya zauna yana tattaro dukkan nutsuwar sa

"Husna." Ya kirata da sunan da ba wanda ya taba kiran ta dashi idan ta cire Abba da shi ma yawanci Asma'ul Husna yake cewa idan yaso hakan, muryar sa me taushi ta ratsa dukkan sassan jikinta, tayi tsam a zaune wani yanayi na ratsa ta, sake kiranta yayi

"Husnaaa, ga Abdallah yazo da kokon barar sa, yana fatan zai samu karbuwa, ba da wasa nazo ba, da gaske nake so mu fahimci juna."

" Uhum. "

" Pleaseee karki ce a ah, ko kice na miki tsufa, yaro ne daidai dake wallahi. "

Sautin dariyar ta yaji, yayi murmushi yana jin kamar ya samu lagon ta tunda har tayi masa dariya

" Kin yarda? Zaki bawa wannan bawan Allahn dama? "

Shiru tayi dan bata san amsar ba, eh zatace ko a'ah, yasan ta taba aure ko kuwa? Zai karbe ta a haka ko kuwa? Wannan tambayoyin su suka dinga mata yawo aka tun daren jiya, sai da kuma aka zo gabar sannan taji da gaske Adam ya cuce ta, ko ta ina kuwa.

"Baki ce komai ba?"

"Bansan me zan ce ba."

"Kice eh, please kice eh kinji? Ki bani dama kawai, ba zaki danasanin hakan ba."

"Na taba aure." Maganar ta fito ba tare da ta shirya ba, bata ga yanayin sa ba, bata kuma san tasirin da maganar tayi masa ba, kafin ya bata amsa aka danno kai ta hanyar banko kofar da take ta bangaren harabar gidan, Adam ne a tsaye tamkar mahaukacin zaki, yana huci fuskarsa a hade

" Dama tun ranar da na ganka naji bana son ka, ashe ashe abinda zai faru kenan, Malam wanann din matata ce, ka kwashi tsummokaran kafafunka kafin na saka a babballamaka su ka bar nan wallahi. "

Murmushi kawai Abdallah yake daga zaunen da yake ko gezau be yi ba, duk hargagin da Adam din yake be saka ya motsa ba, hakan ya sake hassala Adam din, ya kalli Asma'un ya daka mata tsawa

" Dallah tashi ki shiga ciki. "

Wani banzan kallo tayi masa, kallon da ya saka shi shiga taitayinsa, ta kuma juya wajen ABDALLAH da yake hakimce yana kallon komai hankalin sa a kwance tace

"Na amince Allah ya yi mana zabin alkhairi."

"Amin Ya Allah my soon to be wife, nagode sosai da wannan damar, in Sha Allah ba zaki nadama."

Kamar basu san dashi a wajen ba, haka suka yi, ba kamar Abdallah da ya nuna kamar Adam din be dame shi ba, nan kuwa haushin sa ne sarke a  ransa, be niyyar tafiya ba a lokacin amma ba zai iya cigaba da zama inuwa daya da Adam din ba, tashi tayi zata raka shi, ya dakatar da ita dan baya so ya tafi ya barta da wannan mahaukacin, rakata yayi har kofar da zata shiga cikin gidan yana take mata baya, cikin wani yanayi kamar na me tsaron lafiyar ta, sai da ta shiga ciki sannan ya juyo, ya fice daga dakin yana kokarin hana kansa jin kalaman da ke fitowa daga bakin Adam din, a daidai lokacin Abban su Abeed ya dawo daga bayan da ya zagaya, ya hango motar Adam din shiyasa yake ta sauri be san already ya riga ma ya shiga gidan ba.

"Har zaka tafi?"

Yace masa yana waige waige ko zai ga Adam din

"Eh wallahi, amma zan dawo, kamar kayi bako ma,."

"Bako? Yana ina? "

" Yana ciki. "

" Adam! Kayi hakuri dan Allah, babu wanda ya san da zuwan sa, kamar yadda na sanar da kai ne, babu wata alaka yanzu tsakanin su illa ta yan uwantaka, ba dan wannan ba ma na tabbata da yanzu shari'a ake, dan ba zamu kyale ba, dalilin da ya saka na sanar maka kenan, saboda ba'a boye maganar aure a nema. "

" Babu komai, da gaske nazo zan auri Asma'u ko da aure dari tayi ta fito, kuma shi Adam din zan yi maganin abun, so karka damu. "



*RM*

    *22*

***Ciki ya shiga bayan Abdallan ya tafi, ya tarar da Adam din yana kai komo a compound din gidan, yana ganin shi yayo wajen shi da sauri

"Adam kana cikin nutsuwar ka kuwa?"

Ya fad'a ganin yadda kirjin sa je bugawa da karfi, dafa shi yayi jin You know what I don't remember the number Now kamar zai zube a wajen, ya taro shi yana furta

"Subhallah;"

Cikin seat room din ya kai shi,ya taimaka masa ya zauna ya zuba masa ruwa ya mika masa, karba yayi ya kafa kai, be ajiye ba sai da ya shanye tas, ya mika masa cup din ya mike, yana kiran sa be amsa ba, ya fice da sauri ya fad'a motar sa, ya tada ita a guje ya bar layin!
     Unguwar ya nufa yana jin duk abinda za'a yi sai dai ayi, amma sai ya je, yana isa ya tarar da gate din a rufe yan sandan suna zaune daga gefe, horn ya danne yana daga cikin motar suka kallo shi, tasawo sukayi, ya sauke glass din yana zura kansa

"Wajen wa kazo?"

Kafin ya amsa dayan yace

"Baka gane shi bane? Gayen nan ne da yayi mana rashin kunya ranar har Oga Abdallah yace a kaishi gida."

"Oh na tuna, kai me ya kawo ka nan?"

" Wajen uban gidan naku nazo,idan har ya cika shi din jarumi ne, ya fito ya fuskance ni, ni kadai ba tare da ku ba."

" Gayen nan fa kamar yana da matsalar brain, ku wuce muga iya kar haukan sa."

Barin wajen sukayi suka koma suka zauna, ya dinga horn yana kumfan baki, sukayi masa banza hakan ya sake kona masa rai, ya juya ya bar layin. Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya dan mahaukacin gudu ya dinga yi, ko parking din be daidaita ba, ya shiga gidan su, Mama na zaune taga ya fado

"Lafiya Adam? Na shiga uku."

Zube mata yayi cikin wani irin yanayi yace

"Mah Asma'u."

"Me ya same ta?"

"Wani, tare da wani na ganta, Mah zan mutu, wallahi zuciya ta ba zata iya dauka ba."

"Me zan gani? Macen kake wa wannan abun, macen ma Asma'u da kace baka son ta?"

"Karya nake wallahi, I'm a very big liar, ban san me nake aikatawa ba a lokacin. "

" Ka manta babu aure a tsakanin ku toh? "

" Nayi laifi dan Allah mAh karki bari a hukuntani da shirmen da na aikata, a nemi wasu malaman ai ance saki uku a kalma daya, daya ne."

" Saboda irin ku ai masu yin saki ukun na ganganci daga baya ku dawo kuce ba haka ba, aka hana, ka riga ka saki Asma'u saki uku cif ko a kalma daya ko a kalma daban daban ta saku."

Da sauri ya hau rarrafawa zuwa wajen Nadeeya da ta fito daga daki ta bashi amsar nan, ya kama kafarta cikin tashin hankali yace

"Dan Allah sister karki ce haka, sabanin malamai, dan Allah karki haramta min Asma'u wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba."

"Tirkashi, wannan shine abun da na guje maka Adam." Hajiya Mama tace tausayin dan nata na kama ta, janye kafarta Nadeeya tayi tana zama a kujera tace

"Bama tare a wannan lokacin boy, the earlier you realize the better for you, kayi wasa da damar ka Asma'u tayi maka nisa."

"Na shiga uku!"

Yace yana dafe kansa, kallon sa mama take ganin kamar ba adam dinta ba, sai a yanzu taga muguwar ramar da yayi, yayi baki ya wani shiririce, babu tsaftar nan da gayun nan kwata-kwata, girgiza kai kawai ta dinga yi dan al'amarin ya sha kanta yafi karfin ta, bata san ta ina zata bullowa al'amarin ba, shi kadai ya dinga mirgina kansa yana rik'e shi kamar wanda ya samu matsala, suka taso kansa suna tambayar sa me yake ji amma ya kasa magana, wannan wacce iriyar soyayya ce haka ta kama Adam, lallai Allah na azzalumin Sarki bane, duk abinda kayi Yana kallon ka, dole akwai ranar sakayya ko a kusa ko a gaba. Da k'yar Maman ta samu ta lallaba shi ya kwanta a saman kujerar falon, Nadeeya ta samo allurar bacci tayi masa ganin yana ta surutai, kafin allurar ta dauke shi sai da yayi ta nanata sunan Asma'u, har idon sa ya rufe ruf. Tagumi Hajiya Mama ta zabga a gabansa tana kallon sa, ji tayi hawaye na sakkowa a saman fuskarta, ta saka hannu ta share tana komawa dayar kujerar ta zauna abun duniya ya taru yayi mata yawa.
    Shirye shiryen biki Fido take yi ita kadai bata damu da Adam din yana so ko baya so ba, ta riga tayi wa kanta alkawarin auren sa ko yana so ko baya so kuwa, duk abun da ya kamata tayi Faiza ce ke tsaya mata, ita ke sakata a hanyar komai, dama da kudin ta, kashe su kawai take tana shiryawa kanta da auren da zatayi, wanda da yawa kawayenta suke mata bakin ciki akai, ita dai ko a jikin ta, burin ta kawai ta shiga gidan Adam din, ta kuma juyashi a tafin hannun ta tamkar yadda ya dade yana gara rayuwar ta tamkar yar gare-gare.  Dawowar su kenan daga kasuwa tare da Faiza aka kirata a waya, kafin ta ciro wayar ta katse, ta duba taga Hajiya Mama ce, tayi dariya tana nunawa Faiza

"Mutuniyar ki ce."

"Sirikarki wai?"

"Ita."

"Auw wai har kiranki take kenan."

"Wannan ne na biyu, ta matsu watan nan ya kare ayi bikin nan."

"Lallai Malam Ya'u yasan ta kan tsiya , ya bi da ita wallahi. "

" Bari na kira naji me ya faru kuma? "

" Owk kira muji."

Kira tayi Nadeeya ta daga, lokacin Maman ma kan Adam tana tofa masa addu'a, dan duk farkawa tun da allurar ta soma sakin sa yake surutai, da sumbatu, gashi da kunya ta kira Abban su Asma'u ta fad'a masa, bata san me kuma zatayi ba, gaba daya komai ya tsayaa mata chak,

" Bata kusa zata kira idan ta dawo. " Nadeeya tace ta katse kiran tana jan siririn tsaki,

" Kinga fa da gaske Adam yake fa, yanzu ya zamuyi? "

" Ya zamuyi Mama, ba zai yiwu ba wallahi. "

" Kunyar kiran karami nake, bansan me zan gaya masa ba. "

" Karma ki kirashi Allah, ai da kunya. "

" Shikenan sai na bar Adam a haka, tun yanzu ji yadda ya fara komawa inaga nan gaba. "

"Toh ai duk laifin sa ne ma, shi mutum daraja ce dashi, sanda yake wulakanta ta, be tuna irin wannan ranar ba. "

" Yanzu Nadeeya wannan maganganun naki me zasu sauya? " Bayan aikin gama ya gama ai sai ki goyi bayan shi ko sau daya ne, ba wai kiyi ta nuna kamar ma dadi kikeji da hakan ta faru ba, duk tsiya Adam jinin ki ne."

"Toh Mama na yi shiru."

"Yafi dai, bani wayar na kira Karami."

"Mama?"

"Bani nace, Kanina na ne ba naki ba."

Mika mata tayi

"Kira min shi ki bani, ai naka sai naka, ba zan iya jurar ganin Adam a wannan halin ba, hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar, ballantana nasan karami yana kauna ta da duk abinda nake so."

"Gashi an daga." Ta mika mata tana matsawa gefe

"Lafiya lou, ya matar gidan?"

"Alhamdulillah, Adam ne bashi da lafiya wallahi." Sai ta fashe da kuka,

"Dan girman ALLAH ka taimake ni kar na rasa shi, kayi hakuri ka dawo masa da matar sa. "

" Yaya? " Ya katse ta da sauri cikin tsananin mamaki

" Dan Allah ka taimaka min, wallahi yayi nadama sosai ba zai sake ba. "

"Yaya kin manta babu aure tsakanin Adam da Asma'u ne? "

Cikin kuka tace

" Aje wajen malamai, akwai wadanda suke ganin tunda a kalma daya ne, za'a iya komawa. "

" Tirkashi! "

Ya ma rasa bakin magana, magiya ta cigaba da yi masa tana kuka wiwi

" Ka taimaka min dan Allah, ka dubi girman zumunci dan Allah. "

" Zanzo gidan Yaya, wannan maganar ba ta waya ba. " Be jira ta sake magana ba, ya kashe wayar yana murmushi

" Yaya Asabe ce. " Yace wa Umar da yake suna tare

" Wai so take Asma'u ta koma? "

"Eh wai. "

" Allah ya rufa asiri. "

" Toh Amin Babana. "

Har suka zo gida maganar na yawo akan Abba, ya bawa Umma labari tayi dariya kawai, dan bata so tace wani abu ne kawai saboda girman da Hajiya Maman take dashi a wajen Abba, amma da ba haka ba, da anji maganganu manya manya. Missed calls wajen biyar tayi masa, ya daga daga karshe ta cigaba da masa magiyar dan Allah ya daure yazo, yace zaizo zuwa da safe, ba dan taso ba tace toh, amma gani take safiyar tayi mata mugun nisa.


_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276

Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*



*RM*

     23

***Hannun sa rik'e a cikin na Baba Alhaji suka karaso wajen motar, ya bud'e masa ya shiga yana jaddada masa abinda suka tattauna, murmushi ne kwance a fuskar sa har zuwa lokacin da motar ta fita daga cikin gidan, juyowa yayi yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, ya burza shi yana taba airdrop din dake sakale da kunnen sa,  kiran ta yake so yayi tun dazu, yaji zazzakar muryar ta me sanyi da taushi, sai dai Baba Alhaji be bashi damar hakan ba, dan be bar shi ba tun bayan da ya dawo sai da ya tabbatar da ya sake jaddada masa abubuwan da yake so a aiwatar kafin dawowar sa. Tafiya yake a nutse irin ta jaruman maza masu cike da nutsuwa da haiba, ta daga kiran nasa hade da sallama, bata san shi bane dan be karbi number a wajen ta ba, sai bayan ya tafi ne ya tuna ya kira Abban su Abeed ya tura masa, a time din yaso ya kirata amma kuma shi mutum ne me bin komai a kaida da tsari, baya so ya takura ta musamman da rabuwar su kenan be san ko ta shiga wani uzurin ba, sai kuma yazo ya samu Baba Alhaji ya rike shi gam be barshi ba sai da ya tafi, zai je Abuja yayi kwana biyu akan wasu estates din sa guda biyu da yake son saidawa.
  Sallamar ya amsa cikin bawa kowanne harafi hakkin sa, murmushin tayi me sauti, ta gaida shi ya amsa yana karasawa wata yar kujera ta zauna, sannan ya tambaye ta gida da kowa da kowa, ta amsa masa muryar ta tar babu nuku nuku, kwarin guiwar yaji ya samu sosai, ya gyara zaman sa ya shiga yi mata yan tambayoyi a game da abubuwan da yake son sani a tattare da ita, yadda take bashi amsar yafi masa komai, dan a cikin amsar ya fuskanci nutsuwar ta, wadda ya hanga tun jiya a supermarket din, shagala sosai yayi da hirar, dan sosai yake jin dadin hirar har be san an dau lokaci haka ba. MD ne ya dawo yake ta neman sa ya rasa shi, yaje part dinsa yaje masallaci amma duk baya nan, kuma a gate baa ce masa ya fita ba, motocin sa duk suna nan har wadda ya hau yaje zancen dazu, ya matsu su hadu ya tsokane shi, tunawa da yayi da hanyar garden din dake bayan gidan yayi, ya nufi chan da dan saurin sa yana ayyana samun sa a wajen. Ta baya ya hango shi, shi kadai amma da dukkan alamu waya yake, da sanda ya karaso wajen ya labe daga baya yana jin wayar da yake muryar sa tar kamar bashi ba, sai yaji kamar ma har wani makale muryar yayi, ya ji yana cewa pleaseeee, hadda marairace murya, rik'e bakin sa yayi da yake neman tona masa asiri yayi, ya zaro wayar sa ya danna record, ya kara matsawa kad'an daidai lokacin da yayi mata sallama, bayan ta kashe ya furta

"I love you my asmy, love at first sight!"

Sai ya jingina da kujerar yana lumshe ido, ihun dariyar MD din ta sakashi juyowa da sauri, ya dinga tafa hannu yana zuwa wajen nasa, mur yasha sosai yana mikewa

"Dan sa ido, menene na biyo ni nan din?"

"Ai kai ma kasan wallahi dole na saka maka ido, Abuya ne yau yake waya da mace, who's this lucky girl, gaskiya yau za'a yi ruwa da soyayyen kifi, wai."

"Allah MD bana son abinda kake min, me ka maida ni ne!?

" Agogo mana, ko nace dutse dan ni wallahi Allah na dauka ma baka da lafiya ne, ashe ashe kana ankare. "

"Mtss, kana da matsala wallahi. "

Ya juya zai barshi a wajen

"I love you my Asmy... "

MD ya kwaikwaye shi yana buga kafa, juyowa yayi a kunyace zai kai masa duka ya goce

" Haba ango Ma'u, wuce nan na tsaya, kuma wallahi yau zan fasa maganar nan a babban falo, kowa sai yaji musamman ma Mum, bari kaga."

" Tsaya Dan Allah, kar muyi haka da kai, dan Allah karka min haka. "

Kin tsayawa yayi, ya biyo shi da sauri yana

15 / 30