RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 30

33K to 36K   out of 87.6K words

uku, ki fadi ko nawa kike so zan baki amma ki tafi kiyi nisa sosai da nan, dan Allah na roke ki."

" Gaskiya ba zan iya ba, saboda ni ba yarki bace? Bayan shi ya bata min rayuwa ya raba ni da nawa iyayen sannan kice na hakura na tafi, ina zanje da ciki?"

" Toh a zubar, dan Allah ki taimaka min."

" Mah ya zaki tsaya kina bawa wannan yar iskar hakuri."

" Idan ka sake magana sai naci mutuncin ka wallahi, duk ba kai ka jawo min ba."

" Atoh, ni dai wallahi bansan yadda zan da cikin nan ba, ba zan kuma iya zubarwa ba, ko Adam ya karbi cikin sa ta cikin lumana ya yarda ya aure ni, ko na kaishi kotu wallahi."

Sai ta mike,

" Zan dawo gobe, kafin nan sai ku yanke abinda zai fi muku."

Ta harari Adam din, ya kai mata duka ta goce, kunya kamar zata kashe mama, ga takaici ga baccin ran abinda ya faru ga kuma wannan masifar, yanzu ya zatayi da wannan yarinyar? Daga ganin ta, tatacciyar yar bariki ce, ba abinda ya dame ta, bata ki ayi duk abinda za'a yi ba, dan babu kunya ko digo a al'amarin ta.
Tana fita ya dawo kan Maman zai yi magana ta daga masa hannu

" Bana son naji komai, kaje yadda ka ja ra'ayin ta babu wanda ya sani kaje ka roke ta, tayi hakuri ta zubar ko a bata kudi."

" Allah ya kiyaye walalhi, ita din banza, babu abinda ta isa tayi wallahi, karya take ni ban mata komai ba, ta san in da dare yayi mata dan babu shegen da zai sakani na karbi abinda ban yi niyya ba."

" Har ni!?" Maman tace

Kunkuni yayi, ya wuce ta rafka tagumi zafi goma da ashirin kenan, ina zata saka kanta ne taji dadi. Sakayyr da Adam din zai nuna mata kenan bayan duk irin gatan da ta nuna masa.


****Har suka karbi sakon suka bar unguwar MD be daina tsaki ba, gayen yayi masifar bata masa rai, dan dai Abuya yaki barin sa ne da sai ya gane cewa su ba sa'annin sa bane.

" Still dai baka hakura ba MD?"

Ya tambaye shi yana dora kansa saman kujerar motar daidai lokacin da suka shigo layin su

" Kana ganin fa yadda yake daga mana kai, shiyasa ni fa yanzu ban fiya son fita tare da kai ba, ka fiya hakuri wallahi, dani kadai ne da ya gane shayi na ruwa me."

" Menene amfanin rashin hakurin? Beside ba wai yayi mana wani abu bane me muni, ko da ace yayi din ai be kamata mu biye masa ba ko?"

Dukan sitiyarin motar yayi,

" Kullum haka kake cewa, ai kai kam kana da heart of gold, matar ka ta huta wallahi."

Dariya ya saka yana maida ganin sa zuwa cikin katafaren gidan nasu sanda gate din gidan yake budewa, sai da suka shiga ciki motar ta daidaita sannan ya bashi amsa

" Kai kuma matar ka ta shiga uku da mitar ka."

Balle murfin motar yayi ya fita, ya zagayo ta bangaren MD din yace

" Mika musu sakon ka same ni a masallaci,."

"Okh Ya sheik!"

Murmushi kawai yayi, ya nufi masallacin cikin gidan yana nannade hannun rigar sa.

Ciki MD din ya shiga dauke da sakon Baba Alhaji, ya tura kofar falon ya ajiye saboda babu kowa, ya fito ya nufi masallacin dan yasan duk suna chan.
Sallah sukayi tare da ma'aikatan gidan da makwafta na kusa da suke shigowa ta kofar waje, ana idarwa suka zauna karatun bayan magriba har zuwa lokacin isha, sannan suka yi sallar kowa ya fito, tare suka jero da Baba Alhajin suka saka shi a tsakiya suna maganar aiken da yayi musu, MD ne yake bashi amsar duk tambayar da yayi dan shi gogan dama mafi yawancin lokuta MD din ne ke aron bakin sa yaci masa albasa, sai ayi abu sau tari sai dai yayi murmushi kawai, baya dogowar hira idan ba da MD din ba, shi kadai yake sakewa suyi hira sosai, mutane har tambaya suke anya Abdallah yana magana kuwa, dan sai ka wuni dashi baka ji yace komai ba.

Sai da suka rakashi har ciki, ya zauna sannan suma suka zaune cike da girmamawa, ya kalle su dukka, yace

"Abuya, miko kayan nan na gani."

Tashi yayi ya dauko ya kawo masa gabansa ya ajiye,

"Kai kuma Mudassir, tashi ka bud'e mu gani, Allah dai yasa an yi abinda ya dace."

"Amin, suka amsa MD ya bud'e kayan suka dudduba, komai yayi yadda ya kamata, maida su gefe akayi, suka dan taba hira kad'an kafin su tashi su wuce zuwa shashen su.


Suna shiga MD ya fad'a saman kujera ya sauke numfashi,

" Mitar ce?" Yace yana kokarin shiga chan ciki

" Kana da matsala wallahi."

" Toh ai naga abu baya wucewa wajen ka ne fa."

" Wannan din ma be wuce ba, har sai na hadu dashi na koya masa hankali."

" Allah ya bada sa'a."

Ya wuce ciki, ya sauya kayan jikin sa sannan ya dawo falon nasu, ya tarar da MD din yana waya, yana kashe murya tamkar bashi ba, girgiza kai yayi ya jawo laptop dinsa ya jona ya shiga rage ayyukan dake kansa.


***Bangaren Asma'u kuwa, sosai ta kwantar da hankalin ta, dan dama ba wai ta damu bane, kawai dai tana bukatar healing daga abubuwan da suka faru, gata babu irin wanda Abba ya nuna mata, yana dawowa gjda zai saka a kira masa ita su zauna yayi ta hilatarta da hira, tun tana nokewa har ta saki jikinta, tana jin ya dawo idan ta daidaici ya huta take zuwa, hakan ya taimaka kwarai wajen samun nutsuwar ta, bata tuna Adam bare shirgin sa, ranar suna zaune Hajiya Mama ta kira Abba, tunda abin ya faru bata kira shi ba, dan bata da bakin da zata masa magana, yanzu ma maganar Fido ce ta hana ta sakat dan yarinyar babu alamun zata hakura, ita kuma a yanzu duk yadda zatayi ta kare mutunci da martabar gidan ta zatayi. Tashi yayi ya saka Abbati ya kaishi, sai yayi mamakin ganin ramar da Hajiya Maman tayi, kana gani zaka gane bata da lafiya sosai,ji yayi duk babu dadi, ya zauna ya gajshe ta, ta amsa masa a kunyace ta saka aka kawo musu ruwa, fita waje Abbati yayi ya barsu su kadai, ta shiga sansr dashi matsalar da take fuskanta tun bayan rabuwar Adam din da Asma'u, shiru Abban yayi yana nazarin maganar a zahiri, a badini kuwa girman Allah yake sake gani, ko babu komai Asma'u ta wanko, kuma tayi biyayya irin wadda ba kowa ne zai yi ba, ganin yaki cewa komai a tunanin ta ba zai taimaka mata ba, sai ta fashe masa da kuka tana bashi hakuri, da sauri yace

"Dan Allah Yaya kiyi hakuri, komai ya wuce a waje na, yanzu kokarin yadda zamu kauwar da matsalar da take gaban mu ce kawai, abu daya za'a yi, shine tirsasa Adam auren yarinyar nan, idan ba haka ba, matsalar da zata jawo gaba sai tafi haka, kuma kince dalilin sa take zaune a garin nan."

"Haka ne."

"Toh shawara daya, ya aureta,tunda sun fahimci juna sun san junan su, zaman zai musu sauki, sai ta haihu a dakin ta cikin rufin asiri."

"Na shiga uku, yanzu Karami ina rufin asiri a haihuwar tit."

" Toh ya za'a yi Yaya? Ko kina da wata shawarar."

Girgiza masa kai tayi,

" Kin gani, hakan shine rufin asirin mu dukka."

Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta dinga jan maganar ta gaza furta abinda zata ce, bata san da wacce fuskar Abban zai kalle ta ba, kila ya kirata da wadda tafi kowa son kai a duniyar baki daya, har tsawon mintuna ta gaza cewa komai, yana lura da yanayin ta, magana take son yi ta kasa, mikewa yayi yana gyara babbar rigar sa

" Zan koma Yaya, idan akwai wani abu sai a sanar dani."

" Toh toh, nace ba... Dan Allah ba zakayi hakuri Asma'u ta dawo dakin ta ba?"

Chak ya tsaya da abinda yake, ya kalli Maman, tayi saurin dauke kanta, shiru ya biyo bayan maganar ta ta, dan be san me zai ce mata ba, kunya ce ita kanta ta kamata, tayi saurin cewa

"Bansan na furta ba, kayi hakuri."

"Allah ya kyauta."

Yace kawai yayi mata sallama ya tafi, yana fita ta dafe kanta tana jin kamar zai tarwatse mata, sakamakon makauniyar soyayyar da ta nuna wa Adam din kenan, karshe ita zai saka a masifa dan ta lura shi be damu ba da duk abinda yake faruwa ba, kwana biyu ma bata saka shi a idon ta ba, an dai tabbatar mata a gidan sa yake kwana amma baya shigowa nan din, hankalin ta duk yana kanshi tana tsoron kar yaje yayi wani abun.

Ranar da wuri ya shigo gidan, ya kalli dinning area din yaga wayam, tsawon kwanaki uku kenan duk sanda ya shigo gidan sai idon sa ya jashi zuwa dining din, daga nan sai zuciyar sa ta tunzura shi ya kawar da tunanin da yake neman hanashi sukuni, shiyasa baya zama a gidan kwata kwata, da ya shigo sai yaga tamkar ita din zai gani, yau ma dalilin dawowar sa gidan da wuri saboda kansa da yake masa ciwo, neman Fido yake ido rufe amma sam ko a waya baya samun ta saboda ta shirya ci masa mutunci, sosai ya shiga matsala sanadiyyar hakan da shi bashi da burin auren mace irin Fido din gashi kuma tana neman sakashi dole, duk da yana ganin babu uban da ya isa ya sakashi auren da be niyya ba.
Kai tsaye sama ya hau, ya nufi dakin ta, inda koman ta yake a yadda ta barshi sai kayan sawarta kawai da Ya Hadiza tazo ta kwasar mata tun ranar da ta tafi, babu wanda yazo yace zai dauki wani abu kuma bayan nan, saman gadon ya fad'a mayen turaren ta da yake jin yana shigar masa hanci yana nan manne da zanin gadon da blanket din da ta rufa dashi a ranar da ya dake ta, kwanciya yayi, ya rufe kansa da blanket din kamshin na ratsa shi, ya jima sosai a hakan har sai da abun ya dawo kansa, ya tuna a inda yake, ya kuma tuna abinda yake, ya mike zumbur yana yin jifa da bargon ya sakko yana jan tsaki, cikin son karfafa kansa akan abinda yake ganin ba me yiwuwa bane, amsa kuwwa muryar ta, ta shiga yi masa a kunne tana ratsa shi, sanda take masa magiya akan ya daina dukan ta, muryar ta tar cikin yanayin wahaltuwa, kama kansa yayi da hannayen sa biyu ya damke, ya toshe kunne yana girgiza kansa, yana magana da sauri yana barin dakin

"Na tsane ta, bana son ta bana kaunar ta, na tsane ta, na tsane ta!"

Ji yayi zuciyar sa ta karyata shi, ta maida masa da martanin karya yake, da sauri ya suri key din motar sa, ya shiga ya bar gidan gaba daya, sai dai maimakon hakan ya taimaka masa wajen samun saukin abinda yake bijiro masa, sai ma abinda ya karu, yawo ya dinga yi a titi, ya shiga nan ya sauka nan ya rasa in da zai kai kansa, a ganin sa yana da damar da zai iya yin fatali da banzan tunanin da banzar zuciyar sa take saka masa ba, be san cewa, addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi da Allah, kai tsaye Allah yake amsata.
Wasa-wasa sai gashi ya kusan kure duk titinan, gangarawa yayi wata babbar unguwa dake kusa da in da yake, ya shiga wani layi yayi parking motar ya kashe kawai ya kwanta a ciki. Ya dan dade a cikin motar dan layin babu mutane babu hayaniyar kowa duk suna cikin gidajen su, ji yayi an masa knocking a window din sa, ya dago ya kalli mutumin dake tsaye.

"Malam lafiya?"

"Kamar ya?"

"Eh naga kazo nan ka zauna ne tsawon lokaci, idan wata matsalace sai ka fada ko?"

"Ina ruwan ka? Ko tsabar shishigi!? Ku me yasa sam mutane bakwa minding business dinku ne, da kunga mutum sai kuzo ki ishe shi da tambayoyi, mtsw bana son irin haka."

"Daga tambaya? Naga ka dade ne a wajen, kuma a ka'idar unguwar nan matsayin mu na masu kula da tsaron wajen bama barin bare ko wanda bamu sanshi ba, ya zauna haka babu wani abu, ka dauke motar ka kayi gaba, ko kuma ka fuskanci hukunci. "

" In naki fa? "

"Jikinka ne zai gaya maka. "

"Babu in da zani, tunda dai nan din ba gadon gidanku bane ai, idan kuma gadon ku ne sai naji."

"Owk, tunda haka kake so, fine! "

Sai ya kalli bayan sa

" Kuna ina!? "

"Gamu sir."


"Ku dauke shi daga nan, ku dan sassamamin shi ko zai koyi manner's."

"An gama sir, Adam na zaune wai shi uban taurin kai, sai gani yayi sun karaso, suka bud'e motar suka fizgoshi, suka shiga lallasa shi tamkar yadda ogan nasu yace. Gate ne ya bud'e mota ta fito daga gidan Baba Alhaji, Abuya ne, shi kadai babu MD shima zai je ya siyo perfumes ne saboda nasa sun kare, ganin kamar suna dukan wani ya sakashi danne horn, suka dakata ya fito da sauri

" Lafiya kuke dukan sa? "

" Barawo ne! "

" Barawo? " Yace yana leka fuskar Adam din, nan da nan ya shaida shi, dan yana da saurin gane mutum

" Satar me yayi? "

" Tun dazu yake zaune kamar bashi da gaskiya, shine oga yace bari yayi masa magana amma sai ya hau oga da cin mutunci, shine muke dan koya masa hankali."

"Ku kyale shi, tashi."

Ya mika masa hannu. Adam da yaci bugu sosai a wajen yan sandan majiya karfi ya kasa mikewar, bakin sa ya mutu murus dan har ya soma basu hakuri, be taba dakuwa irin ta yau ba tun da uwar sa ta haife shi, sai gashi a banza masu warin kashi sun daddaka shi saboda shegen bakin sa.

Taimaka masa Abuya yayi, ya tashi sannan ya rakashi wajen motar sa,. Ya bud'e masa gefen me zaman banza ya shiga, sannan yace dan sandan guda yazo ya kaishi chemist sannan ya kaishi gida, ba musu yazo ya shiga, ya kalli Adam din da yaki yarda ya kalli bangaren sa yace

"Kayi hakuri aikin su kenan, da ka basu hadin kai duk hakan ba zata faru ba."

Kin magana yayi, ya juyar da kansa dan iyakar muzanta ya muzanta, har baya son ganin mutumin gashi ya tsaya yana bata masa lokaci da wasu maganganun sa na banza, kila ma su suka saka aka sake shi akan abinda ya faru ranar, amma koma menene, ai ba zasu dawwama a cikin unguwar tasu ba, idan kere na yawo, zabo na yawo toh dole zzsu hadu, kuma sai ya rama wulakanci da akayi masa.


*RM*

     18

***Har kofar gida ya kaishi ya ajiye ya wurga masa mukullin sa ya tafi, gidan su ya shiga a maimakon nasa gidan da ji yake ya tsani duk abinda ya danganci gidan nasa, yana shiga Hajiya Mama ta dauke kanta kamar bata ga shigowar sa ba, sai dai yanayin yadda yake tafiya ya saka ta kallon sa, ya wuce zuwa tsohon dakin sa ya shiga, akwai matsala, ta lura abin ka da uwa mahaifiya sai ta kasa jurewa har sai da ta tashi ta bishi zuwa dakin, ta tarar ya cire rigar sa yana kallon bayansa a mudubin dakin, zaro ido tayi ganin layin bayan sa, yayi kamar be ga ta shigo ba, ya hau maida rigar sa

"Me ya same ka?"

"Ba komai." Yace yana to maida rigar jikin sa,

"Karka fad'a min din, jikinka ne ai ba nawa ba, mun yanke shawarar aura maka fiddausi saboda rufin asirin mu."

" Wa zai aure ta? Ni wai? Karya ma fa take bata da cikin komai, idan ma dashi ai baa aure da ciki ko? "

Ya kyalkyale da dariya, shiru Hajiyar tayi, tunanin hakan sam be zo mata ba, tabbas musulunci yayi hani da aure da ciki, duk da akwai masu yi saboda son zuciyar su, itama sam bata tuna hakan ba saboda idon ta ya rufe, amma me yasa Abba ya bata wannan shawarar toh? Shima ya manta ne ko kuwa dai yana daukar ta a yanzu xata iya komai ma don biyan bukatar ta, shiyasa ma be tsaya nuna mata ba yayi komai a dunkule, nufin sa duk abinda zatayi kawai tayi ko da hakan ya saba wa addini, girgiza kai tayi ta juya ta bar dakin, jirin da take ji yana kara karuwa, kwanciya tayi ko zata samu sa'idah amma sai taji a kwancen ma jirin take yi, kiran Nadeeya tayi da ta tafi chan gidan kanin baban su da rikicin nan be bar Hajiyar ta samu halartar komai na bikin ba, saukin ta dama ba a gidan ake taron ba girki dai ne akayi anan da sauran abinda ba za'a rasa ba, shiyasa yau tace Nadeeya din taje ta kara basu hakuri, jin jikin nata ya kara rinchabewa ne ya sakata kiran Nadeeya din, tace ta dawo bata jin dadi, bata dade ba sai gata, ta tarar da Hajiyar zazzabi ya rafke ta, ga jirin da ya dameta a kwance ma yin shi takeyi, auna bp dinta tayi, taga yayi high sosai, ta shiga bata taimakon gaggawa, zuwa dare jikin ya sake rikicewa, dole ta dauke ta, ta tafi da ita asibiti, nan da nan akayi admitting dinta, aka daura mata drip, nabeela ta kirawo sannan ta kira fadeela ta fad'a musu an kwantar da Maman dan duk abinda ake su ba wani sani sukayi ba, nan da nan sai gasu, lokacin Maman ta samu bacci , ta rame sosai kamar ba ita ba.
   Tare duk su ukun suka kwana da ita, dan dama duk babu me wani nauyi akansa, nauyin miji ne kawai babu wacce ta haihu cikin su, basu kira Adam ba, dan haushin sa suke ji sosai, duk shine yayi sanadiyyar shigar Maman halin da take ciki, kuma kamar be damu ba, kansa kawai ya sani.
   Da safe ya shiga cikin gidan ya tarar basa nan, ya tambayi mai aiki suna ina, sai anan yake jin an tafi da Maman asibiti, ya

12 / 30