Author : RANO Category : African Stories & Novels
ciro wayar sa ya kira Nadeeya amma bata daga ba, ya dinga jera mata kira har ya gaji, ya dauki mota dan yana da yakinin asibitin su zata kaita.
Yana zuwa ya samesu a chan dan a barander suka hadu da fadeela ta fito siyan abu, ta share shi yana mata magana tayi tafiyar ta, sai ya bin bayanta har ta siya abinda zata siya ta juya sannan yaga dakin da Maman take. Babu wanda ya kulashi a cikin su, ya shigo ya zauna kusa da Maman yana rik'e hannun ta a cikin nasa, baya so wani abu ya samu Maman dan bashi da tamkar ta kaf duniyar nan, ji yayi yana nadamar wasu abubuwan da ya aikata, wanda ya tabbata su suka janyo shigar matsalar Maman, ba zai kyale Fido ba, duk ranar da ya kamata wallahi sai yayi mata rashin mutuncin da bata taba zato ba, dan yasan ita ce ta sake assasa matsalar da Maman take ciki.
Ko da maman ta farka bata nuna ta ganshi ba, suka dinga maganar su, su kadai babu wanda ya saka shi a ciki, haka ya cigaba da zaman sa ba tare da ya damu ba, dan yasan babu wadda a cikin su zata hanashi zama a dakin. Waje azahar Abba yazo dan sai a sannan ya samu labarin, ya dubata ya wuce da daddare suka sake dawowa da Umma itama ta duba ta, umma ta lura duk kunya ta hana Maman sakewa dasu, har suka tafi bata iya yin magana sosai ba, da safe Abban ya sake dawowa tare da Abbati da breakfast yace da rana umman zata zo ta sake dubata.
Asma'u na kwance umma tace ta tashi ta shirya zata rakata dubiya, tun da ta dawo gidan fitar ta biyu ce shima asibiti kuma tare da Umma suka je da Abbati, Hijab kawai ta saka me hannu maroon ta saka flat shoe ta rik'e wayar ta a hannu ta fito, ta samu umman tana karasa shiryawa. Titi suka fita kasancewar a napep zasu Abbati baya nan Umar ma haka, babu me mika su, shiyasa umma ta bar abincin sai da daddare wani a cikin su sai ya mika musu idan sun dawo.
Sai da suka shiga napep din sannan take tambayar umma in da zasu
"Waye ba lafiya!?"
"Hajiya Mama ce, kwananta biyu a asibiti kamar."
"Allah ya kara sauki." Tace ta ja bakin ta ta tsuke har suka isa, suka nufi dakin kai tsaye tunda already Abba ya riga ya fad'a ma umma room number din.
Dakin a cike yake da mutane yawanci kawayen Maman ne sai su nabeela da fadeela sai sirakar fadeelan da tazo da kannen mijin nata, a waje suka dan tsaya na ciki suka fito sannan suka shiga, Hajiya na ganin su ta washe baki tana kafe Asma'un da ido, daga bayan umman Asma'un ta gaishe ta, ta dubata amma sai ta yafito ta da hannu, ta matsa gaban gadon a darare.
"Ina wuni?"
"Lafiya lou Asma'u, kina lafiya."
"Lafiya lou." Ta amsa tana sunkuyar da kanta k'asa,
"Zauna mana." Ta nuna mata kujerar gefen gadon, ta zauna ba musu tana zama Nadiya ya shigo, ta gaida umma cikin girmamawa sannan ta isa wajen Asma'u fuskar ta na bayysna farin cikin ganin ta, ita kanta Asma'u taji dadin ganin ta ko babu komai Nadiya ta nuna mata soyayya irin ta Yaya da kanwar ta, kuma ta sota da gaske ba kamar Hajiya da dan lelen nata ba, su dama Fadeela da Nabeela ba wani haduwa suka cika yi ba, amma duk da haka ta san ba kamar Nadiya da ta nuna mata soyayya fiye da Adam din da suka fito ciki daya ba.
Ita dai umma nata ido ne ganin yadda suke nan nan da Asma'un, wato baka gane muhimmancin abu sai ka rasa shi, wajen la'asar umman tace Asma'un ta tashi su tafi, fuskar Maman ce ta sauya zuwa bacin rai, tace
"Har yanzu fushin ne umman su?"
"Fushi? Akan me yaya?"
"Akan abinda ya faru."
"Ai da mun dauki fushi ko zuwa nan ba zamuyi ba, ko kuma nazo ni kadai na barta a gida, mu babu komai a zuciyar mu wallahi, ai ya wuce."
"Toh idan da gaske ne, dan Allah ki bar Asma'u ta zauna zuwa anjima sai ta dawo."
Girgiza kai Umma tayi
" Kiyi hakuri."
Sai ta kalli Asma'un da ta riga ta mike amma kuma bata taho ba
" Muje, Allah ya kara sauki Hajiya."
Daga haka ta tisa yar ta a gaba suka tafi, dan ko tasha giyar wake ba zata bar ta ba, akan me? Sai yanzu za'a nuna ana son ta bayan abu ya kwabe musu, hakan ma da suka zo ya wadatar ba sai kuma an nemi wani abun ba. Ita kanta Asma'un ba son zaman take ba, dan dai kawai ba zata saka baki a maganar su Umman ba, shiyasa umman na cewa su tafi tayi saurin bin ta.
Suna kokarin barin cikin asibitin Adam na sako kansa, su suna kasa shi yana mota basu ko lura dashi ba, shi dai ya gansu dan har wani burki ya taka da ya kusan janyowa na bayan shi ya taba shi, allah dai ya kiyaye, gefe ya ja ya matsa masa yazo ya wuce shi kuma ya juya motar yabi bayan su, be san dalilin bin nasu ba, kawai ya samu kansa da zuciyar sa da bukatar hakan, har sun tare napep zasu shiga ya karaso wajen, Asma'u ce ta fara ganin sa gaban ta yayi mummunar faduwa, tayi saurin fadawa napep din kafin ma umma ta gama yi masa kwantancen in da zai kaisu.
"Ai kin tsaya a gama daidaitawa ko Asma'u!?" Umma tace tana shigowa itama, sai a lokacin ta ga Adam din, yana tsaye a gefen su zaune cikin motar sa, be fito ba kuma be tafi ba, dauke kai Umman tayi tamkar bata san shi ba, tacewa me napep din
"Muje."
Bari wajen su kayi ba tare da sun nuna sun ganshi ba, ya daki sitiyarin motar yana jan tsaki, me ya hau kansa ne da har ya aikata haka? Juya motar yayi zuwa cikin asibitin yana me jin haushin kansa. Duk yadda yaso ya yakice tunanin ta ya gaza, duk in da ya juya ita yake gani sanda ta kalle shi da zata shiga napep din, hirar ta yaji su Mama nayi da Nadeeya, ya kasa kunne yana saurara har da murmushin sa, sai bayan yayi ya kuma hade rai yana me jin haushin kansa, tashi yayi ya bar dakin ya fito waje ko zai daina jin abinda yake ji a ransa.
Yana fita Fido na zuwa ita da kawarta, reception ta tsaya sai da ta gano dakin da Maman take tazo dubuta, ita kanta Maman da ta ganta sai da ta ji gaban ta ya fadi, wani irin kwarjini da tsoron yarinyar take ji wanda ta rasa na menene, kamar mutuniyar arziki take gaida Hajiyan, shiru ne ya biyo bayan gaisuwar, har sai da Faiza ta dan zungure ta sannan tace
"Mama dama batun ciki ne."
"Naam?" Mama tace a kideme
Nadeeya da ranta ya baci tace
"Wai baku ga halin da take ciki bane, haba mana."
"Abun da zai sakata warkewa ne ai, dan nasan shine dalilin kwanciyar tata, ciki dai na zubar dashi..."
"Kin zubar?"
"Eh, an ma da sharadi, dole Adam ya aure ni, magana tuni tana hannun hukuma idan ya amince sai na janye idan be amince ba shikenan."
"Ya ma amince, ya amince ma."
Murmushi tayi, suka kalli juna ita da Faiza, sai suka mike a tare suka ajiye ledar hannun su
"Ga kayan dubiya, Allah ya kara sauki."
"Angode, ku gaida gida."
Suna fita Nadeeya ta dubi Maman
"Mama tsoron ta kike?"
"Sosai nadeeya, wallahi ko kallon fuskar ta bana son yi, idan Adam be aure ta ba zan taba samun nutsuwa ba. "
" Innalillah wa inna ilaihi rajiun, Anya mama haka yarinyar nan ta barki? Karuwa ce fa, kalli zubin ta amma a haka zaki sa Adam ya aureta? "
" Shi din menene Nadiya? Sanda yake kula ta duk be san hakan zata faru ba, ko kina ganin shi tunda namiji ne yaci banza, abinda ake nuna musu kenan, baka san da wadda zaka hadu ba, ba kuma kasan sharrin ta ba, tunda har ya kasa zama da mutuniyar kirki irin Asma'u bani da zabi, sai ya auri daidai dashi su karata, dama ai mazinaci sai mazinaciya irin sa. "
Shiru Nadeeya tayi cike da tausayin Maman da Adam din, dan tasan Maman na fadar haka ne dan bata da hanyar da zata hana yarinyar, amma babu wanda zai so auren irin Fido duk lalacewar nasa dan!
***Duk yadda yaso abun ya bar kansa,ya kasa tsawon sati biyu kenan tunda ya ganta ya gaza sukuni,duk abinda yake yi ita yake gani. Gaba daya ya fita hayyacin sa, shiyasa ma ki maganar Fido baya tunawa, tun bayan dawowar mama daga asibiti da tayi masa maganar auren Fido din yaki amincewa, ta nuna bacin ranta sosai akai kawai yace suyi duk abinda suke ganin daidai, be sake sanin abinda ake ciki ba, dan ko yar fitar nan ya daina, yana gida a ko da yaushe tamkar bashi ba. Ba zai iya jurewa ba, duk yadda yaso ya yakice tunanin ya gaza har ya soma fita hayyacin sa, shiryawa yayi ya nufi gidan Abban kawai duk ma abinda zai faru ya faru.
Umma na tsakar gida da yake yamma ce su Abeed sun zo sai dare Baban su zai zo ya dauke su, fitowa Asma'u tayi ta zauna a gefen Umman tana jawo Abeed din jikin ta
"Abba zai barni naje gidan su Abeed umma?"
"Zai iya barin ki, kinsan yanzu lallaba ki yake, ki kirashi dan yace yau zai yi dare, ko ki bari idan ya dawo gobe sai ki shirya kije."
"Ai ban ma hada kayan ba, idan ya dawo din sai na tambaye shi."
"Hakan ma yayi, kwana nawa zaki?"
"Sati daya."
"Kai Asma'u har sati?"
Dariya ta saka
"Umma ai ba yawa satin fa, dan ma Abba ba zai bari ba da nayi ko sati biyu ma."
"Lallai, satin ma ki yi addu'a ya barki, kinsan baya son ki matsa nan da chan, da ya shigo yake fara neman ki."
"Tausayi na yake ji ai, ni kuma fa komai ya wuce na manta ma ni wallahi."
"Shi ai yaki mantawa."
Zatayi magana akayi sallama a dan corridor din da yake kafin ka shigo gidan, gaban ta ne yayi mummunar faduwa, ko a mafarki taji muryar shi sai ta firgita bare har taji shi a tsakiyar cikin gidan su, duk da tsoratar da tayi amma bata nuna ba, tana zaune kyem tana cigaba da wasa da hannun Abeed, umma ce ta amsa tana dan leka kanta, dan bata dau muryar sa, jin an amsa ya saka shi shigowa kai tsaye, ta mike ta kama hannun Abeed din suka shige ciki.
"Adamu ne, shigo mana."
Umma tace ba tare da ta nuna masa komai ba, babu kunya ya zo ya zauna a gefen tabarmar da Asma'un ta tashi, ya gaida Umman ta amsa ba yabo babu fallasa. Shiru ya biyo baya har sai da Umman tace
"Hajiya ce ta aiko ka?"
"A ah, wajen Asma'u nazo."
Kallon ashe baka da hankali Umma tayi masa tace
" Wajen Asma'u kuma!? Ko dai kayi batan kai ne? "
" A'ah, tambayar ta nazo yi ne. "
" Lallai Adam, yanzu kai dan Allah har kana da bakin yiwa Asma'u magana? Toh wai ba ma wannan ba, baka ji kunyar zuwa kace wajen ta kazo ba? Ban ce kwata kwata ba zaka zo gidan nan ba, amma ba wai wajen Asma'u ba, ko dan kaga mun kyale ka bamu kaika wajen hukuma ba. "
Ransa ne ya baci, sai a lokacin yaga wautar sa ta zuwa, umma kuwa ta wanke shi tas dan dama rashin samun dama ne, yana ranta dan da wani ne bare wallahi sai sun yi shari'a dashi, kasa mikewa yayi har sai da ta gama yi masa tatas, tace kuma kar ya sake zuwa da sunan wajen Asma'u dan aure ma zatayi ta samu miji, wannan maganar ta karshe ita tafi firgita shi, har ya dauki hanyar gida baya gane abinda yake masa dadi.
_RM_
*19/20*
_Hafsat Rano_
***Dariya abun ya bawa umma, ita kadai ta dinga janjana maganar Asma'u na jinta taki fitowa, bata san Adam din ma bashi da kunya ba sai yau, ko kuma dai tsabar rainin wayo ne zai wanko kafafu yace wajen Asma'un yazo oho, aikuwa ta wanke shi tsaf dan dama ta jima tana jiran ranar duk da bata saka ran zuwan ta nan kusa ba. Wayar ta dake gefen ta, ta jawo ta kira Ya Hadiza ta bata labarin abinda ya faru, dan ta rasa wanda zasu zanta Asma'u tayi mata kirmisisi kamar bata ma san anayi ba, ita kanta Ya Hadizan sai da ta yaba kokarin Adam din ko tace tsantsar rashin ta ido da har zai iya zuwa kuma kai tsaye yace yana son magana da ita, duk da basu san maganar mece ba amma zuwan nasa kadai ya isa ka gane komai,sun jima suna magana kafin a kira sallar magriba sannan suka hakura.
Duk abinda ya faru Asma'un na ji amma bata da ta cewa, bata kawo zuwan nasa na da wani muhimmanci ba kamar yadda su umman suka zata dan ta riga ta san Adam baya da bukatar wani abu wajen ta dan bata cikin sahun mutanen da yake ganin su da kima da muhimmanci da har zai iya tako kafar sa yazo dan kawai yayi magana da ita, tafi tunanin dai ko yazo na ya kara jaddada mata tsanar da yayi mata ne, wanda idan ta samu damar haka tabbas sai ta sanar dashi yadda itama ta tsane shi, dan kaf duni babu mutumin da ta tsana kamar Adam din ba.
Suna cikin cin tuwon dare ne mijin Ya Hadiza yayi sallama, ita ta amsa masa ya shigo bayan umma ta yafa mayafin ta duk da babu wani haske sosai a tsakar gidan, gaisawa sukayi a mutunce dan shi mutum ne na gari ga kirki sosai sun saba da yan gidan kamar gidan su haka ya dauki su umma tamkar iyayen sa, su Abeed yazo dauka, umma tace ya tsaya a kawo masa tuwon, ba musu kuwa ya gyara zama Asma'u ta kawo masa, umma ta koma cikin falo ya kuwa ci tuwon sa sosai sannan ya kwashe su suka tafi. Suna tafiya Abba ya dawo tare da su Abbati da Umar da suka rakashi zariya daga nan suka tsaya kasuwa sukayi siyayyar kayan amfanin gidan. Dakin sa ya wuce kai tsaye Umar yaje ya kunna gen da Abba baya jure zafi ko kad'an. Bayan ya zauna ya nutsu ya huta sosai ne Asma'u ta shigo tambayar sa zuwa gidan Ya Hadizan da take son yi wanda Ya Hadizan ce da kanta ta roketa tazo ta kwana biyu dan idan ta itace tafi son zaman ta a gida akan ko ina, fuskar sa ce ta fad'ad'a da farin cikin ganin ta, ya amsa sallamar ta yana tsokanar ta
"Ma'u ce?"
"Nice Abba, sannu da hutawa."
"Yauwa sannu Asma'ul Husna."
"Yawwa."
"Akwai labari ne?" Yace yana matsar da plate din da yaci tuwo, tashi tayi da sauri ta kwashe ta matsar gefe ta saka tissue ta goge har miyar da ta zube sannan tace
"Abba dama so nake naje gidan su Abeed."
"Toh, wuni ko kwana?"
"Kwana Abba."
"Kin ganki ko? Har kwana nawa?"
Sai da ta boye fuskar ta a jikin kujerar da take kusa da ita sannan tace
"Sati daya."
"Umma kina jinta ko?"
"Wannan maganar ku ce, ba ruwana." Tace daga cikin daki, dariya kawai Abba yayi
"Shikenan, Allah ya bada sa'a, amma kar a wuce satin."
"In Sha Allah, nagode Abba."
"Allah yayi miki albarka."
" Amin ya Allah."
Tashi tayi ta fita, Abba ya bita da kallon tausayawa, shi dai kawai yana tausayin ta sosai, tayi masa biyayya hakan ya kara masa son ta sosai.
Sai a lokacin ya tuna ya ga missed call din Hajiya Mama, ya kirata a lokacin saboda suna hanya bata shiga ba, duba lokaci yayi yaga tara tayi har da yan mintuna, kiranta yayi bata dauka ba, sai ya ajiye wayar ya mike kafarsa ya chanja channel tv ya shiga kallon labarai.
Daki ta koma ta hada kayan da zata tafi dasu waje daya, ta gama ta kwanta ta dan danna wayarta kad'an zuwa goma ta kashe ta kwanta gaba daya. Da safe ta tashi da shirin tafiya, har umma na tsokanar ta akan ta matsu, dariya kawai tayi, ta gama duk ayyukan da take taya umman zuwa sha biyu bayan Abbati ya kai Abba kasuwa ya dawo ya dauke ta, Abba be yarda da fitar ta ita kadai ba shiyasa ma yasa Abbati din ya dawo ya kai ta, lokacin Ya Hadiza na kitchen suka zo, ta fito da sauri ta rungume Asma'un tana musu sannu da zuwa. Daki ta kai kayanta ta dawo suka baje a falon sai hira, tafi sakewa da ita akan kowa yanzu dan sosai take jan ta a jiki take kulawa da ita, shiyasa tasu tazo daya, tare suka gama abincin ranar Abbati yaci sannan ya koma kasuwa wajen Abba. Yaran basu dawo ba sai yamma likis tare suke hadawa harda islamiyya, da murna suka dane ta dan duk miskilancin ta, tana sakewa sosai da yara, ta iya tafi dasu shiyasa suke nanike mata.
***Tun da Oga Adam ya koma gida sai ya kasa aiwatar da komai, ya dinga jin kamar ana hadeshi waje daya ana daddaure shi, be san me yake ji ba kai tsaye, amma yasan ko menene yana da nasaba da Asma'u, dakin ta ya shiga, wanda yake kamar yadda ta barshi, kayan sawar ta da sauran tarkacen ta kawai suka dauka sauran kayan da Hajiya Maman ce ta zuba basu dau komai ba, gadon ya hau ya kwanta yana tuna wasu abubuwa dangane da ita, runtse idon sa yayi ya bud'e su, yana mikewa a kasalance ya sakko k'asa zuwa kitchen ya dauki ruwa ya sha har lokacin tana sake masa gizo a idon sa, wayarsa dake aljihun sa ce tayi kara, ya ciro ta yana kallon screen din
"Kana ina?"
"Ina gida."
"Ka shigo gidan ina son ganin ka."
" Owk. "
Yace ya kashe ya maida aljihun, maimakon ya je a lokcin sai ya sake komawa saman, ya watsa ruwa ya sauya kayan jikinsa sañnan ya shiga gidan nasu ya samu Maman tana