Author : RANO Category : African Stories & Novels
kwala masa kira, sai da suka zo Balcony din da zai shigar dasu main part din sannan ya tsaya, ya karaso da sassarfa
" Zan fasa fad'a amma under one condition. "
" Menene? "
" Sabuwar motar da kayi order inason daya, I ll pay half ka cika min ragowar. "
" Kai! "
" Shikenan bari naje na siyar da jaridar, bari kaga. "
" Na yarda."
" Yes! Thank you big bro, Allah ya kara arziki me albarka, ya raba ka da iyayenmu lafiya ya baka My Asmy dinka. "
Duka ya kai masa ya same shi kuwa, dariya suka saka a tare, ya rike masa kunne ya ja
" Baka ji sam, ka raina ni. "
" Abuya! " Ya fad'a da sigar tsokana
"Ka bata min suna tun daga yarintar, gashi nan hatta Baba ma haka yake fad'a."
"Amma kasan me? Ina son sunan sosai, ina jin dadin duk sanda ka kirani da sunan, yana tuna min old memories din mu na yarinta."
"Abdallah-Abuya."
Suka sake yin dariya, ya rik'e masa hannu suka fasa shiga ciki suka juya zuwa nasu bangaren suna cigaba da tattaunawa kamar kowanne lokaci.
Da gudu Ihsan ta koma ciki tana kwalawa Mami kira, tare suka fito da Mum ta sakasu a tsakiya ta ratayo kafadar su
"Albishirin ku?"
"Goro." Suka ce a tare
"Ya Abuya yayi budurwa."
"Da gaske?"
"Wallahi, yanzu naji suna maganar da Ya Mudan, yana tsokanar sa."
"Wannan maganar danki ce babu ni a ciki."
Mum tace tana zama, Mami kuma ta cigaba da tambayar Ihsan din abinda taji, ta kwashe komai ta fad'a, murna ta hau yi, tace ta dauko mata Jakarta a daki, ta kawo ta ciro ATM din ta,
"Goron albishir, ki je ki siya abayar da kika ce min kina so."
Ihu ta saka ta dane ta,
"Thank you thank Mami na, you are the best, nagode Allah ya kara girma."
"Amin Mamana."
"Kinji abun farin cikin da ya sameni ko?" Tace wa Mum bayan Ihsan din ta fita
"Dan naki ne sha'anin sa sai shi, Allah sa da gaske ne."
"In Sha Allah ma gaske ne, bari nazo na fara shirin shan biki, grand biki da baa taba irin sa ba."
"Allah yasa kar ya baki kunya."
"Bama zai bayar ba."
" Shikenan zamu gani."
Tace cikin nuna halin ko in kula amma a kasan ranta wani dadi ne ya lullube ta, Abdallan ta ya samu matar aure.
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
*RM*
*24*
***
Daren ranar Hajiya Mama bata runtsa ba, tana kan Adam da ya farka ya kuma nemi barcin ya rasa, sai magiya yake mata akan ta taimaka masa, tayi wa Abba magana. Ta rasa abinda yake mata dadi Abban ma da yace zai zo be zo din ba, tasan ba abu bane me sauki a wajen sa ba, musamman shi da aka batawa, amma ya zatayi? Bata da kamar sa kaf duniyar nan, dole dai shine sai sake rufa mata asiri a san abinda za'a yi kafin Adam din ya karasa zaucewa dan taga abun ba na wasa bane. Da safe ya tashi kamar bashi ba, kamar kazar da aka tsoma a cikin ruwan zafi, yayi laushi sosai, sallah Mama ta sakashi ya rama wadda ya rasa ya zauna aka kawo masa tea yasha tace yaje yayi wanka, maimakon ya tafi gidan sa sai ya nufi dakin sa na cikin gidan ya sake kwanciya yana dasa sabon tunani, ya dade be fito ba har Maman ta biyo sahun sa, ta ganshi kwance kamar ruwa, tashi ta saka shi yayi ya shiga wankan, sannan ta fito ta jawo masa kofar, yana wankan tunanin ganin da yayi wa Asma'u da gayen jiyan nan na bijiro masa, ya dinga huci shi kadai da k'yar ya karasa wankan ya fito ya shirya, ya bar gidan ba tare da Maman ta sani ba, ya nufi gidan Ya Hadiza, be duba karfe nawa ba, ya isa gidan ya fito ya hau kwankwasa gate din, weekend din saboda haka babu wanda ma ya tashi a gidan sai yara da su dama sabon tashin makaranta baya barin su baccin safen nan, Abeeda ce taji ana bugu da dan karfi, ta shiga dakin da Asma'u take ta hau tashin ta
"Anty Asma'u ana knocking a gate."
"Waye?"
"Nima ban sani ba, tun dazu ake yi, su Momy kuma basu tashi ba."
"Owk, Ina zuwa. Kar wanda yaje ya bude zanzo."
"Owk tam." Tace ta juya ita kuma ta tashi, ta sakko daga gadon ta shiga bayi ta kuskure bakin ta, ta wanko fuskarta, ta fito dama tayi sallah tun asuba, sai kawai ta zura hijab ta fito, biyo ta Abeedan tayi, suka je tace waye.? Jin muryarta, ya saka shi jin wani sanyi a ransa, ya tabbata idan yace shine toh ba zata bud'e ba, sake maimaita waye tayi, yayi kokari sosai wajen saita muryar sa, yace Abbati ne. Ji tayi kamar muryar abbatin kamar kuma ba tashi ba, kai tsaye ta zare lock din ba tare da tunanin komai ba, cike da hanzari ya tamki hannun ta, ta turje idon ta na fitowa waje
" Menene haka?"
Da sauri Abeeda ta juya ciki tana kwala kiran Mummy, ya sa karfi ya jata zuwa motar tana kwacewa, sai dai karfin su ba daya ba, tura ta yayi ciki ya rufe da key sannan ya zagaya ya bud'e bangaren sa ya shiga ya bar layin. Daidai lokacin Ya Hadiza da Abban su Abeed suka fito da mugun gudu ya Hadiza ko dankwali babu akanta, amma kafin suzo har ya bar layin, rik'e Abeeda tayi tana fashewa da kuka
"Waye ya tafi da ita? Waye?"
"Uncle Adam ne."
"Na shiga uku, me zan cewa Abba, Adam dama bashi da hankalin ban sani ba?"
"Calm down, tunda ma shine ai da sauki, muje ciki ki shirya bari na kira Abba, dole ya dawo da ita tunda mu ai ba mahaukata bane kamar sa, idan yaki sai a saka shari'ah a ciki, tunda be san addini ba."
Hankali a tashe ta koma ciki ta chanja shigarta dan ba ma zata iya wanka ba, tana jin shi suna magana da Abban, a nutse suke maganar da dukkan alamu ba kamar ita da ta rude ba. Wayar Asma'un ta dauko a daki da handbag dinta suka tafi gidan su, suna zuwa suka tarar da Umma hankalin ta a tashe, ranta yayi masifar baci, shi kansa Abban dan dai namiji ne amma kana kallon fuskar sa zaka ga yanayin sa ya chanja, be kira Hajiya Mama ba, tunda ya fuskanci kamar har yanzu tana goye da bayan dan ta, kuma ma dai baya bukatar wata magana kawai Adam ya dawo masa da yar sa. Dama mijin Ya Hadizan yake jira yana zuwa suka fita a mota tare, sai police station dan shine kawai mafita yanzu a garesu, sai da suka je kofar shigar kuma sai Abban ya kasa sauka daga motar, ya dinga jin kamar hakan tona asirin family din su ne, kamar kuma be kyautawa Yayar sa ba, tunda duk tsiya dai Adam din ma nasa ne, cewa yayi su juya zuwa gidan Hajiya Maman kawai, Abban su Abeed ya jinjina zumunci irin na Abban wanda baa samun sa a wannan zamanin sai an tona. Shi kadai ya fita ya shiga gidan yace mijn ya Hadizan ya jirashi, ya shiga kansa tsaye ya same ta a zaune a falo ta rafka tagumi
"Sannu da zuwa." Tace masa tana mikewa, maimakon ya zauna sai ya tsaya daga kofar shigowar
"Adam yaje har gidan Ali ya dauki Asma'u, bansan me yake nufi ba, ban kuma san ina zai kaita ba, amma inaso ya dawo min da 'yata kafin nan da awa daya, idan ba haka ba zan nemi hukuma ta shigo ciki."
"Na shiga uku, Adam din? Chan ya tafi dama? Wannan wanne irin abu ne dan Allah, na shiga uku."
Ta hau tafa hannu tana salallami, sallama Abba yayi mata ya fita yana jin duk babu dadi yadda abubuwan suka kasance. Wayar ta, ta jawo da sauri ta shiga kiran layin Adam din amma be daga ba, ta dinga jera masa kiran ba kakkautawa.
***Gudu ya dinga shararawa har sai da ya kusa kure titin, be san ina zashi ba,be shiryawa hakan ba, a lokacin da ya ganta kawai tunanin yazo masa. Duk magiya da rokon da take masa yayi kamar be ji ba, shi dai tunda yanzu suna tare burin sa kawai ya samu in da zasu, ya samu wanda zai tabbatar masa akwai aure har yanzu a tsakanin su, sannan ya umarce shi akan ya daura musu aure a take a wajen! Jin kiran da ake masa babu kakkautawa ya saka shi daukar wayar ya kashe ta ma baki daya, ya juya akalar motar zuwa hanyar barin garin baki daya.
***Hankalin Fido yaki kwanciya akan kiran da Hajiyar tayi mata kuma ta kira bata daga ba kuma bata biyo kiran ba, a daren da zata tafi gidan Faiza ta hanata tace ta bari dai da safe, aikuwa wajen goma na safe taga shiryawa, Faizan ko tashi batayi ba, ta dauki hanyar gidan bayan ta tsaya tayi wa Hajiyan siyayyar kayan fruits.
Yanayin Hajiya Mama ya chanja lokacin da ta ganta ta shigo, ta kalli hannun ta kafin ta aro jarumtar yi mata maraba, zama tayi tana gaida hajiyan
"Dama naga kira ne jiya, shine nazo naji ko lafiya?"
"Eh wallahi, lafiya lou bansan na kira ba ma wallahi, jiyan nan ina neman wata number ashe ke nake kira."
"Ayya."
Tace tana karewa falon kallo, ta jima bata ga Adam din ba, bata kuma da bukatar ganin sa har sai ranar da ta shigo gidan sa, a yanzu tasan zai iya cewa zai nada mata duka, shiyasa take mugun takatsantsan dashi.
"Na tura wa chan kannen Baban Adam din address din da kika bani, nasan yanzu sun je ko zasu je ma, ban dai ji daga gare su ba, yau nake shirin ji."
"Allah sarki." Tace tana sinne kai, dadi na cikata saura kiris burin ta ya cika, dan jim ta zauna ganin kamar Hajiyar bata cikin nutsuwar ta, ya sakata mikewa
"Zan koma Maama,dama zuwa nayi na duba ko lafiya."
"Lafiya lou, nagode sosai ki gaida gida."
"Yauwa."
Tana fita ta zauna dabas, zafi goma da ishirin, kira ne ya shigo wayarta, tayi saurin wawurar wayar a tunanin ta Adam ne, sai taga wani kawun su Adam din ne, kawu murtala. Dagawa tayi
"Barka da safiya Asabe."
"Barka dai kawu, ya mutanen gida."
"Lafiya lou, dama batun Adamu ne, akan yarinyar da aka ce muje mu nema masa aure, toh Alhamdulillah, an je kuma mun samu iyayenta da maganar sun yi murna da farin ciki, sun kuma amince sun bashi ita dan a take ma akayi komai muka bada sadaki aka daura aure..."
"Na'am?"
"An daura aure, sai bayan an daura ne ma wani baffanta yake shaida mana ai rabon su da ita yau shekara guda kenan tun wani zuwa da tayi ta gaishe su, tunda har ta turo a nemi auren ta toh su dama haka suke so, shiyasa ma baa bata lokaci ba."
"Tirkashi!" Ta furta
"Sauran bayanin zanzo gidan anjima, wannan dai na fad'a miki ne saboda girman maganar ba zan iya jira sai nazo din ba, jiya muka je kuma dare yayi mana a hanya ga rashin network me kyau da tun a jiyan ma zan kira."
" Shikenan Kawu, sai kazo."
" Yawwa,Allah ya sanya alkhair ya basu zaman lafiya."
Kasa amsawa tayi da Amin, taji kamar kalmar bata chanchanci a fadeta a irin wannan auren na Adam ba, jin tayi shiru sai kawai ya kashe, su yanzu sun zama yan kallo a sha'anin Hajiya Maman da yaranta, duk abinda tace dasu suyi shi kawai sukeyi basa wani duba ya dace ko be dace ba.
***Dukkan su sun hadu a gidan suna zazzaune, Rauda har da kuka da aka gaya mata ta taho a lokacin, Hidaya ma da sauran yan gidan duk sun zo, wayar Asma'un da Ya Hadiza ta dauko aka kira, umma ta kalle ta ita ma ta kalle ta sannan ta kalli wayar, ABDALLAH ta ga anyi saving, ta gane waye amma kuma bata san me zata ce masa ba idan an daga. Katsewa tayi aka kuma sake kira
"Ki daga kice bata kusa."
"Toh." Tace tana dagawa
"Hello, ina kwana."
"Lafiya lou." Ya amsa cike da tantamar wadda ta daga
"Yayarta ce, Asma'un bata kusa."
"Oh... Ina kwana?" Ya gaishe ta
"Lafiya lou, zaa fad'a mata idan ta zo."
" Owk nagode Aunty."
Ya katse yana cike da jin kunya. Tashi yayi daga gadon dan yau ya more baccin sa sosai, yana tashi ita ta fara fado masa a rai, shine ya kirata yaji lafiyar ta, toilet ya nufa yana rage kayan dake jikin sa, ya bud'e drawer a dan corridor din da zai kaika wajen da akayi a farkon toilet din me dauke da wardrobe din kayan sa, laundry basket, mirror , shoe rag da sink a gefe, towel ya ciro ya daura a kugunsa ya tsaya a gaban mirror din yana taba sajen fuskar sa, yana bukatar aski dan ya dan tara gashin sosai, maimakon ya shiga toilet din sai ya jona clipper ya tsaya a gaban mirror din yayi gyaran fuska, ya gama ya mayar da komai wajen sa sannan ya fad'a cikin toilet din in da toilet din da wajen wankan yake. A tsanake yayi wankan ya fito ya gyara jikinsa ya saka kananan kaya riga da wandon, ya zura slippers ya fito falon su, MD ya tarar a saman table yana duba abu a system gefen sa black tea ne, zama yayi a kujerar gefen sa.
"Good morning Sir." Ya dan sauke kansa kasa alamun girmamawa
Dariya MD ya saka yana ture system din
"Waye Sir din? Ai wallahi ban isa ba.".
" Sir Mudan mana, MD K'AREFA GROUP OF COMPANIES."
" Toh ai kai kuma kai ne kankat din Oga, kai na a k'asa."
" Munafuki motar nan na zuwa zaka koma raina ni." Ya buge masa kafada
" Ai ban isa ba wallahi, Oga a kawo maka tea din ne?"
"Eh a kawo, a hado da wani abun me dan nauyi."
" An gama ranka ya dade." Ya mike yayi hanyar barin part din, murmushi kawai Abdallah yayi, yana kara jin kaunar dan uwan nasa, hadin kansu shi yafi masa komai, hakan kuma ya samo asali ne tun a farkon zamantakewar iyayen su, in da har baka iya banbance dan waye wannan a cikin su, shi kansa yasan yafi sabawa da Mami fiye da Mum da ta kasance mahaifiyar sa, haka ma MD yafi sabawa da Mum, tsiran haihuwar sa da ta Mudan shekara daya ce shiyasa suka taso tamkar tagwaye. Koman su daya ne tunda suka tashi har kawo yanzu da suka girma hakan bata chanja ba, banbancin su kawai shine shi Abdallah bashi da hayaniya da magana kamar Mudan din.
_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_
_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ 2
_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_
_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._
_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH
_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_
_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰
_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍
_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰
_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️
_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍
***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*
_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_
_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
______________________
ZAFAFA BIYAR
VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)
VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.
TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
*RM*
*25*
***Dawowa yayi dauke da tray ya ajiye masa a tsakiyar falon, mikewa yayi bayan ya gama karanta bayanin dake kan screen din system din yazo ya zauna ya tankwashe kafarsa, gefen sa MD ya zauna shima bayan ya dauko system din ya dawo da ita kasan, suka cigaba da hira yana breakfast shi kuma yana shigar da wasu informations.
"Kunyi waya da Baba kuwa?" Abdallah yace bayan ya gama ya ture tray din gefe, a ka'idar sa baya taba magana idan yana cin abinci, sai ya kammala. "
"Eh munyi."
"Owk ya maganar dawowar sa? Ko zaka je ka same shi a chan?"
"Anya? Kamar sun ma gama zuwa jibi yace zai dawo."
"Owk,. Allah ya dawo dashi lafiya, akwai aikin da ya bani nima, kafin ya tafi duk da dai naci karfin sa, sauran rarrabawa kawai."
"Aikin zakkar ne?"
"Eh wallahi, shi yake sani kwanciya late kwana biyu,amma an gama fitar da komai kawai yanzu rabawar ne.."
"Ah masha ALLAH, gaskiya Baba yana kokarin sauke hakkin Allah, kasan fa yanzu yan kasuwa da masu kudi basu cika fitar da zakka ba, ko a