Author : RANO Category : African Stories & Novels
da hakuri kaji, da kaina zanyi maganin abun."
Sosa kansa yayi
" Ki kyale kawai Mah, babu komai fa, zata daina ne wallahi. "
Tsaki taja ta shige tana ganin kamar Adam din ma tsoron Asma'un yake ji, duk tsaurin sa da zafin sa akanta baya iya komai.
Sai da ya tabbatar Hajiyan ta shige ya kanne ma Asma'un ido daya ya sa dariya. Jiki a sanyaye ta koma wajen masu aikin ta cigaba da aikin amma rabin hankalin ta na ga abinda ya faru, tana jin ana cewa makircin mata bata san a mazan ma akwai makirai ba, marasa tsoron Allah masu dabi'ar da bata san me ma zata kira su ba.
Dare sosai ta kai a gidan sannan ta koma gida a gajiya tikis, kamar ta dora hannu aka tayi ta ihu haka take ji, zafi goma da ashirin, ta taba jin labarin makirin namiji wanda zai nuna a gaban yan uwansa shi din na kirki ne, ya kuma musguna miki a gida daga ke sai shi, irin Adam kenan shi abin nasa ma har yayi yawa dan ko ita da take mace ma ba zata iya abinda yayi ba wallahi.
Duk da uwar gajiyar da ta sha haka ta dora abincin dare me sauki ta ajiye masa ranta duk babu dadi, tana ajiyewa yazo ya haye yaci yayi kyatsa ya bar mata komai a wajen tazo ta tattare ta kai kitchen dan ba zata iya kuma wanke su a daren ba, burin ta kawai ta ajiye hakarkarin ta a kasa ko zata ji dadi. Kwanciyar ta kenan bacci ma ya soma daukar ta, taji ana tabata, ta yinkurin tashi amma ya danne ta, sai da yayi abinda ya kawo shi sannan ya tsallake yayi ficewar sa, ya barta da kuka me cin rai, ta tsani Adam ta tsani ko da jin sunan sa ne, haka ta tashi ta tsaftace jikin ta, sannan ta dawo ta kwanta amma sai ta nemi baccin da take ji ta rasa, tayi tayi amma sam yaki zuwa, tunani ta hau yi, ta saka wannan ta kwance wannan, ganin kwanciyar haka babu amfani sai kawai ta tashi ta dauro alwala ta raya daren, tana idarwa nan da nan bacci ya kwashe ta.
Da asubah ta farka kasan mararta na dan mata ciwo kad'an kad'an, har ta idar da sallah be daina ba, komawa tayi ta kwanta dan bata jin zata iya yin wani abu, kasala take ji sosai shiyasa har gari yayi sosai bata mike ba. Fitowa yayi ya nufi dinning din kamar yadda ya saba sai yaga wayam, haushi ne ya turnike shi dan yana sane jiya ya shigo da doya dan ita yake sha'awar ci yasan kuma in dai ta gani zata soya musu ita, yana matukar jin dadin abincin ta sosai shiyasa duk abinda yake baya taba yarda ya wuce shi, ji yayi ransa na sake baci, ya koma saman ya tura dakin sai ya tarar da ita a kwance a gado ya lulluba har kanta, yaye abun da ta rufar yayi, suka kalli juna
"Ina breakfast?" Yace yana tsaye kanta
"Babu." Tace kanta tsaye ta juya dayan side din, bankaro ta yayi ya juyo da ita
"Ya ina miki magana zaki juya min baya, uban wa ya saka ki fara abinda ba zaki iya dorewa ba, ko kinyi tunanin zaki sace zuciya ta da girkin ki ne?"
"Dan Allah Ya Adam ka rabu dani, ni na saka kaina nayi girkin kuma yau ban ba, ka kyale ni naji da abinda yake damuna dan Allah."
Tace cike da kosawa da halin sa
"Tashi zakiyi ki soya min doya kiyi min sauce, ina jiranki fita zanyi."
Tana jin sa ya juya ya fice, ta cigaba da kwanciya a wajen ciwon marar na karuwa sosai. Chan wajen minti talatin ya dawo dakin, ya tarar da ita a yarda ya barta, ransa idan yayi dubu ya baci, ya fizgota da karfi ta fado daga gadon, ya shiga kokarin neman abun da zai saka ya daketa. Tunawa yayi da belt din dake jikin wandon sa, ya hau kokarin ballo ta, tayi saurin rik'e hannun shi tuni har ta soma kuka sosai
"Dan Allah kayi hakuri wallahi bani da lafiya ne."
Be ji ta ba, bakar zuciyar shi ta riga ta ingiza shi, ya daddage ya zabga mata da karfin gaske, ta gantsare tana kwala karar azaba, idon sa ya rufe ruf, burin sa kawai yayi mata lilis yadda gobe ba zata sake ja dashi ba, baya son raini da wulakanci ba kuma zai dauka a wajenta ba, ita din da bata da maraba da takalmin sawar sa, wanda yake takawa ya wuce. Sau uku yana zabga mata, ta rarrafa da k'yar ta shige bayan gadon, biyo ta yayi ya sake dagawa yaji an rik'e belt din, daga nan yaji saukar mahaukacin mari a kuncin sa, kafin ya dawo hayyacin shi aka sake sauke masa wani me zafin gaske. Umar ne a tsaye yana huci sosai, sai Umma dake gefe tana kuka sosai, sakin belt din yayi ya fadi kasa, umar din ya shaki wuyan sa ya gwara kansa da bangon dakin.
"Kasheta zakayi? Kasheta zakayi? Wallahi kafin ka kasheta ni zan fara kasheka, shege dan iska mara mutunci." Ya sake kaiwa bakin sa naushi
"Umar zo ka daga ta, mu kaita asibiti kamar tayi bari." Umma tace tana kuka ta tallafo Asma'un jikin ta, sakin sa umar din yayi, babban yayan su Asma'un kenan, yana da masifar zuciya shi yasa baya shiga sabgar kowa, yanzu ma umma ce tazo gidan Hajiyan bayan ta aika da cingam din gayyatar bikin yar kanwar Baban su Adam din wadda ta taba rik'e ta kafin ta koma hannun iyayenta saboda Adam din, duk da Hajiyar bata sani ba, bikin ake shine aikin da su Asma'un suka yi jiya, tayin aikin umman tazo shine tace bari ta fara shigowa gidan Asma'un, sai kuma suka ji ihunta a sama, shine suka hawo da sauri suka tarar da bakin azzalumin yana dukan ta tamkar ya samu jaka.
Bari tayi kamar yadda Umman tayi tunani ganin jini, a asibitin aka kara tabbatar musu sannan aka ce suje suyi scanning a tabbatar ko ya gama fita duka. Daga nan kuma aka bata maganunguna suka wuce gida, gefen idon ta shatin duka ne inda Allah ne ya kiyaye be same ta a ido ba, ajiyar zuciya kawai take babu wanda yayi magana a cikin su, ran umma yayi masifar baci suna isa gida ta kira Abba a waya tace yazo gida babu lafiya, sai gashi nan da nan kuwa, ya tarar da Asma'un a kwance, fuskar ta da ta dan daga ya kalla a tsorace sai kuma ya kalli Umman,
"Gata nan, zuwa mukayi muka tarar da ita yana jibga kamar ya samu jaka, kalli idon ta, bayan ta ma shatin dukan sa ne."
"Duka?"
"Gashi nan ka duba ka gani ai idan baka yarda ba, ko ka kira Baba ai a gabansa akayi."
"Asma'u?" Ya kira sunan ta, ficewa umma tayi daga dakin dan hatta Abban haushin sa take ji sosai.
" Dukan ki adamu yayi wai? "
" Eh. " Ta gida kanta tana goge kwallar takaici
Shiru Abban yayi tamkar ruwa ya cinye shi, jiri jiri yaji yana neman kayar dashi, ya zauna da sauri yana dafe jikin kujerar
" Innalillah wa inna ilaihi rajiun. "
Yayi ta maimaitawa, har ya samu nutsuwa, ya dinga kallon ta tausayin ta na shigar sa sosai. Idan har namiji zai daga hannu ya daki mace, toh lallai ya kai makura a jahilci, be san abun na Adam din ya kai haka ba, be san mahaukaci bane na ajin karshe, waya ya dauka ya kira Ya Asabe, lokacin tana gidan Adam din an kira likita yana goge masa wajen da Umar ya fasa masa, tana ganin kiran Abban ta daga a zafafe
" Yanzu Karami har Umar yayi girman da zai shigo har gidan Adam ya dake shi haka, wacce irin tarbiyya ka bawa yaran nan ne,? Har cikin gidan kazo ka daki mutum saboda kana tunanin wani abu daban? "
" Adamu ya aiko wa Asma'u da takardar sakin ta, yau ba sai gobe ba, idan kuma yaki sai hukuma ta raba mu dashi!"
Yana kaiwa nan ya kashe wayar sa, saroro tayi da wayar a hannu, ta kalli Adam din ta kalli wayar, tana son sake tabbatar da Abban ne dai ya kirata ba wani ya bawa wayar ba, shi din ne dai yayi mata magana babu gaisuwa bare girmamawa!
RM
15
***Ajiye wayar yayi a kusa dashi ya karasa wajen Asma'un yana dubata,
"Tashi kinji."
Yace cikin tsananin tausayin ta, mikewa tayi zaune da k'yar har lokacin kanta na mata masifar ciwo, gefen idon ya dame ta sosai dan ya daga wajen.
"Ina hijab dinki? Zaki iya tafiya!?"
Girgiza wa Abban kai tayi saboda yadda take jin ta very weak, kamar zata fadi haka take ji.
"Ina zuwa." Ya fita yana kwala wa umma kira, ta taso tazo tana kin kallon sa
"Taimaka mata, ta saka Hijab dinta ku sameni a mota."
"Ba dai maida ita zakayi ya karasa kashe ta ba ko?"
Wani kallo yayi wa umman, yayi tsaki yace
"Kuyi sauri nace, ina jiranku."
Kada kai Umman tayi zuwa ciki shi kuma ya fita waje, taimaka mata tayi ta rik'e ta suka fito suka tarar dashi a mota Umar na zaune a mazaunin driver suna magana da Abban.
"Da ka sani ka karairaya shi ka zubar tunda be san mutunci ba."
Abban yace a maimakon tunanin da Umman tayi na zaiyi wa har Umar din fad'a, shiru umar din yayi bayan sun shigo, ya tada motar bayan ya kalli bayan cikin tausayin Asma'un.
"Asibiti zaka fara kaimu, kafin ka kaimu chan gidan tsoho."
" Ok." Yace yana juya motar zuwa hanyar teaching hospital din garin. Tun da suka dauki hanya Abba yake waya, wanda umma ta fuskanci ransa yayi kololuwa a baci, dan duk a fusace yake maganar karshe ya kirawo Ya Hadiza ya sanar da ita umman naji, dan ita ko kiran kowa a cikin su batayi ba saboda bakin cikin da take ciki.
Asibitin Abba ya saka aka sake duba masa Asma'un sosai aka kuma tabbatar masa da babu cikin ya fice idan kuma taji wani abu daga baya sai ta dawo a sake dubawa, magungunan ta da aka bata likitan ta gani ta chanja mata wasu sannan ta ce zasu iya tafiya.
Har sun mike tsaye, sai Abban ya tsaya yace wa likitan yana bukatar ayi wa Asma'un gwajin jini, ta rubuta musu tace aje lab, akaje aka biya komai aka dauki jinin nata akayi mata dukkan tests din da suka shafi HIV, Hepatitis da sauran su, duk suna cikin zulumi har sai da result din ya fito babu matsalar komai, ajiyar zuciya Abba ya sauke da karfin gaske, duk suka kalle shi, yace su tafi bayan an tsaya an sai ma Asma'un abinda zata dan ci duk da sam bata da taste a bakin ta.
Gidan tsoho suka wuce, dama tuni Abba ya sanar dashi zuwan su ya kuma saka shi kiran Hajiya Mama itama yace tazo tare da Adam, toh tace amma zuciyar ta fal take da mamakin yadda Abban ya dau zafi dan tun dazu take kiran sa amma yaki dagawa, tasan yana da hakuri matuka tun yana yaro musamman a abinda ya shafe ta, baya hada ta da komai amma kuma a wannan karon, yana son nuna mata yar sa ta fi masa akan ta, bayan kuma abubuwan da Asma'un tayi wanda shi be sani ba. Mayafi kawai ta yafa tace Adam din ya taso, da farko yace ba zai je ba,amma tace dole ne dan bata isa ta tsallake maganar tsoho ba, ba asan ransa ya shiga motar ba, suna kokarin barin gidan Nadeeya na shigowa a tata motar, ta tsaya tana bin baasin in da zasu, sai kuma ta hango fuskar Adam din da tayi suntum, ya kuma hade rai tamau hakan ya sake taimakawa wajen hayewar fuskar. Dariya ce taso kwace mata, ta daure ta kanne cikin nuna kulawar ta tace
"Boy me ya same ka!?"
Banza yayi mata, Mama tayi kwafa tana sake kallon fuskar tasa
"Wai Umar ne ya shigo dan rashin mutunci har gida ya dake shi, akan wai dan ya tarar dashi yana yiwa asma'u fad'an taki yi masa breakfast, ni wannan masifar da na san haka auren nan zai zama da ba'a yi ba wallahi, daga taimako da zumunci sai kuma abu duk ya lalace."
"Daga kawai ya same shi yana mata fad'a sai ya hau dukan sa? Anya kuwa boy?"
Tace tana kallon shi, juyar da kanshi yayi gefe yana jan karamin tsaki
"Ina ita Asma'un toh, tana gidan ne ko yaya?"
"Sun tafi dai da ita, yanzu haka tsoho ne ya kira ni akan na same shi a gida na san kuma akan maganar ne."
"Gaskiya Mama akwai boyayyen abu da baki sani ba game da zaman Adam da Asma'u, ya fad'a miki gaskiyar komai kafin kuje kar azo ana jin kunya."
"Toh, dama na dade da ganin take taken ki, yanzu maimakon ki goyi bayan kanin ki, sai ki goyi bayan ta? Toh dai idan ma wani abun yayi mata ina ruwan Umar din? Ba mijin ta bane da zai shiga?"
"Idan kuma samun sa yayi yana kokarin kashe musu ya fa?"
"Driver wuce mu tafi dan Allah, sai mun dawo."
Maman tace a kufule, dan ma dai Nadeeya din ce har ta tsaya tana gaggasa musu wannan maganar da wani ne da ba zancen da ake kenan ba. Girgiza kai Nadeeya tayi, ta matsa suka fice tana jin rashin kyautawar maman, da na kowa ne kuma Asma'u da Adam duk na ta ne, duk daya suke a wajenta ya kamata ace tayi mata adalci kamar yadda take kokarin kare Adam din, ita fa duniyar nan kaso naka ne, duniya taki shi, kaki shi kuma duniya ta so shi, shi da da dukiya baa musu mugunta dan baka san wanda zaka mora ba.
Har ga Allah bata ji dadin abinda yake faruwa tsakanin Maman da Abban su Asma'un ba da tun da suka taso suka san yadda Abban yake daukar Maman da yadda itama yake a wajen ta, wanda suka san shine dalilin da har ya iya daukar Asma'u da tafi kowacce yar sa hakuri da saukin kai ya bawa mutum kamar kanin nasu Adam da su kansu watarana basu tsira daga rashin mutuncin sa ba.
***Ganin motar Abba a kofar gidan tsohon ya saka mama tabe bakin ta, tana jin ta shirya wanke Abban har an kawo matsayin da ba zai tsaya shi da ita su fahimci juna ba sai ya kawo maganar wajen tsoho. Kamar Adam ba zai fito daga mota ba, dan ya dan dau sakanni a ciki kafin ya fito tamkar bijimin sa, yabi bayan Maman yana sake tamke fuskar sa.
A tsakar gidan suka tarar da su Abban a zazzaune an shinfida tabarmi guda biyu Umma da Asma'un ba kai daya sai su kuma mazan na daya, wajen su umman Maman ta nufa ta zauna daga gefe sosai shi kuma Adam din ya tsaya a tsaye yaki karasowa har sai da tsoho ya buga matsa tsawa
"Zo ka samu waje ka zauna ka yi mana tsaye aka!"
Sai da ya maula yana daga tsayen suna kallon sa sannan ya dosana duwawun sa a gefen tabarmar ya zauna.
Sai alokacin Mama ta gaida tsohon ya amsa a sake yana tambayar ta bayan saduwa, sai kuma umma ta gaishe ta, ta amsa a gadarance, idon ta na kan Abba da yayi kamar be san da shigowar ta wajen ba, abinda yafi bata mata rai fiye da komai ta dinga satar kallon wajen su sai taga yayi mata kwarjini sosai kamar ba shine kaninta me kaunar ta da kaunar duk abinda ya zama mallakin ta ba.
"Toh Alhamdulillah, abinda ya tara mu anan ba wai boyayyen abu bane, magana ce akan Adamu da matar sa Asma'u, wanda muke so kowanne a cikin su ya dubi girman Allah, ya fadi gaskiyar abinda ya hada su. "
Da sauri Abba ya tare shi,
" Allah ya baka hakuri Baba, ban tari numfashin ka ba, amma Adam ya bawa Asma'u takardar ta kawai, shine dalilin zuwan mu nan ba maida magana ba, maganar abinda ya hada su kuwa duk wanda ya zalunci wani a cikin su, toh Allah yayi masa sakayya tun a duniya."
" A ah karami, ba'a shishigi a cikin al'amarin ubangiji, bari mubi komai a sannu, bamu san abinda Allah ya boye ba."
" Babu abinda Allah ya boye, kuma dai kamar yadda Karami yace ne, babu bukatar a zauna ana maida magana, kai Adam, saki Asma'u anan ba sai an bar nan ba, ka tashi mu tafi."
Ran tsoho ne ya baci, ya kalle su, duk su biyun yace
" Idan har zaku iya yanke hukunci haka menene amfanin zuwa gareni? "
" Allah ya baka hakuri Baba, duk abinda kayi daidai ne. "
Abba yace yana jan bakin sa yayi shiru, itama Maman bata sake cewa komai ba, ya kada kansa yana duban Adam
" Adamu kaine gaba da Asma'u ba a shekaru ba kawai hatta a wajen Allah saboda kai din shugaban ta ne, kuma mijinta, inaso ka dubi girman Allah, ka sanar damu abinda Asma'u take maka a zaman ku da ita."
" Menene ma bata yi min ba, gata nan ai, tasan koma a tambaye ta."
" Bana son sakarci, tambayar ka nayi kuma kai nake son ka amsa min, ai na ganta din kai nake so ka fada min. "
Shiru yayi dan bashi da abin fad'a, kallon sa Hajiya ta dinga yi tana masa signal yayi magana, ya kasa cewa komai har sai da tsoho ya sake maimaita maganar sa sannan yace
" Ta raina ni ne, bata bani girma na a matsayin na, na mijin ta. "
" Muna sauraron ka, kamar wanne irin raini? "
" Raini dai kawai, idan nace tayi abu sai ta ga dama zatayi, ko gaishe ni bata yi bare na samu kuautatawa irin ta mata da miji. "
" Toh Adam, bayan wannan fa? "
" Naam. "
" Bayan wannan fa sai me take maka, karka ji komai ka fada mana. "
Shiru yayi yana kokarin tuna abinda zai ce,
" Shikenan abinda take maka ko? "
Shiru ya sake yi nan ma,
" Toh Madallah,