RAYUWAR MACE BY RANO

Author :  RANO Category :  African Stories & Novels

Chapter   1 / 30

1 to 3K   out of 87.6K words

*RAYUWAR MACE*
     _Hafsat Rano_
             Free Page  (1)

*******
     Sanye take da hijabi ruwan toka dogo har kafarta, kanta a k'asa sanda zata wuce ta daidai majalisar mazan wadda kullum sai ta bi ta wajen idan zata je islamiyya tana kuma jin yadda suke maganar ta a kullum idan tazo wucewa, tun abin na damun ta har ta iiik ya dake makale a kafadarta ta jingine ta a wajen ta nufi dakin nasa kirjin ta n I'm aw dukan uku-uku.
    Shi kadai ne a dakin daga gani ya gama shiryawa fita zai kasuwa, tun bayan da manyan yayanta maza suka taso sai ya zama ba kasafai Abban yake fita ba sai ya dau kwanaki yana gida yana hutawa.
  
"Sannu da hutawa Abba.". Tace tana neman waje ta rabe dan ta riga ta san kwanan zancen, ya kwana biyu be mata maganar ba shiyasa ta dan samu nutsuwa a kwanakin

"Yawwa Asma'u, an dawo!?"

"Eh Abba."

"Toh Madallah, sannu da dawowa."

"Yawwa." Ta amsa a ciki tana sake lankwasa kafarta

"Kina jina ko,akwai wani da yazo ko kuwa har yanzu dai?"

"Babu kowa Abba." Tace a sanyaye dan tuni har yar karamar kwalla ta soma taruwa a idon ta.
   Shiru Abban yayi be tanka ba, tamkar me tunanin abinda zai ce, bayan wasu yan dakiku ya kalle ta sannan yace

"Ko dai kina korar su ne Ma'u?"

Da sauri ta girgiza kai hawayen da take kokarin rikewa suka sakko. Kura mata ido yayi sosai sannan ya soma magana a nutse cikin son kwantar mata da hankali

   Kanta a kasa tana jin Abban har ya kai karshe, cikin nutsuwa tayi masa godiya sannan ta mike ta baro dakin zuciyar ta na sake tsinkewa. Idan tace bata damuwa da rashin aure tayi karya. Tafi kowa son ganin tayi auren kamar yadda yake burin duk wasu iyaye da zarar yar su ta kai munzalin aure! Tabbas tasan duk wasu iyaye da yar su ke gaban su basu da kwanciyar hankali har sai sun ga sun aurar da ita gudun magana da abinda ka iya zuwa ya dawo. Amma kuma abu guda da mutane suka kasa ganewa shine, aure, haihuwa da mutuwa duk lokaci ne mutum be isa ya bawa kansa ba idan ba har lokacin ne yayi ba.
   Da yan yatsun hannun ta, take kokarin kirga adadin kannenta da akayi wa aure kamar yadda ta saba a kowanne lokaci, ta riga ta san adadin su sai dai kirgawar na sake tabbatar mata da dole ne mahaifin ta ya dinga tunasar da ita a kowanne lokaci. Duk da shekarun ta ba wai sun ja sosai bane dududu a yanzu ne ta cika shekara ashirin da biyar sai dai yanayin yadda ake musu aure da kananun shekaru ya saka ake ganin ta tsofe a gida. Kannenta biyu da akayi wa aure karshe ,shekarar su sha bakwai dan haka idan zaa hada su da me shekara ashirin da biyar toh fa tabbas dole a dinga yi mata kallon taki aure.
   Bata san kalar matsalar ta ba, dan ba zata iya tuna lokacin da wani ya tare ta ko a hanya bane. Ta kan zauna tayi ta tunanin ko dai ba zata taba aure ba a rayuwar ta? Kila bata da rabo shiyasa hakan ta kasance dan bata zargin kowa balle tace ko wani abu akayi mata. Ta bar hakan a matsayin wata jarrabawa ce a gareta wanda take fatan cinye wa.
   Daga labulen dakin Ummah tayi, ta leko da kanta tana karantar yanayin ta kafin tace

“Ya kamata a dora girkin rana lokaci yana tafiya kafin yan makaranta su dawo."

Da toh ta amsa ta mike, ta chanja kayanta zuwa karamar riga da skirt ta saka hula a kanta ta nufi kitchen rik'e da wayar ta a hannu, tana zuwa ta ajiye a saman cabinet ta dora ruwa a babbar tukunya sannan ta fito da kayan miya daga cikin ledar su ta soma gyarawa.
    Maganar Abba taji a tsakar gidan nasu yana yiwa Umma magana akan dalilin dawowar sa bayan fitar sa kenan bata jin ma ya bar layin nasu

"H pollo upar fa mun hau titi sai ga kiran Yaya Asabe wai gasu nan zuwa gidan da wata muhimmiyar magana, dole nace ya juyo my dawo dan bansan wacce magana ce ba."

" Gaskiya kam, toh Allah yasa muji alkhair"

Umma tace tana bin bayan sa suka shiga falo. Daina aikin gabanta tayi ranta na sake jagulewa jin Hajiya Mama zata zo, Itace mutum ta farko da abban su yake jin maganarta fiye da ta kowa a duniya, duk wani abu da tace masa toh fa an gama shi, ko da kuwa baya so zai amsa mata. Su biyu iyayen su suka haifa itace kuma take masa role din uwa dan tun yana karami iyayensu suka rasu suka barsu su biyu.
   Turo gate din gidan yayi daidai da tsayawar bugun zuciyar ta, ta window din kitchen din da hange su suna shigowa ita da shi yana rik'e da handbag dinta ya makala ta a kafadar sa kamar wani mace. Daf da zasu karaso wajen kitchen din tayi saurin dukawa saboda kar su ganta, tana jin sanda Umma ta fito tana musu sannu da zuwa Abba na tsaye daga bakin falon sa fuskar sa na nuna jin dadin ganin Yayar tashi.

"Sannun ku da zuwa." Abba da Umma suka dinga jera musu har suka dangana da falon sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta cigaba da aikin ta a nutse.
    Tana cikin aikin wayar ta dake sama tayi kara, ta dauraye hannun ta a sink ta jawota tana kallon wayar, kawarta ce Safiyya take kiranta, ta daga tana saka wayar a handsfree ta ajiye ta suka koma magana.
  
Maganar da yaji ya sakashi dawowa da baya zuwa kitchen din, ya tsaya daga kofar yana kare wa halittar ta kallo wadda take sanye da dogon skirt da riga. Motsi taji, ta waigo sai kawai taga mutum tsaye a bayan ta har ya iso daf da ita yana kokarin taba ta.

"Lafiya!?" Tace tana matsawa da sauri har tana neman gogar tukunyar miyar dake saman gas din.

"Fine Baby, kin hadu." Yace cikin muryar sa ta yan duniya, kallon sa tayi daga sama har kasa, zuwa kunnensa dake sanye da dankunne sai wani jibgegen takalmi da yake jibge a kafar sa, wandon sa irin wanda yake a yagen nan ne ta tsakiya sai askin kansa da ya kara nuna mata ainihin shi din waye.
   Yaya Adam ne, tilon namiji a yaran Hajiya Mama kuma shalelenta, tun suna yara Allah be hada jinin ta da nasa ba dan ko haduwa akayi sai yaci zalinta, ya zage ta yace mata shegiya baka saboda duk yan uwanta sun fita hasken fata. Hannun sa taji a saman fuskar ta yana shafawa, tayi saurin bige shi tana watsa masa mugun kallo.

"Menene haka Malam!?"

"Comman sai kace wadda bata waye ba, kin ganki kuwa!? Haka kika chanja kamar bake ba."

Hararar sa tayi tana sake matsawa baya, dan bata masa kallon me cikakken hankali ko a da ma, balle yanzu da yaje yayi rayuwar turai idon sa ya kara budewa.

Hayaniyar dawowar yaran daga school ya bata damar zamewa ta bar kitchen din tayi saurin zuwa daki ta dauko hijab din ta, ta saka sannan ta koma kitchen din, amma sai daga baya nan, tayi kwafa ta cigaba da aikin ta da sauri sauri karma ya dawo ya sake samunta dan ta lura bashi da kunya sam.
   Fasa fita yayi wajen ya koma falon da ya baro su Abba yana zuwa zai shiga yaji Hajiya Mama na tambayar Abba akan maganar Asma'u ko har yanzu shiru, amsar da Abban ya bayar ya sakashi saurin fadawa dakin

"Uncle ni zan aureta."

Duk suka bishi da kallo,

"Boy me kace?" Hajiya Mama tace fuskar ta kamar gonar auduga

"Yess Mom..."

Kallon Abba tayi, wanda shima yake kallon ta a daidai lokacin

"Kaji wani abun almara, Ashe Adam ne mijin shiyasa aka ta fama, kai Alhamdulillah nayi farin ciki sosai."

Saurin sakin fuskar sa abba yayi duk da be san yadda zai misalta abinda yake ji a lokacin ba, farin ciki ko akasin sa? A zahiri babu abinda yafi so da ji kamar ace Ma'un sa ta samu miji, sai dai kuma be zaci haka ba, sannan be taba kawo mutum kamar Adam din a irin mijin da yake mata shaawa ba, amma kuma ta Yaya zai ki jinin Yaya Asabe!? Matar da ta so shi tamkar yadda uwa ke son dan ta?

"Alhamdulillah!." Ya samu kansa da furtawa yana gida kansa duk da be ji abinda Yaya Asaben tace ba. Umma da ta kusan sakin abinda yake hannun ta sanda taji maganar ce ta karaso ta zauna tana kallon Abban amma sam yaki yarda su hada ido ma balle ya gane abinda take so ta nusar dashi.

"Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya."

"Amin Ahmadu, sai a saka lokacin kad'an tunda dama abinda muke jira kenan, kaji al'amarin Allah, babu yadda banyi da shi ba akan ya fitar da matar aure tunda ya dawo yaki ashe ashe dai matar sa na nan tana jiran sa."

"Haka dama al'amarin Allah yake." Abban ya amsa cikin yak'e, sai ta waiga wajen da Umma ke zaune tace

"Sai a fara shirye shirye kawai bilkisu, bari mu wuce dan tun a yau zan fara shiri auren yara biyu."

"Haka ne. "

Tace itama tana yak'en wanda sarai Hajiya Maman ta ga yadda dukkn su maganar ta dake su amma ya zatayi? Dole ta so abinda danta yake so duk kuwa da bashi ta nagartar da za'a bashi mace amma ai hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar dole sune zasu rufa mata asiri.
   Duk abinda ake Adam na zaune a wajen sai da Hajiya Maman tace ya tashi su tafi sannan ya mike ransa fes yana haskilo irin hutuwar da zai da yarinyar dan ba k'aramar mace bace.
  A harabar tsakar gidan ya tsaya yana sosa keya umma da ta rakosu ta kalle shi tana karewa shigar sa kallo cikin takaici

"Mah please bari na dan sake ganin ta, zan same ku a mota."

Dariya ta saka ta kai masa duka ya goce,

"Mara kunya, tana ina ne bata zo ta gaishe mu ba ma ko bata ji shigowar mu bane?"

Katse Maman yayi yace

"Ke da zata zo gidan ki gaba daya mah!"

"Auw kareta kake kenan, toh ai shikenan." Tace tana cigaba da tafiya

"Muna jiran ka a mota." Tace sanda sukayi sallama da Umma ta fita ita kuma ta shigo, ta tarar dashi a tsaye a inda suka barshi.

"Bari a kirawo ta." Tace sannan tayi gaba, yayi saurin bin bayanta ganin ta nufi daki, tana shiga shima yana shiga Asma'u dake kwance ta mike da sauri, kafin tayi magana ta hangi mutum a bayan umman yana zuro kansa yana kokarin shigowa dakin da dukkan karfin sa.

"Kar a shigo!" Tace da karaji ya tsaya cikin jin tsoro, sai a sannan umma ta san ya biyo ta, ta juya da sauri mamakin rashin kunyar sa na neman kai ta kasa

"Kaje falo zata zo." Kawai tace masa cikin takaici, ya juya ba dan ya so ba, ya fita yana taku dai-dai. Girgiza kai Umma tayi cikin tsananin bacin rai tace

"Ki je wajen sa a falo bari na samu Abban ku, jinkirin aure ai ba hauka bane da za'a dauki wannan mara tarbiyar a baki, ba zan yarda ba."

Sam bata fuskanci in da maganganun  Umman suka dosa ba.

"Umma!"

"Kiyi abinda nace kawai ba sai ya sake dawowa ba, ki rik'e Areef ku je tare karki je ke kadai."

Daga haka ta juya da sauri ta nufi wajen Abban dan a san wacce za'a yi, ta dade da sanin Hajiya Maman bata santa,amma bata san rashin son ya kai haka ba!



Rayuwar mace cike take da kalubale mabanbanta! Kaddara ce tsanin duk wata nasarar ta! Ba zata ce ita din rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale cike da rayuwar tata, wanda a karshe zata kirasu da matakin dukkan nasarar ta!


_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU  IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_🥰

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_🥰

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.


*_TEAM ZAFAFABIYAR_*



*RAYUWAR MACE*
     _Hafsat Rano_
             Free Page  (2)

***
A kofar dakin Umma ta tarar dashi, ta nuna masa falon da hannu sannan ta wuce falon Abban. Yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin tana shigowa ya bi ta da ido dan yasan abinda ya kawo ta.

"Alhaji.."

Da sauri ya dakatar da

"Maganar ba zata chanja komai ba, muyi mata addu'a kawai bamu san me Allah ya tsara ba."

"Amma dai hakkin mu ne mu nema mata miji na gari, wanda muka yarda da addininsa da nagartar sa, amma Adam fa? Ya cika wannan sharadin?"

Zama yayi a nutse bayan ya cire babbar rigar jikin sa da hula sannan yace

" Mu bar wa Allah komai, ya fimu sanin komai akai, ba zan taba iya hana Yaya Asabe abinda take so ba, ba kuma zan taba kin danta wai don munin halin sa, ni ma ban fi karfin Allah ya jarraba ni da irin sa ba."

" Yanzu shikenan muna ji muna gani saboda kawai muna so yar mu tayi aure za muyi mata zabin tumun dare!?"

" Idan da rabo sai kiga ta dalilin ta Allah ya shirye shi, sai tayi kokari ta sauya masa DABI'AR sa tunda mace tana da matukar tasiri a rayuwar namiji."

Wani abu ne yazo ya tokare wuyan Umman, bata tare da masu ganin cewa mace zata iya gyara wa namiji Hali bayan ta same shi da girman sa, kawai idan kaji an ce haka toh fa lallai an shirya zalintar macen. Tana tsaye ya zo zai fita daga falon, ya kalle ta yana gyara hular kansa sannan yace

" Karki nuna mata wani abu da zai sa taki auren, muyi mata addu'a kawai dan babu abinda zai sa a fasa sai dai idan Yaya Asaben da kanta tace sun fasa, amma muddin bata ce ba, toh babu makawa sai anyi."

Kasa tanka masa tayi har ya fice, ta zauna dabas a wajen tana jin da gaske an cuce ta, ta kuma tabbatar da biyu Hajiya Maman tayi dan ta nuna mata ta isa da Abban da ma duk wani abu da ya dangance shi.
  Da k'yar ta mike daga wajen ta fito bayan ta jawo masa falon, ta isa dakin Asma'un ta tarar da ita tana sallar azahar, sai kawai ta wuce dakin ta domin ta gabatar da tata sallar.
   Tana idarwa Asma'un na shigowa, bata ce komai ba ta hau gadon umman ta kwanta rigingine tayi shiru tana tuna abinda ya faru bayan taje wajen sa. Kadan ya rage be rungume ta ba da ta shigo, ya hau surutan da ta kasa gane komai akai, haka ya karaci babatunsa ya tafi bayan yace mata zai dawo da daddare.

"Umma wai me ya faru?"

"Aina da?"

"Ya Adam, ban gane ba wallahi. "

" Kinsan kowanne bawa da yadda Allah yake kaddaro masa rayuwar sa, sannan duk dan ta yayi ma iyayen sa biyayya toh fa ba zai taba tabewa ba, mahaifin ki ya yanke shawarar aura miki dan uwanki Adam... "

A yadda ta mike daga kwancen sai da ta bawa umman tausayi,

" Umma Adam kuma? "

Kai ta daga mata

" Innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma wallahi tallahi bana son shi, bashi da hali me kyau wallahi Umma, wallahi Allah bana son shi dan Allah Abba yayi hakuri. "

Duk ta gigice ta rikice, hawayen da Umman take ta rikewa ne suka soma saukowa tayi saurin maida su tana karfafar kanta.

" Menene haka? Me kike haka? Ashe ba zaki iya yiwa mahaifin ki biyayya ba?"

" Umma Adam fa? Umma dan Allah kice yayi hakuri wallahi ba zan iya ba. "

Wani kallo umma ta watsa mata

" Ki nutsu ki saurare ni, kinsan waye mahaifin ku, kin kuma san wacece Hajiya Mama a wajen sa, kukan ki da magiyar ki ba zasu taba sauya masa abinda yayi niyya ba sai dai idan su suka ce sun fasa, dan haka ba ruwana wallahi, ba zan bari ki hadu da fushin mahaifin ki ba, kiyi masa biyayya ku rabu lafiya nima na rabu da nawa lafiya, kuma in sha Allah zaki ga ribar biyayya. "

Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta fice ta bar ta a dakin tana jin yadda take kuka wiwi, wayar ta ta dauka ta kira babbar 'yarta hadiza ta sanar da ita komai sannan ta kira sauran yan uwan Asma'un da sukayi aure, kafin kace me sai gasu a gidan gaba dayan su, duk kansu kowa be ji dadin labarin ba, amma kuma sai Umma ta hana su fuskar da zasu kushe abun dan ta riga tasan halin Abban su sarai zai iya saba musu akan maganar, sannan tunda tasan babu fashi gwara kawai tayi kokarin ganin basu bawa Asma'un kofar da zata bijire wa mahaifin nasu ba.
  Lallashi da ban baki suka dinga yi mata har suka samu ta dan nutsu amma bata bar kuka ba. A haka Abban da yan mazan suka dawo suka tarar dasu, Abban ya danyi fadan dalilin zuwan su haka sai suka ce ai zuwa sukayi su gaishe su,

1 / 30