KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 42

24K to 27K   out of 125.4K words

zuwa wajen nan ba sonka yake ba, yo ubanwa ke zuwa gaban zaki yay wasa ya kwashe kayan wasan salin alin ya koma gidansu yay barcin hutu.🥱. Amma dai bari muji amsar da MAZAN FAMA zasu baka🤣.

Barkanmu da dawowa, ya weekend?😎


19


.........Ana fitowa sallar azhar driver ya kawo musu abinci da ɗaukar su Aheel. Babu yanda Ruky bataiba suje su amso Nimrah taƙi, dan ita kam haka kawai ganin mutumin nan tayar mata da hankali yake ta rasa dalilin haka. Tana zaune a inda Ruky ta barta ta dawo ta sameta. Tana ma buɗe abincin ta sake ɓata fuska ganin minene a ciki. Dariya Ruky tayi, dan tasan Nimrah bata damu da doya ba sam. Harararta tayi kuwa, ƙarshe ta miƙe wai ita ta ƙoshi bazata ci ba. Sanin butsutsunta yasa Ruky bata takura mata ba, anan ma ta barta ita ta koma aji. Sai da taci iya abinda zata iya ta rufe sauran ta koma ajin itama.
      Sun cigaba da ɗaukar darasi, Nimrah nata mutsu-mutsun yunwa, gaba ɗaya sai Ruky ta damu, har cikin ranta taji haushin su Kulu da suka aiko musu da doya bayan sun san Nimrah bata ci. Jakarta ta ɗakko ta ciri kuɗi tare da miƙewa taje gaban sayyadinsu cikin ladabi ta sanar masa zata fitsari. Bai hanata ba dan hakan normal ne. Tana fita maimakon restroom sai ta wuce shop ɗin makaranta. ALLAH ya taimaketa ta samu sauran meatpie bai ƙare ba ta amso mata biyu ta dawo tunda suna da ruwansu. Sai da ta zauna sannan ta saka mata a hijjab. Kallonta Nimrah tayi, sai kuma ta tattaɓa abinda ta ajiye mata akan cinya. Wani irin ƙaunar Ruky ce ta sake cika mata zuciya. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Thanks you Sweetheart”. A hankali. Murmushi kawai Ruky tai mata.
      Cikin hijjab ta shige tana ci, duk da kuwa hakan doka ne ba'a ciye-ciye a aji. Amma da yake Sayyadi Kamal nada wani ƙudiri a ransa game da Nimrah ɗin duk da ya fahimci abu take ci baiyi magana ba. Haka ta kammala tasha ruwa sannan ta fito itama ta maida hankalin ta a karatun. Ya kammala ya fita wani malamin ya shigo, haka dai har lokacin tashi yayi. Yau dai sambarka ƴan caskalen Mammah basuyi faɗa da kowa ba. Abinda take ji aduk sanda suka haɗu da driver yasa tai juriyar ƙin kallonsa a yanzu har suka isa gida. Ita ta fara fita ta shige ciki. Baƙar yunwar da take ji ya sata wucewa kai tsaye kitchen tace su Kulu su dafa mata noodles da ƙwai soyayye ɗaya. Kafin ta shige ɗakin su. Ruky na kwance a gado tana maida numfashin gajiya, dan haka ita bata zauna ba sai ta wuce bathroom kawai yin wanka. Kafin ta fito kuwa an kawo mata indomie ɗinta har Ruky na ƙoƙarin ɗanɗanawa. Doke mata hannu Nimrah tai tana ƙwacewa, Ruky ta lunƙuma wadda ta ɗiba a baki tana dariya da faɗin, “Shike nan ke in kina jin yunwa sai baƙar rowa”.
       Cike da jin haushi ta bata amsa da, “Ai sai na musu rashin mutunci yau a gidan nan, sun san bana cin doya sukayi, maimakon su dafa min wani abun”. Ta ƙare maganar da ƙwafa idanunta na cika da ƙwalla. Dan harga ALLAH taji haushi, sai dai bata san miya hasala zuciyarta ba kuma har kamar haka. Itama Ruky ta fahimci a hasale Nimrahn take dan haka batace komai ba ta wuce bayi tana murmushi...

      Shaf-shaf suka kammala shirin zuwa gidan Aunty Mimi. Sunyi ƙyau cikin abaya iri ɗaya kalar brown da adon duwatsu masu haske. Daga Ruky har Nimrah akwai son kwalliyar tsiya. Ga iyayi kuma da ƴammatanci kamar ba ƙwailoli ba😝🏃🏼‍♀️. Koda yake sunce su ba ƙwaila bane ba😂, dan duk abinda cikakkiyar budurwa ke taƙamar da shi suna da. Fes suka fito abinsu, kai tsaye ɗakin Biebah suka shiga, itama dai ta shirya cikin nata gayun, sannin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 suka biyo ya sata ɗauke kwalbar tana ƴar hararsu.
       “Kai waɗan nan yara baƙwa mantuwa”.
    Dariya suka kwashe da ita a tare, Ruky ta ce, “Humm Small Mom ya zamu manta da wannan daddaɗan turaren, ai kafin a kawo mana namu muma sai su Ammy sun ɗiba mana komu sato”.
            “Ai dama kun saba ɓeraye”.
     Dariya suka sanya a tare nan ma. Ta daddagwala musu kowa ya shafa suna faman lumshe idanu. Dan ƙamshin turarrukan ba ƙaramin ratsa zukatan mai shaƙa suke ba. (Nima shaida ce masu karatu. Wlhy maza ku garzaya neman turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387.  Kaf turarrukanta babu na yarwa, nayi amfani da su na gani, koma nace ina kan yin amfani da su a yanzu haka. Tana kawo turarrukanta ne masu inganci da tsaftatacen ƙamshi.
:Akwai Turare wuta da khumra kaloli har uku: black khumra, white khumra, brown khumra. Akwai oil perfume da kullacham ma, akwai Genine da Turare kabasa kaloli uku shima: white, black, and brown kai harma abinda ban lissafo ba. Dan tana saida kayan gyaran jiki suma na amare dama mata ƴan ƙwalisa uwargidaye masu san gyaran fata batare da kin ɓata skin ɗinki da mayukan bleaching ba. Karku ji komai ta gida ce tana nan zaune a garin Kaduna kuma tana aika kaya aduk inda kake harda kasashen ƙetare ma. Duk mai so kawai ya nemeta ta nan. Tana bada har sari ma fa masoya. +234 704 229 3387😌💃🏼🥰👍🏼).
          “Kai kuko wane kalar ƙamshi kukeyi haka? ya subahanallah”. Mu'azz ne mai maganar yana faman buɗe hanci. Dariya Ruky da Biebah sukayi, Nimrah kam da duk take jinta cikin rashin daɗin zuciya murmurshi kawai tayi. Ganin haka yasa Mu'azz kallonta, cike da kulawa ya ce, “Yaya dai Ninah? Ko baki da lafiya ne? Naga tunda muka baro makaranta baki da walwala”.
    Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai. Bata basu damar magana ba ta ce, “Ku muje ALLAH na ƙagara naje naga Baby”. Tana gama faɗa ta fice a falon gaba ɗaya. Duk da kallo suka bita suma fuskokinsu na nuna damuwar. Koda suka iskota a waje babu wanda yace komai, kasancewar Mu'azz ne zai jasu sai ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta shiga gaba Ruky da Biebah na baya. Su Afrah dama suna can, dan daga makaranta can driver ya kaisu kai tsaye. Koda maigadi ya buɗe musu gate bata ganshi ba, dan haka ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.
     Suna ɗaukar titi kowa ya fara mata tambaya, saita wayance tace kewar Mammah ce. Duk sun gamsu, dan sun san Nimrah da Mammah sai ALLAH. Nimrah akwai ƙulagucin iyaye, dan haka tai bala'in sakin jiki da Mammah duk da har yanzu bata manta da Ummanta ba, sai dai bata iya tuna fuskarta sosai saboda ƙarancin shekaru na wancan lokacin. Tunda ta fara hankali da wayo cikin hikima Mammah ta koyar da ita yima mahaifanta addu'a kwanciyar kabari cikin aminci. Kulawa da take samu yasa bata jin maraici, ba kuma ta taɓa zaman yin kukan rashinsu ba sakamakon babu wani abu na labarinsu data sani ko take ji a yanzu balle ya tuna mata abubuwa a kansu. Garama Ummanta wasu ƴan abubuwan kan mata flash ɗin baya game da ita a cikin zuciya musamman idan Mammah ko su Aunty Ummi da zasu iya zama sa'annin Umman ita da Ammie (Aunty Hafsat mahaifiyar su Ruky kenan Matar Imran) takanji kamar Ummanta.
    Suna isowa tun Mu'azz bai gama kashe motar ba ta fita da gudu tai cikin gidan. Dariya kawai sukai mata. Aunty Biebah na addu'ar ALLAH ya cika musu burinsu na fitowar Dada sarari wataran Nimrah ta haifa musu Baby gudan jinin sa. Ita kanta bata san yanda zata misalta irin farin cikin da wannan ranar zatazo musu da shi ba balle Mammah....

        “Oh ya ALLAHU ka shirya min Ninah jama'a ke da wa?”.
    Zama Nimrah tai kusa da Aunty Mommy dake rungume da Baby tana saka masa kaya an mata wanka tana murmushi, sai da ta shafa kan babyn sannan cikin shagwaɓa ta bama Aunty Momyn amsa.
      “Mum ba kowa fa, kawai ina gudu na fara ganin Baby ne. Jiya fa dan mugunta Ruky ina barci taƙi tada ni suka taho”.
        Aunty Mimi data kasa haƙuri ta ce, “Ai Dada zai sha fama a wajen nan dai kam. ALLAH yasa sanda zai dawo kinyi hankali Ninah”.
     “Mamy shi Dada ina ruwansa da hankalina koda ya dawo? Kuma ALLAH inada hankali”.
          Kasa haƙuri sukai kowa sai da ya dara. Ita kam ko'a jikinta tunda ta samu ta amshi Babyn gaisuwa ma sama-sama tai musu ta koma gefe. A haka su Biebah suka shigo niƙi-niƙi da kaya suna sanar da zuwan Daddy Imran. Dai-dai lokacin kuma Aunty Hafsat ta fito daga bedroom ɗin Aunty Mimi da alama salla tayi. Ai ko zaram Nimrah ta miƙe ta nufeta tana faɗin, “Ammie na dan ALLAH Babyn nan kalleta da ƙyau dawa take kama?”.
     Dariya Aunty Hafsat tayi ta ce, “Da ke. Sai dai ALLAH yasa kada tayo ƙiriniyar taku ke da hassanar ki”.
      Aunty Lailah dake fitowa a kitchen ita da Aunty Shariffa sai ƙanwar mijin Aunty Mimi ta ce, “A'a gara dai ta biyo komai da komai zaifi armashi Aunty”. Nan ma dariyar aka shiga yi, a haka Imran ya shigo ya samesu.
Sai da ya zauna kowa ya gaisheshi cike da girmamawa sannan ya dubi Nimrah data ƙanƙame Baby bata da niyyar bayarwa.
         “Daughter baza'a bani Babyn bane?”.
    Murmushi tayi har haƙoranta na bayyana, sai kuma ta miƙe ta je gabansa tana faɗin.........✍️


20

.......“Daddy ai kaine za'a baka. Amma minti biyar zatayi ka sake bani. ALLAH ji nake kamar kada na ajiyeta fa. Daddy dan ALLAH na dawo nan da zama har ayi suna?”.
        “To Nimrah in kin dawo makarantar fa?”.
    “ALLAH Daddy in ta dawo nima sai na dawo”. Ruky ta faɗa itama. Cikin girgiza kai yace, “Ai bama zan bari ku dawo ɗin ba. Daga yau ba zaku sake zuwa ba sai ranar suna.”
     Zasu fara magiya ya ce, “Okay nace Mammah tai zamanta kada ta dawo goben kenan?”.
      Ai tuni suka saki batun dawowa gidan suka fara murna jin Mammah zata dawo. Abin zai birgeka har su Auntys ɗin farin ciki suke yi. Shi dai Imran yay ma Baby addu'a sosai ya ɗan zauna suka taɓa hira sannan ya miƙe zai tafi. Dole Aunty Hafsat ta miƙe suka wuce tare. Su kuwa sai anyi sallar magriba sannan koma isha'i....

>>>><<<<★★>>>><<<<
          ★DUBAI★

  Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana kallonta dan komai tayi birgeshi take. Shi kaɗai yasan irin wutar masifar sha'awarta da yake ji tsahon shekaru. Ya kuma kasa binta ta ƙarfi batare da yasan dalili ba. Bayan kuma hakan abu ne mai sauƙi a garesa duk da kuwa yasan tana da aure. Yasan inda wata ce ba ita ba yanda yake narkama uwarta kuɗi duk da hakan ba komai bane a garesa da tuni ya mata fata-fata ta yanda ko rayuwarta sai ya ce ga yanda zatayi sannan zata gudanar da ita.
      Yanzu haka yana ƙasar Garmany ne harka business ɗinsa Hajiya Hasiba ta tura masa saƙon kudirin Nabeeha, yana gani hankalinsa ya tashi, a take ya kira duk wani Companyn sauka da tashin jirage yasa aka rufe damar Nabeeha na barin ƙasar. Amma duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya a daren ya baro ya dawo dubai ɗin. Kai tsaye gidan nasu yayo, cikin sa'a kuma ya sami Nabeeha a falo zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Zama yay kusa da ita da kai hannu zai taɓata ta zabura, shine take zazzaga masa ruwan masifa data sakashi zuba mata ido kawai yana kallonta...
        Su Ismat dake laɓe farin ciki ya kamata, dan itama wlhy ta tsani guy ɗin nan, dan bata da wani burin daya wuce Nabeeha ta koma ɗakin aurenta. Ta haka ne kawai itama zata samu cikar nata burin na mallakar Ja'afar. Cike da munafunci Amima ta dannama Hajiya Hasiba kira da mahaifiyarsu data shigo gari tun cikin satin daya gabata. Aiko cikin mintinan ƙalilan suka iso dan duk suna kusa da gida ne dama. Wata tsawa Hajiya Hasiba ta dakama Nabeeha. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu zata mareta caraf Adeel ya riƙe hannun.
       Cike da gadara ya ce, “Karma ki fara dan ina ganin mutuncinki na haihuwarta da kikayi, amma da a maimakon riƙe hannun nan naki sai dai ki jisa a ƙasa yana lilo”.
    Maimakon jin zafin abinda yay mata murmushi Hajiya Hasiba tayi daga ita har ƙanwarta Mamawo. Cike da girmamawa suka shiga faɗin, “ALLAH ya huci zuciyar babba ɗan manya jinin alkairi. Nayi kuskure ayi haƙuri raina ne ya ɓaci. Taya zata zauna tana gaya maka irin wannan shirmen..”
       “Karki damu ta isa ne ai, girmanta ne. Ni zan koma kawai, amma zan dawo anjima anan zanyi dinner”.
    “An gama ranka ya daɗe”.
Hajiya Hasiba ta faɗa cike da girmamawa. Yayinda Mamawo ke wani shegen murmushi tana binsa da wani kallo zuciyarta cike da abubuwa. Amma a zahiri baka isa karantar abinda ke ranta ba dan cikakkiyar ƴar bariki ce data iya takunta. Yana ficewa suka koma yima Nabeeha faɗa da nuna mata karfa ta dawo tana dana sani da wannan damar da ALLAH ya bata. Wai miye akai akayi wani Haysam can da bata da tabbacin yana ma raye ko an jima da kashe shi ne.
      Kuka ta saka musu cike da bori da rashin kunya tabar wajen. Dole sukai shiru bayan duk sun ja tsaki. Bayanta itama Ismat tabi zuciyarta na zafi. Koda ta shiga ɗakin taga Nabeeha ta kwanta tana kuka zaman lallashinta tayi, ganin taƙi yin shiru ta ɗauka wayarta a karo na farko ta danna kiran Jiddah, abinda sai ta jima batayi ba saboda duk haushinta suke ji akan gaskiya da take gaya musu.
   Batai zaton zata ɗaga mata ba ma, amma sai gashi ta ɗaga cikin tsaftatacciyar sallama. Da ɗan rawar murya Ismat ta amsa mata, sai kuma ta fara gaisheta. Ɗan jimmm Jiddah tayi kafin ta amsa tana kallon Abban su dan taje barka gidan Aunty Mimi ne shine ta biyo gidan gaishe su. Kukan da Ismat ɗin ta fashe da shi ne ya saka Jiddah faɗin, “Ismat lafiya kuwa? Ko wani ne ya rasu?”.
       “Aunty babu wanda ya rasu, kawai abubuwa ne suka mana yawa. Mom ta takura dole sai Aunty Nabeeha ta kashe aurenta ta auri wannan mayen mutumin. Jiya mukai shirin gudowa kawai ta sace passport ɗinmu ta ɓoye. Yau kuma sai gashi yazo. Aunty ki taimakemu ki sanar da Abba yazo ya tafi damu. Wlhy gida muke son dawowa, aunty Nabeeha na son komawa gidan mijinta”.
      Jiddah dake jin jikinta ma na rawa ta ɗan saci kallon Abbansu. Ai ko yayi kicin-kicin da fuska yama maida hankalinsa a television inda ake hira da ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar SGP, wato tsohon janar ɗin soja kuma ɗan majalisan tarayya mai ci Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. Yawu masu kauri ta haɗe, cikin damuwa ta maida kallonta ga Hajiya Zuwaira da suke kira Ummu a gidan. Idan ka cire Nabeeha da Ismat da har yanzu basa ko gaisheta. Kai Ummu ɗin ta girgiza mata alamar ta kwantar da hankalinta, dan taji komai itama kasancewar hansfree ta saka wayar.
     Cikin dauriya Jiddah ta ce, “Wannan shi nake nuna muku tun farko amma kuka kasa ganewa Ismat daga ke har Aunty Nabeeha. Yanzu dan ALLAH yaushe rabonku da kiran wani a cikinmu har Abban, aƙalla shekara uku kenan fa. Ni kuma kun saka ni a black list kona nemeku bata shiga harta WhatsApp. Ni yanzu a wannan gaɓar mizan iya yi, wane tabbaci ne dani akan baku biye ma Momy ɗin ba akan ƙudirinta.....”
        “Wlhy aunty bamu taɓa aikata wani abu saɓanin abinda kike tunani ba mu kammu balle Aunty Nabeeha”.
    Duk da Jiddah bata da tabbaci sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, duk da tasan wacece mahaifiyarsu akan son duniya babu abinda bazata aikata ba. Itafa ko uwarmi zasuyi suyi ba ruwanta tunma suna ƙananunsu indai kuɗi zai shigo fine. Hawayen da suka cika mata ido ta haɗiye, ta ce. “Shike nan Ismat ki bani zuwa gobe, yanzu haka ma bana gida naje barkar Aunty Mimi ne data haihu. Amma zan yi magana da Abban”.
          “To aunty dan ALLAH ki taimaka mana, ke kaɗai ce hope ɗinmu a yanzu wlhy”.
     “Karki damu in sha ALLAH duk yanda muke zan taɓoki, ni dai fatana ku cigaba da riƙe mutuncinku kada ku biyema Mom”.
    “In sha ALLAHU Aunty ki mana addu'a”.
       “Ita nake muku kullum”.
Daga haka ta sauke wayar. Tun kafin ma tai magana Uncle Nasiru ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi ki wuce gida dare yayi? ALLAH ya bamu alheri”.
     Yanzu kam sosai idonta ya tara hawayen, ta waiwaya tana kallon Ummu. Kai ta jinjina mata alamar taje, tabar komai a hannunta kawai. Sai kawai ta miƙe tai musu sallama ta fita. Dama ita ta tuƙo kanta. Aiko tana shiga motar ta kife kanta a sitiyari kawai ya fashe da kuka. Ta jima tana kuka har sai da maigadi yazo yana mata knocking glass sannan ta haƙura ta share hawayenta taima motar key......

<%>°<%>°<%>
      PRISON

      
     Wani zuba masa kaifafan idanunsa yay a hankali, tare da sakin wani murmushi mai zafi da izza, mai tabbatar da cikakken izgili da raini fiye da nashi. Dan a ƙarshe da wani salo irin na maida mutum banza sakarai Dada ya taɓe baki. Sannan cikin son tunzurawa ya ɗan karkatar da kansa, fuskar sa ta cika da izza mai nutsuwa. Like yana magana da wani shasha can ya furta,
       “Tofa!

9 / 42