Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
shugaban prison, sai dai babu dama, babu dalilin bijirewa.
A karo na farko, kai tsaye Brig. Haydar Usman Galadima ya furta, “Muna so a fito mana da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu yanzu.”
Duk da shugaban prison yasan abinda ya kawosu kenan sai da numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi, jikinsa yay wani yamm kamar an jefasa da dusar kankara. Amma bashi da zaɓin daya wuce bin umarni na zahiri da gaskiya. Gudun kada yaransa dake zagaye da shi, da yake da tabbacin akwai idanun ɓoyayyun mutanen da suka kawosa wannan gidan suka ɗora a wannan kujerar yasa ya ɗanyi jarumtar son cizawa. Murya a takure ya furta,
“Sir… zuwa yanzu babu wani…”
Cikin zafi Imran daya gama fahimtarsa ya katsesa da faɗin, “Shi kawai muke buƙata a gabanmu. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Ko akwai wani daga cikinku da zai ce bai san ma’anar wannan tambarin ba?”.
“I'm sorry, Sir!”.
Shugaban prison ya faɗa yana ƙara ƙamewa. Kafin ya juya yayma yaransa umarni da idanu. Duk da mamaki na neman kashe da yawansu saboda fahimtar abinda ke shirin faruwa basu da zaɓin daya wuce bin umarnin suma. Dole da sauri suka shige domin zartar da abinda aka saka su.....
★A dai-dai lokacin da suke ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, Dada na zaune ne ya idar da sallar walha yana karatun Alqur'ani. Motsin buɗe ƙofar da shigowarsu bai saka ya dakata ba balle kallonsu. Dan haka suma suka tsaya tsamm alamar jira. Sai da ya kwashe mintina biyar cir da shigowar tasu sannan ya rufe Alkur'anin yana mai ɗagowa ya kallesu. A tare suka nuna girmamawar soja, kafin suyi gaisuwa da sanar masa umarnin da aka basu.
Maimakon amsawa idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya kife zuwa sujuda. Minti biyu cir kafin ya ɗago. Ya ɗauki Alkur'anin sa ya maida inda yake. Sai kuma a dai-dai nan jami'ai biyu dake tare da su Imran suka shigo. Suma sunyi gaisuwar sannan suka fara tattara kayansa na buƙata masu muhimmanci. Komai baice ba, sai bin ɗakin da yay da kallo, kallo irin na bankwana da tuna abinda ya shuɗe, kafin ya juya a hankali ya nufi ƙofa jami'an farko suka take masa baya.....
A hankali ƙofar corridor ɗin ta buɗe. Sai kowa ya sake nutsuwa da zubama ƙofar ido musamman Imran, Faro, shugaban prison. Yaran sojojin uku da suka rage a wajen kawunansu a ƙasa na girmamawa. Sakan goma tsakani jarumin jarumai ya bayyana, bayyanar data saka gaba ɗaya sojojin wajen harda su Imran ƙamewa a tare suka sara masa.Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansu, sannan shima ya dunƙule hannaye duka yana ɗan miƙasu gaba alamar amsar girmamawar su. A karo na biyu, shugaban prison, Imran, Faro suka sake ƙamewa da sarawa irin ta girma da girma. A yanzu kam shima sai ya ƙame ya sara musu su ukun murmushin mai nauyi ya bayyana a fuskarsa. Kai tsaye ya saka idanunsa cikin na Faro da shima ke murmushi, ido ɗaya Faro ya kashe masa da sake yin wani salute na abokantaka da amintaka.
Dada ya girgiza kansa yana murmusawa da yima Faro alamar (bazaka taɓa canjawa ba) da idanunsa. Sai kuma ya janyesu a slowly ya maida kan Imran da ya tsaya cak kawai yana kallon sa shima. Idanusu ne suka haɗu cikin juna, shekaru takwas na ɓacin rai, rashin adalci, fushi da raɗaɗi duk suka bayyana cikin wannan idanuwa huɗun tamka a film ɗin da aka dannama pause.
Zak-Shadow ya sakarma Imran murmushi cikin nauyin zuciyar da ya saba ɓoyewa.
“…Imran Abbas?”.
Dada ya faɗa a karo na farko da wani irin salo na jini yaga jini.
Imran ya saki murmurshi tare da matsawa kusa da shi gab, sai kawai ya rungumeshi.
“Shagwaɓaɓɓena”.
Dada ya faɗa cikin kunnen Imran jin saukar hawayensa akan kafaɗarsa. Share hawayen yayi sannan ya ɗago yana murmurshi.
“Alƙawarin ALLAH ya cika. Rubutacciyar ƙaddara daga littafi na gaskiya ta taƙaita. UBANGIJI ya tabbatar mana zai jarabcemu, sai dai da jarabawar nan zai ɗaga darajojinmu a sama idan mun kasance masu haƙurin cinyeta. Ƙasarka ta jira dawowarka. Zuri'a bata manta da kai ba. Rundunar soji na kwatance da sunanka. Bararka da zuwa mai son a gina gaskiya a zartar da ita koda zata ƙona kai da kai. ALLAH ya cigaba da amintar da wannan RUHIN bisa kyakkyawan gini na gaskiya. A yau zan buɗe muryar data disashe saboda kukan kewa na faɗama duniya cewar Haysam Abdul-rasheed Shehu is back again”.
Murmurshi Dada ya saki mai nauyi, zuciyarsa ta rikice da son fitar da abinda ke zagaye da ita na kewa tsahon shekaru, ba dan prison ba, ba don wahala ba, sai dan kalaman Imran dasuka ratsata har cikin jini da jijiya dama ƙashi. Amma da yake mazan maza ne sai suka rikiɗe da ƙarfafa kai bayyananne. Da nayin kamewa da nutsuwa ya furta,
“Imran! You are my destiny. I am proud of you........✍️
34
..........“Almu na maka kiran gaggawa ne saboda ƙarin abokin aiki da zaka samu”.
Cikin tashin hankali maigadi ya ɗago yana kallon mutumin dake zaune cikin lallausar kujerar ƙayataccen falon. Sai kuma ya sake maida kan nasa ƙasa da sauri. Zuciyarsa na bugawa da yin rawa a cikin ƙirjinsa ya furta, “Ranka ya daɗe nawa aikin baya tafiya dai-dai ne?”.
Sai da mutumin yaja fin sakan uku kafin ya amsa cike da isa. “Aikin ka na tafiya dai-dai Almu, anzo gaɓar da shima wannan ɗin dole sai ya shiga gidan ne”.
“Shike nan ranka ya daɗe, yanda kace haka za'ai. Ni dai ALLAH ina sake roƙon arziƙi kada a cutar min da ƴar uwa. Kaima ka sani mu marayu ne, bamu da kowa a wannan duniyar sai kammu mu biyun nan rak.”
“Bijirema umarni na ne kawai zai iya sakawa ta cutu. Idan ka kiyaye ta kiyaye lokaci kaɗan ya rage muku ku samu freedom.”
“Zamuyi duk abinda kake buƙata in sha ALLAHU ranka ya daɗe. Amma dan ALLAH zan iya ganinta?”.
Wani banzan kallo daya saka maigadi sake nutsuwa mutumin ya watsa masa. Sai kuma yaja tsaki yana ɗaukar wayarsa dake gefe yay danne-danne. Kunnensa ya kai, sai dai a taƙaice ya furta, “Zaka iya fitowa”. Daga haka ya ajiye wayar. Shiru falon ya ɗauka, sai ƙarar tv dake fita ƙasa-ƙasa dana ac. Cikin abinda bai gaza mintuna biyar ba wani ya fito. A ƙalla dai bazai wuce shekara talatin da shida ba. Shima cike da tashi izzar yay ma Almu kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Sai da ya zauna a kujera sannan wancan mutumin dake kallonsa fuska da murmurshin da tun da Almu ya shigo bai gani a fuskarsa ba.
Almu ya nuna yana gyara zama. “Wannan shine mutumin da nake gaya makan. Yana aikin gadi a gidan kusan shekara huɗu ke nan, bayan mun tsige wancan ganin bazai iya mana komai ba.”
“Shi wannan yana yin abinda ake so kenan?”. Saurayin yay magana a karo na farko.
“Tabbas yana yi, dan tunda ya fara aiki babu wani kuskure da zance mara daɗi. Sunansa Almu.”
“Okay”.
Ya faɗa a taƙaice. Mutumin bai nuna ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Zaka shirya ne ku wuce tare? Ko zaka bishi daga baya?”.
“Kawai mu wuce taren, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe. Sai dai ya kamata nasan wane aiki zan iya samu a gidan?”.
Yanzu kam mutumin baice komai ba, illa juyawa da yay shima ya kalla Almu. Da sauri Almu yace, “Ranka ya daɗe sai dai in munje can ɗin, amma a yanzu gaskiya a gidan nan babu wani aiki. Dama a wata biyu daya wuce ne driver ɗinsu ya samu hatsari to da an samu sai ya maye gurbinsa. Amma yanzu ma inada tunani guda, akwai mai sharar tsakar gidan kullum da bama filawoyi ruwa. Yakan zo da safe yayi ya dawo da yamma. Sunyi-sunyi ya dinga zama nan koma kwana yaƙi, acewarsa yana wasu ayyukan ne idan ya kammala da nan. To ko shi zamu tunɓuke ta hanyar maƙarƙashiya sai shi ya maye shi?”.
“Eh wannan ma kazo da zance mai ƙyau. Amma miyasa ban san da labarin driver ba? Bayan kuma na sanar maka ko sabuwar kaza akai a wannan gidan nasan da ita. Ko cokali ya faɗi nasan da sautin ƙarar faɗuwarsa....”
“Ka gafarceni ranka ya daɗe, na nemeka amma ban samu ba, idan baka manta ba jiya daka turo min saƙon kana son ganina na tura maka amsa da dama inada wata magana. To dama maganar kenan”.
Maimakon amsa zancen sai cayay, “Kaje waje ka jira shi zai fito”.
Idanun Almu cike da ƙwalla ya jinjina kai. Yayi kamar zai miƙe sai kuma ya sake komawa ya duƙa. “Ranka ya daɗe dan ALLAH ko zan iya ganin ƴar uwata ɗin?”.
“No!”.
Ya bashi amsa a ɗan tsawace. Da sauri maigadi ya miƙe jikinsa na rawa ya fice a falon. Idanunsa kuwa tuni sun cika da ruwan hawaye. Zuciyarsa kam raɗaɗi take masa. Tabbas badan da ƴar uwarsa da mutanen nan suke amfani wajen juyashi yanda suke so ba sun san basu isa ba. Shine fa Almu, Almu na babba ƙarfe bashi ratsa jininka. Guduma mai fasa kan tantiri.... Ƙwafa yayi yana mai cije laɓɓansa, daga haka ya samu waje a bakin baranda ya zauna......
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A gidan Mammah rashin barcin wuri saboda murnar dawowar Uncle Bilal yasa yau kusan kowa sai da ya makara. Gasu Nimrah zasu je makaranta tunda an koma hutu. Ganin yanda lokaci yaja suka so lanjarewa akan bazasu je ba, gashi yau monday fa. Amma Uncle Ammar ya buɗe musu wuta dole suka shirya suna faman ɗaga baki. Uncle Bilal dake biye musu kuwa suna fitowa ya fara lallashinsu, ƙarshe yace shine ma zai kaisu school ɗin da kansa. A take bakunansu suka washe da farin ciki, dan suna matuƙar ƙaunar Uncle Bilal.
Breakfast ɗinsu aka shirya musu a lunch box Mammah tace suci a mota. Sun fito Mu'azz na tsokanarsu wai sun zama su Abees ƴan Nursery, Uncle Bilal ne yace karsu kulashi, dan haka harara kawai suka zuba masa suka shige mota. Tunda suka ɗauki hanyar school suna karyawa suna ma Uncle Bilal hira, duk da kuwa jiya babu kalar labarin da bai sha ba da ƙyar suka barshi ya kwanta. Su Aheel ya fara saukewa a tasu school ɗin, su Rukyn suka taimaka masa ya raka su har ajinsu yay magana da class masters ɗinsu. Dan Aheel da Abees ajinsu ɗaya. Afrah da Ayyan ma haka. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka koma mota.
Suma har aji Uncle Bilal ya raka su, sunyi sa'a Teacher Khalil ne a ciki. Ya gaisa da Uncle Bilal cikin mutunci kasancewar sun san juna. Sannan ya bada hakuri akan makarar ƴaƴan Mammah. Fuskar Teacher Khalil da murmurshi ya ce, “Ba komai Uncle ai yau da gobe sai ALLAH. Sai nazo gida cin tsarabar turai.”
Ƙaramar dariya Bilal yayi da faɗin, “Sai kazo ina nan ina jiran ka.” daga haka yayma su Nimrah bye ya wuce. Ƴan ajin kam da yawansu sun ƙyasa, yo sunga handsome masha ALLAH. Cike da neman magana Nimrah taja tsaki da taɓe baki tana magana cikin ƙunƙuni. “Mudai kar a cinye mana uba, naga mayu sunyi yawa a ajin nan haba irin wannan kallo haka kamar sabbin kwartaye”.
Dariya Ruky ta sanya, sai kuma tai saurin toshe baki saboda tunawa akwai Teacher Khalil a ciki. Kuma sarai yaji mi Nimrah ɗin ta faɗa da dariyar Rukyn. Dan kai tsaye ya juyo daga rubutun da yake akan allo. Sai dai baiyi magana ba, suma duk sun wayance sun ɗauka books kamar basu suka aikata ba. Yayinda mafi yawan ƴan ajin suka shaƙa da baƙar maganar Nimrah, sai dai sun san ba damar maida murtani Zakanya da Damisa su daki banza. Hibba dai tunda taci duka a wajensu take neman shishshige musu ayi ƙawance. Amma wulaƙanci irin na Ruky da Nimrah sai yarfata suke.....
★★★
“Wai Mammah ko duk farin cikin dawowar Bilal ne. Tunda na shigo gidan nan na fahimci farin cikin ki a bayyane yake”.
Murmurshi Mammah ta sake yi tana kallon Aunty Ummi mai maganar, ganin suma su Shariffa da su Mimi sun zuba mata ido sai ta sake sakin murmurshin da faɗin, “Inaga dawowar Bilal ɗin ce, dan yau kam wani farin ciki mai girma da ni kaina na gagara misaltashi ne zagaye da zuciyata. Dan haka na saka su Kulu suyi abinci mai yawa a fitar sadaka.”
Addu'a suka shiga jero mata da fatan ALLAH ya ƙara mata farin ciki da nisan kwana masu albarka. Ta amsa musu da amin tana shafa kan Mimi data kama hannunta ta sumbata. Dai-dai nan Bilal daya dawo daga kai su Nimrah school ya shigo falon. Ture Aunty Mommy abokiyar karawar tasa yay daga kusa da Mammah ya zauna yana faɗin, “Mi ake tattaunawa auntys.”
Aunty Mommy dake harararsa ta ce, “Anƙi a faɗa ɗin. Kawai dan neman faɗa kazo ka wani ture ni, da kama samu nazo ganinka tuzuru kawai”.
Cikin dariya Bilal dake amsar Babyn Aunty Mimi a hannun Aunty Lailah ya ce, “Humm kwantar da hankalinki yarinyar nan, kwanan nan kalmar nan ta tuzuru zaki bar faɗarta ne.”
Cike da zumuɗi Aunty Mimi ta taso ta dawo kusa da shi. “Dan ALLAH da gaske Yaya Bilalu? Dan ALLAH guntsa min wacece?”.
“Uwar gulma kenan”.
Cewar Bilal. Dariya gaba ɗaya suka sanya. Aunty Shariffa ta ce, “Wlhy dama nasan sai ka faɗa haka. Dan ALLAH a bamu musha Yaya Bilal. Dama gidan shiru kwana biyu babu shagali dan ma mun ɗan rage da sunan Baby Nawal ne”.
“Aunty Shariffa karki damu, lokaci ne zaku sani, amma shagalin biki sai Dada na nan in sha ALLAHU”.
A take falon yay tsitt, Dan shima yayi maganar ne muryarsa na ɗan rawa. Mammah ce tai gyaran murya, dan tasan yanzu zasu fara mata koke-koke. Cikin canja hirar ta ce, “Mudai yanzu tashi ka ɗakko mana tsarabar mu nan duk ita mukai zaman jira”.
Cikin dariya Bilal ya ce, “Kai Mammah harda ke? To kowa yay haƙuri baza'a buɗe tsarabar nan ba sai yarana sun dawo school gaskiya. Dan sune zasu buɗe ta”.
“Yau muna ganin jalala, har sai su kafi auta sun dawo za'a bamu tsarabar?”.
Yanda Aunty Lailah tai maganar yasa kowa fashewa da dariya........✍️
35
.......... ★PRISON★
9:30am dai-dai motocin sojojin biyu suka fice daga cikin prison ɗin cikin tsaro mai cikakken sirri, yayin da hukuncin UBANGIJI da ƙarfin ikonsa suka tabbata a daidai wannan lokacin wani razani ya gitta a zukatan wasu mutane daga ɓangaren Ƙungiyar duhu, a ƙasan rayukansu suka dinga jin cewa abu mafi hatsari ya faru. Sai dai daga ina? Daga wane yanki? Akan mi? A dalilin mi? Duk UBANGIJI ya toshe wannan amsoshin daga garesu, koda ata hanyar yaransu dake cikin prison ɗin babu wani labari da suka samu saboda gargaɗin shugaban ƙasa......
★A ɓangaren su CSP Alpha shugaban prison bayan fitar motocin su Imran biyu sai wajen ya sake nutsuwa takar an ɗora dutse a zukatansu, ga iskar da suke shaƙa ji suke kamar ta rikice da wani irin nauyin da babu mai iya fassara shi. CSP Alpha bai iya ya motsa daga tsayen da yake ba har bayan an kulle ƙofar gate ɗin. Jikinsa ya ƙara sanyi, numfashinsa na fita a cure, zuciyarsa ta kumbura cikin ƙirjinsa. Jin tamkar hajijiya na neman zubar da shi babu shiri ya jingina da bango kaɗan, hannunsa na riƙe da takardar Presidential Pardon da yake jinta da uban nauyin da yafi na takarda a hannunsa, ta koma mata tamkar nauyin dutse ne.
Dai-dai nan wani sojan da ke tare da shi ya matsa kaɗan yana son yin magana, amma CSP Alpha ya kaɗa masa ido cikin gargaɗin tsoro da rashin tabbas....
“Ka tafi! Ku tafi ku duka…!”
Muryarsa ta fita da ɗan kauri cike da bada umarni irin na manya. Kai tsaye sojojin suka bar wajen, sai dai zukatansu nata tsalle-tsalle, tsallen da suka tabbatar da in ya wuce zuciya yace zai zo kan harshe zasuyi nadama ne ta har abadan. Dan haka kowa ya ajiye abinda yaji ya kuma gani anan dan wata shirun tafi alkairi. Musamman ma daya kasance an musu gargaɗi na haƙiƙa dan tamkar an zaɓesu ne akan al'amarin...
Sai a lokacin shima CSP Alpha ya tuna da maganar da shugaban ƙasa janar Yusuf ya yi masa kwanaki biyu da suka gabata a cikin waya…
“Ka kiyaye sirri fiye da kiyaye rayuwarka. Idan ka yi kuskure, ba zan iya kare ka daga hukumar tsaro ko daga mutanen dake a waje suna jiran Zak-Shadow ba. Kuma wlhy duk wanda ya san wannan al’amari kafin lokacin da ya dace, to kai kanka ka yi masa jagora zuwa lahirarsa”.
Wannan kalamai ne da har cikin jinin CSP Alpha suke da tasiri mai saka razani da ƙaulanin zuciya har yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, goshinsa ya cika da zufa. Hannu ya kai ya sharce gumin, kafin ya furta da ƙasa-ƙasa kamar mai roƙon iska. “Ya ALLAH an sakani a tsakiya?. Wane irin mutum ne wannan Zak-Shadow ɗin da shugaban ƙasa ya zo kan al'amarinsa haka da gaggawa?”.
Bashi da amsa, babu kuma mai bashi ita a yanzu. Dan haka bai yiwa kansa dogon tambaya ba ya haƙura. Tsoron da yake ji game da maƙudan mutanen da ke bayan fage ya fi ƙarfin neman amsoshin tambayoyin nan dake danƙare a zuciyarsa.......
<<<%>>><★><<<%>>>
Tunda suka baro cikin prison ɗin shiru ya ratsa motar, sai sautin AC da numfashin su dake