KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 42

99K to 102K   out of 125.4K words

saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa.
      “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”.
    Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa.
      “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”.
      “ALLAH ya shirya min Ninah”
Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara.
     “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”.
     “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.”
           Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.”
       Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai.
        “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”.
    Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”.
       “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya.
           “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”.
     Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.”
    “A’a. Ba da gaggawa ba.”
  Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da,
    “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.”
       A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya.
Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita.....

>>>>>>>%<<<<<<<

       Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna..
       Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”.
      Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta,
     “Hmm.. yaranka basa ji.”
Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai.
       “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?”
    A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa.
      “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”.
    Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa.
      “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”.
      “ALLAH ya shirya min Ninah”
Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara.
     “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”.
     “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.”
           Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.”
       Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai.
        “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”.
    Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”.
       “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya.
           “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”.
     Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.”
        Dada ya ɗan yi ƙwafa kaɗan, murmushi na neman kufce masa. Ya dai juyo gefe yana ƙoƙarin ɓoye abinsa. Kamar baya so ya furta,
      “Yara ne. Amma ba ƙanana bane tunda har suna da wayon banbance abubuwa. Dan itama Ruƙayya aure zan mata”
      Cike da neman magana Daddy Imran ya ce cikin raha,
      “Hmm… yanzu ka fara ganewa kenan?”
      Dada ya kallesa.
“Gane mi?”
   Imran ya ɗaga masa gira cike da tsokana da son ganin ya ƙure shi.
      “Cewa ɗiyata Nimrah ta girma.”
Nan ne Dada ya kasa danne kansa. Ya saki ɗan murmushi mai nauyi, ya kauda kai gaba ɗaya yana girgiza kai a hankali.
          “Kar ka fara”.
Ya faɗa cikin gimtsewa.
Dariya Daddy Imran ya saki.
   “Wlhy dole in fara. Saboda kallon da ka mata yau a station… ai na san wannan kallo.”
       Dada ya ɗaga kai yana harararsa da sake ɗaure fuska, sai dai murmushin dake makale a fuskarsa ya neman fallasa shi.
     “Imran!”
Ya faɗa da gargaɗi.
“Yi haƙuri Babban Yaya, wannan idanun bana son suna hararata.”
      Sake hararar tasa kuwa Dadan yayi yana ɗauke kai. Imran ya murmusa da cigaba da faɗin, “Amma kai ka fi kowa sanin damuwar ka. Ka ƙi kace komai akan dawowar Nabeeha. Zak.. shekara takwas fa ba wata takwas bane. Lemon tsami, kanwa, azumin nan duk basa hana komai, kwantarwa ne kawai na lokaci. Ya kamata kayi abinda ya dace, bance Nimrah ba, dan tabbas tayi ƙanƙanta a shekaru, amma da wayonta. Sannan Nabeeha ba sakinta kai ba balle kace. Komai ya dai-daita, sai dai ka sani aiki bazai samu dukkan ƙarfinka ba, sai kaima ka Dai-daita. Wannan danne damuwar ta tsiya-tsiya bazata haifar da ɗa mai ido ba”.
         Dada da ya ce, “Hummm” kawai ya yi shiru. Sai dai wannan shiru ba na ɓacin rai bane. Na tunani ne… da ɗan murmushi a zuciya. Dai-dai nan suka iso inda suka nufo. Ɓoyayyen guesthouse dan haɗuwar ta sirri ce da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida...........✍️

65


........A gidan Mammah kam bayan komai ya lafa, aka taimaka wa Afeef aka kai shi sama, ƴan uwansa Hanoon da Dayyan na tare da shi. Dan wata irin tsanar Nimrah da Ruƙayya suke ji na ƙara tasiri a zukatansu. Hatta ƴan gidan kowa ya basu haushi yau, yanda ko sau ɗaya ba'ama Nimrah faɗa ba balle cigaba da tuhumar gaskiya. Dan koda su Ma'aruff suka shigo kasancewar basa gidan su duka huɗun sunje duba wani makwafcinsu ne da baida lafiya da aka basu labari ko nuna zargin ma Nimrah basuyi ba su. Ƙarshe ma hira suka koma abinsu kamar komai bai faru ba. 
     Hanoon ta kira Abbansu ta sanar masa komai, baya ƙasar dan tunda ya kawo su gidan yay tafiya. Shima ransa ya ɓaci har yana faɗin sai yayi maganin Nimrah idan ya dawo. Tunda yaga tsoronta suke ji a gidan. Shi yama rasa dangantakar su Adda A'isha da yaran duk da dai adadin jikokinta kawai ta sanar masa batai masa bayani ba bayan hakan. Shiyyasa yake tunanin jikokinta ne. Wayar yace a bama Afeef, ya lallasheshi da tabbatar masa zai dawo a cikin satin nan. Idan kuma zasu koma gida Lagos ne to ya saya musu ticket. Caraf Afeef yace shi bai yarda ba, yafi son Nan ɗin, dan wlhy bazai tafi ba sai ya rama..
     Sallama yay musu da faɗin sai ya zo to. Daga haka aka yanke wayar Hanoon na cigaba da faɗin, sai ta koyama su Nimrah hankali a gidan nan. Shi ko Dayyan ƙudirinsa daban a cikin rai. Dan tunda yazo gidan hakanlinsa akan yaran nan biyu yake. Rashin mutuncin su ya saka shi haɗiye kwaɗayinsa.
     Sun jima a ɗakin kafin su fice su bar Afeef, dan abokin kwanan nashi Mu'azz bai shigo ba.
     A daren Afeef ya jima bai yi bacci ba yana ƙulla abinda zai ma Nimrah. Dan can cikin dare ma zaune ya tashi a kan gado kafarsa na masa masifar zogi, fuska a haɗe kamar ya ci lemon tsami. Waya ya ɗauka yana danne-danne, amma tunaninsa na kan ƙulle-ƙullensa.
    (Wallahi ba zan bari ba)
Ya tuna murmurshin da Nimrah ta masa da gwalo bayan fitar Dada. Da yanda suka kalla juna da Ruky da munafukin nan Mu'azz sukai wani salo da yatsu suna gimtse dariya. Itama Ruƙayyan yana ganin yanda take kallonsa tana murmurshi. Harda gwada masa yanda shugaban ƴan iska ta saka masa ƙafa. Hakan na nufin itama ta gani amma da yake mufuka ce bakinsu ɗaya ne ta musanta harda bata kariya.
     “Yar iska… zanyi maganinki ta yanda ko takuna kika ji sai kin firgita ” ya faɗa ƙasa-ƙasa. Sai kuma yay ƙwafa da sake faɗin, “Ba kince kina da wayo ba.” Ya saki murmushi yana cizar lips da ƙara faɗin, “Zan tabbatar muku na fiku zama tantiri. Zaku san ni cikakken rainon yahudawa ne. Idan ba yau ba, gobe. Idan ba a falon ba, a wani wuri.”
     Ya saki wata shegiyar dariyar data farkar da Mu'azz a barci. A fili ya sake faɗin, “Sai kin gane baku kaɗai bane jiƙaƙƙun tantiran ƴan iska a gidan nan”.
     Sarai Mu'azz yaji furucin Afeef na ƙarshe. Sai dai bai ce komai ba, baima nuna masa ya farka ba. Amma ya fahimci akwai abinda yake shiryawa kuma akan Nimrah. Ji yay tausayin Afeef ɗin ma ya kama shi, dan wlhy ya tabbatar yace zai cigaba da shiga sabgar Ninah da Ruky a gidan nan to da wahala ba'a fita da shi a ambulance zuwa asibiti ba wataran. Dan yafi kowa sanin yaran nan, zaman lafiyarka da su kawai kada ka shiga sabgarsu. Anan kam zaka ga biyya, amma saɓanin hakan ALLAH ne kawai mai ƙwatarka saboda hanyoyin mugunta iri-iri sun santa kamar goyon iblis. Bari ya barsu da shi jikinsa zai gaya masa....
       
       ★A ɓangaren Nimrah tuni tama manta da wani batun Afeef. Dan koda suka shiga ɗakin su tsara yanda zasuyi yawo a weekend ɗin nan suke yi, suna fatan ALLAH ya ɗorasu akan Mammah kada ta hana su duk da suna hutun tahfiz ne. Sun jima kafin su kwanta sanin gobe akwai makaranta, duk da dai basu san ya zata kaya ba tunda sun bazar da ɗan shugaban ƙasa mai sauka a ƙasa. Nimrah ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwa. Ruky ko tuni ta yi bacci tana sauke numfashi a hankali. Ita kam… ido biyu a rufe amma zuciya a buɗe. Haka kawai abinda ya faru ɗazu a falo kuma ya shiga dawo mata a rai. Ba kuma akan kowa ba sai kallon Dada ne yake dawowa mata a kai. Ba tsawa. Ba magana. Sai shiru da kallonsa mai kaɗa hanjin ciki..
         Dai-dai lokacin dogarinsa ya kammala zuba coffee a kofuna masu shegen ƙyau na zallar farin gilashi mai garai-garai daga haɗaɗɗen coffee maker dake saman Centre table ɗin. Gaban kowa ya kai ya ajiye. Kafin cikin girmamawa ya nema izinin tafiya. Kai Janar ya jinjina masa alamar bashi dama. Sai ya sake risinawa sannan ya fice ya maida ƙofar ya rufe musu, bayan ya ƙara rage hasken falon ya bar blue ɗin wuta mara ƙarfi kamar waɗanda ke cikin club.........✍️
66


.........Shiru falon ya ɗan ɗauka na mintuna. Shiru irin na manya kowa na nazartar ɗan uwansa. Kafin Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ya katse yanayin. Bada murmushi mai yawa ba, amma da girmamawa ta gaskiya kuma ta musamman da amana ya furta,
     “Zak-Shadow”.
         Kai daga jin yanda sunan ya fito daga bakinsa kamar sirri da aka daɗe ana ɓoyewa kasan yana cikin farin ciki mara misali ne.
       Dada ya wani ɗan lumshe idanun sannan ya buɗe su. A nutsensa ya amsa da.
      “Ranka ya daɗe, Your Excellency.”
Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi. Hakama Imran dake kai coffee bakinsa sai da ya murmusa.
     “Anan… babu ‘Your Excellency’. A yau, ni da kai ne da Imran kawai. Ba matsayin shugaban ƙasa ba, matsayin abokin aiki a gidan soja kawai. Idan kun so zaku iya ƙarawa da wani abinda kuke ganin ya dace ku ambace ni. Amma ba bigiren siyasa ko shugabancin ƙasa ba”.
      Yanzu kam ba Daddy Imran kawai ba, har Dadan sai da ya saki wani guntun murmushin gefen baki yana sake gyara zamansa na ƙasaita.
       Shiru ne ya sake ratsa ɗakin, shiru mai nauyi, irin wanda ke gwada ƙarfin zuciya da girmamawa. Shugaban ƙasa ya cigaba da faɗin,
      “Na jira sati guda. Ba don rashin gaggawa ba… sai don na tabbatar kana lafiya. Sannan ka huta, ka gana da Mammah da ƴan uwa da iyalai yanda ya dace.”
       Dada ya ɗan jinjina kai, kafin ya furta, “Na gode ranka ya daɗe. Dama ni ba na son gaggawa. Nafi son tabbaci.”
      Shugaban ƙasa ya jinjina kai.
“Wannan dalilin ne yasa ka dawo.”
Dada bai yi mamaki ba. Sai dai ya ɗan murmusa, sai kuma ya ɗan harari Imran.
       Ƙaramar dariya Imran da Janar sukayi a tare. Janar ya sake faɗin, “Ba Imran bane ai. Na sani tun kafin ka taka ƙasar nan. Kuma na sani cewa dawowar ka ba ta nufin hutu. Hakan ya mun daɗi, dan na sake gaskata har yanzu wannan ƙasar tana cikin zuciyar Zak-Shadow, kuma itace gaba a cikin manyan burukan sa na rayuwa.”
      Dada ya ɗan jingina da kujerar yana furzar da iska mai nauyi, sai kuma ya zuba kaifafan idanunsa cikin na Janar. Ba wargi, amma ba wasa. Cike da dakiyar sa matsayin soja da bai san tsoron tunkarar matsala ba ya ce,
       “Idan haka ne… me yasa kuka kira ni nan?”.
    Shugaban ƙasa ya ɗan yi shiru yana kauda idanunsa, sannan ya ce cikin murya mai kauri:
       “Domin wasan ya sake farawa Haysam. Dan a yanda na ilimantu cikin siyasar ƙasar nan babban yaƙi ne a gabanmu ba murƙushe ƙunya kawai ba”.
      Idanuwan Dada suka yi kaifi akan Janar. Cikin wani yanayi ya furta, “Kana tsoron Ƙungiyar duhu bazata iya mutuwa bane cikin sauƙi?”.
          “Ba haka nake nufi ba Haysam, ai tunda kafiran baya masu taurin kai da izgili irin su Abu Lahabi suka ƙare a doron ƙasa, daular musulunci ta kafu

34 / 42