KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   40 / 42

117K to 120K   out of 125.4K words

Imran tunda abu ne duk na gida. Shiyyasa sam Dada baya zaman gidan. Bama zai iya cewa yasan wace waina ake toyawa ba. Suma sun maida hankalinsu akan wancan gidan da suke shirin maidawa na sirri. 
Tabbas, wannan gida a zahiri Dada da Imran sun maida shi tamkar gida na yau da kullum, amma a gaskiya UNIT ZERO ne, cibiyar sirri da aka gina domin yaƙin da ba a sakawa suna ba a fili. An sauya duk wani abu mai ƙarancin tsaro zuwa mafi girman matakan tsaro. Tun daga ƙofar shiga, komai ya sauya. Ba ƙofa ce da ake buɗewa da hannu kawai ba. Ana amfani da multi-layer authentication: lambar sirri, na’urar biometric, da kuma time-based access. Ko su da kansu, idan lokacin bai dace ba, ƙofar ba za ta buɗe ba.
       Tagogi kuwa an maida su bullet-resistant glass harbi ba zai iya ratsa su ba. An saka ɓoyayyun cameras ko’ina. An kuma tanadi ɗaki guda na musamman domin ajiye ayyukan sirri, ɗakin da Dada shi kaɗai ke shiga, sai Imran da Faro. Smart perimeter sensors sun zagaye gidan gaba ɗaya ba wai don mutane kawai ba, har da motsin iska, ƙasa, ko duk wani abu da bai dace ba. Akwai silent alarm system: babu ƙara, babu haske, amma UNIT ZERO ya riga ya zama ido da kunne na komai. Thermal cameras suna iya gano mutum ko da cikin duhu ko ta bayan bango. Ƙofofi kuwa EMP-resistant ne ko an katse wuta, ko an yi hacking, ba za su buɗe musu ba..........✍️



76


.........Cameras marasa gani da ido, ba su da haske, ba su da amo. Wasu an saka su a cikin bango, wasu ma a cikin furanni. An tanadi blind-spot tracking a inda babu camera, akwai sensor. Duk motsi ana adana shi ne a local encrypted server, ba tare da haɗin internet ba. A wasu sassa ma babu wata waya da ke kama signal, musamman a EMI shielded rooms.
      Hatta talabijin da ke nuna dukkan motsin gidan ta hanyar cameras suna cikin ɗakin kula da tsaro. Akwai na'urorin aiki na musamman da shugaban ƙasa ya samar, irin waɗanda manyan ƙasashe ke amfani da su a duniya. Manyan monitors suna nuna duk motsin gidan, sarrafa cameras, da ajiye bayanan sirri. Babu waya, babu recorder, babu wani motsi da zai faru ba tare da sun sani ba, ko da basa cikin gidan. Abin da aka faɗa a nan, ya mutu a nan. Ko hoto ma ba ya ɗaukuwa a gidan, balle a ɗakin sirri.
       A tsararren ɗakin sirri, dukkan takardu suna cikin classified physical files da aka kulle da code da fingerprint. Wasu bayanai ba su da suna, sai lambobi kawai. Wasu hotuna da bayanai ana ajiye su ne a dead vault, ba a buɗewa sai an cika sharaɗi guda uku. Ana amfani da dead-drop system wajen musayar bayanai, ba tare da haɗuwa kai tsaye ba.
      Akwai makamai iri-iri makaman da ba a rubuta su a kowanne rijista ba. Na'urorin sauraro, bin sawu, da ɓoye fuska. Haka kuma akwai kayan fitar gaggawa idan aka kai hari, da wuraren ɓoye ainihin jami'an sirri masu kai ɗauki. Da zarar ka shiga wannan ɗakin, zaka fahimci cewa an shirya yaƙi ne yaƙi na gaske, ba wasan yara ba.
     Ba kayan aiki kaɗai aka tsaya ba. An tanadi hanyoyin fitar sirri ta ƙasa, waɗanda kai tsaye ke haɗuwa da manyan magudanan ruwan unguwar. Hanyoyin ƙasa da aka ɓoye cikin tsarin gine-gine. Ba hanya ɗaya ba fiye da uku. Wasu suna kaiwa wurare daban-daban a unguwar, wuraren da ba za ka taɓa tunanin suna da alaƙa da gidan ba.
          Tabbas shugaban ƙasa yayi ƙoƙari wajen zuba kuɗi akan wannan aiki, duk da dai ba'a fitar da su daga asusun gwamnati kai tsaye da wannan manufar ba, an laɓe bayan wani aiki ne da aka bada kwangilarsa kai tsaye, a bayan fage kuma akai wannan aikin. Kowa da zaiyi aiki da UNIT ZERO bai san ainihin shugaban tawagar ba. Umarnin aiki zai dinga zuwa ne ta code name. Idan aka kama mutum, babu abin da zai iya faɗa da zai rushe tsarin gaba ɗaya. UNIT ZERO ba gida ba ne kamar na shirin Film kawai, babbar FADAR YAƘI ce a ƙarƙashin umarnin ZAK-SHADOW. Wani gawurtaccen station blinding ne da zai ruguza duk wani mai tsautsayi da zai iya shiga tarkon ZAKI. Dan duk wani shiri an kammala shi yanzu kam hatta filin saka mazare rawa da sarƙa a kafa. Shi kansa uban gayyar ya furta “YANZU NE AIKIN ƘARSHE ZAI FARA. A kashe ko ya kashe, wannan shine ƙarshen BURI......”

        “Alhamdullahi komai ya kamala, lokacin fara aiki yayi. Yanzu minene shiri na farko?”.
        Iska Dada ya ɗan furzar yana ajiye takardun hannunsa ya gyara zama da kallon Imran mai maganar. Cikin sake maimaita godiyar ga UBANGIJIN shima ya bashi amsa da, “Inaga zan gana da su dabo a daren yau. Kai ma lokaci yayi da zaka koma aiki sosai kafin su fara tsarguwa da rashin zamanka office.”
      “Nima nayi wannan tunanin. In sha ALLAHU kuma zan koma wannan Monday ɗin. Yaya batun karatun yaranka, ya kamata su koma makaranta fa. Dan in ka biye musu su wannan zaman shiriritar daɗi yake musu, musamman daya zam babu islamiyya. Ammien su tace a zaman jegon nan babu abinda suke sai rashin ji, kawai dan baka yini gida ne kai ma. Dan jiya ALLAH ya kiyaye suda yarinyar nan Hanoon da anyi babu daɗi.”
         Murmushi kawai Dada yayi. Daddy Imran ya hararesa. “Kace mune ke ɗaure musu ƙugu, amma ka fimu. Nazata dawowarka zata saka su nutsu amma shirun da kake musu yayi yawa, ya kamata ko sau ɗaya kaci ƙaniyarsu.”
      “Basuyi abinda zanci ƙaniyar tasu bane shiyyasa. Makaranta kuma zasu koma. Dan baza'a canja musu ba akwai shirin da nakeyi kafin su koma ɗin, da kaina zan maida su”.
      “Hakan yayi ALLAH ya kaimu. Sai mutuminka ya dameni akan batun Auta. Wai kunyarka yake ji shiyyasa ya kasa magana. Kar kaga kamar yayi gaggawa.”
    Nan ma murmushi Dada yayi da faɗin, “Ai yayi ƙoƙari, ya kamata ka duba masa. Sai ka haɗa da Bilal da Ammar. Dan suma bana son zamansu haka. Ya kamata duk su ajiye iyali”.
        “Eh wannan shawara ce mai ƙyau. Amma ban taɓa ganin Ammar da budurwa ba. Gara Bilal”.
     “Na tambaye shi nima yanata min ƙunshe-ƙunshe. Shine nace masa yaje ya tura min saƙo to. Sai jiya yake tura min wai ai bata girma ba, kuma tana a gidan tare damu. Amma bai taɓa nuna mata ba sai ta kammala Secondary”.
        “Tofa ji ja'iri, wacece haka?”.
     “Bai faɗa ba, amma ni na fahimci Ruƙayya yake nufi”.
   “Kai amma Ammar mashiririci ne. Yarasa mata sai wannan kayan shirme da shiriritar. Kuma a haka kake cewa a haɗa da shi, ciwon kai kawai ka nemar masa”.
        “Ko?”.
    Dada ya faɗa yana ɗan ɗage gira sama. Baki Daddy Imran ya taɓe. “Kaima ka san yarinyar nan taka sai a hankali”.
       “Ba komai zata bari wataran. Ai dama na gaya maka aure zan mata”.
     “To ALLAH ya taimaka. Sai kai kuma uban gayyar. Dan ALLAH kayi haƙiri muje bikon Nabeeha. Dan ina cikin mamakin yanda har yanzu bataji ko labarin dawowarka ba. Ko har yanzu tana fushi ne”.
      “Dawa zaka je ɗin?”.
   “A! Dakai mana. Zakina dan ALLAH ka rage taurin kan nan. Sufa mata ba'ai musu haka. Lallaɓasu ake, a riritasu. Ayi haƙuri da halayensu marasa ƙyau. Tunda har akace mana tun daga tushe a karkace suke, tsaurin mu bazai sa su miƙe ba fa. Idan ma muka tsananta zasu karye ne.”
         “Ni babu inda zanje, ƙafarta data fiddata idan ta gaji da zaman ta dawo da ita”.
      “Kai kuma halin da kake ciki fa?”.
   “Ni na gaya maka ina cikin wani hali ne?”.
    “Kasan na sanka fiye da kowa. Ai ba sai ka faɗa min ba. Koda kake ganin dama can kana azumin ka ai na yanzu yasha banban. Sannan yanzu fa kake faɗar su Bilal su ajiye iyali saboda shine cikar kamala. Amma kai kana bijirewa. Kai ne fa uba, ko Mammah na tabbatar ta maka shiru ne taga iya gudun ruwanka. Idan kai bazaka je ba, ni ka barni naje to”.
      “Wlhy bazaka ba”.
   “Harda rantsuwa? To shike nan Nimrah ta tare”.
    “Amma baka da hankali”.
  Dariya Imran yayi sosai, ya ce, “Naji banda shi. Miye a ciki to. Naga yaran ƙauye ana musu aure ƙasa da shekarunta. Balle su suna cin abinci mai ƙyau kuma ALLAH ya kawo girman da wuri. Kadai duba al'amarin nan. Bar ganinsu haka sun san abubuwa da yawa tunda suna zuwa islamiyya. Idan ba hakaba kana nan wasu zasu fara koya mata abinda kai kake ganin bata sanshi ba. Dan kwanaki sai da naci ƙaniyar wani malamin islamiyyar su wai shi Kamal. Daga baya ma na bincika wai yabar makarantar, amma da ya dage shi son Nimrah yake yi. Har ya fara zuwa gidan fa”.
       Wani mugun kallo Dada kema Imran kai kace shine Kamal ɗin. Aiko mi Imran zai yi inba dariya ba. Sai kawai Dada ya miƙe abinsa daga nan hirar ta watse ma. Har ya kawo shi gida bai sake kulashi ba. Haka ya sauke shi shima ya kama hanyar gida yana kwasar dariya. Dan shi kaɗai yaga bala'in daya hango a idanun zakinsa. Ai ko a fagen fama albarka.
      Ƙasa daurewa yay sai da ya bama Ammie labari. Itama taita dariya. Daga ƙarshe tace, “Ni kaina nayi tunanin fara shiri sai naga bakuce komai ba, amma share masa ɗaki a sashen Mammah. Amma magana ta gaskiya bana son Nabeeha ta dawo gidan nan Yarinyata bata tare ɗakinta ba.”
         “Ai kunji matsalarsu iyayen zamani, zaku fara koya mata kishin banza ko”.
     “Ba wani koya kishi Daddyn Khalifa magana ce ta gaskiya. Tunda ita bata da hankali dan mijin ya ƙara aure kin ɗauki ƙafa kin tafi gida. Ya shiga wani hali ki dawo ɗakin ki ki zauna kuyi jimami, kuyi kuka tare da ƴan uwansa da Mahaifiyarsa amma kin biyema taki uwar sai yawon gantali. Yanzu duk randa yasan wannan zaman Dubai ɗin da taje tayi mi kake tunani dan ALLAH. Zargi ma bazai shigo ciki ba”.
        “Ai babu ma wanda zai gaya masa. Yanzu dai mubar maganar, gyara kuma kiyi tayi, sai ki haɗa da Biebah da Asma'u harma da Ruƙayya”.
     Idanu sosai ta waro na mamaki. “Ruƙayya fa?”.
        “Eh, ubanta yace aure zai mata, yama mata miji. Gara ma yayi hakan, dan zanfi samun dama a kansa nima game da tarewar Nimrah ɗin”.
      Ammie da abin ma ya bata dariya ta ce, “To ALLAH ya sanya alkairi, yasa ayi damu, amma dai wannan miji zai kwasa.”
       Dariya Daddy Imran yayi itama tana taya shi. Ya ce, “Kamar kina wajen abinda na faɗa kenan nima. Amma tunda mai abu da abunsa sai ka tayashi da sambarka.”
       “Haka ne kam, ALLAH yasa ayi da rammu to”.
     “Amin ya rabbi”.........✍️



77


........Ana gobe suna su Gwaggon Alawiyya suka iso. Ai fa gida ya kacame. Su Nimrah amarori. Dan ma ita damuwa ta raba mata hankali biyu, dan ta gama shirya a cikin rarumar sunan nan zata haɗu da Dagger. Shiyyasa ma tai luff abinta a kwanakin da suka gabata kamar komai baya damunta. Amma da yake ita Ruƙayya na tare da ita tsaff ta gane damuwar kwanaki tana neman dawo mata. Koda ta dameta da tambaya sai tace rashin zuwa makarantar su ne ke damunta. Har tana bada shawarar idan anyi suna su sami Dada da maganar, dan gani suke kamar Mammah ce bata son su koma tana tsoron a musu wani abu. Ruƙayya ta gamsu da hakan shiyyasa ta saki maganar. Itama kuma Nimrah sai ta sake canja takunta. Dan yarinya ce mai shegen wayo da iya rikiɗa kamar hawainiya.
    Cikar gidan kuma ta sake maidata busy, dan ranar su aunty Ummi ma duk anan suka kwana. Dada ne dai basu gashi a gidan ba kwata-kwata tun safe. Babu ma wanda zaice ga sanda ya fita.....

<>%<>%<>%<>

A ɓangaren Malam Buba jinsa yake sharr, dan kuwa shugabannin ƙungiya sun sake zama na biyu da shi. A cikin satin nan ma akwai babban aikin da zasu fitar. Ya samu cikar burinsa an bashi shugabanci harda yara a ƙarƙashin sa, sai dai ba yaran Dagger aka raba aka bashi ba kamar yanda yaso. Sabbin yara ne waɗan nan da baima san dasu ba. An basu horo mai suna horo. Sai yaji ya sake tsoro da shakkar al'amarin ƙungiyar duhu. Dan hatsabibancinsu na gaske ne ƙwarai da gaske. Sannan sun wuce dukkan inda ake zato da tsammani. Duk iya hasashenka baka isa iya ƙare musu gudu ba. Suna da ɓoyayyun abubuwa da sai UBANGIJI ne kawai ya sansu sai su.
     Abinda dai ya tayar masa da hankali shine sun tabbatar masa dole ne yabar gidann su Nimrah. Dan zamansa bazai yiwu ba dan yau da gobe zata iya kwaɓewa kasancewar sun san waye Zak-Shadow, sun karanceshi sun kumayi imani da mutumin ne mai shegen wayo. Na biyu ɓoye fuskarsa da nisantar Nimrah zai bashi damar cimma burin dawo da ita cikin rayuwarsa. Duk kuma randa zata san shi waye a gareta zata ji martaba da girmansa matsayin uba.
      Ya gamsu, duk da hakan ya saka shi a damuwa. Amma sun bashi shawarar ziyartar gidan lokaci-lokaci koda da nufin gaisuwa ne, hakan zai sa ya dinga ganin nata...

    Na biyu Sanda. Sanda har yanzu yana wasan ɓuya da Dada, bai taɓa bari Dada ya ganshi ba. Yaƙi kuma sanarma maigadin komai. Tun yana tambayarsa harma ya daina. Nimrah kuwa dakan ari wayarsa bai taɓa hanata ba. Gashi Sarkin wayon data gama take goge number ɗin. Sai dai yana nan ya shirya. Dan yana son yasan abinda take ɓoyewar. Tunda duk da akwai camaras a gidan ta iya kaucewa hakan ta ɓuya a inda babu tayi wayarta. Ya saka mata ido sosai batare data sani ba. Dan ita tana ɗaukarsa ne a garan ƙauye da baya gane komai....

      ••••••••••••••
            ••••••••••••••

       RANAR SUNA.....

RANAR DA ABUBUWA UKU MASU MUHIMMANCI SUKA FARU A CIKINTA.

  NA FARKO....

      Yau take suna a gidan Mammah, tun daga sallar asuba aka raɗa sunan yaro da yaci Uncle Nasiru. Wato Naseer. Dada ne kuma ya zaɓa masa wannan suna bai kuma sanarma kowa ba sai a yau ɗin. Kowa yayi farin ciki da abinda yayi, musamman Mammah dake ta saka musu albarka. Tun kafin tara tayi su Nimrah suka cika gidan da hayaniya.
         Dan party suka shirya ita da Ruky, Bintu, Feedo. Babu wanda kuma yasan sun shirya abinsu sai Mammah. Sai Uncle Bilal da suka tasa a gaba ya basu kuɗi. Sunyo gayyar ƙawaye sai dai ba wani da yawa ba, yawancin su ma ƙawayen Feedo da Bintu ne, dan masifar Ruky da Nimrah tasa ko ƙawaye basa iya zama da su. Su biyun nan sun ishi kansu suke cewa, sai su Bintu. Girkinsu suka ƙirƙira daban, duk da an biya kuɗi za'ai na suna su sunce zasuyi nasu a gida, saboda ba abinci sukai ba duk kayan kwaɗayi ne da shiririta. Hakan yasa su wannan sammakon tashi suketa cacai-cacai.
         Dada da suka isa da hayaniyarsu, dan tun daga sama yana jiyo su, ga kiɗa sun kunna ya tashi kawai yay shirinsa. Dan gara yabar musu gidan shi kam. Zai je kawai ya gaida Baffa suyi hira tunda ya dawo dama bai nutsu sunyi hira ba sai dai yaje ya gaishe su shi da Hajjo sama-sama.
Lokacin da yake sakkowa sam su Nimrah basu sani ba, dan sun dage suna shan rawa abinsu bil haƙƙi. Biebah na musu video ita da Mu'azz. Kansa kawai ya girgiza ya wuce abinsa batare da kowa ya lura da shi ba sai Aunty Mommy, da ido kuma yay mata alamar kar tai magana. Dole tai shiru tana murmurshi, shi kuma ya fice.
     

NA BIYU

   Fitar Dada babu jimawa labari da ɗumi-ɗuminsa ya iso sashen Mammah. Wai ga wasu mutane sunzo sashen Dada da babu kowa a ciki tare da Nabeeha da ƙannenta. Falon yay tsitt, kafin kowa ya iya magana sai ga Hajiya Hasiba ta shigo Amima biye da ita. Sai da ta gama bin falon da kallo sannan tai murmurshi tana ƙarasawa inda Mammah take da su Gwaggo Khadijah. A ranta kam faɗi take (Ni Hasiba yaushe mutanen nan sukai kuɗi haka? Ya akai Banda labari) a zahiri kuma da murmushi nan na fuskarta takai zaune a kujerar da Aunty Badiyya matar Uncle Jamilu ta bata tana faɗin, “Hajiya A'isha ashe suna ake gidan haka bamu da labari”.
         Mammah a duk yanda kake ta iya da kai, sai itama ta saki murmurshi. “To ayi haƙuri munyi laifi. Wani lokacin abubuwan nauyi suke a kai sai ka manta da wasu”.
      “Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Dama ɗiyarki ce zata dawo ɗakinta, shine muka zo da kamfanin da zasu saka kaya a sashen nasu, kinga ba'a maida waccan ba ai”.
     Nan ma murmurshi Mammah tayi, ga falon yayi tsitt kowa na jiran yaji amsar da Hajiya Hasiba zata samu. Musamman su Aunty Mimi da wani tarnaƙin baƙin ciki ya lulluɓesu. A bazata suka ji Mammah ta ce, “Keys ɗin suna hannun Muhammad ai, ta kira shi nasan zai kawo muku. Dan babu ma jimawar nan ya fita”.. 
          Dariya Biebah ta ƙumshe, haka ma Aunty Mimi. Su dai su Nimrah basu fahimci komai ba. Hankalinsu ma nakan ƙulla kayan da zasu raba dan Mammah ta saka sun kashe kiɗan dan kunensu ya huta. Maimakon Hajiya Hasiba ta nuna jin

40 / 42