Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
samun su Aunty Mimi yau ma a gidan. Duk da su kaɗai ne babu yara ko ɗaya sai Baby Nawal dake ɗakin Mammah tana barci. Bayan sun gama rungume Mammah da mata shagwaɓa suka gaida iyayen nasu.
Dai-dai suna cire hijjabai Ruky ta makama Dayyan daya zuba musu ido kamar tsohon maye harara. Maimakon yaji haushi sai ya sakar mata murmushi. Ita Nimrah bata lura ba, hankalinta nakan magenta dake matuƙar shan gata a gidan kamar ƴar mutum. Tayi girma abinta tayi ƙyau kai kace magen turawa ce. Ta ɗaga ta tana mata kiss da rawa Ruky ta ƙaraso inda take. Dai-dai nan kuma Daddy Imran ke sakkowa daga upstairs Dada a bayansa. Sai dai da yake Daddy Imran ɗin ne a farko shi suka fara gani, sai dai shima sai da yay magana tsabar yanda su duka hankalinsu ke kan magen da suke kira da suna Mishi. Wani lokacin kuma suce Peppy.
“Halan yaran nan yau basu ganni bane”.
Muryar Daddy Imran ta shiga cikin kunnuwansu a bazata. A tare suka juya inda yake, sai kuma Ruky ta zabura ta rungumeshi. Sai dai Nimrah batai hakan ba, dan tun suna ƙanana ma sosai ko tazo rungumesa kamar Ruky cikin wayo yake hanata yin hakan, tun bata fahimta harta fahimta, bayan sun ƙara girma a islamiyya ta fahimci kuma dalilinsa na yin hakan, shiyyasa bata taɓa damuwa ba sai ma kima da daraja daya ƙara a idonta. Kusa da shi ta matso tana masa sannu da zuwa itama, sai kuma ta juya a hankali jin motsin kamar mutum a kusa da su. Da sauri ta janye saboda saukar idanun nata akan Dada dake ƙoƙarin ɗaura agogo. Sai dai kuma tamkar walƙiya hoton agogon ya gilma mata a brain, da sauri ta kuma ɗagowa ta kalla hannun nashi. (Wlhy agogon ne fa na ɗakin Mammah) Wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata.
Sai dai gaisuwar da Ruƙayya kema Dadan ta katse mata lissafi. Cikin satar kallon agogon ƙasa-ƙasa itama ta gaishe shi.
Kamar yanda ya amsa ma Ruƙayya a taƙaice itama a taƙaicen ya amsa mata. Daddy Imran dake kallonsu ya ce, “Halan yanzu ma kuka shigo gidan?”.
“Eh Daddy ko ɗaki ma bamu shiga ba.” Nimrah tai maganar cike da shagwaɓa tana ma magenta wasa. Ƴar dariya Daddy yayi da faɗin, “To aje ai wanka a huta, ALLAH dai ya bada ilimi mai albarka. Mishi ina gaisuwa”. Ya ƙare maganar da taɓa kan magen.
A tare suka amsa da amin. Suna nufar hanyar ɗakinsu. Ta ƙasan ido Dada ya bisu da kallo, can ƙasan zuciyarsa yana nazarin kallon da yaga Nimrah nama agogonsa a sace. Sai dai bai kawo komai a ransa ba tunda bai san ta gansa a ɗakin Mammah ɗin ba suka ƙarasa cikin falon. Dan zasu ɗan fita ne zaga gari kamar yanda Dadan ya buƙata. Duk da Imran yaso ƙi Dadan ya nuna masa sai fa sunje, tunda a mota ne wazai wani ganshi tunda yasan abinda suke gudun dai kenan. Shi kuma a yanda yake jin ransa ma bashi da dalilin wani hutu aiki kawai yake son fuskanta..........✍️
59
..........“Waye ya tura wannan saƙon?”.
“Baban yarinyar nan ne da Dagger ya kawo mana hotunanta kwanaki”.
“Shi ba a ƙarƙashin Dagger ya ke ba?”.
“Tabbas a ƙarƙashinsa yake, shiyyasa nima nayi mamakin saƙon. Dan haka na kawo maka ma ka gani, dan zancen sa ya ɗauki hankalina kuma ba abin wasa bane ba”.
“Kayi ƙyan kai, kuma tabbas muna buƙatar mu sanshi a zahiri. Kwanaki nama Dagger umarnin ya kawo min shi amma shiru, ban san mi yake nufi ba. Ga Scythe shima shiru bayan yasan shi muke jira da bayanai”.
“Oga na tabbatar zuwa anjima zamu iya ganin Mr Scythe, dan a daren jiya na samu tabbacin ganawarsa da Tafidan. Na wannan ne abin dubawa. Dan ya kamata musan wane saƙo yake son isar mana da baya son Dagger ya sani harya zagayo ta bayan fage”.
“Haka ne, ka masa reply da muna son ganinsa. Sai kayi ƙoƙarin yanda za'a yazo nan ɗin daga yanzu zuwa sati guda bayan ka gama karantar al'amarinsa da bincike sosai akansa.”.
“An gama oga. Ka daɗe kayi ƙarko”....
===================
★1-WEEK LATER★
Satin Dada ɗaya kenan da dawowa gida. Abubuwa sun faru sosai a cikin satin. Ta kowane ɓangare komai yayi tsauri da yin zafi. Sai dai har yanzu maƙiya sun kasa samun tabbacin dawowar Dada cikin zuri'ar sa. Ƙarshe ma sun ɓige ne da binciken asibitin da suke zargin yana jiyya ne.
Shi ko Malam Buba sai yawo yake ma Dagger da hankali, acewarsa ya rasa hanyar da zai bama Nimrah wannan takarda kullum tana tare da Ruƙayya. Tun Dagger na yarda har ransa ya fara ɓaci, zuwa yanzu ya fara tunanin bin sabuwar hanyar samun Nimrah ɗin batare da sanin Malam Buba ba. Shi ko Malam Buba bai taɓa tunanin Dagger zai nemi wata hanya ba, hankalinsa ma gaba ɗaya nakan jiran shubaninsu da suka bashi sati guda akan ganawa da shi fuska da fuska, dan haka a ƙagare yake da hakan, dan ya tabbatar da in har ya samu wannan damar Dagger bai isa cigaba da juya shi ba, shima ya zama ogan kansa sai dai a raba yaran da Dagger ke jagoranta biyu a bashi rabi.
★SCHOOL★
Kamar yanda suka saba idan anyi break zaka samesu group-group ne kowa na sha'aninsa. Wasu hira ce ta ƙawaye, wasu da samarinsu kasancewar makarantar haɗe take maza da mata. Wasu kam samarin ne zalla ke sabgarsu suma. Da yawan ƴammatan kan so haɗa ƙawance da su Nimrah, sai dai sanin halinsu kesa suji shakkar raɓarsu. Hakama samarin suna son suyi mu'amula da su, sai dai sanin kaɗan daga aikinsu su maka zagin ƙare dangi kesa su kama kansu.
A yanzu ma suna gefe su biyu zaune, note Nimrah ke ƙwafa a littafin Ruky dan ita ɗazun ƙinyi tai, duk da ba wani note ɗin kirki bane kasancewar kowane subjects ɗinsu suna da textbooks ɗinsa. Ruƙayya na gefenta tana cin cin-cin, hirar Hanoon suke suna dariya, dan wani rashin mutunci suka mata yau da safe kafin su taho school. Nimrah ta ɗiba cin-cin ɗin tana faɗin, “ALLAH yasa mu tarar Dada baya gidan, yanda in ta tambaya muci uwarta da armashi, shegen fuska tasha mayukan bleaching kamar an silala carrot”.
Sake tuntsurewa da dariya Ruky tai tana faɗin, “Sai da ke Trouble Queen. Hot pepper! Naj... Naj... Naja bombs”.
Ƙulli Nimrah tai mata a baya da faɗin, “Muguwa irin jera min wannan suna haka, so kike sai na mutu naji ana Naja bomb yau zaki sha bamai-bamai...”
Dariya sosai yanzu kam Ruky keyi, itama Nimrah na tayata....
“Hy beauty Barbies”.
Wani yaro mai sanye da irin uniform ɗinsu ya faɗa. Tsagaitawa sukai da dariya suna masa kallon daga sama har ƙas. Ya girmesu sosai, dan kuwa ɗan ss3 ne. Hasalima shine headboy ɗin ƴan ss. Yaron baya ji a makarantar, dan ya tara ƴammata yanata haɗasu faɗa. Kasancewar sa ɗan tsohon president yasa ko ƙararsa makaranta bata taɓa kaiwa ba gidan su, dan tun yana js yake tsula tsiyarsa. Ya jima da sanin su Nimrah sai dai bai taɓa shiga sabgarsu ba duk da suna birgesa, amma fahimtar da yay yaran basu da kunya ya sa ya kama kansa. Yau dai yana zaune cikin group ɗin dake haɗe maza da mata ana shafta amma hankalinsa duk yana kan su Nimrah, ji yay ya kasa haƙuri ya taso ya samesu. Shine maimakon sallama ya ce musu wai (Hy Beauty Barbies).
“Lafiya dai ko?”.
“Eh to da sauƙi gaskiya. Mutanen naka ne dai suka aikata abinda suka saba, ga kuma wanda suka buge ɗin nan kwance baya numfashi ma. Kuma yaron tsohon shugaban ƙasa ne”.
“Bugewa kuma? Sai kace wasu ƴan fashi...”
“Wlhy ranka ya daɗe abin babba ne fa. Kuma suma can gidansu har mun kira su. Kaga kafin suzo wani abu kuma ya faru gara ku ku fara zuwa. Dan yaran nan gasu nan ko'a jikinsu kamar ma basu aikata komai ba.”
Iska Daddy Imran ya ɗan furzar da faɗin, “Okay ba damuwa. Gani nan akan hanya”. Daga haka ya yanke kiran. Dada ya ɗan kalla da faɗin, “Inaga zamu wuce makarantar su Ninah akwai matsala, wlhy yaran nan nakan rasa mike damun kawunansu. Anya ba aljanu ne da su ba na faɗa. Da wahala ga Ruƙayya da Nimrah su cinye sati biyu ba'ace sunyi faɗa a makaranta ba, daga Islamiyya har boko. Idan anyi magana suce yaran ne basu da tarbiyya, shike nan su sun zama malaman koya tarbiyya kai jama'a”.
Ko uhumm Dada baice ba, ta aikinsa ma yake hankali kwance. Shima Daddy Imran bai sake magana ba har suka iso makarantar tasu. Sai da ya samu waje yay parking sannan Dada ya bi makarantar da kallo. Imran dake ƙoƙarin fita ya ce, “Ina zuwa”. Daga haka ya maida murfin ya rufe yana barin wajen..........✍️
60
..........★Ko sakan ashirin Daddy Imran baiyi da barin wajen ba motar ƴan sandan farin kaya ta iso. Ta ɓangaren da yake sukai parking. Dan haka kunensa ya jiye masa abinda ɗaya daga cikinsu dake waya yake faɗa. Da kallo ya ɗan bisu har suka bar wajen, kamar zai share ya cigaba da aikinsa sai kuma ya dakata, ƙofar da Imran ya shiga suma ƴan sandan suka shiga ya kalla, tare da ɗaukar waya dake gefensa. Ɗauke idonsa yay yana ƙoƙarin kiran layin Imran, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.
“Mike faruwa?”.
Banji mi Imran ɗin ya sanar masa daga can ba, naga dai kawai ya yanke kiran yana sauke laptop ɗin tsakkiyar kujerun, hakama takardun ya tattare su ya riƙe a hannu har sai da ya fita ya ajiye su a kujerar daya tashi. Motar ya kulle gaba ɗaya, ya saka norse mask daya cira a gaban motar, dan a sati gudan nan in har suka fito idan ba'a mota ba zaka ganshi da facemask ne.....
A dai-dai lokacin a office ɗin vice principal jami'an farin kayan nan ke magana cikin gadara. Acewarsu dole su tafi da su kansu hukumar makarantar kamar yanda aka tafi da su Nimrah. Dan har yanzu yaron mai suna Zahir bai farfaɗo ba, duk da an wuce da shi asibiti ne tare da su principal tun ɗazun, su kuma suka tafi da su Nimrah. Amma koda shi tsohon shugaban ƙasa ya isa asibitin da matarsa sukaga halin da ɗansu ke ciki sai ya bada umarnin komawa a kama suma hukumar makarantar bayan suma nan su principal an tattare su dukansu an wuce da su station ɗin.
Dada na tsaye jami'an suka fito da vice principal dake faɗin ai ga mahaifin yaran nan sai shima a haɗa da shi. Yana maganar ne yana nuna Daddy Imran cikin ɓacin rai. Sai dai su kuma basu saurareshi ba, dan umarni suke bi kawai, kuma shi akace su kamo ai na mahaifin yara ba, tunda yaran na hannunsu ai dole iyayensu sukai kansu da kansu. Sai da suka wuce Imran ya ƙaraso, ganin kallon da Dada ke masa ya ɗan furzar da iska yana faɗin, “Sun kaisu station, yaron kuma naji kamar suna batun asibiti ma wai bai farfaɗo ba. Ban san mi sukai masa haka da zafi ba. Ina ga mu bisu dan musan ina suka kai mana su”.
Komai Dada bai ce ba, suka bar wajen zuwa inda motarsu take. Haka suka dinga bin motar jami'an tsaron a baya har station ɗin su. Ta hakan ne suka fahimci wane irin jami'ai ne ma. Da farko hanasu shiga station ɗin akayi, sai da Daddy Imran ya nuna id card ɗinsa sannan.
A yanzun ma Daddy Imran ne kawai ya shiga, Dada yay zamansa a mota. Da farko hana shi ganin su Nimrah akayi, sai da ya nuna id ɗinsa anan ma sannan, a hakan ma wani a cikinsu ne yay kiran ogansu ya sanar masa, shine yay magana kan a bar Daddy Imran ya gansun, dan sauran idanunsu ya rufe umarnin da aka basu kawai suke iya kallo da girman wanda ya basun, duk da baya kan mulki a yanzu. Sai dai tunda ƙasar tamu in dai wane na amsa suna wane dole abu umarninsa shike nan.
Idanu ya zubama Ruky da Nimrah ganin su hankalinsu ma kwance. Dan suna ganinsa ma suka nufoshi fuska da murmushi suna faɗin, “Daddy kai ne?”.
“A'a aljanun ku ne”.
Ya basu amsa yana hararsu.
Bakuna suka rufe da hannaye alamar dariya ma suke son yi, sai ya girgiza kai kawai da cewa, “ALLAH dai ya shirya min ku”.
“Amin Daddy. Kuma wlhy a shirye ma muke. Kawai idan aljanun suka motsa ne al'amarin namu ba daɗi”.
Cikin ɓacin rai jam'in daya fito da su ke hararar su da faɗin, “Yaran nan kanku rawa yake na lura, aljanu ko? Zamu sauke muku su kuwa. Dan yanzu zaku koma cikin call ai marasa kunyar ƙarya”.
Daddy Imran ya fara nuna musu hakan bazai yiwu ba, sai dai a jira daga nan har wasu awanni aji daga asibitin dole. Amma sunƙi saurararsa sai wani gadara suke masa dan a farin kaya yake ba uniform ba. Har wani maimaita masa minti goma suka bashi a maida su suke. Sosai zuciyar Nimrah takai wuya, cike da tsiwa da takaici ta ce, “Daddy ka barsu, dan ALLAH ba cell ba su kaimu cikin kabari, daga ni har Ruky ba tsoron su muke ji ba. Shi daya aikata rashin ɗa'a ba'ace za'a kalleshi ba ma sai mu? Kuma wlhy shi da ire-irensa yanzu ma muka fara musu haka, tunda su bunsuraye ne.
Ai duk wanda uwarsa tace masa JEKA KA GANI idan har ya yarda ya fito ɗin MU ZAI GANI. Duk an saki yara ba tarbiyya kamar ɗiyan aladu a ƙasa. Tunda shi yace ɗan iska ne miyyasa bazai je ya rungumi uwarsa ko yayarsa ba. Sai mu tunda iyayenmu basu taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa ba, balle kuji tsoron su ko?.”
Caraf Ruky ta amshe da faɗin, “Barsu Ninah. Ɗan shegiya ni wlhy yanzu ma da zaku kaimu mu gansa sai mun danne masa kai da pillow ta yanda ko ya farfaɗo ɗin zai sake komawa mutuwar gaskiya......”
Sai kawai suka cafke ita da Nimrah suna dariya.
“Eh lallai yaran nan baku da mutunci da kunya. Anya kunsan gaban wanda kuke kuwa? Hukuma ce fa”.
Wani ya faɗa a cikin jami'an farin kayan yana latsa waya da kaita kunensa. Baki kuwa Nimrah ta taɓe irin na kai ka sani ɗin nan ƙasa-ƙasa tace, “Ko gaban gwalando muke miya shallemu, mu ubanmu soja ne ma baban ɗan sanda”.
“Mi kika ce?”.
Ɗan sandan ta tambaya dan baiji mita faɗa ba. Kanta ta ɗauke kamar bata jishi ba itama. Sai Ruky dake dariya ƙasa-ƙasa.
Daddy Imran daya rasa abin faɗa sai ya girgiza kai kawai shima. Ya ɗauki waya zai kira lawyer ɗinsa. Nimrah kuwa na hararar jami'in nan da suka fahimci kamar yafi kowa nuna gadara da tsanarsu kamar ɗansa sukama abinda suka yin.
“K! Ni kike harara?”.
Nimrah ta yamutse fuska zatai magana Dada ya shigo office ɗin a bazata.....
Ɓamm ta ɓame bakinta batare data bari kalmar dake ƙoƙarin fitar ta ƙarasa fita ba. Dan a cikin tsakiyar idanunta nasa idanun suka shiga, duk da fuskarsa akwai norse mask hakan bai hanasu gane shi ba. Shi ko ɗan sandan ya hasalo ne kamar zai mareta kiran daya shigo wayarsa ya katse shi. Sai ya ƙare da balla mata harara shima yana kai wayar kunnensa yana fita a wajen. Hakan yasa ɗakin komawa daga su sai su.
★Daga can wani office na station ɗin wani ɗan sanda ne dake tabbatar da oga ne a wajen, zaune yana kallon duk abinda ke faruwa ta computer dake desk ɗinsa. Sakamakon ɗakin da su Nimrah suke akwai cctv. Babu abinda yake saki sai murmushi, dan ba ƙaramar dariya yaran nan ke neman saka shi ba. Ganin ma suna neman hasala ɗan sandan da ke tare da su ɗin ne ya sashi kiranshi a waya. Dai-dai nan ya shigo office ɗin, sai da yay salute ɗinsa sannan ya ce, “Gani Sir!”.
Ogan daya kafe Dada da idanun ta desktop ɗinsa bai maji shigowar yaron nasa ba balle abinda yace, sai da ya sake maimaitawa sannan ya kawo ajiyar zuciya yana kallonsa.
Cike da mamaki yaron ya ce, “Sir! Akwai matsala ne?”.
Kai ya girgiza masa, tare da faɗin, “Waye ya shiga wajen yanzu?”.
“Ban sanshi ba Sir, amma da alama tare suke da shi. Dan yana shigowa naga sun nutsu alamar suna shakkar sa.”
Oga ya sake kallon Dada da ƙyau, sai kuma ya furta, “Koma inda suke, amma kasan maganar da zata fita a bakinka, baka gani yara ne”.
Cike da girmamawa ya amsa yana fita. Mamakin ogan nasu fal ransa. Badan yasan halinsa ba daya zargi wani abu, sai dai yasan ba hakan bane ba....
★Anan kuwa. Maƙalewa Ruky tai bayan Nimrah ganin yanda Dada ya zuba musu zafafan idanunsa da suka gagara fassara abinda ke cikinsu. Itama Nimrah kanta a ƙasa tana faman cuɗa yatsunta cikin juna. Murmurshi Imran yayi a ransa yana raya, (Marasa ji ashe ni kuka raina da su Ma'aruff). A zahiri kam sai ya mike abinsa yana faɗin, “Bari na shigo da lawyer”. Bai jira amsawarsa ba ya fice abinsa.
Kusan mintina biyu da fitar Imran sannan yaja kujera ya zauna. A take suka ƙara jin ya cike musu waje. Duk girman wajen kamar an sake matse su. Ruky ta fara gaishe shi da rawa baki, kafin itama Nimrahn