KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 42

21K to 24K   out of 125.4K words

Ruky da Biebah suka shiga baya, sai Afrah da Ayyan tare da su. Mu'azz ne ya dinga nuna masa hanya har suka iso. Islamiyyar su babba ce sosai, dan harda securitys. A inda ya dace yay parking duk suka fita. Karaf suka haɗa ido da Nimrah, yanda tsigar jikinta ta wani tashi sai da ta ambaci hasbunalahu wani'imal wakil a zuciyarta. Da sauri ta kama hannun Afrah suka bar wajen. Shima kansa ya kauda yana maida idanunsa kan Mu'azz.
      “Ɗana zan tafi ne ko zan jira ku anan har ku fito?”.
    “A'a Baba zaka koma gida, sai ƙarfe ɗaya kuma in sha ALLAHU sannan an tashi su Ayyan kazo ka ɗaukesu mu kuma ka taho mana da abinci, sai anyi la'asar kuma ka dawo ka ɗauke mu.”
          “To to ba damuwa ALLAH ya nuna mana”.
    “Amin ya rabbi, zadai ka gane hanya ko?”.
     “Sosai kuwa, karka damu zan gane. Ai na taɓa aiki tanan wajen sosai dan nayi taxi”.
     “Oh ALLAH sarki, shike nan sai an jima ɗin to baba”. Daga haka shima Mu'azz ɗin yabi bayan su Nimrah da tuni sun shige.....

    }}}{{{{}}}}{{{{

          “Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign”.
     “Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu”.
       “Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari.”
    “Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana.”
        “In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba”.
     Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, “Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi.
Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran”.
        “Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci.”
     “Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi.”
       Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, “Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi”.
     Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu...
        A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi.
        “Cin abinci a office sai kace tuzurai?”. Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, “Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?”.
     “Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay”.
        Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, “Gobe su Mammah zasu dawo ko?”.
     “In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu”.
        “Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi”.
Received at 2:05 PMReactions    Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, “Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa”.
      Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️

18


.........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata.
      Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin.
           “Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?”.
       Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, “Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya.”
          “Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?”.
    “Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne.”
        “Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta.”
     “Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna”.
      “Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?”.
     “A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba”.
        “Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan”.
     “Ba damuwa sai na jika”.
Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen.....

(Hummm wa kuke tunani wai?)

}}}}}}}}}{{{{{{{{{
    ★PRISON★
      
   Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa.
      Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen.
       “Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa”.
    Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa.
Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da.
        “Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana”.
      Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, “Mune akuyoyin kenan?”.
       “Amsa mai ƙyau”.
    Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi.
       “Sir! are you all right?”.
   Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana.
    “Okay”.
Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, “Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab...”
       Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, “Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?”.
     Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya ɗago idanunsa yana kallonsa cike da izza da nutsuwarsa da ALLAH ya mallaka masa a kowane hali. Sai kuma ya ɗan matso kaɗan ya dafe duka hannayensa dake sanye da handcuffs a saman table ɗin, idanunsa ya sake ajiyewa kai tsaye cikin nasa tamkar zai soke ruhinsa da su. Da golden voice ɗin nan tasa mai razanasu ya furta, “Jarumin gaske sulƙen yaƙi da linzamin dokinsa ne kawai GUZIRINSA. Duk lokacin da kaji abokin faɗa ya zagaye kansa da MAKAMI ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi na faɗa maka tsoro ne ya saka shi”.
       “Tsoro!?”.
   Baƙo ya faɗa cike da son aro jarumta da ƙarfafa kai na dole. Sai kuma ya murmusa yana ɗan buga yatsunsa akan tebur.
   “Kana da yawan cika baki a magana. Amma ka sani mu ba da suna muke aiki ba. Idan suna ya bayyana, haske zai shigo. Idan haske ya shigo, tsarin ya lalace. Mu mune mazaunan ƙasa a ɓoye. Mu ne masu murɗa jijiyoyin gwamnati. Mu ne masu rubuta dokar da gwamnati ke karantawa.” Ya sake matsawa kusa kusa sosai.
      “Yau shekaru takwas kenan muna kallonka daga nesa. Kana tunanin wannan gadarar taka ce ta baka wannan filin? Ko har yanzu gurɓataccen tunaninka na cigaba da baka wancan ƙarfin ikon da kake gadara da shi a baya har yanzu yana da tasiri? Ka manta cewa ƙasar nan tun kafin ka yi tunanin kare ta, mun riga da mun shafe shekaru muna sarrafa zuciyar manyan da kake kira shugabannin cikinta. Kalli kanka mana, har yau baka ɗauki darasi daga ikonmu bane?. Mu muka bar ka a nan. Mu muka hana a kashe ka. Mu muka hana a sake buɗe shafin ka. Ba wai saboda kana da muhimmanci a garemu bane. A’a…” Ya yi kakkarfan numfashi yana wani murmushi, ya cigaba da faɗin, “…saboda muna son ka zauna ka kalli yadda ƙasar da ka ɓata shekarun ƙuruciyarka a kareta ta koma filin WASAN ƘWALLON ƙafarmu. Da jinin abokanka, zuri'arka, ƴan ƙasar taka zata zame mana mai danshin da zamu ji daɗin gudu a kanta. Kaɗan da zamu rage a cikinsu ka kalli yadda suke bauta mana. Ka kalli yadda za mu rusa duk tsarin da ka kare rayuwar taka a karewa. Ka bar gudanar da tunanin cewa kai ka san makircin ƙasa.
Kai ɗan wasa ne a wani katafaren wasan da muka fara shekaru masu yawa da suka wuce tun kan haihuwarka, kaga hakan yayi kama dana masu TSORO?”.
      Ya ƙare dogon sharhin nashi yana gyara zama da jifan Dada da kallon raini yana wani dariyar iskanci da izgili. Sai dai maimakon yaga Dadan ya firgita ko nuna tsorata da matsanancin tashin hankali kamar yanda sukai tsammani sai yaga saɓanin hakan a bayyane. Domin kuwa da wata nutsuwa da baƙon bai taɓa gani ba, ya ɗaga kansa ya kalle shi da idanun da suka saba ganin bala’i ba tare da girgiza ba.........✍️

A gaya masa gaskiya ko a barshi da Dadan kai?. To bari dai mu gaya masa ko kaɗan ne 😂💃.

😝Kai kam baƙo duk wanda ya baka shawarar

8 / 42