Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
suna gab da shigewa Ruky ta riƙe hannun Nimrah ta tsayar da ita, batare da tayi magana ba takai hannu tana gyara mata hijjab ɗinta ganin bandage ɗin kanta ya fito. Hakan yasa suka rigasu shigewa. Dai-dai suma suna ƙoƙarin shigewa suna gulmar su Mu'azz ɗin ƙasa-ƙasa suka kusa cin karo da mutanen dake ƙoƙarin fitowa. Da sauri Ruky tai baya tana jan hannun Nimrah, sai dai cikin rashin sa'a ta tafi zata faɗi, a cikin waɗan can ɗin ɗaya yakai hannu zai riƙota.
Cike da tsiwa ta ce, “Malam miye haka, karka taɓani”.
Duk da da hausa tayi, bai ji mita faɗa ɗin ba saboda ba yarensa bane yanda sautin muryarta mai cike da tsiwa ta daki kunnensa sai ya tsaya cak, tare da ɗago manyan idanunsa ya kalleta. Sai akai sa'a kuwa dai-dai itama ta balla masa harara...........✍️
32
.........Ba ƙaramin motsawa zuciyar Adeel tayi ba, batare da ya shirya ba ya saki murmurshi mai faɗi yana ƙare mata kallo. Sake balla masa harara Nimrah tayi tana bin Ruky dake jan hannunta sukai ciki.
Yako lumshe idanu ya sake buɗewa a kansu. Zai iya rantsuwa tunda yake bai taɓa ganin baƙar fatar data gama tafiya da duniyarsa lokaci guda irin yarinyar nan ba. Gata dai ba wata ƙatuwar budurwa ba, hasalima a ƙasarsu bata wuce babyn raino ba, amma tayi masifar tafiya da dukkan zuciyarsa. Abin mamaki kuma ba irin son da yake jin yanama matan baya bane na sha'awa, wannan wani baƙon al'amari ne mai girman gaske a gareshi da ban mamaki...
“Oga ya dai?”.
Wanda suke tare ya faɗa yana taɓa shi. Juyowa yay ya kallesa, sai kuma ya ɗan sake murmusawa da faɗin, “Mi ta faɗa ɗazun?”.
Murmurshi wacan ɗin yayi, duk da bai san wanene Adeel ba a matsayi na rayuwa balle ma ƙasar da ya fito. Dan kuwa daga hotel ɗin daya sauka ne ya buƙaci ɗan rakiya zaga gari shine aka bashi ma'aikacinsu ɗaya da mota, har sun wuce wajen nan ya ɗauki hankalinsa yace su shigo dan ya ga harda kilishi ake saidawa. Cikin harshen turanci ya sanar masa abinda Nimrah ta faɗa. Kawai sai ya sanya dariya. A ransa yana raya (Wato ita tana jinta wata mace ce karna taɓa ta). A zahiri kam waje ya ƙarasa fita, sai dai ya tsaya a jikin motar su ne ya zubama hanyar shiga da fitar idanunsa....
Babu jimawa kuwa su Nimrah suka fito su Mu'azz biye da su. A gaban idanunsu duk suka shiga mota, sai da yaga Imam daya amsa tuƙin yanzu ya tada mota sannan shima ya shiga tasu yana faɗama abokin tafiyar tasa su bisu. Bai kuwa musa ba tunda aikin kuɗi yake. Haka ya dinga binsu a baya ta yanda bazasu gane ba har gida. Daga can ɗan nesa kaɗan suka dakata, har motar ta shige aka maida gate ɗin aka rufe.
Kai tsaye Adeel ya ce, “Ya sunan Street ɗin? Sannan kasan gidan waye?”.
Kai ma'aikacin hotel ɗin ya girgiza masa da faɗin, “Ban san gidan waye ba gaskiya. Amma sunan nan ɗin KOBI STREET.”
Sunan Kobi Street ɗin ya maimaita da karyayyen harshensa, kafin yace, “Okay zaka iya sake kawoni gobe?”.
“In sha ALLAHU Sir!”.
Fuskarsa da murmushi yace, “Muje inda zan samu layin ƙasar nan da waya”.
“Okay Sir”.
Daga haka suka bar wajen.
____
A cikin gida kuwa tunda su Nimrah suka fito a mota sabon driver malam Buba dake tsare da gate a yau ya zuba mata ido. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa, sai da ya iso inda suke yana tambayar lafiya kuwa yaga bandeji a goshin Nimrah ɗin. Imam ne ya bashi amsa a taƙaice da cewar “Ciwo taji a islamiyya”. Itako da tunda tai masa kallo ɗaya tsigar jikin nata ta fara tashi ta kauda kanta. A taƙaice ta gaisheshi kamar kowa sukai gaba ita da Ruky. Haka ya bisu da kallo yana jin kamar ya bisu ciki. Sai dai ya danne zuciyarsa da ƙar, amma can ƙasan rai ayyanawa yake (Lokaci yayi da zai fitoma Nimrah ɗin a mutum tasan shi ɗin waye).
A ciki ma hankalin Mammah da su Aunty Shariffa ba ƙaramin tashi yayi ba. Dan su Yaya Ja'afar sun tafi Airport ɗaukar Yaya Bilal dake gab da sauka, tuni sun cire mata hijjab suna duba wajen. Sai ita ke magana cikin shagwaɓa da son kwantar musu da hankali tana faɗin, “Babu fa zafi. Tunda aka min allura ya daina ciwo”.
Faɗa Aunty Biebah ta fara akan cewa bazasu yarda ba, gobe sai taje islamiyyar da kanta dole yaron nan a hukunta shi. Sai da Mammah tai maganar “Baza'a kai ga nan ba. Tunda ance kuskure ne to a barshi a hakan ALLAH ya kiyaye gaba.”
Badan sun so ba suka haƙuran. Amma Mu'azz dama ya ayyana a ransa sai yaci uban yaron tunda shima islamiyyar yay sauka, yanzu kuma weekend kawai suke zuwa Tahafiz shi da Aunty Biebahn. Ɗaki suka wuce yin salla. Mammah tace Biebah ta bisu tasa towel a ruwan zafi ta gasa mata goshin da fuskarta. Da to ta amsa tana bin bayan nasu...
<<<<<<<。◕‿◕。>>>>>>>
★RANTSUWA★
A yau sati uku da fadar da tabbatar da Janar matsayin shugaban ƙasa ta cika, a yau kuma ake shirye-shiryen rantsar da shi da shiga gidan gwamnati da aka kammala gyarawa tsaf. Tuni a cikin sati ukun nan ya kammala komai akan fiddo Dada, office kawai yake fatan shiga ya zartar da hukunci. Yanda kuma suke komai a sirrance daga shi sai Imran, da Haydar yasa zai mamayi mutane da yawa akan wannan kyakkyawan ƙudiri nasa.
Kamar yanda aka tsara an gabatar da rantsuwa tako wane fanni a ƙasar, sabbin shugabanni da wanda suka sake komawa tenure ta biyu duk sun shiga gidan gwamnati a wannan rana ta litinin tare da sabbin ofisoshin su. Sai dai mu cigaba da musu fatan alkairi da nasarar yin adalci ba satar kuɗaɗenmu ba😝🏃🏼♀️.
(Mai son soyayya da ɗan shugaban ƙasa tamun magana mu sasanta ta biya cin hanci na haɗasu🥱💃. In baki da ko sisi karma kizo😏🙄🤭🏃🏼♀️.)
★A yau daren farko na sabon shugaban ƙasa Janar Yusuf Shu'aibu Tafida cikin gidan gwamnati. Tsaye yake cikin ƙayataccen falon daya kasance na ƙarshe sai bedroom ɗin barcinsa, tunda ya shigo gida bisa rakkiya bai buƙaci ganin ko ɗaya daga iyalansa ba, sakamakon son fara zartar da babban birinsa. Komai kashe yake a falon in ka cire ac kawai shima ba'a wani sakashi da ƙarfi ba, an sauƙaƙa hasken fitilu gaba ɗaya dan falon na cikin ɗan duhu-duhu, zaune yake shi kaɗai kamar yanda yafi buƙata, tunaninsa gaba ɗaya ya tsaya ne akan mutum guda ɗaya, mutumin da yake ma kallo mafi muhimmanci na farko da zai shimfiɗa wannan mulkin mai cike da cakwakiya da ƙalubale kashi-kashi da shi, dan tun a yau ɗaya da fara shigarsa office ya fahimci hakan. Saboda haka bazaiyi ƙasa a gwiwa ba ko sakaci, yana buƙatar Haysam Abdul-rasheed Shehu a cikin wannan tafiyar tasa tamkar yanda ƴan ƙasa ke buƙatarsa koda basu san muhimmancin sa a garesu ba.
Ƴar ƙarar buguwar agogon dake bango falon ya katse tunaninsa, numfashi ya sauke a hankali, dan ƙarar ta bugane tamkar da bugawar umarnin zuciyarsa dake ambaton (lokaci ya cika, ka fitar da takardar zartarwa kawai, rikicin da kake kallo da ƙalubalen bai fi nauyin burin nan naka ɗaya ba, cikashi tun a wannan daren masalaha ce ta zuciya da kwanciyar hankali ka, fitar Zak-Shadow daga dunkulallen makircin da aka garkame shi cikin kurkuku tsawon shekaru takwas itace zai tabbatar ma masu shirin mamayeka kai ba kurar wasansu bane, aiki kazo yi ga ƙasa da al'ummar ƙasa ba aikin aljihunansu ba).
Cike da gamsuwar shawarar zuciyarsa ya sauke numfashi, cikin nutsuwa ya ɗauki wani file da takarda a cikinsa mai tambarin ofishin shugaban ƙasa (Presidential Seal). Wannan shi ne takardar ikon afuwa da zai miƙa wa Ministan Tsaro, wanda zai tafi kai tsaye zuwa hannun Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa. Duk da yasan aikin bamai sauƙi bane a garesu; dan akwai al’amuran cikin gida da ya sani zasu taso, munafukan dake da hannu akan lamarin Haysam, waɗanda ba a san ainihinsu ba har yanzu, amma yasan zasu bayyana ne da wuri akan wannan fitar ta Haysam, dan dole suna da tasiri a cikin gwamnati harda tasa kamar yanda Haysam ɗin ya faɗa. Shi kansa daya samu wannan mulkin cikin sauƙi duk da yasan komai hukuncine daga UBANGIJIN, amma sanin wacece wannan ƙasar tasu akwai tambayoyi a ransa: Su wanene ainihi? Kuma me yasa Zak-Shadow ya zama barazanar da suka ƙuduri aniyar kawar da ita? Miyasa kowa Haysam dai Haysam dai?.
(Fitar tasa ce zata baka hasken samun wannan amsar) Zuciyarsa ta ayyana masa. Murmurshi ya saki mai ƙayatarwa cike da gamsuwa ya ɗauki wayarsa dake gefe. Kai tsaye number Imran yay kira.....
★A yau gaba ɗaya Imran ya kasa barin office har zuwa wannan lokacin, zaman jiran kiran mutum ɗaya tak yake, kuma bazai ƙosa da wannan jiran ba daga nan har wayewar gari in sha ALLAHU. A dai-dai wannan lokacin da Shugaban kasa ke neman layinsa yana tsaye jikin windown ofishin sa yana kallon titin da ke cike da motocin jami’an tsaro. Rabonsa da cikakken barci tun dare shekaran jiya, gaba ɗaya barci ya gushe masa a cikin idanu tun bayan samun saƙon shugaban ƙasa ta text message bayan kammala rantsuwa.
Dan haka ya ƙare wannan yinin gaba ɗaya da ƙagautar jira, jiran kiran Janar da a yanzu ya shigo wayar tasa a bazata. Jikinsa har tsuma yake wajen kai hannu ya ɗaga.
“Assalamu alaikum Your Excellency…” ya faɗa cikin ladabi da kuma farin ciki da bai iya ɓoyewa ba.
Janar daya fahimci ƙagautar Imran a bayyane ya saki murmurshi, batare da jan rai ba ya furta “Imran, lokaci yayi. Takardar afuwa ta kammala.” Ya ɗan yi shiru, irin shiru mai nauyin tasiri, kafin ya cigaba da faɗin, “Ina so ka shirya tawaga mai tsabta. Ba na son hayaniya, ba na son labari ya fito. Ka tabbatar da babu wanda idonsa ke buɗe a kanku”.
Da wata irin sauke ajiyar zuciya mai masifar nauyi Imran ya lumshe ido cikin jin daɗin kalmar da ya dade yana jira kamar mafarki. Muryarsa na rawa ya furta, “Za’a yi sir. Da izinin ALLAH Zak-Shadow zai fito gobe ƙarfe tara na safe.”
“Good. Kai nake son ka jagoranta Imran. Na san kai kaɗai zaka iya tsallake duk wata inuwa daga ƙalubalensu. Zaku wuce inda na tanada dan duba lafiyarsa da saituwar al'amarinsa. Ka tsare shi da ranki. Har sai ya koma randa zai dawo ƙasa ya zama barazana, dan Zak-Shadow nake son a gani ba firsinan shekara takwas ba”.
Daddy Imran ya murmusa, murmushin jarumi wanda ya dace da mai ɗauke da nauyi mai girma na tsakanin soja da dangi. Sai da ya ƙame tare da salute sannan ya furta, “Na rantse da ALLAH za’a yi fiye da umarninka Sir. Ba zan bari koda iska tai barazanar kaɗa nauyin daya rage masa ba kafin ka gan shi duniya ta ganshi zuri'armu su ganshi.”
“I'm proud of you, Soldier”.
“Thank you, Sir. I'm proud of you too”...
Daga haka suka katse kiran, amma zuciyar Imran kamar zatayi tsallen kwaɗon sojoji dan farin ciki. Sai da yay sujidar shukur sannan ya miƙe bakinsa ya kasa rufuwa dan murmushi, ji yake kamar UBANGIJI ya sauke masa wani babban nauyi daya toshe bugun zuciyarsa a tsawon shekaru. Wayar ya ɗauka ya tura sako ga ɗaya daga manyan abokan amana da zai jagoranci motar sirri zuwa prison wato Haydar Galadima (Faro)........✍️
33
..........Fuskar former First Lady ɗauke da murmushin ƙasaita take kallon Hajiya Hasiba, sai kuma ta girgiza kai da faɗin, “Hummm.. Adeel! Adeel. Yanzu kina nufin tare da shi kuka zo ƙasar nan?”.
“Sosai kuwa ranki ya daɗe. Dan yanzu haka ma yana masauki. Kuma abinda na sanar miki ya ambata ne ya kawo shi, wato kashe Haysam. Sai dai bamu san ta wace hanya zaibi ya tabbatar ba”.
“Yana da daman bin kowace hanya, dan yana da ƙarfin ikon dukiya da sunan zuri'ar gidansu. Sai dai abinda ke ban mamaki wace manufa yake da ita akan Nabeeha har haka? Dan nasan Adeel matuƙar sani, nasan al'amarinsa akan mata. Tabbas idan yana a giyar kwaɗayin tarayya da mace komai yana iya aikatawa, da zarar ya cika burinsa kuma shike nan.”
“Amma yana iƙirarin auren Nabeeha zai yi ai. Shiyyasa ma ya iya juriyar shekaru kusan tara kenan a kanta.”
Murmurshi mai haɗe da ƴar dariya First Lady tayi. “Bazan ce miki ƙarya yake kai tsaye ba Hajiya Hasiba, sai dai zan iya miki yaƙinin ba haka bane ainahin abinda ke ransa. Duk wannan iskancin da kike ganin Adeel nayi yana matuƙar tsoro da bin dokokin ahalinsa. Ba Nabeeha ba, ko ƴar shugaban ƙasar wannan ƙasar tamu zuri'arsa bazasu bari ya aura ba. Maybe da a yankin turawa ne su barshi yay hakan, dan sunfi ɗaukarsu da kima da daraja fiye da al'ummar yankin Afirika da suke amsa sunan baƙaƙen fata. Mu a wajensu bayi ne kawai, bayin da zasu musu bauta a gidaje da masana'antu, sannan bayin da zasu gusar da kishirwarsu cike da wulaƙantarwa da izgili. Ƙalilan ne a cikinsu masu mana kallon mutane, bari na miki ƙaramin misali mana, Kinga dai ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma ko a saudia idan kinje ibada baki taɓa lura da yanda in kika haɗa sahun salla da mai jan kunne ke ƙoƙarin hana gangar jikinsa raɓar taki ba?”.
“Tabbas nasha ganin hakan ranki ya daɗe”.
“Good. Idan har basu so baƙin fata a sahun bautama UBANGIJIN daya tabbatar musu su da mu babu banbanci ba sai wanda yaji tsoronsa ta yaya zasu zo mu a haɗaka ta mu'amula mai girma irin wannan? Dan haka zan sake tabbatar miki ƙarya Adeel yake yana da manufa akan bibiyar Nabeeha, akwai burin da yake son cimmawa kuma bana jin na sha'awa ne”.
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kai biri yayi kama da mutum gaskiya. Bazan ɓoye miki ba kullum cikin yima kaina irin tambayar nan nake. Sai dai ganin yanda take masa rashin kunya da nuna halin ko'in kula balle nuna jin haushi kan shafe min tantama ta. Yanzu ranki ya daɗe minene mafita? Kin san mutumin nan nada ƙarfi, kota wace hanya zaibi dan cimma manufarsa a kammu”.
“Tabbas zai bi, dan shafe babin rayuwar ɗan adam ƙaramin aiki ne daga tarin ƙananun ayyukansa. Sannan kunyi gangancin sanar masa mijin Nabeeha na rufe ne, duk da nasan idan yaso sanin hakan zai yi koda bata hanyar ku ba. Yanzu kije gida ki bani lokaci zanyi tunani, abinda na yanke zan kiraki mu haɗu ko nazo gidan na sameki, shima kuma zan je har masaukin nashi duk da banda isasshen lokaci, saboda gobe zamuje gidan gwamnati domin ganawa da sabuwar First Lady. Kin san ɗan takarar CSP candidate ɗin Excellancy ne. Dama nayi niyyar nemoki a satin nan kizo ƙasar saboda rantsuwa da akai, sai kuma gaki ALLAH ya kawo ki ma duk da an riga an gama dai”.
“Ranki ya daɗe duk abinda kuke so zamuyi, ni dai a taimaka na fara maganin wannan matsalar dan samun nutsuwa”.
“Karki damu Hasiba. Idan ta kama Excellancy ya shiga wannan maganar zai shiga. Zan saka ya nema Adeel da kansa koya gayyato shi nan gidan idan ALLAH ya ɗaura mu akansa dan abune mai wahala yazo ɗin. Amma zamu gwada sa'ar mu”.
“Nagode sosai ranki ya daɗe. ALLAH ya bar zuminci. Ya tabbatar da nasarar ku daga nan har ƙarshen rayuwa”.
“To amin Hasiba”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
★★..10/9/2021..★★
🔥8:55 AM🔥
Duk da kasancewar hantsi ya ɗaga kurkukun ya yi shiru yau fiye da kowanne rana. Tun 8 aka kammala basu abincin safe kamar yanda komai yake a tsari aka saka kowa komawa ciki saboda baƙin sirri da zasu shigo. Sai irin su Dada da ba'a bari su fito sai da ƙwaƙwƙwaran dalili dan haka kai musu akeyi su har ɗakunansu.
Received at 12:27 A bakin ƙofar gate 8:55am motocin sojoji ne masu duhun glass guda biyu suka tsaya kamar taurari a cikin duhun dare. A motar farko kawai aka sauke gilashi ƙasa tare da miƙama securitys ɗin ƙofar takarda. Suna duba abinda ke ciki suka ƙame jikinsu tare da salute ɗin motocin. Kafin da hanzari a wangale musu ƙofar suka shige a jere. Basu tsaya ko'ina ba sai a ƙofar sashen da Dada yake. Inda shugaban prison ɗin da kansa ke tsaye tare da jami'an soji na gidan guda uku alamar jiransu suke dama.
Sai da sojojin ɗayar motar suka gama fitowa da hanzari suka zagaye wajen kafin a buɗe ta ƙarshen. Col. Imran Abbas ne a ciki, cikin farin kaya na musamman bana soja ba, sai Brig. Haydar Usman Galadima (Faro). Cikin nutsuwar girma irin na masu kamewa suka fito a hankali, a take sojojin da suke tare da su harda na cikin prison dake tare da shugaban su suka ƙame tare da sara musu.
Suna ajiye hannu shugaban prison ya ƙaraso shima gabansu, ƙame jiki yay shima tare da salute nasu irin na girmamawa, suma sai suka ƙame ɗin sukai salute ɗinsa na girmamawa. Hakan na nufin kowa ya girmama girman kowanne, dan su duka ukun kowanne nada matsayin girmama ɗan uwansa a dokance. A karo na biyu sukai musabaha, kowanne fuska da murmushin mutunta juna. Kafin Colonel Imran Abbas ya miƙa takardar Presidential Pardon ga shugaban prison.
Sai da ya ƙame a karo na biyu yay salute ɗin Imran sannan ya amsa takardar. Shima sai Imran ɗin ya sake salute nashi a karo na biyu idanuwansa sun yi kaifi tamkar yana hango duk wani inuwa da zata takura masa a cikin idanun