Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
takai kan Imran. “ALLAH yay muku albarka”. Ta faɗa hawaye na sake zubo mata.
A tare suka amsa da amin. Imran da a wannan gaɓar zuciyarsa ta matuƙar raunana da tausayin wannan ahali ya haɗiye abinda ya toshe masa maƙoshi da ƙyar, dan baima san kuka yake ba shima sai da yaji saukar ɗumin hawaye akan tashi fuskar. Da ƙyar ya iya dauriyar dai-daita kansa ya fara lallashinsu.
Sai lokacin Nimrah ta farga da jikin wanda take. Mutumin da ko gama tantance wanene shi batai ba. Sai suna biyu da taji Mammah da Mamy sun ambace sa da shi kacal a yanzu. (Dada! da Muhammad). Yanda take mutsu-mutsu yasa shi shima farga da abinda ke faruwa. ALLAH ya soshi dai-dai Mammah na ƙoƙarin tashi ne, Daddy Imran ya kamata ya zaunar da ƙyau. Har neman faɗuwa Nimrah take wajen barin jikinsa, sai da Aunty Ummi ta riƙeta. Shima Dada sai ya basar kawai tare da maida hankalinsa kansu Mimi, hannu ya miƙa musu, da sauri kuwa suma suka nufoshi suka rungume sa suna kuka. Hannunsa ya ɗaura a bayan Biebah da Mu'azz yana ɗan bugawa alamar lallashi, sannan ya shafa kan Ruƙayya itama. Kafin a hankali ya furta, “It's okay”.
A tare suka shiga jinjina kawuna suna ɗagowa da share hawayensu. Yayinda su Bilal suka kasa daina kallonsa, dan bayyanar fuskar tasa a garesu ta ƙara zama wani abu mai girma da kimantawa. Dadan ne dai da suka sani, sai dai sajen dake kan fuskarsa da basu taɓa gani a baya ba ya canja shi kaɗan. Shima ganin yanda suka zuba masa idanun gaba ɗaya ga falon yayi shiru tamkar an musu tsawa sai ya motsa tausasan laɓɓansa kaɗan ya furta,
“Kallon fa?”.
Cikin yanayin ɗage gira kaɗan akan su Ma'aruff. Tamkar waɗanda ya farkar a barci duk sai su Ja'afar suka fara sakin murmushi, kafin su Ammar su sake rungumesa kamar wanda suka ji kunya. Ya ɗan murmusa kaɗan shima a karo na farko, yana shafa bayansu. Cikin golden voice ɗin nan tasa data iya shanye abubuwa da yawa ya sake furta, “Shi dai wannan kukan bazai ƙare ba halan. Imran kama ƙannenka magana su daina min kuka”.
Murmurshi Imran yayi yana kallonsu, yayinda su Bilal da suka ɗago a jikinsa ke goge hawayen suna murmushi. Cike da lallashi Daddy Imran ya ce, “Gaskiya Haysam ya faɗa, yanzu ba lokacin kuka bane lokacin farin ciki ne. UBANGIJI ya nuna mana wannan ranar batare da mun biyasa ko sisi ba, hasalima ba muyi zato ko tsammani ba. Dan haka a maimakon kuka sai muyita jera masa godiya da kirari zaifi mana alkairi da ƙarin farin ciki a zukata”.
Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai suna ƙara share hawayensu. Dai-dai nan cikin kasa haƙuri Ruky ta rage murya da faɗin, “Mammah dan ALLAH waye?..”
Mammah da idanunta ke jajur na kukan da tasha ta ɗaga tana kallon Dada dake zaune a kujerar kusa da ita hannunsa riƙe da nata, murmushi tayi mai cike da abubuwa da yawa, kafin ta janye ta maida kansu dan Nimrah da Rukyn na zaune ne ɗayan gefenta, sai dai daga ƙasan carpet ganin haka su Biebah sukayi, duk sun ƙagu ta basu amsa... Zatai magana caraf Uncle Bilal ya ce, “Mammah karki faɗa dan ALLAH, sai sun bada goron albishir sannan”.
Murmurshi Mammah ta sake saki mai faɗi tana share hawayen da suka sake silalo mata. Yayinda shima Bilal ɗin hawaye yake sharewa tamkar su Biebah da nasu suka gagara tsayawa. Sanyi jikin su Nimrah ya sake yi, tamkar zasu saki kuka suma suka sake maida kallonsu ga Daddy Imran.
Hannu ya ɗaga musu alamar shima babu ruwansa, dan haka akai ƴar dariya mai zuwa batare da an shirya mata ba. Dan shi kansa Dadan sai da ya ɗan yi gajeren murmushi yana kallonsu su duka biyun ƙasa-ƙasa. Sai kuma karo na farko ya miƙa musu hannu alamar su zo garesa...
Ruƙayya dai babu musu ta rarrafa inda yake, Nimrah kam ɗan shiru tayi kamar mai tunani, sai da Mammah ta kamo hannunta tare da mata nunin taje da ido sannan. Itama matsawar tai, amma sai ta zauna kusa da Ruky idannunta a ƙasa dan gaba ɗaya jinta take kamar a cikin matsa-tsi, ba kamar sanda suka shigo ba da take sakayau. Ba ta san dalilin rawar jikinta ba. Ba ta san dalilin bugun zuciyarta ba. Ta san sunan Dada kawai, sunan da take ji a bakin kowa na gidan, suna mai nauyi da daraja a cikin gidansu, sunan da ake furtawa da girmamawa da bege. A karo na farko hoton bidiyon nan ya ratsa cikin tunaninta. Sunansa na ainahi yay mata amsa kuwwa acan ƙasan ƙirji matsayin wanda akace ya kashe mata Ummanta, (Aka ce ko kika gani da idon ki) wani sashe na zuciyarta ya tuna mata, samun kanta tai da matse yatsun hannunta cikin juna, ta sake sunkuyar da kai, dan ji take tunaninta na neman hargitsewa da rabuwa kashi-kashi a kwakwalwar ta.
A lokacin suma su Shariffa suka ƙaraso. Cike da matuƙar girmamawa suka shiga gaisheshi. Idanunsa dake karantar yanayin Nimrah da babu wanda zai iya fahimta ya ɗauke. Kallo ɗaya yay musu suma ya janye idanunsa, su ɗin ƙanne suke a garesa koba auren ƴan uwansa a kansu, sai kuma ga alaƙar auren ya ƙarama matsayin ƙarfi. Cikin kamewarsa da cikar kamala ta uba kuma babban wa ya shiga amsa musu, tare da musu fatan alkairi a cikin aurensu. Sosai suka sake shiga cikin yanayin kunya, girmansa ya sake mamaye musu waje ko kallonsa sun gagara yi, dan koba shekaru shi ne uba ga mazajensu, sannan shi ne garkuwa, shi ne ginshiƙi. Babu wacce ta iya amsawa a cikinsu sai ma sake sunkiyar da kawuna da sukayi. Sai su Mammah ne suka amsa addu'ar tasa da amin.
Sai da suka miƙe suka koma wajen zamansu sannan Ruky da Nimrah suka fara gaishe shi. Suma ya amsa musu da tambayarsu karatu. Suka amsa da Alhamdullah har yanzu kan Nimrah a ƙasa tana cuɗa yatsunta cikin juna. Yatsun nata ya ɗan sake zubama idanu a fakaice tare da janyewa duk a lokaci ɗaya dan cikin sakanni harya gama karantar akwai abinda ke damunta bayan kasancewarsa baƙon ido a cikin waɗanda ta sani, sai dai babu wanda zai ce kallon nata yake, sai ma maida hankalinsa da yay kan Mammah can ƙasan ransa kam mamakin girmansu yake ita da Ruky da Mu'azz fiye da kowa. Ƙasa-ƙasa yay maganar da babu wanda zaice ya ji abinda ya faɗa mata. Sai murmushin ta kawai da kowa ya gani a bayyane....
Shigowar Daddy Imran daya fita ta katse Mammah daga maganar datai niyyar yi, ya dubi su Ma'aruff yana faɗin Su tashi suje gida kafin mutane su farga da abinda ke faruwa. Dan tabbas ana gama sanin Zak-Shadow ne a airport ɗin ba ƴan media da jama'ar gari ba hatta munafukai bazasu barshi ba, dan dama ce mai sauƙi a garesu duk da zagaye suke da jami'an tsaro da suka fara fargar da mutane akwai wani babba dake airport ɗin, saboda a fitar nan tashi ya fahimci hakan ta hanyar ƙananun maganar da ya fara jin na tashi, da ƙyar su Ma'aruff suka miƙe, dan sun san gaskiya Yaya Imran ɗin ya faɗa. Dada ne ƙarshen miƙewa riƙe da Mammah da har yanzu hawaye sun gagara barinta. Ya kuma maida facemask ɗinsa.
A yanda suka fito cikin tsari da nutsuwa duk da kuwa ta hanyar sirri ce yaja hankalin tsirarun mutane dake ta wajen kansu. Dan tamkar ƙyaftawar ido sojojin da suka zo da su da jami'an tsaron da suka tarar na farin kaya a airport ɗin suka zagaye su, suma an ajiye su ne a sirrance batare da sanin su Imran ɗin ba. Wannan kuma duk aikin shugaban ƙasa ne. Mutane da son ɗauke-ɗauke a waya kam har sun fara batare da sun farga da sanin su wanene ba. Sai dai yanda jami'an tsaro sukama mutanen zobe yasa kowa fahimtar koma su waye su lallai masu muhimmanci ne a ƙasar.
A haka suka shiga motoci babu ɓata lokaci aka bar wajen. Sai dai mi, kafin ma su isa gida guntayen videos ɗin da wasu suka ɗauka da ƙananun magana da ake a airport ɗin har ya fara yawo a media, sai dai anata canki-in-canka ne na rashin sanin wanene. Mike faruwa?. Yayinda ƴan bin ƙwaf nacan sun fara bibiyar al'amarin dan sunyi ma kansu alƙawarin kafin dare sai sun gano su wanene ɗin.........✍️
53
.........3:21pm
Jerarrun motocin masu baƙin gilashi suka fice daga filin jirgin cikin tsari mai ɗaukar hankali. Babu jiniya ko wani babban motsi da zai saka ace wani babban ƙusar ƙasa ne, amma tsaron dake zagaye da motocin ya isa ya sanar da kowa ba tafiya bace irin ta yau da kullum, sannan koma su waye sunada wani girma da muhimmanci.
A motar tsakiya da Daddy Imran ya ƙarɓi tuƙin Dada ne a gefensa. A baya Mammah da ƴan gatanta Ruky da Nimrah sun sakata a tsakkiya. A binda zai baka mamaki kamar basu ba bakin surutun nan ya mutu murus. Dan har Daddy Imran ya kasa haƙuri sai da yay magana..
“Mammah wai yau bakunan kafi autanki sun mutu ne? Na jisu tsitt kamar basa a motar nan”.
Murmurshi Mammah tayi da ɗan kallon Nimrah da Ruƙayyan da suka lafe a jikinta. Dan gara ma Ruky wayar Mu'azz ce a hannunta tana kallon hotunan da sukai a airport ɗin. Nimrah kam idanunta a rufe suke da alama tayi zurfi a tunani. Ba kuma tunanin kowa bane face na wannan baƙo nasu da Uncle Ammar ya faɗa musu shine Dadan da suke ji ana faɗa tun tasowarsu. Duk da fuskarsa ta canja daga waccan fuskar data gani a video. Waccan fuskar da babu gashin saje sam, sai dai kuma sajen ne kawai ya bambanta ta da wannan fuskar ta yanzu da itama babu yawan murmushi, babu sakewa, babu filin kai wargi. Sai tsabar kwarjini, kamala, hasken ibada, kamewa da tarin cikar haiba irin ta masu tantsar riƙe girma. Tabbas a wannan gaɓar ta shiga ruɗani mai tsanani akan wannan fuskar da zuciyarta ta kasa yankema hukuncin daya dace. Jitai hotunan bidiyon na son dawowa. Sautin muryoyin da ke zargi na so sake yi mata amsa kuwwa.....
Tunaninta ne ya katse saboda girgizatan da Mammah tayi. “Nimrah mi kike tunani haka?”.
Mammah ta faɗa tana kafeta da idanu. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tana girgizama Mammah kai da faɗin, “Mammah ba komai”.
“Karya take yi wlhy Mammah, gaba ɗaya yanzu haka ta koma, haka kawai sai kiga ta shiga tunani bare ma idan muna ɗaki mu kaɗai, a gaban ku ne batayi”. Ruky ce mai maganar tana hararar Nimrah. Itama ramawa tayi, sai dai batace komai ba. Sai Daddy Imran ne ya ce, “Nima dai naso lura da haka, duk tayi sanyi babu kuzari. Daughter mike faruwa? Ko baki da lafiya ne?”.
Idanun Nimrah suka ɗan ciki da hawaye, muryarta na ɗan shigewa ciki ta ce, “ALLAH ba komai Daddy sharri take mun. Kuma lafiyata ƙalau” sai ga hawaye sharr. Mammah da taji hankalinta ya tashi ta kamota jikinta, dan ita kanta a tsakanin nan tana lura da Nimrah ta ɗan rage kauɗi, sai take tunanin ko exam ɗin da suka fara ce a makaranta. Itama dai Ruky idonta har ya tara ƙwalla. Ta riƙo hannun Nimrah cikin nata tana faɗin, “Dan nace haka kike kuka, to kiyi haƙuri bazan ƙara ba”.
Cikin ɗan tura baki Nimrah dake kwance jikin Mammah ta ce, “Nifa ba dan kinyi magana bane ba, kawai kaina ke ciwo”.
Sannu Mammah da Ruky suka shiga jera mata. Daddy Imran kam ya saki murmushi da faɗin, “Mammah kina fama.”
Duk abinda suke Dada na jinsu. Amma ko motsawa daga yanda yake zaune bayansa kwance jikin kujera ya lumshe idanunsa baiyi ba. Zama ka rantse barci yake a hakan...
Dai-dai nan jerarrun motocin dake tafe da tawagar jami'an tsaro suka iso cikin anguwar. Tsakiyar KOBI STREET. Dai-dai gate ɗin gidan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi da yasa mutane fara farga da abinda ke faruwa. Dan kuwa duk da akwai jami'an tsaro a tare da su hakan bai hana wasu biyosu ba tun daga airport dan samun labari duk da su ɗin ba ƴan jarida bane, amma ganin Imran da yaso fargar da masu wayo yasa suka tsargu shiyyasa suka biyo su dan tabbatarwa, da alama kuma zasu samu abinda suke so ɗin musamman ganin inda motocin suke ƙoƙarin shiga.
Maigadi kansa ya girgiza da abinda ya gani, balle su Malam Buba dan su Mammah basu fita da driver ko ɗaya ba daga gida duk su Ammar ne suka ja motocin sanda zasu fita. Yanzu kam wasu motocin ma sai sojojin nan ne suka dawo da su dan har suka iso gida hawaye wasun su sun kasa tsayawa. Sai da gaba ɗaya motocin suka gama shigowa kafin kowa ya fara ƙoƙarin fita.
Su maigadi dai sunyi tsuru-tsuru suna kallon ikon ALLAH. Kusan motar su Mammah ce ƙarshen buɗewa, Nimrah da Ruky suka fara fita, kafin itama Mammah ta fito hankalinta duk akan Nimrah datai mata wani kalar tausayi. Riƙota tai tana kai hannu a goshinta,
“Ciwon kan ne?”.
Nimrah ta ɗan girgiza kai tana Kama hannun Ruky da itama ta zagayo inda suke cike da damuwar yanayin twiny ɗinta. Dai-dai nan aka buɗe ƙofor ɓangaren da Dada yake, a nutse ya fara sauke ƙafafunsa dake sanye cikin baƙin takalmi Boot mai ɗan tsaho. Kafin bayyanar baƙin wandonsa zuwa shafaffen cikinsa dake kwance cikin bakar t-shirt ɗin jikinsa kasancewar yayi zanzaro ne. Daga maigadi har Driver suka ɗan zuba masa ido daga can inda suke tsaye tamkar an basu aikin yin hakan ne. Har sai da ya kammala tsayawa cak akan ƙafafunsa sannan suka ɗaga idanun nasu a hankali zuwa kan fuskarsa dake sakaye cikin norse mask da p-cap.
Shi kam da bai san sunayi ba, sai ma a bazata juyayyun idanunsa suka sauka akan Nimrah da Mammah kema magana ƙasa-ƙasa tana tattaɓa mata kai, anyi sa'a itama ta ɗago nata zata harari Mu'azz daya ƙaraso wajen yana tsokanarta wai tana ma Mammah shagwaɓa, ai ko sai idanun Dada cikin natan. cikin sauri ta janye dan har tsakkiyar ƙwalwa taji kaifinsu da tasirinsu ya riski tsakiyar zuciyarta.
Shi kam baima nuna yasan mi akai ba ya maida idanun nasa ga kallon gidan cike da mazewa.......
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
★Gaba ɗaya tambayoyin zuciya sun gagara ƙarewa a zukatan su Maigadi dama jami'an sojan da aka bari gidan, dan suma dai har yanzu basu san wanene ba balle abinda ke faruwa. Sai dai duk sun sha jinin jikinsu. Amma a ɓangaren mutane biyu da suka san Dada tun a baya sun shaida tabbas shi ne ba saƙo ba ba kuma mafarki ba duk da yaƙi buɗe fuska. Dan haka suka kasance a firgice fiye da sauran. Saboda ɗimuwa ce ta gaske ta samesu da ruɗani na bazata. Tambayar kawunansu kawai suke ta yaya hakan zata kasance? Dan tabbas wanda akace an fitar a prison kwanaki biyar kacal da suka shuɗe ba zaiyi kama da hakan ba sam a idanun mai kallo. Yafi kama da jarumin dake rayuwa a ni'imtaccen muhalli da kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwa. Da alama ana raina musu hankali ne ko wani abu daban gaskiya......
<<%>><<%>><<%>>
Gab da magriba Daddy Imran ya bar gidan. Su Aunty Ummi kam har akai isha'i suna nan abinsu suna hidima da Dada. Dan abubuwan da aka shirya masa harma ya rasa mizai ci a ciki.
Abin zai baka mamaki yanda gidan ya nutsu babu hayaniya duk da yaran dake cike da shi. Amma kowa ya nutsu waje guda alamar wargi ma waje yake samu. Duk da kuwa baƙon idon daya saka su nutsuwar ko harara baima kowa ba. Hasalima cike da so da ƙauna ya dinga rungumesu lokacin da ake gabatar masa da kowa da sunayensu. Dan Mammah bata rage kowa ba hatta ƴaƴan Uncle Tasi'u ya masa bayanin su a taƙaice, sai dai komai baice akan su ba. Ga shi macen ta mugu-mugun jin mutuwa akansa. Dan a cewarta bata taɓa ganin namijin daya daki zuciyarta a kallon farko irin Dadan ba, wanda ita kanta ta tabbatar ko cikakken kallo ɗaya bai mata ba. Lokacin da akai masa rakiya ɗakinsa da aka zubama kaya jiya jitai tamkar tayi tsuntsuwa ta bishi, sai dai babu dama...
Duk wannan bidirin da ake babu Nimrah a falon, dan tunda suka shigo tai wucewarta ɗakinsu. Kayan jikinta da gaba ɗaya ƙamshin turaren Dada ya gauraye ta cire, jin ƙamshin yaƙi barin har jikinta dole tai wanka kafin al'awalar la'adar. Koda ta fito tai sallar sai ta haye gado ta kwanta dan wani ma ɗan zazzaɓi take ji. Lokacin da za'aci abinci bayan dawowar mazan sallar la'asar Mammah taga babu ita ta fara jajenta. Dan haka ta aika a duba mata ita. Nusaiba da tazo kiranta ta sameta kwance, sai tai tunanin barci take, dan haka ta koma tace tana barci. Mammah datai tunanin ko ciwon kan ne tace a barta tayi barcin...
Nimrah da sarai tana jin sanda Nusaiba ta shigo tun tana juye-jiye da tunane-tunane har barcin gaskiya ya ɗauketa, daga nan kuma zazzaɓin na gaske ya rufeta. Gab da magriba Mammah ta shigo ɗakin da kanta, anan taji jikin nata da zafi. Babu ɓata lokaci ta saka Biebah ta haɗo mata abinci da magani, tashinta Mammah tayi,