KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 42

51K to 54K   out of 125.4K words

fita iyakar motsin ƙirazansu. Baradan jaruman haziƙan sojojin uku Imran, Faro, Zak-Shadow. Ba wanda ya ce komai. Kowa da abin da yake tattaunawa da zuciyarsa.
      Sai rufaffen gilashin motar da ke nuna hasken rana daya fara zafi, launin duhun sa ya bayyana fuskokinsu dake da sanyin annuri.
      Daddy Imran yana kallon Dada akai-akai tamkar idan ya ɗauke idanun nasa zai ɓace masa ne, ko yana son tabbatarwa wannan ba mafarki ba ne. Faro dai sai murmushi yake yi irin wanda yake nuni da cewa (Na gaya maku wataran ƙaddara da ƙarfin ikon wanda ya fiku iko zai dawo da shi a duniyar ku).
      Amma shi Dada ya rufe idanunsa cikin nutsuwa, yana fitar da numfashi a hankali da shaƙar mai tsabta fiye da duk wanda ya shaƙa a cikin shekaru takwas. Yawan jin idanu a kansa dan in har ana kallonsa sai yaji a jikinsa, balle wannan kallon yana jin ƙarfin idanun mai su a cikin ƙirjinsa. Ya kuma tabbatar da Imran ne ke da wannan tasirin. A hankali ya buɗe idanuwan nasa, sai ko suka sauka kai tsaye akan Imran ɗin da yay hasashe. Hararasa ya ɗanyi, tare da ɗage masa gira ɗaya, da murya ƙasa-ƙasa amma cikin zurfi ya furta,
“Kallon fa?”.
Ƙaramar dariya Imran yayi da faɗin, “Ina tsoron karka sake ɓace min ne”.
Kauda fuska Dada yay kaɗan da sakin ƙaramin murmushi, batare daya tanka batun Imran ɗin ba ya sake jeho masa sabuwar tambaya.
“Motar nan ina take son kai mu?”
Daddy Imran ya ɗan taɓe baki da matsawa kaɗan ya jingina da kujera. Shima cikin salon raɗa ya ce, “Wurin da ba wanda zai same ka. Wurin da babu ƙungiya, babu siyasa, babu duhu. Wurin da zaka samu iska ta ƴanci bayan shekara takwas daka rasa”.
       Dada ya girgiza kai a hankali tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda. “Na gode muku Imran, Faro, na gode sosai.”
     Kafin Imran yace wani abu Faro ya katse su cikin siririyar dariya mai armashi da jin daɗi. “Zaki wlhy idan ka sake irin wannan sakon godiyar, zan fara tunanin da gaske zaka canja halinka.”
    Dada ya kalle shi yana murmushin ƙasaita sai kuma ya maida kansa ya kwantar a jikin kujera ya lumshe idanunsa har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Sai a lokacin ya furta, “Ga shi kai baka da ranar canzawar da wannan sa idon naka”.
       Dariya Imran da Faro suka sanya, cikin irin dariyar da ta bayyana ƙyallin ruwan hawaye daga idanun Imran da ya kasa ɓoyewa....
       Dada dake murmushi zuciyarsa ta tafi sabon tunani. (Shugaban ƙasa da kansa ya yanke wannan hukuncin da gaggawa? Mi yasa? Mi ya faru da ƙasata cikin wannan lokacin? Mi ake shirin bani? Mi ake buƙata daga gare ni?). Kafin ya samo amsoshin waɗan nan tambayoyi masu nauyi Imran ya katse shi da faɗin,
“Muna da tsaro mai ƙarfi, babu wanda zai kusance ka har sai ka shirya. Koda likitoci sun gama duba ka zaka cigaba da zama a ɓoye. Babu wani abu da zai kusanto ka. Sai mun kammala gyara rashin adalcin da aka yi mana, dan ƙasa tana buƙatar komawar ka a Zak-Shadow ɗin data sani ne. Mammah zatafi farin ciki idan ta ganka a Haysam ɗinta itama. Balle kuma ƴaƴan Dada”.
     Dada ya ɗan furzar da numfashi da buɗe idanunsa dake a rufe, zuciyarsa cike da wani nauyin da bai gama wargajewa ba. Tabbas a yanzu ba wanda ya fi buƙatar son fara gani kamar Mammah da ƙannensa, amma zai daure ya jure dan yasan duk yawan kwanakin da suke so yayi anan bazasu kai yawan wanda yayi a baya ba. Shima zai fi son Mammah ta gansa cikin ƙyaƙyƙyawan kamanni ba wannan kamannin da yake a yanzu ba da zasu iya raunana zuciyarta har ta gagara mantawa da su. Numfashi ya sauke a hankali, a yanayinsa na Zak-Shadow da suka sani ya furta, “Imran kun tabbatar babu wanda ya san dawowa ta?”.
     “Ai ko motar nan ta bari wasu suka ji Zak-Shadow ya dawo, ta riga ta mutu.” Imran ya ƙare maganar yana dariya mai taushi. Faro ma hannu ya ɗaga yana dariya da faɗin, “Duniya zata san dawowar ka ne lokacin da ka yanke hukunci, ba lokacin da kowa yake jin yanada ƴancin faɗar abinda ya gani ba koda Imran da Faro da shugaban ƙasa ne.”
         “ALLAH ya shiryeku, yau kuma kun zama ƴan comedy”. Cewar Dada yana ɗaukar takardar dake gefensa. Yanzun ma dariya suka sanya, dan har ƙarƙashin zukatansu suke jin wannan nishaɗin mara misali. Shi kansa Dada yana jin fiye da nasu, kawai dai ya fisu kamewa ne, sannan halayyar su dama can ba ɗaya bace, su sunada faran-faran da magana, sabanin shi da ko wasa bai iya ba, dama dai da Imran ne wani lokacin idan ya matsa masa, sai shima Faro ɗin idan ya gallabesa wasu lokutan yakan maida musu murtani.....

      ⭐ 10:43am dai-dai Motocin biyu suka isa secret medical base wuri na musamman mai tsafta, nutsuwa, da ƙa’ida. A yanda gurin yake a killace zaka ɗauka Shugaban ƙasa yasa an tsara shi ne tamkar dan ɓoye Dada ɗin ne anan. Dan tuni har likitoci suna jiran su, likitoci kam na musamman ne aka tanada dan duba lafiyarsa, saboda duk ƙarfin halin da Dada ke nunawa su sun san abu na farko da yake buƙata shine duba lafiyar tasa.
       Sun masa tarba ta girmamawa suma, dan duk da halin da yake ciki kwarjinin yawan ibada da UBANGIJI ya bashi yana nan a tare da shi sai ma ƙaruwa da yayi da sake ɗaga darajarsa ga duk mai kallonsa.
Received at     Shi ɗin DODO ne a kowane irin yanayi, dan haka a nutse yake bin komai da aka shirya da nazari irin na masu nutsuwa: Kayan aiki, ma’aikata, da tsaro mai ƙarfi. Sai da Idanunsa suka gama tantance kowanne daga cikinsu, kamar yadda yake nazarin duk wanda zai shiga cikin binciken sa.
      Imran dake lure da shi ya saki murmurshi ya juya kansa zuwa ga Faro. “Faro, ka tabbata babu wanda zai san dawowar sa.”
     Faro daya fahimci saƙon da Imran ke son isarwa ya ɗaga hannu tare da kashe masa ido ɗaya ya ce, “Babu wanda zai sani, har sai lokacin da Zak-Shadow ya yanke hukunci.”
       “Kayi ƙyan kai Faro. Lokaci zai bayyana komai da kansa. Duk wanda ya ga fitowarsa ba a shirye ba kuwa zai zama....” Imran yay alamar mutuwa.
      Su suke maganar, amma Dada nazartar likiticin daya tabbatar su su Imran kema wannan zaurancen yake. Ganin yanda suka duƙar da kawuna yasa shi fahimtar suna fahimtar komai suma. Baiyi magana ba yay gaba kai kace yasan wajen ne. Da sauri likiticin suka zabura dan masa jagora, Imran da Faro suka sake kallon juna da murmurshi, sai suma sukabi bayansu..........✍️


36


........Ciwon kai sosai ya gallabi Nimrah a makaranta saboda raunin kanta da bai gama warkewa ba. Babu shiri wajen sha biyu aka maidata gida bayan an kaita clinic ɗin cikin makaranta sun dubata. Ba ƙaramin tashi hankalin su Mammah da su Aunty Ummi dake gidan yayi ba. Dan duk ciwon da zakaga ya kwantar da Nimrah haka ba ƙaramin jinsa take ba. Ga jikinta zafi zau da zazzaɓi. Mammah ɗakinta ta Kaita ta kwantar bayan kowa ya gama jera mata sannu da addu'a. Da kanta ta zame mata uniform ɗin jikinta ta barta da vest da shot kawai, ita ta goge mata jiki da ruwan sanyi tasa aunty Mimi ta ɗakko mata riga mara nauyi a ɗakinsu. Aunty Shariffa ta kawo mata kunun madara, da ƙyar aka lallaɓata tasha tana hawaye dan ji take kamar kan zai rabe mata biyu, kaɗan tasha kunun tasha magani Mammah ta kwantar da ita tana tofa mata addu'a har barci ya ɗauketa......

<<<<<★★★★>>>>>   

          “Sir na bincika kamar yanda kace. Gidan nan gidan wani soja ne, akwai mahaifiyarsa a ciki da ƙanensa, amma shi yana ɗaure shekaru takwas kenan. Ita kuma yarinyar ban sani ba ko ƙanwarsa ce ko ƴa gaskiya. Dan ban samu wani cikakken bayani a kanta ba, a dai gidan take, kuma ƴar gidan ce”.
     Gaba ɗaya ma'aikacin hotel ɗin yayima Adeel bayanin ne da harshen turanci, dan da shi suke magana kasancewar shi baya jin yarensa shima baya ji, amma dukansu sunyi tarayya akan yaren turanci. Ajiyar zuciya Adeel dake saurarensa ya shiga saukewa. Dan tun marecan jiya da yaga Nimrah bai sake jin cikkiyar nutsuwa ba a zuciyarsa. Yau ɗin nan yana da zama da tsohon shugaban ƙasa, amma bai iya yaje ba saboda ba waccan damuwar bace yanzu gabansa ta yarinyar da ko sunanta bai sani ba ce. Hatta su Nabeeha bai sake bi takansu ba. Ko wanda yasa yana bibiyarsu da yazo da safen nan masa bayani kamar yanda ya bashi umarni cayay yaje kawai yana buƙatar hutu.
     Da turancin ya ce, “Miye sunanta?”.
        “Nimrah!”.
    Sai da ya wani lumshe manyan fararen idanunsa ya buɗe sannan ya saki murmurshi. Dan kuwa sunan ya dace da ita. Dan a cikin sakannin da suka haɗu ya tabbatar da ita ɗin zakayyarce, zuciyarsa ta shiga wassafo masa ɗan mitsitsin bakinta na tsiwa mai ɗauke da kyawawan lips pink da baƙi. Yanda ta zazzaro masa dara-daran idanunta farare tas masu suffar ƙwai da masa gargaɗin kada ya taɓata da yaren da bai gane komai ba. Ya saki ƴar dariya da sake hango idanunta da suka watsa masa harara.
     Galala ma'aikacin hotel ɗin yay hana kallonsa, dan lallai ya yarda wannan guy ɗin ya faɗa da yawa. Koda yake baiga laifinsa ba. Dan yaran fa sun haɗu, su duka biyun wanke hannu ka taɓa ne. Daga gani kasan ƴan hutu ne kuma ƴan gata ƴaƴan manyan ƙasa. Duk da basu wani gama cika manyan ƴammata ba ko a haka za'aje da su, damma a cikin hijjab suke ba komai nasu ake gani ba face fuskoki.....
      “Ka samo number wayan ta?”.
  Adeel ya katse masa tunani. Kansa ya girgiza da faɗin, “A'a Sir, bayan waɗan nan bayanan babu abinda na samu gaskiya. Dan gidan nan ba ƙaramin gida bane da samun information ɗinsu zai mun sauƙi. Wannan ma sa'a akaci na ga wanda na sani a street ɗin, shima kuma bai wani jima da kama haya ba.”
      “Good kaje ka zomin da shi”.
  Kai ya jinjina masa a ransa yana mamakin irin wannan haukacewa haka daga ganin yarinya? To amma ina ruwansa, aikin kuɗi yake yi, ya tabbatar kuma idan Adeel ya samu abinda yake so shima zai ja kaya. Dan Vvip ɗin da ya kama kawai ya isa ya sanar dakai mugu-mugun mai kuɗi ne shi. Balle manyan agogo da designers kayansa zuwa takalmi, kai wayar hannunsa kanta kai kasan lallai akwai manda. Dan zai iya rantsuwar bai taɓa ganin irinta ba balle kamfanin da ake yinta. (😜Ƙaryar marubutan ta motsa anan. Ya kuka iya🤣 ku karanta kawai🥱. Amma in gaskiya za'abi ai akwai masu kuɗin nan dai ko🥱😎).
    Hannu Adeel ya ɗaga masa, ya ɗan risina na girmamawa sannan ya fice.....

   >>>>>>>%<<<<<<<

       Kamal na ƴar dariya da shafa kai ya ce, “To kusan haka baba, amma ai da sauran lokaci tunda nasan baza'a mata aure yanzu ba nima kuma haka”.
     “Kai! A wannan shekarun naka?”.
“Baba tsahon ƙafa ne kawai, amma ba wasu shekaru bane dan ashirin da biyar ne kacal”.
        “To ai sune dai-dai auren ɗana. Mutum ya more yanda yake so ba auren bariki ba sai an gama tsofewa a ɗakin soro. Mu kaga iyayenmu sun mana gata a sha tara ma suka mana auren”.
     “Baba sha tara fa?”.
  “Sosai. Ba gashi mun mora auren yanda ya kamata ba. Itama kuma ai in a ƙauye ne yanzu ta isa haihuwa ma ta biyu ko ya yaye na farko tana da cikin na biyu. Shekara sha biyar fa tana cikin ta sha shida koba haka ba?”..  
        “Tabbas haka ne Baba”.
    “To ka gani, ai karka wani damu kanka, ka fara yaɗa manufa kawai muma zamu tayaka”.
    “To baba ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.
     “Yawwa haka nake so naji ka faɗa”. Cewar Malam Buba yana miƙewa. Ya cigaba da faɗin, “Kaga jirani bara na kirata, dan naga kwana biyu ma bata zuwa makaranta sunce bata da lafiya. Kwana kusan biyar kenan taji ciwo a islamiyyar su ne...”
     Cike da jimami Kalam ya amsa masa da, “Haka ne Baba, wlhy a islamiyya ne fa.....”
   Ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Malam Buba dake saurarensa cike da nazari yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa. Dan kuwa tabbas yau ya samu hanya mai sauƙi da yake nema da fata. Tabbas Kamal shine zai kasance makamin amfaninsa akan cimma burinsa kan Nimrah. Labarin nan kuwa yay masa matuƙar daɗi da ɗaukar hankalinsa. Tuni ya nufi cikin gida kiran Nimrah.........✍️



.........Imran ya miƙe kenan zai wuce Malam Buba yay sallama. Amsa masa suka yi shi da Mammah, kafin Mammah ta bashi izinin shigowa. Koda wasa bai kalla sashen da Imran yake ba, dan haka kawai yake jin tsarguwa idan Imran ɗin na kallonsa. Daga bakin ƙofar ya rissina ya gaishesu, sannan ya isar da saƙon Nimrah tayi baƙo.
      Cike da mamaki a tare Mammah da Imran suka furta, “Baƙo kuma?”. Har yanda sukai ɗin ya bama Malam Buba mamaki. Amma sai ya shanye mamakin nasa yay ƙarin bayani da, “Yace malamin su ne na islamiyya, mage ce ya kawo mata, yace kuma itace da kanta ta buƙaci haka.”
     Mammah tasan labarin mage, dan har Nimrah a kwanakin tana mitar batun kawota da malaminsu baiyi ba. Kusan yanzu ma take jiyosu daga kitchen Nimrah na batun da tasan number sayyadinsu data kira a wayar Biebah ta tuna masa batun magenta. Sunan Nimrah ɗin ta kira, ta amsa tana fitowa daga kitchen ɗin hannunta da kofin tea, ganin sabon driver ɗin su da ko sunansa bata riƙe ba har yanzu ya sata ɗan tsayawa turus, sai kuma ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ƙaraso wajen Mammah.
      Hannu Mammah tasa ta amshi kofin shayin hannun nata tana faɗin, “Saka hijjab kije ga malamin ku yazo kawo miki magen taki”.
      Washewa fuskar Nimrah tayi da murmushi, cike da farin ciki ta ce, “To Mammah. Ta ɗauki hijjab a inda suke ajiyewa ta saka. Malam Buba na gaba tana biye, haka kawai ta samu kanta da zubawa bayansa ido duk da zuciyarta dake bugawa. Imran na daga ciki sallama yay ma Mammah ya fito dan kiran Faro nata shigo masa a waya, yasan kuma zai iya yiwuwa Dada ne, shi kuma baya son ɗagawa a gaban Mammah dan ko a fuska bai nuna mata fitowar Dadan ba. Dai-dai Nimrah na kaiwa gate, cikin ɗan risinawa ta gaida Sayyadi Kamal daya zuba mata ido. Ita kam kanta a ƙasa batama san yana yi ba.
        Idanu sosai Imran ya zubama Kamal ɗin daga inda yake tsaye cike da nazari, yayinda shi kuma hankalin Malam Buba yake kan Imran a kaikaice shima yana nazarin kallon da yake ma Kamal ɗin. Nimrah kam bata ɓata lokaci ba ta miƙa hannu amsar kwalin magen. Kamal na murmushi da kallonta ya miƙa mata tare da miƙewa, kaɗan ya matsota yana magana ƙasa-ƙasa. Nimrah ta yamutsa fuska da ɗan jan jikinta baya, yayinda fara'ar fuskarta ke raguwa alamar maganar daya gaya mata ce batai mata ba. Dan kamar wadda take a ƙage ma yana sakar mata kwalin ta baro wajen tana masa sallama da tafiya duk a lokaci guda. A haka ta ƙaraso inda Imran yake tsaye yana kallon Kamal dai dake binta da kallo..
       “Daddy kaga mage na”.
   Nimrah ta faɗa dai-dai tana isowa gabansa, murmushi ya saki yana ciro hannunsa daga aljihu ya amshi kwalin cike da kulawa. Da kansa ya kwance ɗaurin zaren da akaima kwalin yasa hannu ya ciro kyakkyawar magen fara tas ƴar ƙarama.
       “Masha ALLAH Babyn daughter ta iso gida lafiya. ALLAH ya rayata ta haifa mana yara da yawa duk a raba mana”.
     “Amin Daddy”.
Nimrah ta faɗa cike da farin ciki. Maida mata ita yay a kwalin. “To ya sunanta?”.
      “Uhmm Daddy sai Ruky ta dawo zamu saka mata suna”.
     “Oh na manta, Ussaina bata yanke hukunci sai Hassanarta na nan. Bari na wuce idan an saka sunan maji a waya”.
          Nimrah na dariya ta ce, “Daddy ALLAH ya tsare hanya. Ka gaida Ammie da su Aunty Ma'u gobe zamuzo daga nan muje gaida Grandpa tunda Grandma taƙi dawowa daga ƙauye. Sai mu wuce mu gaida Ummu da Grandpa suma ko”.
      “Tunani mai ƙyau Daughter, ALLAH ya kaimu. Amma ki kwantar da hankalinki ma su Asma'u suna hanyar zuwa nan gaida Mammah suma.”
     Wani irin farin ciki ya sake kamata. Tai ciki tana murna da faɗin zataje tai ƙwaɓa fulawa nayin ɗanwake da kalallaɓa”.
     Fuskarsa da murmurshi ya bita da kallo harta shige. Kasa riƙe abinda yake ayyanawa a zuciyarsa yayi sai da ya ambata, “My Zaki ɗiyata ta zama macen nan da kake tunanin za'a jima bata kai ba, Abu na farko kenan da zai fara baka mamaki idan ka taka ƙafarka a gidan nan”. Sai kuma ya sake sakin murmushi yana girgiza kai saboda hasaso cakwakiyar dake gaba.
Har yanzu Nimrah bata san akwai aure a kanta ba, shiyyasa suke kaffa-kaffa da al'amarinta ko nan da can ba'a barinsu zuwa su kaɗai sai da driver ko Mu'azz.. dai-dai yana isowa wajen motarsa, kallon da yaron nan da akace malaminsu ne ya faɗo masa a rai. Juyawa yay ya kalli gate ɗin, sai yaga sabon drivern nan daya sakama alamar tambaya ne kawai a wajen yaron baya nan alamar ya wuce. Lallai dolene yay saurin tsaida wannan alaƙar, dan ya

18 / 42