KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 42

102K to 105K   out of 125.4K words

a cikin idanunsu, a cikin ƙasar da suke alfahari da ita, a hannun marayan nan da suke iƙirarin an haifa a gabansu, sadauki uban sadaukai, masoyin ALLAH ɗan gatansa, mai faɗa da cikawa kyakkyawan balarabe ɗan dangi. To waɗan nan dauɗar duniyar ba komai bane ba. Idan ma mu mun shuɗe a cikin yaƙin, wasu da zasu ƙarasa mana ZASU TASO NE. Kawai ina son ka fahimta, a yanzu ƙungiyar duhu ta ɓoye. Ta canja fuska. Ta sake yin mamaya ta mutane da dukiya. Amma tana nan kuma tana motsi da motsin ƙarfin ikon ƙasa da masu shugabancin ƴan ƙasar. Amma bana son hakan yasa kaji tsoro, dan tsoro shine matakin farko na rauni da tarwatsewar ƙarfin iko, sannan shi ke bama marasa ƙarfi ƙarfi akan masu rinjaye. Shike bama masu taka baza da bazar ƙarfin masu ƙarfi gadara da ɗauka sune a sama dole a bisu. Shi ke sawa suji kamar zasu iya juya duniyar bayan talakawan ƙasar da suke amsa suna ƙasar tasu”
         Murmurshin da Dada ya saki a yanzu har sai da ya bayyana fararen haƙwaransa a cikin idanun shugaban ƙasa da Imran. Sai kuma ya ɗan taɓe baki. “Na riga na ji motsinta tun ina sakaye. Sai dai ranka ya daɗe ka sani bazamu ce mu bama jin tsoro ba, saboda mutane ne tamkar kowa. Muna da rauni, muna da ruhin mutuwa tamkar kowa. Muna son rayuwa, dan wannan ɗan adam taka ce irin na kowane rai. Sai dai hakan bazai hana mu sadaukarwa ba, saboda addininmu addinin jarumta ne.
Mun san kammu, mun san makomar mu da darajar rahamar da mahalicci mu yayi mana. Yanda sahabban MANZON ALLAH suka ƙare rayuwarsu wajen bama MASOYINMU kariya da kafa daular da har a yanzu muke ci daga arziƙinta, muma na baya da bamu ganshi ba, amma soyayyarsa bata da iyaka a jininmu bazamu bari wasu munafukan cikinmu da azzalumai suka mamaye da ƙyale-ƙyalen duniya ba su saida mu a hannaye marasa daraja. Zamuyi da basirar mu, da ƙarfin mu, da lokacin da UBANGIJI ya bamu, randa umarninsa na gushewarmu ya tabbata sai mu kwanta mu barma na baya sauran aikin, dama mun san duniya kasuwa ce, sanda wani ke kammala cin tashi sannan wani ma ke shirin shigowa tashi sayayyar. Dan haka ba ruwana da ƙarfinsu, dukiyarsu, mamayarsu, dan koda da Imran da su Ma'aruff suka mamaya zamu haɗa duka mu zubar da su da ƙarfin ikon ALLAH”.
       Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi yana jinjina ƙudirar UBANGIJI mai bada ƙarfin iko ga wasu zukata. Sannan ya gina tsokokin jikinsu da ƙarfi mai bayyana a idanu. Ya rage naka ka zama irin Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi wajen nuna godiyarka ka gina kyakkyawan aiki, ko ka zaɓi butulce masa wajen lalata wannan baiwar a neman duniya da burge mutanen ciki dan kawai a kiraka wane a riga ko dukiya ko suna. Imran da yasan duk abinda zai fito daga bakin Zakin sa tun daga ƙarƙashin zuciya ne bawai cika baki ko gadara irin ta wawayen mutane ba, sai ya lumshe idanu yana ɗan sakin ajiyar zuciya.
         Shugaban ƙasa ya sake katse shirun da faɗin, “UBANGIJI yayi ma rayuwa albarka, ya ƙara mana ƙarfin zukata da jajircewa. Ya ɗora nasararmu akan masu zalunci. Duk mai son kaimu ƙasa ya Rabbi ka kaishi a lokacin da muke barci batare dama mun sanshi ba. Haysam ka godema ALLAH kaji, dan ya baka abubuwa da yawa da bai baima da yawan mutane ba. Irin ku kai da Imran kaɗanne a cikin wannan haɗamammiyar al'ummar tamu da basu da burin komai sai na son tara dukiya da suna cikin haɗama da babakere. Burin kowa ace shi ɗin shi ne dai, yana mantawa da ranar tafiya babu ko zoben ƙarfe a ɗan yatsa, sai farin ƙyalle da a kwana uku zai fara ruɓewa ma, sai wannan halayen dai da in ka gagara ginawa akan gaskiya, amana, imani, tsoron ALLAH. Kowa gani yake kawai daya mutu ya huta. Bai hango kwanciyar shekaru da za'ai a cikin kabari balle ranar rarrabe ayyuka, kowa dai sai yace aljanna ta mai rabo ce. To aljannar an faɗa maka layin rabon kunu ce balle kace idan kaga idon sani a wajen zai ƙara maka kofi ɗaya akan kasonka naka ya ƙara yawa. Iya nauyin sikelinka, iya matakin da zaka taka daga falala ko uƙuba. Ya rabbi kasa mu cika da imani”.
        “Amin ya rabbi”.
   Dada da Imran suka amsa a tare.
        Karan farko Imran ya saka baki a tattaunawar tasu. “Ranka ya daɗe nima ƙarfinsu bashi yafi damuna ba ko nake kallo a barazanar wannan yaƙin. Zak.. ka san abin da ya fi haɗari?”
      Dada ya girgiza kai.
“Ba kai bane”.
Imran ya cigaba da faɗa.
          “Ban gane ba”.
     Cewar Dada yana tsare Imran da idanu. Sai dai maimakon Imran ɗin ya bashi amsa sai shugaban ƙasa ya amsa masa da.
       “Gaskiya Imran ya faɗa, ba kai ne haɗarin ba a yanzu. Abin da ke kusa da kai ne. Shiyyasa dole a fara wannan aikin a rufe, dan zuwa yanzu koda sun sami labarin dawowarka zasu fara maida hankali a binciken tabbatarwa ne kafin shiri”.
        Shiru ya ratsa falon kamar hukunci. Dada bai tambaya ba. Bai kuma ƙaryata ba, sai ma nazartar maganganun yake dalla-dalla a ƙasan zuciya.. Fin minti biyu kafin ya kallesu su duka. Kai tsaye ya furta, “Minene shirin yanzu?”.
        Shugaban ƙasa ya ɗaga gira kaɗan. “Ajiye aikin soja a zahiri. Sannan sabon muƙami a ɓoye. Ba muƙami na takarda ba. Ba wanda zai gani. Ba wanda zai sani. Ba wanda zai ji, sai mu ukun nan kacal”.
         Shiru kawai Dada yayi yana kallonsu. Sai Imran ne cikin dunƙule hannu ya furta, “Yes ranka ya daɗe. Wannan itace power ta gaskiya, power ta ruɗani. Power ta mamaya, sannan ta ƙarfin iko”.
      Ƙaramar dariya shugaban ƙasa yayi, dan yanda Imran ɗin yayi dole kai dariya. Shi kansa uban gayyar duk da ya fuske sai da ya murmusa a zuciyarsa.
       Janar ya buɗe drawer jikin center table ɗin ya zaro wata takarda, Imran ya miƙawa yana faɗin, “Ba takardar aiki ba. Umurni ne. Jagorancin sashen tsaro na musamman”. Ya maida idanunsa kan Dada. “Kai kaɗai zaka ba da rahoto kai tsaye gare ni. Kana da damar haɗa ɓoyayyar rundunar aiki, a cikin kowanne jami'an tsaro na ƙasar nan ko farar hula. Sai dai ka sani zan saka ɓoyayyen tsaro a bayanka, dan kai ma tsaron lafiyarka zai koma ƙarƙashin ikona ne daga yau a gida da waje. ALLAH ya bamu fiye da nasarar da muke fata da buƙa”.
        “Amin ya rabbi ranka ya daɗe”. Cewar Imran cike da farin ciki. Dada ma ya ɗan yi murmushi kaɗan. Sai kuma cikin ɗan taɓe lips ya furta.
     “Sir! A ɓoye baiyi ƙarfi ba? Karfa ka manta akwai soji biyu tare da ni.” ya ƙare maganar da kallon Imran...........✍️
67


.......“Hakan shine yafi dacewa”. Shugaban ƙasa ya amsa yana kallon Imran ɗin shima, sai kuma ya cigaba da faɗin, “Domin idan aka bayyana, za su motsa. Idan aka ɓoye… za mu gan su suna motsi. Dole Imran zai koma ɓoyayyen ma'aikaci a wajenka daga shi har Haydar, dan karka manta akwai kaki a jikinsu, kuma suna da ƙarfin iko a waccan bishiyar ma. Dole kuma su cigaba da zama dan inuwarsu zata mana amfani cikin wannan ɓoyayyar tafiyar, ta haka ne zasu banbance ganyen daya bushe akan bishiyar da suke”.
       Cikin gamsuwa da jinjina kai Dada ya miƙa hannu ya ɗauki takardar a karo na farko, bai kalle ta ba. Sai dai kai tsaye ya furta,
       “Yaushe aiki zai fara?”
   “Ba a wannan daren ba. Amma daga yau… ka riga ka fara.”
      Dada ya ɗauki kofin sabon shayinsa da Imran ya sake zuba masa, dan sun shanye coffee ɗin farko tuni, ya kai bakinsa. Sai da yasha ya ajiye sannan ya furta.
      “Idan haka ne, ku shirya kawai.” daga haka ya miƙe. Shugaban ƙasa ya miƙe shima, hakama Imran da ya furta kalmar;
       “Da me?”
  Dada ya kallesa, idanuwansa sun yi sanyi amma murya ta yi kaifi. Kai tsaye ya bashi amsa da.
       “Da komai ma. Domin wannan karon… ba zan tsaya tsaka-tsaki ba. Zan yi aiki kunne a toshe, ido a makance. Ba uba, ba ɗa, ba ƙani, ba aboki, ba mata koda tsautsayi ya gitta”.
         Shugaban ƙasa ya kalleshi na ɗan lokaci yana siririyar dariya, sannan ya ce, “In sha ALLAHU ma baza'a kai ga nan ba ZAKIN IMRAN”. Ya ƙare maganar yana miƙa musu hannu alamar su yi musabaha. Sai da suka ɗan dara a tare, kafin musabahar dake nunin abubuwa masu yawa.
      Ba murmushi. Ba alkawari mai yawa akan ɗagama kowa ƙafa. Sai dai akwai fahimta. Sannan akwai tabbatarwar a waje ƙungiyar duhu na jira. A gida, zuri'a da iyalai na kusa.
A ɓoye munafukai na motsi.....

       
>>>>>>>%<<<<<<<

      WASHE GARI JUMA'ATU babbar rana. Ranar da kan biɗa ka samu da izinin UBANGIJI mai taskar da bata girgiza balle ƙarewa. Babu wanda yasan lokacin da Dada ya dawo gidan a daren jiya. Wayar gari kawai sukai suka ganshi. Ganin nasa ma su Uncle Ja'afar ne kawai a wajen fita massalaci sallar asubahi. Su Nimrah kuwa har suka kammala shirin makaranta suka fito basu san ma mi gidan yake ciki ba. Sai da suka fito kai tsaye Mammah tace bazasu makaranta ba sun mance abinda suka aikato jiya. Dole su jira sai anji halin da yaron ke ciki gudun abinda zai iya zuwa ya dawo.
        Ko'a jikinsu dan daɗi ma suka ji, tuni suka koma ɗaki suna tsallen murna suka cire uniform. Hankali kwance suka sake hayewa gidajensu suka duƙun ƙune a barguna bayan sun kashe fitilu sun saki labulale da ƙara gudun ac. Babu kuwa wanda ya sake jin labarinsu bare motsin su har sha biyun rana. Koda Mammah ta saka Kulu ta tado mata su suzo suyi breakfast samu tai sun kulle ƙofa ma. Bugun duniya kuma babu ƙo motsinsu sai kawai ta ƙyalesu.
        Kaf mazan gidan yau suna gida. Dama su Ma'aruff basa fita kasuwa juma'a, Bilal da Ammar ne kawai sukaje aiki. Kuma sun taso da wuri saboda tafiya massalaci. Dada kam babu wanda ya gansa a safiyar har yanzu. Yana ɗakinsa. Da yake ya sanar ma Mammah zai yi barci ne sanda ya shiga suka gaisa da asuba, dan shi yama ce ta hana su Nimrah zuwa makaranta shiyyasa bata damu da rashin fitowar tasa ba balle tayi jajensa...
        Sai misalin ƙarfe sha biyu da kwata duk suna falo ana hira sai gashi ya sakko. Ƙamshinsa shi ya fara ratsa hancinansu kafin bayyanarsa. Babu wanda baiyi tasbihi a ransa ba ga UBANGIJIN halittar wannan bawa. Dada ko yaya sutura take idan ya saka tana masa kyau matuƙa, koda ba mai daraja bace. Sai dai fa manyan kaya sukan zama na musamman dake ƙara masa kamala da cikar haiba tamkar uniform ɗin aiki. Dan a shekarun baya Imran yasha tsokanarsa da kalmar (bai taɓa ganin wanda uniform kema ƙyau a jiki irinsa ba). Ko a lokacin baya ce masa komai, wani lokacin ma sai dai ya samu tukuycin harara.
          Shi ya fara gaishe da Mammah kafin su ma duk su gaishe shi. Koda Mammah ta masa maganar abinci ce mata yay sai sun dawo massalaci.
    “Zama da yunwa ko Muhammad? Bafa ka karya ba”.
     Murmurshi yay mata. “Mammah nasha Coffee”.
        “Coffee ba abinci bane ai, yanzu dai ko milk tea a haɗa maka”.
    Bai ce komai ba, dan yasan in ma bai sha ba hankalinta bazai kwanta ba. Kafin Mammah tai magana Biebah ta miƙe kusan lokaci guda da Lailah. Mammah tace Lailah ta koma ta zauna ita dake fama da kanta. Dan yau Shariffa ma gaida Mammah kawai tazo tayi ta koma sashenta alamar ɗan baba nata harama. Dan har asibiti ma Yaya Ja'afar ɗin yaso su wuce taƙi, acewarta a ɗan dai saurara tunda ba wani ciwo take ji mai tsanani ba, kawai dai jikin ne baya mata daɗi. Biebah ce taje tai mata komai a sashenta, su Abees kam sai Lailah ta haɗasu tai musu shirin makaranta dan su sunje.
      Yana kammala sha suka wuce massalaci. Bayan wucewar tasu Mammah da kanta taje ya tada su Nimrah. Da ƙyar suka zo suka buɗe mata ƙofar kuwa. Korasu tai suje suyi wanka, ita kuma ta fice nata ɗakin. Koda suka fito fes da su, duk da ba wasu kaya masu nauyi suka saka ba amma da yake yaran Mammah masha ALLAH sai suka fito darr. Hanoon kawai suka samu a falon tana kallo, ko kallon inda take basuyi ba suka wuce kitchen, dan tsabar neman magana ma hanci Ruky ta rufe, sai kuma ta ɗauki turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta saka bonner. Mi Nimrah zatai inba dariya ba. Harda wani faɗin, “Sai dake Trouble Buddy na”.
       Ruky kam ta fuske kamar bata aikata komai ba. Hanoon ta shaƙa sosai, sai dai batayi magana ba. Haka suka zauna suka fara cin abinci suna hira da dariya data saka Hanoon daina fahimtar Film ɗin ma gaba ɗaya. Fitowar Biebah ya taimaki Hanoon. Dan Biebah data fahimci abinda ke faruwa sai ta ɗauke musu hankali da labarin ƙawarta Chef Yakudima, tace su tambayi su Yaya Ma'aruff su biya musu su shiga makarantar koyon girke-girken ta tunda gashi za'a shiga hutu.
      Ruky na bala'in son harkar girke-girke, Nimrah ce ma sai a hankali tanan ɓangaren, dan ma Ruky na jan ra'ayinta shine ma take ɗan taɓawa. Suna tsaka da wannan hirar ne Mammah ta fito. Koda taji batun da suke sai itama ta gamsu da shawarar Biebah ɗin, tace ta binciko ya tsarin yake. Cike da farin ciki Ruky ta rungume Mammah. Dariya suka saka mata harda su Kulu da suka fito, dan kowa yasan yanda take son harkar. Daga nan aka fara hirar girki. Nimrah da yake ba so take ba taƙi saka baki, Hanoon ma sai wani yatsine-yatsinen fuska take yi.
     Mammah datai tunanin ya kamata a gyaro ɗakin Dada duk da baiyi magana ba tace Nimrah taje ta gyaro tunda ba hirar take ba. Nimrah bata son aiki, dan haka kamar zatai kuka ta fara roƙon Ruky ta rakata suyi, ita ko Ruky hankalinta nakan kallon videos ɗin Chef Yakudima a YouTube channel tace bazata ba. Nimrah taji haushi kuwa ta wuce fuuuu. Sai kawai Hanoon ta saka mata dariya. Ta juyo zatai magana Ruky ta ƙyafta mata ido alamar karta kulata. Bako ta tanka ɗin ba ta wuce, itama Rukyn ta cigaba da kalle-kallen ta kamar ba'ai komai ba. Biebah data fahimci abinda sukayi sai taji tausayin Hanoon tayi kamata, dan wlhy tasan wata tsiyar zasu ƙulla mata ne, ga dai Afeef nan ya koma ɗangyasa ƙafa yau, baki yayi tumm na kumbura abin tausayi.

       ★Tunda ta buɗe ƙofar ta shigo, wani ƙamshi mai ratsa zuciya ya daki hancinta, kasa haƙuri tai sai da ta wani lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Harga ALLAH tana son ƙamshi, dan ƙamshi duniya ne. Ɗakin ta fara bi da kallo bayan ta zube kayan sharar, babu wani tarkace sannan babu datti, sai saman gadon ne ma dake barbaje da takardu, sai laptop. Sannan daga study table ɗin da basu san sanda aka shirya shi ba an saka wani babban board fari, an mammana hotuna a jikinsa. Ba iya gane hotunan take ba, saboda an saka board ɗin sama sosai, hotunan kuma kanana ne kamar na passport.
     Baki ta ɗan taɓe kawai zuciyarta cike da ƙananan tunani. Bayi ta fara shiga dan gyarawa, shima babu wani datti sosai, amma haka ta nutsu ta fara gyara komai yanda ya kamata. Dan-danan ya ƙara ƙyau da ƙamshi. Fitowa tai tana duba kayan ɗakin suma da tunanin ta ina zata fara, sake saukar idanunta a study table ɗinsa yasa ta nufi can ta fara, ƙananun abubuwa ta fara tattarewa, musamman su pens da flash drive masu yawa dake a saman study table ɗin. Ganin basu da wajen ajiya ta fita, ɗakinsu taje ta ɗakko wasu ƙyawawan baskets ƴan mitsi-mitsi na kaba da suka taɓa saya ita da Ruky. Sai kawai ta zuba masa flash drive ɗin a cikin ɗaya, hakama pens, makers suma, da pins, komai dai ta ajiye shi a tsare da ƴan uwansa ta jerasu a table ɗin bayan ta ɗaga ta goge komai na wajen har desktop ɗin. Ta koma kan mirror ɗinsa nan ma ta gyara turarrukan wajen tsaf da mayuka, harma da abubuwan da bata san amfani su ba. Tsabar son ganin ƙwaƙwaf sai ta buɗe wadrobe ɗinsa. Yanda kayan suke komai a tsare da muhallinsa sai abin ya birgeta, ta tuno tasu wadrobe ɗin ita da Buddy ɗinta dake a up side down kullum sai ta sheƙe da dariya. A fili ta ce, “Buddy na ALLAH ya ƙara mana hankali, muma mu dinga gyara wadrobe ɗinmu kamar haka”.
      Gado ta dawo ta fara tattare takardun, kamar abin almara ta ma gama tattare su tas ta ɗora saman laptop ɗin data rufe tana shirin sauka a gadon dan hayewa tai ɗare-ɗare, kawai taja Duvet zata sauka da shi sai taga wani file ɗin a wajen. Ta ɗaga file ɗin batare data fahimci ta riƙe gefe ne ba sai kawai abubuwan dake ciki suka tarwatse mata a jiki. Harda hotuna.........✍️


68


.........Cikin ɗan jin takaici ta furta, “Wayyo ji salon ƙara min aiki” Ta furta a hankali, tana ƙoƙarin fara tattaresu. A bazata taci karo da hoton Umman ta da shima ya faɗo daga cikin file ɗin. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, ta ƙurama hoton ido zuciyarta na hanƙoro, “Miya kawo hoton Ummana wajensa?” ta sake faɗa a fili tana fara ɗaukar sauran hotunan da suka kife tana birkitosu. Hotunan

35 / 42