Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
yana tare da Dada ba ko'a lokacin. Ya dai tabbatar mata da yana nan dawowa gida a satin nan.
Dan haka yanzu ma daya kira sunyi gaisuwa yanda suka saba irin ta mahaifiya da ɗa. Daga nan yake sanar mata a gyara ɗakin da babu kowa anan ɓangarenta. Yayi magana da wani kamfanin funichars za'azo a saka. Ɗan jimmm Mammah tayi na alamar tambaya, sai dai fahimtar kamar Imran bai son buɗe zancen yasa bata tambayi mi za'ai da ɗakin ba tace to kawai. Daga ƙarshe take sanar masa ya kira su Ma'aruff yay musu magana dan Uncle Tasi'u na son zuwa da yaransa yau da daddare amma tasan halinsu da shegen taurin kai.
Bata son a samu matsala kuma, fatanta suyi haƙuri su barsa da halinsa su yafe masa komai ya wuce a cigaba da zumunci. A cewarta duka ma rayuwar nawa take. Murmurshi Imran yayi yana sake jinjina ƙyawawan hali irin na Mammah. Cikin lallashi yace mata karta damu, in sha ALLAHU zai musu magana. Daga haka sukai sallama.
Duk wannan wayar da Daddy Imran keyi Dada na zaune a wajen. Sai dai hankalinsa na'a kan laptop zaka rantse baima san mi Imran ɗin keyi ba. Sai dai sarai yana fahimtar komai, dan ji yayi kamar ya kwaci wayar yayi magana da Mammah ɗin. Amma ya danne baiyi magana ba koda Imran ɗin ya kammala wayar ma. Sai ma wani zancen ya ɗakko masa akan aikin da yake yi a laptop ɗin.
Kusa da shi Imran ya dawo ya zauna shima yana maida hankalinsa ga screen ɗin laptop ɗin......
<<<<<<<★>>>>>>>
Washe gari a gidan Mammah bisa umarnin Daddy Imran abubuwa biyu suka faru. Na farko isowar Companyn da zasu shirya ɗakin daya buƙata. Ba kuma wani ɗaki bane daban, ɗakin da Nimrah ta shiga ne tai kallon video kwanaki. Dama tun safe su Ammar suka fidda komai na cikinsa su Kulu suka sharo suka wanke bayin da ba'a taɓa amfani da shi ba. Lokacin da masu zuba kayan suka zo aikinsu kawai suka fara cike da ƙwarewa.
Abu na biyu isowar Uncle Tasi'u gidan a karo na biyu, sai dai a wannan gaɓar harda yaransa uku. Biyu maza, ɗaya mace. Kamar kowa sai da sojojin nan suka musu bincike ciki da bai aka kuma tabbatar da sanin masu gidan suka zo kafin a barsu su shigo. A lokacin su Nimrah basa nan, suna makaranta iyayen gidan ne kawai sai su Aunty Ummi da kullum yanzu suna gidan sai dare suke komawa nasu gidajen. Shariffa ce kawai babu a falon dan yau ta tashi bata jin daɗi sosai kasancewar cikinta yafi na Lailah tsufa.
Babban ɗansa yana kamanni da shi sosai da Mammah. Sai dai ko Ammar zai iya girmarsa da kusan shekara biyu. Sai mace itama budurwa, daka ganta kaga wayayya, gata fingai-fingai kamar kazar mayu. Itama dai Biebah zata iya girme mata kaɗan, dan bazai fi irin shekara ɗayan nan ba ta bata. Sai Auta namiji, shi kam zasu iya dai-dai da Mu'azz. Kai da ka gansu kasan rainon ƴan gayu ne, sai dai kuma da ganin inda suka zo ɗin yama fi gidansu komai suka kama kansu. Ga Mammah ta musu tarba ta mutuntawa da soyayya kamar zata haɗiyesu. Su Aunty Mimi ne ma dai sama-sama suka amshesu dan ma gargaɗin Yaya Imran ne. A haka su Nimrah suka dawo gidan suka samu baƙi, duk da dama a kwanakin nan kullum gidan bai rabo da baƙin. A gidan nan babu wanda yakai Nimrah da Ruky wulaƙanci idan mutum bai musu ba.
Sun gaida Uncle Tasi'u da girmamawa matsayinsa na uba. Amma ƴaƴansa kallo ɗaya sukai musu suka watsar da su kamar sun ga kashi. Sun kuma yi musu haka ne saboda ganin yanda suketa wani jijji da kansu su a dole ga rainon turai. Kota kansu kuwa basu sake bi ba suka shige ɗakinsu, bakuma su sake fitowa ba ko abinci sakawa sukai masu aiki suka kai musu dan yau alhamis ne babu Islamiyya. Sai da Mu'azz ne ma ya dawo gidan yazo ya jajibesu suka haura sama ganin ɗakin da aka zubama kaya. Anan suka lalace sunata santi da hotuna da wayar Mu'azz ɗin. Dan ɗakin yayi ƙyau matuƙa. Haka suka fito suna damun Mammah da tambayar wazai zauna a ɗakin. Tace bata sani ba itama Daddynsu ne kawai yace a gyara....
★RANA BATA ƘARYA......★
Tabbas wannan batu haka yake. Dan kuwa washe garin juma'a kamar jiya yau ma Daddy Imran ya kira Mammah a waya yace su shirya za'azo a ɗaukesu bayan sallar juma'a zuwa wani waje. Kan Mammah ya fara ɗaurewa, amma sai nan ma bata tambaya ba saboda halin girma da dattako irin nata tace kawai to. Su Bilal ne ma data sanar mawa suka fara shan jinin jikinsu. Jiya an gyara ɗaki, yau ance su shirya anya kuwa?..
Kasancewar baƙin ido a gidan yasa basu ja maganar da nisa ba. Bayan sunyi shirin massalaci sun fita harda ƴaƴan Uncle Tasi'u Dayyan da Afeef, suma su Mammah dake gida suka hau shiri. Sai ga su Aunty Ummi sun fara isowa da tasu tawagar suma. Dan yaran basu sami sukunin zuwa gidan ba sai yau saboda makaranta. Shiyyasa yau juma'a kowa da ɗansa yazo.
Nan fa aka sake kacamewa har wani baya jin zancen wani.
Banda yara za'ai fitar, dan haka su Nimrah a gida akai shirin barinsu da yara amma suka shiga magiya da roƙon Mammah dole tace su shirya. Kasancewar harda Aunty Biebah da su Aunty Lailah su Nimrah sune ƙanana. Su yaran ma murna sukai da tafiyar tasu, dan a sanin da sukai musu basa ɗaukar raini, idan aka barsu da su dole su daku. Dan kaɗan daga aikin Damisa da Zakanya yaro yaci duka kafin uwarsa ta dawo....
Ba ƙaramin ƙyau sukai ba kuwa da kwalliyar tasu. Nimrah skirt da riga ne na atamfa da tai mugun zama mata a jiki, sanin ba barinta ake fita da ƙaramin gyale ba idan ta saka irin waɗan nan kayan yasa ta ɗora after dress a sama, ba ƙaramin ƙyau tayi ba ga fuska tsaff da kwalliya mai nutsuwa. Hakama aminiyar tata tana sanye da irin kayan nata sai dai ita kam gyale ta saka. Suka kawo turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. suka saka, gashi dama sunyi kabasa da shi a kaya..
Suna fitowa Ya Mu'azz ya fara tsokanarsu wai kamar ranar auren su. Ba raga masa suke ba, dan haka suka shiga ramawa ana dariya. Daga haka suka fito harabar gidan kowa ya shiga mota. Ninah da Ruky na tare da Mammah, Uncle Bilal ke tuƙi sai Mu'azz a gefensa. Ana buɗe gate suka fito motocin sojoji biyu dake jiransu suka take musu baya. Ɗaya a gaba ɗaya a baya. Wannan matakan tsaro na ba kowa mamaki a cikinsu, dan ko yanzu su Nimrah sai da sukai magana. Dan har a makaranta ma yanzu tare suke zuwa da sojojin da a yanzu suka zamewa kowa dogari a gidan batare da sun san dalilin yin hakan ba. Abinda kawai sojojin suka sanar musu tun a ranar farko da aka kawosu shine umarni suma kawai suke bi........✍️
KIƊA A RUWA 2
51
.........★AIRPORT★
Ba ƙaramin mamaki su Mammah sukai da ganin inda aka kawosu ba. Airport fa, sukam wa garesu da zai dawo daga wata ƙasa. Imran ne kawai yay tafiya, basa jin kuma dan zai dawo zai musu irin wannan tattarowar iya su kaɗai. Kowa da magana a bakinsa sai dai sunyi dauriyar dannewa.
Ba a kai su Mammah da iyalanta cikin waiting hall na jama’a ba. Sai ma wani mamakin da aka sake basu, dan kuwa Jami’an tsaro masu bakaken kaya suka sake tarbarsu anan ɗin sannan suka jagorance su zuwa wani ɓangare na musamman a airport ɗin da zasu iya rantsuwar basu taɓa sanin akwai shi ba. (VIP lounge) wurine da ya sha bamban da hayaniyar waiting hall. Ga tsaro ko’ina. Iska mai sanyi ga ƙamshi mai saka nutsuwa. Ga kujeru masu taushi da ƙawa kai kace wani shiryayyen falon hutawar shugaban ƙasa ne. Koda yake ko ba'a faɗa ba kai kasan wannan wajen sai dai tanadin zaman shugaban ƙasar.
Sai da Mammah ta zauna sannan kowa ya zauna ana kallon kallo. Su Nimrah kam kasa haƙuri sukai cikin raɗa-raɗa sukace Ya Mu'azz dake kusa da su yay musu hoto. Bai ko yi musu ba ya fara ɗaukarsu, daga ƙarshe ya koma yima kowa video sai da Mammah ta masa daƙuwa.
Cikin dariya ya ce, “Mammah yi haƙuri, ALLAH wajen ne ya haɗu. Idan bamuyi hoto ba ai ansha damu. Wai dama a waiting hall na airport akwai vip room irin wannan?”.
Kowa murmurshi yake da zancen Mu'azz. Uncle Ja'afar ya bashi amsa da, “Ai dole ne ya zama akwai irin wannan ɗin Mu'azz kodan shugabanni ko”.
Cikin gamsuwa Mu'azz ya ce, “Haka ne kuma Uncle. Tunda dama kasarmu komai yana da banbanci dana talaka dana masu mulkin”.
Basuyi ko zama mintun goma ba jirgin da ake tsumayen zai sauka ya sauka ɗin. Sai dai da yake a ɓangaren ɗaya suke na masu jira basu san wainar da ake toyawa ba har matafiyan da suka fito a jirgin suka fara fitowa. Tun suna tsumayen ganin fuskar wanda suka sani ya shigo vip lounge ɗin har suka haƙura. Dan kusan sai da sukai zaman fin mintuna talatin zuwa lokacin har ruwa an kawo musu da lemo, bayan nan kusan wasu mintina uku security ɗin dake ƙofar ta waje ya buɗeta. Duk ƙofar kuwa suka zubama idanu dan a ƙage suke su kam.
A bazata Daddy Imran dake gaba ya bayyana a idanunsu. Kusan a tare duk suka miƙe, idan ka cire Mammah da bata motsa ba ta dai zuba masa idannunta na girma kawai. Yayinda zuciyarta ke wani irin bugawa da bugu mai girman gaske a cikin ƙirjinta. Hakama Nimrah dake kwance a jikinta tana game da wayarta, kasancewar hankalinta na kan game ɗin bata san mike faruwa ba ita kam.
“Oh kona koma ne?”.
Daddy Imran ya faɗa yana ɗan wara idanunsa akan su Ammar dake tsaye kawai sun zuba masa idanu abubuwa na musu yawo a zuciya da ƙwaƙwalwa. Murmurshi suka saki a tare, kafin su ɗaga ƙafafunsu da sukai musu nauyi na rashin dalili su nufesa a jere, zaratan mazajen Mammah kenan guda huɗu, masu kamanni ɗaya, dan su duka huɗu da mahaifinsu suke kama, Dada ne kawai ya ɗakko hasken fatarta amma shima kamaninsa irin nasu ne.
Dai-dai lokacin itama Nimrah ta ɗago saboda zaburar Ruky da uhununta na ambaton Daddy!... Sai dai ta yunƙura zata tashi itama ta tsaya cak, kamar yanda suma Uncle's nasu suka tsaya ɗin. Dan takunsu bai gaza biyar ba suka iso inda Imran ya ke, sai dai kamar jira yake su iso ɗin suna ajiye ƙafafunsu a takun ƙarshe shi kuma ya matsa gefe tamkar mai shirin basu hanyar wucewa, hannunsa ɗaya riƙe dana Ruƙayya, ɗaya kuma ya nuna musu ƙofa. Dai-dai nan ƙofar wajen da suka zubama idanu su duka ta shiga buɗewa, buɗewar data kasance tamkar tare da zukatansu dake rufe ne tsawon shekaru takwas da wata shida....
Ɗasss! Ɗassss! Ɗasss!! Sautin takunsa ya fara bayyana a cikin shirun su mai nauyin gaske, dan a wannan gaɓar ko numfashi mai ƙarfi babu mai yi idan ka cire Imran da fuskarsa ke cike da wani irin murmushi mai nauyi da armashin gaske. Kafin bayyanarsa cikin kwarjini da kamalar masu natsuwa ta wanzu cikin idanunsu. Shi ɗin ne dai, shi ɗin da suke zaman jira tsahon shekaru da hawaye da bugawar zukata a kowace daƙiƙa ta kwanakin da suka shuɗe da abubuwan da bazasu lissafu ba.
Duk da basa ganin ainahin fuskarsa, sannan ba wasu kaya bane na alfarma a jikinsa. Hasalima sanye yake da ƙananun kaya da suka kasance baƙaƙe daga sama har ƙasa. Baƙin wando da riga t-shirt mai gajeren hannu data bayyana murɗaɗen damtsen hannunsa duk da kuwa jikinsa bai gama dawowa ba kamar da, sai dai ya ciko fiye da sanda ya fita a prison. Fuskarsa da norse mask daya ɓoye bakinsa da hanci, sai ƙwayoyin birkitattun idanunsa da ko yana a cikin kwanciyar hankali basa zama tas-tas, daga sama da hula p-cap itama baƙa. Hannunsa ɗaya a aljihu, ɗaya rataye da jacket ɗinsa da itama ta kasance baƙa. Sassanyan ƙamshin turarensa da duk suka sanshi da shi kuwa ya cika wajen...
Kamar yanda suka tsaya cak suna kallonsa haka shima ya tsaya cak yana musu kallo mai matuƙar nauyi da tsawa a zuciya. Dan kuwa Imran ya matuƙar yi masa bazata. Sam bai sanar masa da zuwansu tarbarshi ba, kasancewar dama saukar tasu sauka ce ta sirri kamar yanda ya buƙata. Da wani irin slow motion ya janye idanunsa daga kallonsu ya maida su kan Mammah dake zaune a inda take, sai dai kamar wadda ta suma dan babu inda ke motsi a jikinta sai idanunta dake tsaye a kansa cak... Nimrah kwance a kafaɗarta itama dai ta zuba masa ido ne kamar yanda kowa ke kallon nasa. A bazata idanunsa daya janye slowly daga kan Mammah suka shige cikin nata. Shigewar data saka mummunar faɗuwar gaba riskarta. Dan ji tai tamkar an matse zuciyarta da hannu ne har sai da ta kumburo kamar zata fashe sannan aka saki. Kasa jurewa tayi, a hankali ta fara lumshe idanun nata dake cika da hawaye na rashin dalili. Hakan kuma yay dai-dai da cigaba da takowar Dada inda suke kai tsaye dan burinsa kawai ya iso gaban Mammah...
Karo na biya ya fara motsawa a hankali, yanda ɗakin yay musu shiru tamkar an tsaida duk wani motsi na ƙasar da mutanen cikinta yasa sautin takalmin nasa cigaba da bada sauti kamar ɗazun. Sautin daya cigaba da bugawa da bugun zukatansu har ya ƙarasa inda Mammah da Nimrah suke ya tsaya cak. Kafin a hankali ya tura ƙafarsa ɗaya baya, ya sauke gwiwar ɗayar ƙafar itama a ƙasa tamkar mai shirin bama budurwa zoben baiko. Hannunsa ya kai ya zare p-cap ɗin ya ajiye a ƙasa, ya sake maidawa ya zare norse mask ɗin shima. Duk dai Mammah na kallonsa tamkar sumammiya, dan idannunta ne kawai dake yawo a kansa ke motsawa...
A ɓangaren su Ja'afar da su Aunty Ummi, Lailah, Mimi, Mommy, Shariffa da Biebah kam idan akace maka suma sun suma ɗin ne tamkar Mammah kada ka musa. Dan yanda duk suka kasance a tsaye ƙyam babu motsi babu ƙyafta ido ya isa shaida ga mai kallonsu. Dai-dai yana gama sauke norse mask ɗin cikin tamkar fisgar numfashi Mimi ta furta kalma mai nauyi da girgiza zuciya a karo na farko, kalmar data zama tamkar ta yayyafa musu ruwan sanyi ne daya farkar da su a suman nasu...
“D..a...da!!”.
Sai kawai ta tafi luuuu zata zube ƙasa saboda yanda jikinta ya ɗauki rawa. Da sauri suka zabura kanta dan taro ta, sai dai kuma hankalinsu ya rabu biyu. Dan a dai-dai wannan lokacin itama Mammah da sunan Dadan ya daketa sakamakon fitarsa a bakin Mimi jikinta ya hau rawar, duk da ƙoƙarin da take na riƙe kanta hakan ya gagara. Hannunta ta motsa a hankali tare da kai shi kan fuskar da ta shafa kumatunsa dake ɗauke da kwantaccen gashin saje mai adon farin gashi tsilli-tsilli. Da wani irin gudu hawayen da take riƙewa suka zubo a saman fuskarta, lips ɗinta dake rawa suka motsa a hankali ta furta,
“Muhammad!”.
Sai kawai ta tafi itama luuuuu ɗin kamar Mimi, sai dai ita da alama suna ma tayi. Ƙarar firgita Nimrah ta fasa tana cukuykuye Mammah jikinta na rawa, hakan yasa shi kuma Dada tarosu su biyun duka a jikinsa ya rungume....
Ƙarar Nimrah ce ta kasance tamkar zaburarwa garesu duka. A tare sukai kansu suma. Wata irin runguma Ammar daya fara isowa yay ma Dada tare da fashewa da kuka mai matuƙar dukan zuciya, dan a wannan gaɓar wlhy ya manta da kansa a matsayin namiji. Tamkar yanda Ammar yayi suma su Ma'aruff rungumesan kawai sukai suna hawaye..
A hankali Dada ya lumshe idanunsa da suka juye lokaci guda, cikin wani kalar sanyin jiki da tsinkewar jini ya shiga ƙoƙarin shanye hawayen da yake jin tamkar suna neman ciko masa idanu shima. Da ƙyar Imran daya ƙaraso inda suke da ruwa a hannu ya shiga ɗagasu ɗaya bayan ɗaya. Nimrah dake jikin Dada male-male batare data fahimta ba ya fara kallo, janyewa yay kawai yana murmurshi a zuciyarsa da ƙoƙarin shafama Mammah dake jikinsu su biyun ruwa. Cikin sa'a kuwa ta kawo nannauyan numfashi.......✍️
KIƊA A RUWA 2
52
........“Mammah are alright?”.
Nimrah ta faɗa tana shafa fuskarta ga hawaye na gudu suna ɗiga har kan fuskar Mammah ɗin. Mammah ta buɗe idanu a hankali tana kallonta, sai kuma tai ƙaramin murmushi da kai nata hannun kan fuskar Nimrah ta shafa da jinjina kai. Sake lumshe su tai kafin ta sake buɗewa kai tsaye akan Dada. Shima dai ita yake kallo, cikin wani irin yanayi mai zafi da kamilalliyar fuskarsa ta kasa iya shanyewa. Dan in mai kallonsa bai ƙarya ba ma ƙyallin hawaye idanun nasa keyi. Mammah kam ta kasa jarumtar riƙe nata hawayen tamkar shi, a take ta sake su suka fara kwarara tamkar an buɗe fanfon ruwa. Hannun nata dai data shafa fuskar Nimrah shima takai kan fuskarsa ta sake shafa fuskar a karo na biyu, ɗayan hannun kuma