KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 42

114K to 117K   out of 125.4K words

koda hannu ta taɓa kayan miya sai su yini suna mata zogin yaji shiyyasa ta ƙara tsanar girki.
        Dada bashi da zaɓin daya wuce riƙeta, dan duk wanda ya kalleta yasan a gigice take, kuma dole ka tausaya mata. Gashi iyayen nata duk sun miƙe suma fuska cike da tashin hankali kamar zasu tayata kuka. Ya tabbatar yayi sake zasu iya cewa ma baya ƙaunar ƴar tasu ko ya mata mugunta.
         A nutsensa ya furta, “Ki nutsu”.
    Ina ita ba saurarensa take ba, dan ita tasan mitake ji. Shima ya fahimci hakan, dan haka ya kamata kawai yana komawa zaune a kujerar daya tashi, ita ko da yake tana a jikin nasa sai kawai ta zauna a cinyarsa. A nan ɗin ma Dada bashi da mafita, baiyi magana ba kawai ya hau ƙoƙarin buɗe mata idon, ita kuma ta ƙanƙame masa hannu tana faman tirje-tirjen da kuka da kiran Mammah-Mammah.
      Matsowa Mammah tayi ta kama hannun nata cike da lallashi tana faɗin, “Kinga ya isa nutsu a cire miki. Da ya fita zaki ji zafin ya daina.”
         “To Mammah dan ALLAH ki cire. Wlhy ji nake kamar zan haukace.”
       Bilal ya kawo tissue, riƙe mata hannun da Mammahn tayi yasa Dada samu ya buɗe idon nata. Sai ko ga ƙaton yaji a ciki harda ɗiya. Idon kuwa yayi wata masifar rinewa jazurr kamar garwashin wuta. Tissue ɗin hannun Bilal ya amsa, yana saka mata taji zafin yafi nada, sai kawai ta sake ƙanƙameshi tana son ƙwace kanta. Sai dai riƙon na manya ne, dan haka ya matseta da ƙyau sai da ya cire shi gaba ɗaya.
    Babu wanda baiji tausayinta ba da ganin yajin babba da shi. Ita ko ta kife kanta tana sauke numfashin wahala da sauran azabar da take ji akan ƙirjinsa. Dada da ya san wannan yanayin haɗari zai zama mai girma da shiga cakwakiya sai kawai ya miƙe a hankali da ita a jikin nasa ya nufi doguwar kujera ya kwantar da ita. Yana ɗagowa zai bar wajen suka haɗa ido da su Ma'aruff dake murmushi. Da sauri suka gimtse shi da Ja'afar. Shima sai ya ɗauke idanun nasa cike da basarwa kamar bai gansu ba ya bar falon gaba ɗaya. Sai da suka tabbatar ya gama haurawa staircase ɗin suka fashe da dariyar. Kallonsu Mammah tayi itama, da sauri suka sake gimtsewa.
     Ammar, Bilal da Mu'azz daya dawo yanzu basu fahimci inda dariyar Yaya Ma'aruff da Yaya Ja'afar ta nufa ba sam. Itama Mammah da farko ba fahimta tai ba, sai da taga suna satar kallon upstairs suna ƙus-ƙus sannan ya harbo jirgin su. Kanta kawai ta girgiza tana maida hankalinta ga Mu'azz tace yaje ya ƙarasa dafama Nimrah indomie ɗin taci taje ta kwanta.......

^^^^^^^^^^^^^^^^

           A wannan daren ƙungiyar duhu sukai meeting na sirri. Meeting ɗin da gaba ɗayansa ƙulle-ƙullen masifu ne na tashin hankali ga ƙasa dama shugabanta Janar. Dan abinda yay musu sun tabbatar da babu bashi sai sun hukuntashi. Sai Dada, gaba ɗaya shirinsu a kan Dada kuwa ya ta'allaƙa ne akan yin amfani da Nimrah. Sun fahimci dole su canja taku, takun da zasu haifar da rauni mai raɗaɗi da ƙuna a zuciyar sa. Wannan kuma raɗaɗi da ƙunar ba zasu iya samar da shi ba sai ta hanyar taɓa zuri'arsa. Ta ko ina kuma sun fahimci dole sai da wani na jikinsa zasu iya hakan, musamman da a yanzu tsaro yayi yawa a gidan, dan Mole ya zama mai kawo musu bayanai sosai akan gidan yanzu fiye da Dagger. Hatta haihuwar Shariffa ta yau ɗin nan tazo kunensu, shima Dagger ya sanar musu kiran da Nimrah tai masa da buƙatar su haɗu da tayi sai dai hakan bai faru ba sakamakon rashin fitowar ta. Ta haka ne ma suka sake samun tabbacin Zak-Shadow ɗin ne dai a gida Mole baiyi ƙarya ba.
        Sai da suka gama tsare-tsaren su iya su manyan Sannan aka sake wani sabon meeting da saura members duk a daren dai. Hukuncin da suka yanke da tsarin da suka kammala yi yasa shima Dagger suka buƙaci ganinsa zuwa safiya. Dan yanzu kam aiki ne zai tashi ba wasan yara ba. Sannan zasu bama Mole dama irin ta Dagger, sai dai ba'a kan Nimrah ba. Nimrah Dagger zai cigaba da aiki kanta kamar yanda ya fara tunda ta riga tasan fuskarsa. Canjawa zai saka ta iya zargin wani abu daban tunda sun fahimci tana da wayo............✍️


Idanunsa dake lumshe shima ya buɗe yana sauke ƙaramar ajiyar zuciya, kafin ya ɗagota a hankali zai maidata ya kwantar ta sake ƙanƙamesa cikin ƙunƙunan barci name magagi tace, “Uhmm-uhmm Mammah, ni zan kwanta ana....”
       Batare data ƙarasa ba ta cigaba da barcinta. Wani ɗan murmushi mai fidda sauti cikin ƙirji kawai ya saki. A ransa yace (Trouble maker, idan kin kwanta anan ni kuma twin ɗinki ta farka ta ganni fa?). A zahiri kam kwantar da ita ɗin yayi a hankali, sannan ya haska mata fuska da waya. Idon da gefensa har ya kumbura, yakai hannu ya ɗan shafa wajen kaɗan, sai kuma ya ɗan furzar da iska yana zame hannunsa data riƙe gam a ƙirjinta. Sake ƙoƙarin cafkowa tayi, kawai ya saka mata bargo a ciki. Sai ko ta damƙe tana juya kwanciya ta matse bargon har abin yaso bashi dariya ma, ya dai gimtse ya tashi abinsa da ledar maganin ya fita, dan yasan idan ya bari da safe sai sunta shelar neman waya ajiye a gidan, ba man kai ne da su ba.

               °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
       °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

           Washe gari gidan Mammah ya cika da ƴan barka. Musamman sashen su Lailah. Danginsu sai zuwa sukeyi. Sai dai duk wanda ya shigo sai yazo ya gaida Mammah. Kuma duk wanda zai shigo securitys ɗin nan sai sun masa ƙwaƙwaf.
      Yanayin da Nimrah ta tashi akan idonta ya taƙaita al'amarin tana nanuƙe da Mammah. Ruƙayya kam duk ta damu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan saita ce, “Ninah ba zafi?”.
     Tun Nimrah nace mata eh, harta koma tsokanarta idan ta tambaya sai tace akwai, sai taga ta damu sai ta saka dariya. Mu'azz ya tasa su gaba da tsokana sai da Mammah ta Koresa a falon. Hakama Afeef ko sau ɗaya bai nuna tausayin Nimrah ba balle Hanoon. Biebah kam har ɗan gasa mata idon tayi da ruwan zafi dan fuskarta ya ɗanyi fushi, a haka ma dan Dada ya saka mata magani ne ai da ba'a san yanda zata tashi ba.
     Har kusan sha biyu Dada bai sakko ba. Dan haka Mammah tace Nimrah dake zaune Ruky tayi filo da ƙafarta tana barci ta tashi ta kai masa abincin breakfast. Saboda ta kirashi a waya yace aiki yake shiyyasa. Kuma yaga yau gidan nasu hayaniya tayi yawa. Mammah tace shike nan bari tasa a kawo masa. Shine ta yanke wayar tace Nimrah ɗin ta tashi.
        Cike da shagwaɓa Nimrah ta ce, “Mammah banda lafiya fa”.
            “Haba auta, to wa kike son ya kai? Bakiga Ruƙayya barci take ba? Mamanku kuma tana aiki a kitchen”.
    Caraf Hanoon ta ce, “Mammah kawo naje”.
    Kafin ma Mammah ta bata amsa Nimrah data watsa mata harara ta miƙe. Ta sake watsama Hanoon kallon banza tana nufar tray ɗin da kulu ta kawo da faɗin, “Dama mutum ya kama kanshi. Mu uban mu bazai auri finga-fiyau ba. Mace sai kace taɓaryar gwari ba sama ba ƙasa.” dariya kamar zata kashe Kulu, da ƙyar ta iya matsawa ta shige kitchen. Hanoon kam da kallo tabi Nimrah dan ba komai ta gama ganewa ba. Mammah ta girgiza kai tana murmushi, a zuciyarta addu'a take ALLAH ya shirya mata Nimrah da Ruƙayya ita kam. Yara baƙar magana a bakinsu kamar dangin mahauta. Muhammad ne yay tashen baƙar magana yana yaro, ba yawan surutu amma idan ya yaɓa maka mai zafi kamar ka mutu. To ga magada nan ya samu har suna neman zartashi.
        Koda Nimrah tazo kofar ɗakin sai abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata. Bana tattaunawarta kawai da shi ba, harda na abinda ta gani, har yanzu take neman mafitar fita amma ta gagara samu. Tafi minti ɗaya a tsaye kafin tai sallama dan babu daman knocking hannunta da tray. Sarai ya jita amma yaƙi tasowa ya buɗe mata balle amsawa. Yau ƴan sarautar ne aka. Itama jin shiru babu motsin kowa tayi kuma har sau kusan huɗu sai kawai ta rungume tray ɗin da hannu ɗaya, cikin dabara ta saka ɗayan ta buɗe. Koda taci karo da shi a zaune sai da taji shock. Ta ɗanyi diri-diri sai kuma ta nutsu jin tana neman yin ɓari.
      Yi yay kamar baima jita ba. Nan ko ya gama kalleta ta gefen ido. Amma sai ka rantse hankalin nasa akan rubuce-rubucen da yake yi yake. Ƙananan kaya ne a jikinsa, yanda rigar ya kamashi sosai gashi ƙaramin hannu yasa kallo ɗaya datai masa bata sake gigin yin na biyu ba.
Sai kuma ta tafi tunani mara dalili daya sakata shagala a wajen ta kasa ƙarasawa ta ajiye abincin..
         “Idan kikai ɓarin abincin nan sai kin cinye shi”.
     A bazata furicinsa ya shiga kunnenta. Da sauri ta dawo hayyacinta. Saman table ɗin gaban sofa taje ta ajiye tray ɗin. Dan shi yana a study chair ne zaune. Desktop ɗin sa a kunne gefe yana rubuce-rubuce. Ta bayansa kaɗan ta risina ta ce, “Dada ina kwana”.
        “Haɗa min abincin”.
    Ya faɗa batare daya amsa gaisuwarta ba. Baki ta zumɓura dan taji haushin ƙin amsa matan da yayi.........✍️

75


..........Harta gama zuba komai dai-dai misali ta zuba shayin lemon tsami da na'a-na'a dake ta ƙamshi bakinta na a sama. Inda yake ta nufo, ya matsar da takardunsa kafin ta kife masa abincin a kansu. Shiru bata ajiye ba, hakan ya sashi ɗagowa dole ya kalleta. Suna haɗa ido ta risinar da nata, shima sai ya kauda kansa ya cigaba da aikinsa. Kusan sakan biyar sannan ya furta,
        “Fishin mi kike yi?”.
    Bakin ta ƙara turawa taƙi magana.
Yay ɗan jimm na mamaki, sai kuma ya ɗago ya sake kallonta.
       “Abincin naku ne baƙya son naci?”.
      Yanzu ma kai ta girgiza.
  Ya dai sake daurewa ya ce, “Idon ne?”.
       Sai kawai ta sakar masa kuka. Mamakin duniya ya gama mamaye shi, kaji yarinya fa dan ALLAH kamar wata mai aljanu. Bai sake magana ba ya zuba mata idanu kawai. Ganin kukan ma daɗi yake mata sai ya amshi abincinsa da kansa ya ajiye. Kafin ya furta, “Tunda bazaki  yi magana ba wuce ki tafi”.
         Gurin tai ƙoƙarin bari tana sake fashewa da kukan da ita kanta bata san dalilin yinsa ba, kawai jitai tana son yi masa kukan ko a cikin drama ɗinta ne, duk da da gaske taji haushin bai amsa gaisuwar datai masa ba. Jiyay bazai iya barinta ta tafi tana kukan ba, ko wani abu akai mata. Sai ya riƙo hannunta ya dawo da ita inda take da. Bai saki mata hannun ba ya cigaba da kallonta har kusan mintuna biyu.
          “Kina son na zane ki?”.
    Kanta ta girgiza masa.
Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Bana son wannan kukan. Faɗa min mike damun ki? Wani ne ya miki wani abu?”.
     Hawayen ta fara sharewa da faɗin, “A'a. Kai ne”.
       “Kiddo ni kuma?”.
    Kanta ta jinjina tana tura baki.
“Ikon rabbu, to mi nayi?”.
“Na gaishe ka baka amsa ba. Sai naga kamar kana fushi da ni”.
         Sagale kawai yay yana kallon ta, mamakin duniya ya gama mamaye shi. A ransa yace (Ƙuruci dangin hauka. Kaji yarinya fa) a fili kam baima san ya furta, “Ni kuma yau a hannun ƴan sari na tashi kenan!. To sake gaisheni sai na amsa ba shike nan ba”.
       “To ba fushi kake ba?”.
    Tai maganar cikin yanayin ɗan waro masa idanu. Sai kawai ya girgiza mata kansa yana ƙoƙarin danne murmushin dake neman bayyana a tsukakkiyar fuskarsa. Ajiyar zuciya kuwa ta saki, sannan ta sake gaishe shi. Ɓoyayyar ajiyar zuciya shima ya saki ya amsa yanda take son, harda ɗorawa da, “Yaya idon ki?”.
         “Da sauƙi, amma yana zafi kaɗan”.
      “Tunda kina kukan da babu dalili ba dole yay zafi ba. Ɗauka min leda gashi can a mirror na sa miki magani”.
        Ya kai ƙarshen maganar yana sakar mata hannu. Inda ya aiketan ta tafi, ya bita da kallo yana girgiza kai kawai. Tabbas yana da son yara, bai sani ba kodan baida su. Duk da Nimrah da Ruƙayya sun girma a yanzu, ganinsu yake ƴan 7years ɗin nan daya tafi ya bari... Dawowarta da ledar ya saka tunaninsa katsewa. Amsa yay ya buɗe, ya ciro maganin sannan ya kalleta, kamar ta fahimci mi yake nufi ta tsugunna kawai tana mai dafa hannun kujerar. Kanta ya dafa da hannu ɗaya, tare da buɗe idon sosai da babban yatsansa ya zuba mata maganin.....
         “Wayyo Dada zafiiiiii”.
     “Shiiiii!”.
  Ya faɗa yana riƙe da kan nata, dan ya hanata ɗagowa kar maganin ya fita. Sai da ya tabbatar ya shiga sannan ya barta. Har zata miƙe ya ce, “Ɗauka wannan abinci ko canja ya huce. Kije ki kira min Ruƙayya itama”.
       Cike da tsantseni ta amsa, dan duk wannan biye matan da yake shakkarsa na nan damar a zuciyarta. Musamman da fuskar na tsukenta ne babu ko murmurshi. Sai dai son cikar burinta da shirinta a kansa yasa take danne zuciyarta da bama kanta ƙwarin gwiwa. Alhamdullahi kuma taga tasirin hanyar data biyo masa. Bayan ta ajiye wani sabon abincin dan ALLAH yaso ba plate ɗaya Kulu ta saka ba, haka ma kofi. Tana kammalawa ta fita a ɗakin.
     A ƙasan ransa ya furta (Kiddo kina bani ciwon kai)...
     Babu jimawa suka dawo ita da Ruƙayyan, dan ta iske ta tashi barcin. Yanda yay ma Nimrah tambayoyi jiya cikin wayo da dabara akan makarantarsu haka ya dinga musu a tare yau, suka dinga bashi labarai kala-kala, har kansa ya fara ciwo sai da ya gaji ya korosu.
Oho ko'a jikinsu, dan daɗi ma suka dinga ji Dada yayi hira da su, koda suka dawo wajen Mammah sai suka dinga yi ma Mu'azz wulaƙanci. Har sai da yaji haushi ya haura saman yace shima ya tafi ɗakin Dadan. Mammah dai murmurshi take kawai da jinjina shiriritarsu. Sauran Uncles ɗin nasu ma duk wanda ya shigo sai an bashi labari yau sunyi hira da Dada. Congratulations suka dinga ce musu suna dariya..

      Wannan hira ta bama Dada haske sosai akan makarantar su Ruky. Koda suka tattauna da Daddy Imran yayi mamakin wayon yaran. Dan abune ma da shi kam bai taɓa kawoma ransa ba...

))))★(((((★))))))★((((

           A bangaren Hajiya Hasiba kamar yanda First Lady tace tayi hakan tayi, ta buɗe su Nabeeha. Ta kira likitanta ya fara duba su saboda damuwar da suka sakama kansu duk sun rame. Ya tabbatar mata da basa tare da wata matsala sai damuwar kawai. Amma ya basu shawarwari sosai da suka fahimcesa. Bayan tafiyarsa itama ta zauna da su. Ta nuna musu ta haƙura, amma su kiyaye gaba. Sannan tace Nabeeha ta fara shirin komawa gidan mijinta.
      Ba Nabeeha ba hatta Ismat ta shiga matsanancin mamaki. Dan har sai da ta furta, “Momy da gaske kike yi?”.
       “Oh na saba miki ƙarya ne Ismat?”.
    “A'a Momy kiyi haƙuri. Wlhy mamaki ne kawai abin ya bani”.
      “Humm to sai ya daina baki. Kawai shawara likitan nan ya bani akan na barta ta koma kada ta kamu da wani ciwo. Dan haka na amince ta koma. Kema kuma na baki nan da wata uku ki kawo mijin aure, idan ba haka ba ni inada wanda zan bama ke. Masu gyaran jiki zasu zo gobe idan ALLAH ya kaimu sai ki shirya”.
    Tai maganar ƙarshe tana kallon Nabeeha. Kai kawai Nabeeha ta jinjina mata, dan al'amarin Momyn tasu a wannan gaɓar ya razanata fiye da ko yaushe. Tana sonta sosai, amma maganar gaskiya ta fara jin tsoron ta mai girma.
        Tun daga ranar suka fara ganin canjin abinci masu ƙyau, saɓanin wanda ake basu a kwanakin nan da suke a kulle. Sannan ta dawo musu da wayoyinsu. An kuma dawo da network ɗin gidan. Sukan fita falo su zauna, har ma tayi hira da su. Ƴar Kamaru tazo ta fara aikinta na gyaran jiki wa Nabeeha. Dan maƙudan kuɗaɗe First Lady ta biya kamar bata san ciwon kuɗi ba. Koda yake bata san ciwon nasu ba tunda an tara musu, ta yanda ko jikokinsu bazasu yi talauci ba idan ba wata jarabawar UBANGIJI ba kuma....

    <•••><••••><••••><•••>

         A lokacin da can ake gyara Nabeeha anan Dada da Imran sun matuƙar maida hankali wajen haɗa runduna ne akan aikin da zasu fara. Dan kamar yanda shugaban ƙasa ya bama Dada damar samar da masu taya shi aiki cikin kowanne jami'an tsaro dama farar hula haka yaketa tattarasu. Sai dai fa dukansu kowa bai san da zama ɗan uwansa ba. Hasali ma su Dabo aka saka suke yi basu san waye shugaban tawagar ba.
       Har yanzu suma su Dabo basu ga Dada da idanunsu ba, sai dai su duka yayi waya da su ta hannun Imran. Duk abinda zasuyi Faro ke basu umarni. Sai yau ne ma yake tunanin zama da su. Dan akwai tsofaffin bayanan da yake so a hannunsu. Sannan yana son jin bayani akan duk wanda suka ɗakko a cikin tafiyar dan tantance ko zai iya aiki da shi ko bazai iya ba.
          Kwanaki biyar kenan da haihuwar Shariffa, tunda kuma akai haihuwar kullum su Aunty Ummi na gidan nan. Hakama ɓangaren dangin su

39 / 42