KIDA A RUWA BOOK2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 42

15K to 18K   out of 125.4K words

da dawowarka cikinmu”.
    Hawaye Baba ya share, “Na sani ku mutanen arziƙi ne masu tarin alkairi, har abada kuma bazan manta da tarayyata da ku ba. Amma mizai hana ku cigaba da kai yaran makaranta da kanku?”.
        “Baba bazai yiwu ba, kasan yanda uziriri sukai mana yawa dai, idan muka ce mune zamu kaisu za'aita samun matsala. Ga boko ga islamiyya, ga cefanen gida kai Mammah anguwa da iyalanmu”.
        Baba yay shiru zuciyarsa na kai-kawo, dan yasan bazasu fahimci mi yake nufi ba daman kai tsaye, shi kuma tsoro bazai barshi fitowa ya buɗe musu komai ba kai tsaye, sai kawai yace to su bashi lokaci zai kira a waya. Cikin gamsuwa sukai musu sallama suka tafi. Cikin damuwa matarsa ta ce, “Wai miyasa kake ta musu kwana-kwana malam? Mutanen nan mutanen kirki ne, banyi zaton zasu zo da damuwa kanada damar musu maganinta ka kasa ba”.
       “Ba kasawa nai ba Tabawa, kawai ina duba al'amarin ne dai kawai, kin san yanda rayuwa ta lalace yanzu ba kowa ke raɓarka da ƙyaƙyƙyawar zuciya ba. Ko ni ɗin ma alkairin su da hukuncin UBANGIJI ne ya sauya ni daga dalilin raɓarsu”.
    Cikin rashin fahimta ta ce, “Kamar ya? Ban gane ba malam!”.
    Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba ya barta da wasi-wasi. Awa ɗaya ba'ayi da tafiyar su Yaya Ma'aruff ba Baba Driver yayi baƙo. Kasancewar matarsa tasan mutum ya saba zuwa wajensa bata kawo komai a ranta ba ta shiga ciki gida ayyukanta ta basu waje. Dan yana jiyyar a ɗakin soro ne...
             “Rabe! Kana ganin taurin kanka zai cigaba da baka nasara ko? Halin da kake ciki bai zame maka aya ba kenan?”.
      Murmurshi Baba Driver yayi mai ciwo, idanunsa cike da ƙwalla ya ce, “Ba darasi ne ban ɗauka ba Ari, ina tausayin bayin ALLAHn nan ne. Wlhy mutanen nan munanen kirki ne su da mahaifiyarsu.
Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......”
        “Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka”...
      Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba.....

★>><<<<★>>>><<★
        ★DUBAI★

   Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, “Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?”.
         Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️


12

.........“Ismat zan koma ƙasata, wlhy na gaji da wannan rayuwar, bazan iya ɗaukar huɗubar Momy ba, gara na koma gidan mijina nai zaman jiran dawowarsa ko nan da shekara hamsin ne ma ba ashirin da biyar ba”.
       Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ismat ta sauke, dan koba komai itama an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi dama. Ta kama hannun Nabeeha suka koma bakin makeken gadon ɗakin da yaji shinfiɗu na alfarma, dan duk da haɗuwar gidan da komai na cikinsa ɗakinta na musamman ne. Gyara irin na ƴar gata Adeel yasa akai mata. Hannayenta duka a cikin na Ismat ta ce, “Aunty wlhy koni ina bayanki ki koma gidanki, dan ita Momy idannunta sun rufe da son kuɗi bata duba abinda muke so koya dace damu. Ita kawai tafi kallon abinda zata samu. Gamu dai a cikin ƙaton gida a kuma ƙasa irin ta Dubai da kowa ke buƙatar yazo, amma wlhy Aunty Jiddah ta fimu kwanciyar hankali, tana rayuwar auren ta ga yaranta abin sha'awa, shiyyasa wlhy nima na fara ji a raina zanyi na nata na koma gidan Abba na bashi haƙuri na samu miji nayi aure. Dan in har muka cigaba da rayuwa da Momy anan wataran sai mun lalace, dan waɗan nan shaggun mutanen babu abinda suka iya sai son mata kamar su babu matan a cikin nasu ƙabilar”.
       “Ismat wlhy ni duk bama wannan ba, babban abinda ke bani mamaki da Momy itafa kawai na kashe aurena saboda wannan mutum yace mata aurena yake son yi, haba miyasa ba zatai tunanin daya dace ba, dukiya irin ta mutumin nan, da nasaba ta gidan mulki, mulkin ma mai ƙarfin gaske ne zai zauna wani auren baƙar fata ƴar Africa saboda rainin hankali da ɗaukar mutane jakai. Kiga yanda suke wulaƙanta matan African fa kamar wasu dabbobi dan ko bayi na baya sun fi matan da ake kawo musu suna iskanci da su a yanzu mutunci da daraja. Wlhy Ismat ina son mijina, duk da ina jin takaicin auren shegiyar yarinyar nan har yanzu a zuciyata....”
       “Na sani Aunty, ki share wani batun yarinya kawai muyi tafiyar mu, dan uwarta mune zamu miki maganinta, da ƙafarta zata bar gidan batare da kowa ma ya sani ba ta koma ƙauyen su, idan tace ita ƴar hau ce mu ƴan hau-hau ne to”.
     Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Nabeeha ta saki, tana mai jin nutsuwa da gamsuwa da zancen autar tasu. A gefe zuciyarta na jin matsanancin kewar mijinta da buƙatar son kasancewa da shi da akoda yaushe take yaƙi da kanta a kai, sauƙi-sauƙin ma da take samu kullum cikin mafarkinsa da yanda yake tafiyar da ita a shimfiɗa take, shiyyasa take samun sassauci da jinsa kamar a kusa da ita har yanzu.....

        Da baya-baya Hajiya Hasiba tabar bakin ƙofar ranta a matuƙar ɓace da tattaunawar yaran nata. Ƙayataccen ɗakinta ta shiga, ta zauna a bakin makeken nata gadon hannunta dafe da kanta. Jitake kan nata na wani mugun sara mata, sai dai abinda ke mata kai-kawo na takaicin yaran nata na son danne ciwon. Lallai lokaci yayi da zata nunama su Nabeeha ita ba sankaran uwa bace sha-sha-sha kamar yanda suke tunani. Taya zata bari ma Nasiru yaci nasara a kanta, bayan ya rabata da Jiddah ya rabata da Nabeeha da Ismat da suka rage mata kuma. Ta jima da fahimtar soyayyar da Ismat kema Ja'afar, sai dai bata damu ba ganin yanda shi Ja'afar ɗin yaƙi kulawa, amma yanzu ta fahimci Ismat na zuga Nabeeha ne su koma gidan ubansu saboda son da take ma Ja'afar, kenan da sunje sun kwantar ma da ubansu kai itama sai ya aura mata shi, shekenan ita kuma A'isha ta haifama ƴaƴa ko? To kuwa zasuci ubansu.
      Da wannan tunanin tai ƙwafa, tare da miƙewa zuwa gaban wadrobe ɗinta, ta ɗibo duk passport ɗinsu dake wurinta, cire na Nabeeha da Ismat tayi ta canja musu waje, daga haka ta hau shirin fita. Dan tana buƙatar ganawa da Adeel yanzu nan basai gobe ba.....

      
 §§§§§§§§§§§§§§§§
       ★EGYPT ★
      
             “Mammah muje ki huta yau kam kin gaji fiye da kullum. Ga su Yaya Ma'aruff nata kira nasan burunsu kawai suji yanda results ɗin suke ne. Aunty Ummi ma naga ta kira video call ta WhatsApp”.
Received      Murmushi Mammah tayi, cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Ammar yarana duk sunyi kewata ne, nima ina tsananin jin kewarsu. Dan haka ni kam ba sai sati biyun nan ya cika ba zuwa jibi tunda sunce babu wata damuwa suna bamu maganin nan kawai mu koma gida”.
         “Duk yanda kike so haka za'ai Mammah”. Yay maganar yana ɗan rungumota ta gefe, dama kuma suna tafiyar ne hannunta riƙe a nashi. A yanda ya ɗan rungumetan yana dariya itama yana murmurshi da kai masa rankwashi a kai yasa basa kallon gabansu balle mai tahowa. Karaf kuwa sukaci karo da wani abun da ya saka Mammah faɗin, “Subahanallahi”. Shima sai Ammar ɗin ya sake ta yana waiwayawa da ambaton, “Ya salam”. A dai-dai lokacin shima wanda sukai karon ya ambaci, “Subahanallahi” ɗin yana kaiwa duƙe da son riƙo takardun hannunsa da suka tarwatse a ƙasa. Cikin sauri Ammar ya bishi shima yana ƙoƙarin taimaka masa da sake faɗin, “I'm sorry sir”.
       Fuskar mutum da murmurshi ya ce, “Karka damu ɗana, nima harda nawa laifin hankalina nakan takardun ne shiyysa ban lura da tahowarku ba. Mama kiyi haƙuri kem......”
    Ya kasa ƙarasawa saboda dai-dai ya ɗago ne zai kalla inda Mammah ɗin take sukai ido biyu. Dan itama ta miƙo masa takardar data ɗakko ne datai gefe zatai magana a lokacin, sai ta dakata cak tana kallonsa. Ko shekara dubu tayi bazata manta wannan fuskar ba a duniyarta, balle shekarun da basu wuce talatin ba. Jin sunyi shiru Ammar daya gama tattarowa shima ya juyo yana kallon su, Mammah ya fara kallo datai tsaye ƙyam baki buɗe tana kallon mutum, da sauri ya maida kallonsa kansa shima. Ai da sauri ya wani ja baya yana waro idanu waje da faɗin, “Ya rabbi! Mammah waye shi?”.
      Mammah da gaba ɗaya kanta yay wani dimmm ta gagara cewa komai, sai hannunta dake ƴar rawa har sai da Ammar ya matso ya riƙota jikinsa, sai dai har lokacin idanun nasa akan mutumin da alamu ya nuna shima dai yayi sumar tsugunne ne......
       
>>✿<<>>✿<<>>✿<<
       
           “Assalamu alaikum”.
    Aka kwaɗa sallama daga bakin ƙofar falon bayan anyi knocking har sau biyu. Ƙaramin tsaki Mu'azz dake zaune shi kaɗai a falon yana cin abinci yaja, ya tsani tashi yana cin abinci, dan yana tashin shike nan abincin ya fita a kansa kuma. Hanyar kitchen ya kalla inda yake jiyo surutun Nimrah da dariyar Biebah. Sai kawai ya ɗaga murya ya ce, “Ninah!”.
       Daga can ta ce, “Kai Yaya Mu'azz miye kuma dan ALLAH? Bana kawo maka harda ruwa ba”.
          “To uwar son jiki, dalla fito kiga waye ana knocking ne”.
      Baki a sama ta fito, tana sanye cikin shirt da riga na lass milk da furanni coffee. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga ƴammatan zamani masu shegen iyayi da rawar kai. Harta nufi ƙofa ya ce, “Haka zaki fita ba hijjab?”. Baki ta ƙara turawa gaba, ta dawo ta ɗauka hijjab da sukan ajiye a falon saboda irin haka, dan Mammah ta saba musu sakawa musamman idan akai baƙon ido ko suka saka ƙananun kaya, wani lokacin ma sai taga kamar anfi takura mata da sakawa fiye da Ruky da Aunty Biebah. Sai da ta saka ta zura hannayensa sannan ta nufi ƙofar da aka sake bugawar, sallamar maigadi ta amsa tana buɗe ƙofar. Ya ɗan ja baya yana gaisheta.
          “Baba ni dai ka daina rissina min dan ALLAH. Ina wuni?”.
    Murmurshi maigadin yayi da faɗin, “Ai girmanki ne Hajiya. Dama baƙone yazo yace kuma sabon driver ne Malam Buba tsohon Driver ya aikosa”.
     Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Okay to bari na sanarma Yaya Mu'azz, dan su Uncle's duk basa nan. Ammie da Ummie ma sun tafi gidan Mom (Aunty Mimi suke kira Mom) data haihu ɗazun”.
       Fuska ɗauke da murmushi ya ce, “ALLAH sarki ALLAH ya raya, ya albarkaci abinda aka samu”.
     “Amin ya rabbi”.
Ta faɗa tana rufe ƙofar ta juya ciki.
“Yaya wai sabon driver ne, kuma Baba Driver ya turoshi”.
     Ɗagowa Mu'azz yay yana kallonta, sai kuma ya maida kansa ga television yana faɗin, “Oh to sannunsa da zuwa. ALLAH ya iyakance min jigilarku kullum kuna damuna da surutun ku da fitina. Ki haɗa abinci ki kai masa dan abinci nake ci sai na kammala na fita mu gaisa”.
Received          Sai da ta cika baki da iska cikin ƙunƙuni ta nufi kitchen tana faɗin, “Ni wlhy yau ƙafafuna duk ciwo suke, dan anga Mammah bata nan sai wahala ake bani, yau tunda muka dawo school ban huta ba komai ni....”
     Fiiiffgg! Filon kukera da Mu'azz ya jiho ya sameta a baya. Tako dage ta ƙwalla ƙarar data saka Biebah fitowa daga kitchen da gudu tana tambayar lafiya da riƙo Nimrah ɗin. Kai Mu'azz ya girgiza cike da takaici yana nuna fillon daya jefeta da shi.
       “Small Mom fillo fa kawai na jefa mata dan tana min ƙunƙuni shine take wannan ihun. Wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH. Wai uwar wa ma ya hanaki bin su Ammie ne kamar yanda Ruƙayya tayi?”.
        “ALLAH sai na gayaka da Uncle, kuma ai dai naji zafi. Tunda na dawo kaketa sani aiki, na maka gyaran ɗaki, kace na maka ɗan wake, duk baka gani ba sai da ka ci zalina”.
     “Oh gori kike min saboda kin min gyaran ɗaki da ɗan wake? Lallai ma Ninah ni ko”.
    Kai Biebah ta girgiza da jan ƙaramin tsaki ta koma ciki tana faɗin, “Kudai bazaku taɓa canjawa ba ALLAH ya shirye ku. Ba sai ku cinye kanku ba jarababbu. Wlhy na ƙagara Mammah ta dawo gidan dan kun isheni”..........✍️
    
15

........Shi ma'abocin ibada ne da ƙoƙarin ganin ya kiyaye dokokin UBANGIJI da kusantuwa da shi a lokacin da yake rayuwa kamar kowa. A yanzu daya ɓuya bisa faifan ƙaddararsa da jarabawa da makircin masu makirci hakan bai sauya komai ba. Sai himma da dagiya da hakan ya ƙara masa wajen sake kaɗaice UBANGIJI da bauta. Halin da yake ciki bai taɓa sakawa yaji kasawace ko tauyewa daga UBANGIJIN SA ba. Bai kuma taɓa jin nasara ce ga azzalumai ba. Bai taɓa mantawa da ƙasar da talakawan ƙasar ba. Yanda yakema kansa addu'a da zuri'arsa haka yake addu'a ga ƙasa baki ɗaya.
     Tabbas a siffa ta jikin ƙarfi da ALLAH ya bashi zuwa yanzu ya risina, sakamakon canjawar tsarin abincinsa zuwa zaɓin wanda ake ciyar da shi a yanzu. Shiyyasa ya zaɓi ɗaukar matakin yin azumi yau, gobe ya huta, azumi ibada ce mai girma, sannan kariya ce daga jarabawar ɗan adamtaka ta lafiya da halittun jiki da UBANGIJI ya ni'imata mu da su musamman akan abokan rayuwa. Nauyin jiki da raunanuwar ƙarfi bai sa ya gaza wajen ƙoƙarin cigaba da ƙarfafa ƙashi da tsoka da sauran ƙarfin daya rage masa ba, dan a cikin wannan nan dai tsukun ɗakin da yake ciki yakan gudanar da ibadarsa ya kuma motsa jiki da salo-salo irin nashi. Rashin ƙarfafa damuwa a zuciya, ya bashi kariya daga cututtukan zamani irin su hawan jini balle ciwon zuciyar da maƙiya ke fatar masa a kowane motsinsu. Ya riga ya amince UBANGIJI shine mai komai da kowa, idan kunga alkairi daga gareshi ne, saɓanin hakan daga shaiɗan ne ko halayenku ko jarabawar da zata sake ɗaukaka darajar ku zuwa wani mataki na duniya ko lahira. Yayi imani da hakan shiyyasa damuwa ta kasance abu na ƙarshe da zai iya cewa yana yi. A duk sanda ya tuna da ahalinsa musamman jajirtacciyar uwa irin Mammah, yakan mata addu'a da fatan samun nutsuwar zuciya daga shiga damuwar halin da yake a ciki. Hakama ƴan uwansa da suke masa kallon uban da matarsa daya tabbatar soyayyarsa mai ƙarfi ce a zuciyarta. Hatta ƴar amanarsa tana nan zaune daram a zuciyarsa, yana kuma mata addu'a da fatan rayuwa mai nasarori a yau da gobenta, sai dai daga ita har Nabeeha yana jiran wani lokaci ne da zai sawwaƙe musu suje suma su sake gina sabuwar rayuwar su.
       Bai yanke hukuncin fita a wannan wajen ba, dan bashi da wani tabbacin fitar. Sai dai yana fatan aikin daya ɓuya domin yinsa da hana Imran shiga cikin tarnaƙin su tabbata. Dan in har ALLAH ya bashi tsohon rayuwa a kurkukun nan, akwai matsayin da Imran zai kai a gidan soji da zai sa babu wanda ya isa hanashi zuwa ziyartarsa a-kai-a-kai. Idan kuma har UBANGIJI ya bashi damar cika shekarun da suka ɗiba masan ya tabbatar lokacin da zai fita koda bashi da ƙarfin jiki dana aiki, yana da zuciyar bin waɗan can azzaluman ɗaya bayan ɗaya ya hukunta su da hannunsa. Balle ma ko a yanzu ya gama shirya in har yay wasu shekaru a wajen nan sai ya nema hanyar dinga fita yana aiki yana dawowa koda a ƙarshe zai bayyana kansa a ƙarasa yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai koma kashe shi kai tsaye....
       Motsin buɗe ƙofar da akai ya saka tunaninsa katsewa, dan yana duk wannan tunanin ne tare da push-up daya sabama kansa yi sama da ɗaruruwa a kowane rana koda yana azumi. Dan haka har yanzu jikinsa a bubbuɗe yake sai dai raguwar ginanniyar tsoka da bata samun sinadarin da take buƙata kamar baya. Daga yanda yake push-up ɗin kawai ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla yaran sojin guda biyu ya janye yana cigaba da abinsa.
     Suma sake nutsuwa duk sukayi, dan su sun san badan zaki na keji ba basu isa ziyartar ko gefen dajin da yake farauta ba. A

6 / 42